Showing 159001 words to 162000 words out of 304903 words

Chapter 54 - FULANI COMPLETE

ba, sai dan haka ka rubuta zai same ni, haka ka rubuta rayuwata zata kasance, Allah ya dubi ka tallafi rayuwata ka zame min gata, Allah wannan zabin da mahaifina yai min bana so kuma ka sani, amman All

ah ina rokonka idan wannan hadin alheri Allah ka bani ikon bi musu biyayya ka bani ikon dauka kuma ka bani ikon juriya, idan kuma ba alheri ba ne Allah ka musanya min ka canja min kuma karka saka matsalar ta taso daga gareni, Ya Alimu ya Azizu ga gatan mar

ar gata, ya gatan mai gata, ya Ubangijin sammai da kassai....”

Haka ta cigaba da yabon Allah tana fada masa damuwarta, daga karshe ta cika da fatiha ta rufe da salatin Annabi, sannan ta tashi ta koma ciki, tana kwantawa sai ta ji ta samu sa'ida da sakew

ar zuciya sabanin farkon daren da tunani da kuka ya ki barinta tai bachi. Bata farka ba sai da asuba, ta farka da nauyin zuciya na damuwa da kukan da ta sha kamin ta kwanta domin idonta har ya soma kumbura, sai dai ta nemi bacin ran ta rasa, tana jin bata

son mutumem amman bata jin kunci da damuwa kamar na jiya abun ya mata sauki sosai.

Bayan ta gama sallah tai azkar dinta na safe data saba sannan ta dauko qur'ane ta karanta sai da rana ta fara dan bullowa sannan ta rufe qu'anen ta dauko maganinta ta saka

a kunne ta saka kada, sannan ta maida ta aje ta fito harabar gidan tana gaishe da Tumba.

“Lafiya kalau”

Ba da wani karfi ta amsa mata ba, amman hakan be hana ta ji ba duk kuwa da kasancewar ta saka kada a kunne. Lumshe ido tai ta bude tana jin wani

irin sanyi a ranta, sannan ta mike tsaye ta nufi inda Babanta yake zaune rike da redio asuwaki a bakinsa ta durkusa har kasa ta gaishe shi.

“Baba ina kwana?”

“Lafiya kalau, Tumba ta fada miki sako jiya ko?”

“Eh ta fada min”

“To yayi kyau bana

son na sake ganinki da wani a waje, kuma bana son ki samu matsala da mutumen nan”

“To Baba”

Ta amsa sannan ya daga mata hannu ta mike tsaye ta juyo gurin iya tana kallon dumamen tuwon da take yankawa.

“Zan tafi gurin aiki”

“To Allah ya kiyaye

, kin san dai Babanki ya hana a baki abinci da sai na zuba miki ko da sanyi ki ci”

“Aa a can nake karyawa ai”

Tumba ta juyo ta kalleta da kyau.

“To ki ce kayan dadi suke baki, shiyasa na ga kin yi kyau jiki sai fitowa yake, kwai kike ci ko?”

F

almata dai ta yi shiru sai kallon yatsun hannunta take.

“Wata dai ya kusa yau sauran kwana biyar kar a baki kudin nan ki taba su, dan na san halinki da keta”

“Ba zan taba ba Umma”

“To Allah ya tsare hanya”

“Ameen”

Ta amsa sannan ta sa kai t

a fice daga cikin, fitar ke da wuya Naja ta dawo kusa da Tumba ta risina tana mata magana murya kasa kasa dan kar Baba ta ji.

“Umma da ni aka maida aikin nan, ji fa har zuwa daukarta, kuma Allah kadai ya san dadin da take sha a can”

“Wuyar da take s

ha dai, wani dadi zata sha? Ke baki masu kudin nan ba? Ai ko kallo bata ishesu ba, kuma rainon yara an fada miki sauki ne da shi? Ita ce kashinsu fitsarinsu da komai na su, kuma idan suka yi kuka ita zata dauke su tana basu hakuri ta ciyarda su, way sani b

a ko har wanki take musu, kuma ke da kika karatu? So kike ki lalata karantun na ki ne?”

Cewar Tumba tana tubo baki gabana irin yadda magulmata suke yi idan za su yi magana.

“Gashi ma idan ta fita bata dawowa sai dare, ni ina zan iya wannan”

“To k

in gani ki daina wahalar da kanki ma”

Sai da Naja ta saci kallon Baba sannan ta mike tsaye ta bar gurin.

