Showing 21001 words to 24000 words out of 304903 words

Chapter 8 - FULANI COMPLETE

yau, Zainab irin matan nan ne da basa bin kawaye sai dai kawaye su bi su dan suna jin sun isa, tana ji da Sarautar da ba ta jininta ba tana jin naira ga kuma d

aukaka da ta samu sakamakon aikinta na daukar hoto wanda ba kasafai kake mace bahaushiya kuma musulma tana yi ba, bayan daukar hoto Zainab fitattaciyar yar daukar wanka ce  Instagram hakan yasa hotunanta suka yawo a duniya kamar wata yar film ko mawakiya g

a kuma kyau da Allah ya hore mata da cikar sura irin ta ya mace.

  Katon bakin gilashin idonta ta cire tana kara kallon mijin kawarta da kyau, sai ta ga yafi kyau a fili ma fiye da hoton da Humaira ta dora lokacin anniversary su. Daga inda take tsaye sany

e da dogon wando na jean da half gown ta atamfa kanta da jar hulla waccw ta bayyana rabin gashin kanta daya sha gyara, ta daga masa hannu alamar HI tana wani yauki da fingers dinta kamar ba farata ba sai wani murmushi take masa na daukar hankali. Da mugun

mamaki ya dago mata hannun shi ma wai celebrity ta dago masa hannu da kanta ya santa dan yana daya daga cikin followers dinta na instagram, secondly kuma Humaira na yawan ba shi labarinta ta nuna masa hotonta ya fi a kirga third kyauta ya wuce yadda yake g

aninta a hoto domin a fili farinta har wani haske yake kana ganinta ka ga yar fulanin asali kuma wayayyiyar mace.

“Ba laifi bayan kyau kana da naira”

Ta fada a ranta tana karewa tsaddadiyar motar da yake kokarin hawa kallo, sannan ta doshi cikin gid

an tana wani irin taku na daukar hankali, murmushi ya cika kyakkawar fuskarta ko ba komai zuwan da tai yau saboda mijin kawarta ne domin tun a lokacin fa Humaira ta saka shi a status dinta na happy anniversary ta ji ranta ya biya, kuma bukatarta ta biya tu

n da ta yi arba da shi.

Door bell din ta danna in few minutes house help din Humaira ta bude mata kofar, sai ta nasa kafarta a katon falon tana kare masa kallo, a ranta ta raya ba laifi ita kam ta ga gurin zama. Cike da far'ah da jindadin ziyarar Humai

ra ta fito ta rumgume ta.

“Oyoyo manyan kasa yau ke da kanki Hajiya Karama”

“To ya za'ayi muna so ne ai dole mu biyo, ykk”

“Lafiya kalau ya gida ya su Hajiya da Ammy”

“Suna nan kalau ina yaranki?”

“Suna makaranta”

Ba laifi Hajiya Karama

ta saki jiki suka sha fira da Humaira har abun ya bawa Humaira mamaki domin ba kasafai Hajiya Karama take sakewa tai fira da kawaye haka ba no matter how close they are, ita din tana da wani irin jin da kai da isa idan ana fira sai dai ta rika jefo zance c

an sama-sama, hakan kuma be hana kawaye binta domin tana kashe musu kudi kamar bata san zafinsu ba, ga kyauta da alheri ga kowa.

“Bude min wayar na ga hotunan anniversary tun da ba a fada mana ba”

Ba musu Humaira ta cire mata password tana dariya ta

re da fadin.

“Ba mu gayyaci kowa ba fa daga ni sai yara mu kai sai uban gayyar”

Cikin hotuna Hajiya Karama ta shiga tana dubawa, sai da ta bari Humaira ta tashi sannan ta shiga long calls dinta tana bin numbers din da kallo, number da aka sakawa Alon

e da hoton heart ta bude tayi copying digit din ta shiga message ta saka number ta ta aika ma kanta da number sannan ta goge sakon ta aje wayar tana murmushi.

“Humi zan wuce daman na biyo ne kawai na gaishe ki”

Har gurin motarta Humaira ta rakota ta

na ta mata godiya domin ba karamin dadin ziyarar taji ba, ba ta bar Hajiya Karama ta wuce ba sai da su kai hoto.

Cikin farinciki ta dawo Masarautar ranta fes domin ta samu abunda take so, part din Ammy tai parking sannan ta fito tana wani irin taku na

kasaita kamar wata yar sarki ta shiga cikin gidan. Ko kallon mutane dake gaisheta ba su isheta ba, balle har ta amsa gaisuwar da suke miko mata, yadda take lumshe ido ta bude ma kadai wani abun kallo ne. A natse ta shiga katon falon na Ammy, babu kowa a ci

ki sai plasma da Ac dake ta aiki bada sanyi, ta kalli farantin dake cike da sweet an dora shi saman kujera, ko ba a fada ba ta san aikin Nana ne ko Yusra. Kusa da farantin ta zauna ta bude wayarta ta soma dannawa, can kuma ta kai hannu ta dauki sweet din t

a bude ta fara sha. After like 30 minutes Ammy ta fito daga dakin sanye Holland Nana na rike da gyalen nata tana kuka kamar wata yar 6 years.

