Showing 123001 words to 126000 words out of 304903 words

Chapter 42 - FULANI COMPLETE

garin suke masa kallon yana sonta cikin hai da mahaifinsa. Daya bayan daya take kallonsu kamin ta kurawa Fadime ido, bata taba ganin Zainab ba, amman tabbas ta taba ganin Fadime, ba zata iya sha

idar inda ta santa ba, but tabbas ta taba ganinta, Fadime ma na ganinta ta gane ta.

“Ya akai....?”

Wasim ya tambaya da yarensu yana mata wani kallo wanda ya dauke annurin fuskarsa gaba daya. Kallonsa tai da sauri kamin ta ce komai Fadime ta ce.

“Wannan matar muguwa ce na taba ganinta, lokacin daya wuce ita kuma ta zo na ce ta dora ni da tuluna, sai na cire mata gashin kaza a kai shine ta fasa min baki”

Ta karasa tana kallon Wasim irin na yaro ya kai kara a gurin babba, domin ta fada ne da zimm

ar Wasim yai mata hukunci sai ta ga ya lumshe ido, kamar be jidadin maganarta ba, ita kuma Liya sai tai dariya marar sauti tai baya-baya tana kallonta.

“Liya...”

Wasim ya kirata, sai ta daga masa hannu alamar babu ruwanta tana ta tafiya da baya-baya

sai murmushi take wanda ya bayyana duka hakoranta. Wasim ya kalli Fadime.

“Miyasa kika yi magana?”

“Ai baka ce kar nai magana ba”

Ta bashi amsa kai tsaye, Zainab ta mike tsaye daga dukena da take.

“Akwai matsala ne?”

Shiru yai ya sauke aj

iyar zuciya.

“Ki saka camera da komai naki a jakar nan ki bar nan”

Kamar mai jiran Umarni tai saurin yin abun da ya fada.

“Gida zaka maida mu?”

“Ba zai yiyu na fita da ku a yanzu ba, saboda ta yi magana Liya ta gane ta, Fateme zata iya samun m

atsala...”

Yana fadar hakan cikin Fadime ya murda sai fitsari.

“Wayyo Inna, na shiga uku yau Bappa na can na nemana, yau kashina ya bushe...”

Ta fashe da kuka, sai yai mata alama da tai shiru.

“Shiiiiiiiii daina kuka kuma komai aka baki karki

ci”

“Tau, amman dai na shiga uku, daman Inna tace kar na zo, ni ban ji magana ba”

Ta kara fashewa da kuka.

“Daina kuka”

“Dole ne nai kuka, ni kadai zan shiga ukuna, ita wannan matar data janyo ni ba zata shiga uku ba sai ni mai shegen surutu,

dole nai kuka... Amman na yi shiru”

Ta amsa da karfi tana kokarin datse kukan, ta rufe bakinta jikinta har bari yake cikinta na ta kuka kamar wacce zawo ya cikawa ciki.

Zainab kam jin tai kamar kafafuwanta ba za su dauke ta ba hango wasu maza kusan s

u hudu su doso inda suke, rike da wutar ice a hannu.

FALMATA POV.

sai da ta kalli Sirleem ta sauke kanta kasa sannan ta soma magana.

“Sunana Fateema, ana kira da da Falmata ne saboda na ci sunan Kakata ta wajen uwa ne, amman Mama na Fulani ta

ke kirana, daga Mamana har Baba duka fulani ne, amman Mamana baka ce sosai sam ba zaka ganta kace ita Fulani ce ba”

“Ita kika biyo kenan”

Sai tai murmushi kamar yadda shi ma yake murmushin.

“Haka mutane suke cewa, domin mahaifina fari ne kamar ka

i”

Ta fada tana kallonsa sai ya nuna kansa.

“Ni fari ne?”

Ta sauke kanta kasa cike da kunyar kallon da yake mata. Duk abun da suke Shattima na tsaye jikin window yana kallonsu kuma yana jinsu.

“Go on cigaba, aikin mai babanki yake su waye kane

nki?”

“Mahaifina dan kasuwa ne, yana siyar da kayan masarufi irin gero masara da shinkafa, a kasuwa idan ya fita baya dawowa sai dare”

“that's how step mother dinki ta samu damar azabtar da ke ko?”

Ta kalleshi sai kuma ta sauke kai.