         ***

A inda mai napep din jiya ya sauke ta ta tsaya, tana ta kwankwanto ko dai ya zo be same ta ba ne ya tafi? Ko kuma yana kan hanya

r zuwa ne, domin tun jiya ya fada mata cewar ta rika jiransa a nan, saboda Napep da Mota basa shiga longunsu sai dai achaba. Sai dai tai jiran minti shirin sannan ya iso, daidai ita ya faka ta shiga tana masa ina kwana.

“Lafiya kalau, kin ta jirana ko?

Wallahi na tsaya daukar wasu ne, na dauka baki shirya ba”

A nan ta ji abun da ya fada, duk d be daga murya sosai ba, sai ta ji wani irin dadi marar misaltuwa, sai dai tana jin maganar ne kamar daga wata duniya, kamar ana fisgo maganar da karfi aa jefow

a kunnenta haka take ji. Sai dai ko kadan hakam be dameta ta san idan ta cigaba da amfani da maganin zata warke ta koma kamar da, daman lafiya raguwa ce da rarrafe take farawa.

“Ni ai tun bakwai nake tafiya”

“Kai kina kokari gaskiya, aikin me kike y

i a gidan?”

Rasa tai abun da zata ce masa, Momy dai bata da yara balle tace raino take.

“Aikin gida haka, kuma ina tsare mata gidan saboda tana zuwa aiki”

“Okay. Allah ya taimaka ya sunanki ma?”

“Falmata”

“Falmata ai ba suna ba ne”

“Fatee

ma”

“Ashe ke Mamana ce”

Ta yi dariya kamar yadda yai daga haka bata sake cewa komai ba, har ya isa bakin gate din gidan.

“To Mamana sai kuma na dawo daukarki ko?”

“To Allah ya tsare”

“Ameen”

Yaja Napep dinsa yayi gaba ita kuma ta kwankwa

sa kofar gate din mai gadin ya bude mata.

“Ina kwana?”

“Lafiya Kalau an iso”

“Eh”

“To madallah”

Ya bude mata gate din ta wuce ciki. Harabar gidan take ta kallo ciki har da wata bakuwar mota da bata taba ganinta a gidan ba. Kamar yadda ta ga

Sirleem haka tai bayan ta danna door bell din kuma ta kwankwasa kofar, Momy ce da kanta ta bude mata kofar.

“Ahhh na dauka ma Sirleem ne shiya ko ya miki wannan knocking din ko?”

Ta yi murmushi sai Momy ta matsa mata ta shigo cikin falon.

“Bakow

a kika yi”

Cewar Hajiya Umaima tana kallon Falmata.

“Eh to ba bakuwa bace, yata ce tana dan rage min aiki ne”

“Oh Allah sarki”

Cewar Hajiya Umaima tana murzawa yarta Nafiza allurar da akai mata.

“Ki shiga kitchen akwai dankali sai ki firay

e, zan zo na dora girkin a gas saboda ki ga yadda ake”

“Tau”

Falmata ta amsa sannan ta mikawa Hajiya Umaima gaisuwa ta nufi kitchen din. Da kallo Hajiya Umaima ta bita har sai da ta shiga sannan ta kalli Momy ta ce.

“Ke kuma haka kawai zuciyarki

ta raya miki ki samo mai aiki? Kina zaune kalau ta aure miki miji”

Momy ta yi dariya tana kokarin zama.

“Ah haba dai wannan yarinyar da kika gani bata da matsala Wallahi ko kadan, magana ma be dame ta ba, tana cikin halin rayuwa ne, ni ma ba son me

aikin nake ba ai kin sani kawai dai dan na taimaka mata ne”

“Allah sarki, to ko dai dashen za a mata ne?”

Ta karasa tana mere baki, Momy ta kalleta da mamaki domin ta manta da ta taba mata maganar.

“Dashe kuma? Uhm Hajiya Umaima kenan, ni ai na wa

tsar da wannan alamarin tuni”

“Aa fa Zaliha, ni ba abokiyar da za a boyewa sirri ba ce, kin san mun saba kashewa mu binne babu wanda yata taba ji, kuma na san kin taba min wannan maganar”

“Eh kuma daga baya na zafafa bincike sai nake ganin kamar be d

ace ba, malamai ma suna fadar yin hakan yana da illa gaskiya”

“Ke ba wata ila, idan kika biye malamai ai ko azumi sai wani yace be dece ki yi ba, ke a yadda kika cikin halin nan kuma kina bukatar haihuwa har dama ta same ki haka ki yi wasa? Haba dai Zal

iha, kowa fa yana son haihuwa musamman ke da shekaru suka fara ja, sannan ga gorin yan'uwan miji, sai ki mutu shikenan ba ki da copy nunawa? Mijinki dai na san ba zan hana ba tun da shi ma yana son ki samu haihuwar, kuma ke fa likita ce kin san yadda zaki

yi abun nan”

Momy ta nisa duniyar tunani tana sauraren kalaman da Hajiya Umaima take mata.