“Baby what happened?”

Hajiya Karama ta tambaya tana kallonta cike da kulawa. Nana kamar mai jira ta saki ha

nnunta ta dawo gurin Hajiya Karama ta zauna tana kukan da ba hawaye.

“Ammy ce Hajiya”

Hajiya Karama ta kalli dake kokarin zama a dinning.

“Ammy me aka mata?”

“Iskancinta ne ya motsa”

Ammy ta fada ba tare da ta kalli inda suke ba. Hajiya Kar

ama ta kamata ta dawo da ita saman kujera ta zaunar da ita.

“Fada min me kike so baby?”

“Wai na ce ma Ammy bana son driver dake kai ni school a canja min shine tace wai ba za a canja ba”

Ta karasa tana rushewa da kuka kamar gaske alhalin idon nat

a ko hawaye babu. Hajiya Karama ta kalli Ammy.

“Haba Ammy dan wannan dai?”

“Ki tambaye ta me direban yai mata da za a canja shi? Tsabar iskaci da jindadi? Wata na can kullum a kafa zata je makaranta ta dawo a tsakar rana ke dan kin samu ana kai ki a

dauko ki a mota da ac da komai ki dawo mana wani zance na banza yanzu”

Hajiya Karama ta kalli Nana.

“Mi driver yayi miki?”

“Hajiya Tsoho ne fa, kan shi har da hurhura ni bana son gani”

Ta karasa da kukan da ba hawaye tana buga kafa kasa, Haji

ya Karama ta mike tsaye ta nufi dinning room taja kujera ta zauna tana kallon Ammy.

“Haba Ammy idan ba yi ma Nana abunda take so ba wa za ayi ba? Canja driver ba wani abu ba ne fa, ita yake kai wa kuma ya dauko idan bata ra'ayinsa ba dole”

Ammy ta t

sayar da cin abincin da take ta kalli Hajiya Karama.

“Nana da ban isa na saka ta aiki ba, ko kofi na ce ta dauko yanzu zata ce min ta gaji jikin ta ciwo yake bla bla bla iskanci kala kala, tun dazu na ce yarinyar nan ta dauko min abin ci na ci a daki t

a ce min kafarta ce ciwo, na ce taje waje ta kira min wani daga masu aikin gidan nan a kawo kin abinci a daki na ci tace kafartana ciwo ba zata iya sauka kasa ba, and now kina tunanin tace na canja mata driver saboda wani selfish interested na ta kuma na y

i saboda ita ta haife mu”

Shiru Hajiya Karama tai, ita kanta ta sani idan halin Nana za ayi mata abu to ba za a mata ba, domin ko ita da take mata gata bata isa ta saka ta aiki ba, wani lokacin ko cewa tai ta dauko mata abu sai tace kaza nata ke ciwo ba

ta iya tashi.

“Gurin Mai Martaba janye na fada masa, ai Wallahi shi komai na ce ina so yi min yake, yana so na”

Nana ta fada cikin daga murya dan Ammy ta jiyota domin akwai tazara sosai tsakanin falon da dinning room di. Ammy ta juyo daga inda take

zaune tana nuna Nana da yatsa da fuskar dake nuna babu wasa a tare da ita.

“Kin fi kowa sanin halin da Mai Martaba yake ciki, Wallahi ko da wasa kika kuskura taba kofar dakinsa da sunan kai masa complain sai na baki mugun mamaki Nana kuma ki gwada”

Tashi tai ta fice tana kuka kamar gaske.

“Zainab ki daina biye Nana kuna kara lalata, duk abunda take da gangan take dadi ne yake mata yawa”

Ammy ta fada ba tare da ta kalleta ba, domin har cikin ranta bata jindadin yadda Hajiya Karama, Shattima da

Hajiya Babba suke yi ma Nana. Hajiya Karama ta yi murmushi tana mikewa tsaye.

“Ai mun kusa bar miki gidanki Ammy, ina yin aure zan dauke Nana mu tare a can”

“Auren da babu rana”

Ammy ta fada tana tabe baki, sai Hajiya Karama tasa dariya.

“No

very soon Ammy, domin na samu wanda na ke so”

Ammy ta kalleta.

“Da gaske?”

“Wallahi Ammy, yana da mata daya yara uku ban dai san real name dinsa ba amman dai ya min, ban fada masa ba but very soon zan sanar da shi ina son shi kuma zan aure shi da

gaske”

Magana Zainab take kamar abunda take fada ba komai ba ne. Ammy ta kalleta irin kallon nan na mamaki da tunani.

“Ke za ki ce kina son shi? Ban gane ba”

“Yeah normal ne ai Ammy”

Tana fadar hakan ta nufi hanyar sauka downstairs dake dinni

ng, bata son tsayawa kar Ammy ta fara karanta mata wasu haruffan da ba zata iya hadasu ta tada ba.

Tana saukowa, ta nufi dayan stairs din da zai sadata da bangarenta ita da mahaifiyarta, kamar ta wuce dakinta sai kuma ta nufi dakin mahaifiyar ta ta. Za

une ta same ta hannunta rike da wuri, sai dai ganin Zainab din yasa tai yi saurin boye wurin a bayanta ta kalli yarta ta manya idanuwanta da suka rine su kai ja kamar barkono.

“Na fada miki ki daina shigo min daki babu sallama”

“Na manta ne”

Ta f

adi hakan bayan ta zauna kusa da ita, sannan ta bude wayarta ta shiga gallery ta kamo hoton mijin kawarta ta nuna mata.

“Iya kin ga surukinki”

A razane Iya ta kalleta kamin dubanta ya kai gurin hotonta sai da ta kare masa kallo sannan ta dauke kai t

a hade rai.

“Shi kika zabo bana?”

“Yes kuma wannan karon da gaske aurenshi zan yi, mijin kawata ne, thought dai ban fada masa ina son sa ba amman zan fada masa soon”

“Zainab kenan, kin san miyasa ake kira da Hajiya?”

Iya ta tambaya tana kare ma

ta kallo, kamin Zainab tace komai Iya ta bata amsa.

“Saboda ina son ki zama isashiya, tun da aka haife ki na saka mahaifinki da kansa ya rada miki sunan Zainab uwargidan Mai Martaba, ni da kaina nai miki lakani da Hajiya sai dai ganin akwai wata Hajiya

r matar Mai Martaba ta biyu yasa ake kiranki da Hajiya Karama, so a komai ki isa, kuma ki amsa sunanki yadda Mahaifiyar Shattima take matar Sarki kuma uwar Yarima da Gimbiya ke ma ki taka wannan matsayin”

Zainab ta tsotsa mintin dake bakinta tana jin ma

ganar Iya na wuce mata ta bayan kunne.

“Iya ba mu da gadon Sarautar nan fa karki manta, kuma ni bana son wani an mutu an dawo, finally dai na samu miji kuma shi zan aura that's all”

Tana gama fadar hakan ta mike tsaye ta fice daga dakin dan ba gane y

aren mahaifiyarta take ba. Iya ta bita da kallo har ta fice sannan tai murmushi ta fiddo wurin dake boye a bayanta.

“Ba ki da miji a waje Zainab, mijinki a cikin masarautar nan yake, idan ba mu da gadon sarauta to ya kamata jikokin mu su gaji sarauta..

...”

Ta karasa tana daga wani bakin kullin da aka nade da zare kamar laya ta matsashi.

“Mai Martaba ko kuma Labib?”

Ta tambayi kanta tambayar da ita kadai ta san amsarta tana lasar bakinta.

FALMATA POV.

“Sallamu Alaikum wai an ce an

a sallama da Falmata a waje”

Almajirin ya fada yana tsaye daga bakin kofar gidan.

“Falmata aka ce ko dai Naja?”

“Falmata”

Ya amsa mata, sai da tai kamar tace aje ace tace ba zata zo ba, sai kuma ta tuna da yan kudin da take shigo mata da su na

zance.

“Tashi ki tafi”

Falmata kamar tana jira ana fadar hakam tai saurin mikewa ta saka Hijabinta ta fice, Tumba taja tsaki.

“Ni wannan abun mamaki yake ba ni, kamar a kasa nake zubarwa, a maimakon abu ya ragu sai karuwa yake na Naja na raguwa?”

Ta fada slowly tana mamakin lamarin Falmata. Da mugun far'a Falmata ta fito dan ta san mai kiran nata Maniru ne, har zumudin zuwansa take saboda yana kunna mata wakar Sirleem M2 audio da video, wannan ya saka duk a cikin samarinta ta fi kaunarsa.

S

ai da ta fara masa sallama ya amsa mata da murmushi suka gaisa sannan ya zauna a dakalin dake kofar gidan suka dasa hira, can kuma ya kunna mata wani sabon video da M2 ya fitar, tsabar zumudi da farinciki sai ta ji kamar ta rumgume shi. Bayan sun gama zanc

e ne ya bada dari uku da lemun yanka a leda, cikin kunya ta karba domim har ga Allah bata son karbar abu a hannun wani sai dai ta sani idan ya koma cikin gidan ba tare da komai baa Tumba za ta iya mata fada ko ma ta doke ta.