“Amman irin wannan abun yana da matsala Umaima, saboda yana bukatar sirri kuma yawan idan akai wasu za su yi amfani da damar ne su rika tasar kudi a hannunka

ko su maka barazanar tona asiri”

Hajiya Umaima ta tabe baki.

“Ita wannan karamar yarinyar kike tunanin zata iya miki wannan? Kuma ai be zama lallai ki yi da saninta ba, dan ba kowa yake yarda ba, idan har kika da sanin mace shine zata yi amfani da d

amar tana cin duduniyarki, amman wacce akai wa cikin hikima zata nemi rabuwa da abun ne kawai, haba dai Zaliha, sai kace ba ke ba, duniya fa ta cigaba yanzu, ke fa kika fada a kullum baki cire rai da samun haihuwa ba, kuma duk wannan be saka kin yi tunanin

mafita ce Allah ya kawo miki ba?”

Momy ta kalli agogon falon a kokarinta na kawar da zancen Umaima.

“Bari naje na hada abun karyawa yau da wuri zan shiga office”

Hajiya Umaima ta mike tsaye tana yar dariyar mamaki.

“To yayi Allah ya bada sa'

a mu dai mun gode da ejection, sai kuma idan asman ta sake tashi, mu na gaida Yaya idan ya dawo”

“Zai ji inshallah”

Momy ta amsa tana kallonta har ta juya sai kuma ta juyo tana fadin.

“Wai Ameer ya koma ne?”

“Eh ya wuce jiya”

“Ah lallai kuw

a, shi ne ko sallama? Ko da yake ba laifinshi ba ne laifinki ne ai”

“To ma zauna kullum ana ta dora muku dawainiya, abun kuma ai sai yayi yawa”

Cewar Momy tana murmushin da be kai zuci ba.

“Hmmm To Allah ya dawo da shi lafiya”

“Ameen”

Momy

ta amsa tana binta da kallo har ta fice sannan Momy ta soma cire safar hannunta tana ta tunanin maganarta. Upstairs ta nufa tana sauke ajiyar zuciya, sai da ta shiga dakin ta jingina da kofar dakin ta rufe ido can kuma ta bude tana karewa dakin kallo kamar

wani bakonta. Bed dinta ta nufa ta zauna still thinking, kamin ta shiga bandakin ta wanke hannunta ta fito daga bandaki kamar wanda bata son tafiya.

_________

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi

mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi mal

am aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwa

r da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasa

r nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

38

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 0803612

6660*

Lalabe take tana nufar inda take zaton kofar bukkar take sai kiran sunan Inna take tana kuka. Kamin ta karasa Inna ta shigo da sauri sai tai tsaye cak ganin tana lalabe ga idonta a bude.

“Fulani?”

“Inna akwai rana?”

“Akwai rana mana, baki

gani ne ke?”

“Bana iya ganin komai sai duhu Inna, Inna kina ina?”

Inna ta karasa kusa da ita ta taba hawaye na sauko mata.

“Inna bana ganin komai sai duhu kawai”

Cewar Fadime tana fashewa da kuka, a lokacin ne wani irin tashin hankali ya samu

Inna, sai ta rasa inda zata saka kanta, kukan data fashe da shi ne yasa Bappa shigowa bukkar yana tambayar ba'asi, da farko be yarda Fadime bata gani ba domin abun ya zo masa kamar almara, ya kuma san halinta da rashin jin zata iya yin hakan dan ta razana

mutane, hakan yasa shi daka mata tsawa.

“Hiyy yo in baki bar wasan nan ba ina dauko sanda in buge miki kai”

Duk da irin tsoron Bappa da take ji be hana ta magana ba, sai ta kamkame Inna hawayena na mata zuba gwanin tausayi.

“Wallahi bana ganin k

omai Bappa dan Allah ku kai ni asibiti, dan Allah ku kai ni kar na makance gaba daya, wayyo Allah na”

Ta sake fashewa da kuka, Inna na rike da ita itama tana nata kukan, Bappa ya tsaya mata kallon mamaki kamin ya kai hannunsa a fuskarta yana yawo da shi

, sai dai har yai ya gama bata san yana yi saboda bata ganin da gaske.