Cikin natsuwa ta shigo cikin

gidan ta nufi inda Tumba take ta aje mata ledar lemun a gabanta sannan ta mike mata kudin da hannu biyu.

“Gashi ya ba ni”

Kallonta kawai Tumba take irin kallon na mamakin yadda take tsallake duk wani abu da take mata.

“Umma”

Falmata ta kira s

unanta ganin kamar bata san ma tana mika mata kudin ba, sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya sannan ta karbi kudin ta kuma kalli Ledar.

“Dauki daya”

Cikin ladabi Falmata ta saka hannu ta dauki lemun daya kamar yadda ta bata umarni

ta nufi dakinsu, tana shiga tai shirin bachi babu komai a fuskarta sai murmushi yau kam ranta fes ta ga sabon video M2, har ta kwanta sai kuma ta tashi tana rare wakarsa a hankali tana rawa tana kallon inuwarta wacce kyandir ya haska, sai ka rantse da All

ah ba Falmata bace yarinyar da ko a hanya ka hadu da ita ba zaka taba saka ran tana magana ba. Sai da taji motsin shigowar Naja sannan ta yi addu'ar bachi ta kwanta.

Washe gari ma kamar ko yaushe, sai da ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta saka

wasu tufafin ta fito ta sha kokon da Tumba ta dama, kamin ta sake mika mata wani rubutun ta karba ta sha da Bismillah. Sannan ta fito ta kama hanyar zuwa gurin aikinta tana tafiya a natse, kana kallonta ka ga natsantsiyar yarinya mai kamala da tarbiya.



Ba ta yi mamakin sake karo da Iya a Harabar gidan ba, domin kusan kullum sai ta ganta a gidan duk da bata san aikinta ko alakarta da masarautar ba, amman ta tabbatar da ita din wata babba ce a ciki. Ta gaishe ta kamar yadda ta saba sai dai Iya bata amsa ma

ta ba yau kam ko kallon inda Falmata take Iya bata son yi. Sai dai gaishe da kowa sannan ta wuce cikin gidan, a tsanake ta hau stairs din ke sada mutum da falon Ammy sannan ta danna door bell. after like 5 minutes Shattima ya bude mata kofar, wani irin jan

numfashin Falmata tai ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallon Shattima idonta a waje kamar irin ka ga wanda ka dade ba ka hadu da shi ba ko kuma kake mafarkin gani, ba ido kadai ba har bakinta a bude yake a wannan lokacin. Shattima kan sakin kofar yai ya

dawo falo ya zauna yana taba wayarsa daman indai shi zai ce mata ta shigo ko ya tambaye abunda take so sai dai ta shekara a gurin, budewar ma ta yi sa'a yana tsaye jikin kofar ne. Na so kafarta tai ta shigo cikin falon tana cigaba da kallonsa kamin idonta

ya sauka a gurin Hajiya Karama wacce ke kallonta, wani irin kallonsu take kamar bata taba ganin mutane ba, ita a rayuwarta bata tana ganin fararen mutane da farinsu ke haskawa sosai kamar Shattima ba, gaba daya kallon Balarabe take masa sam bata yarda bafu

llanin mutum ne take kallo ba, ta kallin fatar jikinta da take baka ta sake kallon Shattima, ba farin ba ko gashin kansa da ke a gyare abun kallo ne, ga wani dogon hanci kamar biro kai ko cikin larabawan wannan na musamman ne. Shi ne abunda zuciyarta take

raya mata.

“Me kike so?”

Hajiya Karama ta tambaya, a lokacin ne Falmata ta kara rikicewa, ta sara abunda zata ce, gaishe su zata fara yi ko fada musu aikin da ya kawo ta, tun da take zuwa gidan bata saba karo da daya daga cikinsu ba sai yau, sai dai

jiya ta hango Zainab a stairs sai dai bata dauka a kusa kyauta yayi haka ba sai yau.

“Me kike so?”

Zainab ta daka mata tsawa, a take jikim Falmata ya hau rawa sai ta fashe da kuka domin ba karamin tsorata tai ba.

“Easy mana”

Shattima ya fada

yana kallon Hajiya Karama.

“To ana mata magana sai tai ma mutane shiru, kuma sai kallonmu take kamar mayya i hate nonsense”

Ta karasa tana mikewa tsaye ta fice daga falon tana wani yatsinar fuska kamar ta ga abun kazanta.

“Baaba ware”

Shattim

a ya kira taohuwar yana kallon inda take tsaye rike da turaren wuta, sai a lokacin Falmata ta lura da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login