“Inna...Inna dan Allah ki kai ni asibiti kin ji”

Inna ta kasa cewa komai sai sakin Fadime tai ta fito waje, Bappa ya sake kai hannunta a fuskarta.

“Nawa ne nan?”

“Bana gan

in komai Bappa dan Allah ku kai ni asibiti”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Bappa ya furta ganin da gaske take, a take labari ya canja, unguwar ta dauki wani sabon zance, Fadime ta dawo amman ta makanci, mutane sai shigowa ganinta ake, wasu na A

llah ya sawwake wasu na fadin a kaita babbar asibitin Katsina ganin abun ya shafi idanu, hankalin Bappa da Inna duk yabi ya tashi, gashi ita kadai Allah ya bar musu idan suka rasa ta ko kuma makantar ta bita har karshen rayuwa sune a matsala da kuma wahala

da ita. A take Bappa ya saka Naggensa daya a kasuwa ya tallata a unguwar wani bafulani dan'uwansa ya siya a wulakanci, shanuwar dubu dari da hantsin ya siyeta a dubu 80k.

Yana shigowa da kudi Inna ta shiga ta dauko hijabinta ta dauko na Fadime ta saka m

ata, aka kira musu wani mai achaba ya dauke su biyu, Bappa kuma ya nufi bakin tashar garin ya samu wani, kan babur suka isa garin Kaita, sannan suka shiga motar Katsina. Duk abun da ake Fadime bata ganin komai sai da ji murya ko sautin mota.

Direban be s

auke passengers dinsa ko ina ba sai cikin tashar Katsina, Inna ta fito motar rike da hannun Fadime, Bappa na gaba suna baya har suka isa bakin gate din tashar suka samu Napep suka shiga, be sauke su ko'ina ba sai General Hospital Katsina, dake Muhammad Dik

ko Road, sai da suka fita sannan Bappa tambaye shi nawa za a biya shi, ganin kamar baki ne yasa ya tsaga abun da ransa yake so ya fada musu. Bappa ya dauko 1k ya bashi ya karbi canjinsa sannan suka nufi cikin asibitin, duk tafiyar da ake Fadime na lake da

littafinta a cikin Hijab da dayan hannunta dayan kuma yana rike da Inna.

Da tambaya suka isa gurin da ake karbar kati suka biya suka karba sannan suka koma bin line mika katin, matar na kallonsu tace.

“Kun yi latti, abun da ake zuwa tun safe? Sai dai

ku jira likitan yamma idan ya zo, ko kuma ki bari gobe da safe ku sake dawowa”

“Dan Allah ki taimaka min”

Fadime ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, domin jin take kamar da sun ga likita ya bata magani ido mata zai bude.

“Babu wani taimakon

da zan iya muku, ko dai ku dawo gobe ko kuma ku jira likitam yamma ya shigo, domin lokacin tashin likitan safe yayi”

“Inna ki saka baki dan Allah”

Cewar Fadime tana riko hannun Inna da kuka, Inna zata yi magana Bappa ya tari numfashinta.

“Shiken

an zamu jira har yamma, ai dai za su zo dai ko?”

Ta watsa masa wani kallo.

“Idan ba za su zo ba karya zan maka ne?”

“Aa Hajiya dan tabbatarwa ne kawai”

Bappa ya fada yana ja da baya, daman can ma'aikan asibiti idan sun ga alamar kai wani bagid

aje ne sai su fara neman wulakantata, kalilan ne masu kirki da mutuncin a cikinsu. Komawa su kai can gafe kasa suka zauna kamar wasu mabarata.

“Ba a zama a nan ku koma daga waje”

“To”

Suka sake mikewa tsaye suka fita wajen gurin suka zauna a kujer

un dake gefen gurin, Bappa na gafe Inna na hagu an saka Fadime a tsakiya bata komai sai hawaye, ashe gani ma wani abu ne, duk abun da ake yau bata ganin komai, idonta a bude yake amman duhu take gani. Lallai bayan ni'imar musulunci da imani babu abun da ya

fi ji da gani. Idan Allah ya hada maka duka to ya maka babbar kyautar.

  Suna zaune a gurin Shattima ya shiga gurin ba tare da ya kalli inda suke na balle ya san da su, a natse ya wuce yana wani irin takun kasaita kamar asibitin Mai Martaba, kana ganin

tafiyarsa da yanayinsa da siffarsa da yadda yake zuba kamshi kai kasan babban mutum ne dan babban gida.

Sai da ya gama abun da zai yi ya fito yana tafiya kamar dazun, black T-shirt ce jikinsa sai red blazer suit ya rike lab coat din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login