“Da can ya

na so na sosai, komai zai ce Fulani na, a da mu uku ne, Mamana tana da yaya biyu mace da namiji da ta haifa da wani namiji kamin ta auri Babana, domin baba shi saurayi na a lokacin da ya aureta ita kuma ta taba aure, a lokacin ta fada min a kauye suke zaun

e shi kuma yana zuwa birnin yola yana sana'a yana komawa, ganin yan'uwansa sun dora mata tsana saboda ya aureta tana bazara da yaya biyu sai ya dauke ta ya kama gida nan ya dawo da ita, har da yaran da wacan mijin ya bar mata sai ta dawo tare da su, saboda

mahaifinsu ya tafi abuja neman kudi kuma tun da ya tafi baya aike kuma baya zuwa dubasu, a lokacin data dawo nan ta haife ni, sai baba ya saka namijin makaranta ganin shi ne babba, ni ma a lokacin da ina karama ya taba fada min zai saka ni a makaranta, a

lokacin dukanmu baban mu yana son mu har wadancan da b yayansa ba, Mama na bata da kawa kamar Umma (Tumba) domin a da gidan da Umma take aure yana kusa da na mu ne, komai a tare suke yi da mama ni ma Umma tana so na sosai a da kowa yana yabon halinta sabod

a tana da kirki da kima a gurin mutane, baba yana taimako mijinta sosai kamin ya rasu, a lokacin ne ma babana da mama da kowa suka rika mata abun arziki, abinci tufafi da komai ma, bayan ta gama takaba zata koma garinsu sai Mama da Baba suka hana, baba ya

dauki nauyin ciyar da ita ganin irin kusancin dake tsakaninta da mamana, har yan'uwansu sun san junansu, ashe ba mu sani ba baba ya shirya aurenta ne, duka ba mu sani ba sai da aka daura auren aka kawo ta dakin da muke kwana ni da yayan mamana, tun daga lo

kacin komai ya canja, Baba ya daina son mu ya ce baya son yaya mama sai an maida su gida, da kansa ya dauke su ya kai su kauye, sai namijin ya ki ya zauna aka dawo da shi, Mama ta cigaba da rika shi, rana daya muka neme shi muka rasa, ba mu san abun da ya

faru da shi ba, ba a fada mana inda yake, kuma har yau mama bata sake maganar shi ba, ita mace ance ta rasu tun da dadewa, a lokacin ina karama sosai”

Ta yi shiru, sai Sirleem ya rika kafadarta ya zaunar da ita a daya daga cikin kujerun dake gefensu, ha

r ta zauna kamar wanda ta tuna wani abu sai ta tashi da sauri.

“Aa manya suke zama a nan”

Ganin hakan yasa shi ma ya mike tsaye, domin ya san duk yadda zai ce ta zauna ba yarda za tai ba.

“Fada min babanki ya saka ki a makarantar?”

“Aa be sani

ba, amman ya saka Naja yar da Umma ta haifa da abokinsa Malam Usman, Umma tana da wasu yaya manya a kauye da sukai aure mata uku namiji daya, bayan ni Mama ta haifi yaya biyu maza su ma baba baya son su, yana yi ma Mama na fada sosai ko da kuwa ita take da

gaskiya, wani lokacin a gabanmu Mama take kuka, wani lokacin kuma sai ta boya, kullum Umma ce mai gaskiya a idonsa kuma yana yawan fadar wai Mama bata tausayinsa sai Umma, ni ma idan muka yi fada da Naja ni yake duka ko da kuwa ni nake da gaskiya, har kud

in cefa ne da abinci sai ya koma hannun Umma, sai abun da taga dama za a girka, gidan Mama bata da lafiya ni zan girka, wata rana nai girkin be yi kyau sai Umma ta zuba min tuwon a kafa”

Ta daga zanenta ta nuna mishi kafar, kasancewarta baka ya bawa kun

ar damar fitowa kamar an mata tabo. Sirleem ya kalli kafar da mugun tausayinta ta gama bayyana a fuskarsa.

“Kwana biyu da faruwar haka akai amai da gudawa a unguwar, a gidan mu an yi kowa ya warke ban da Mamana, tun tana iya tashi har ta kasa, karfinta

duk ya kare kullum ni nake hadimar Baba ya daina kula mu ni da ita, idan ta fadawa mutane abun da Umma take mata sai ace Kishi take, saboda kowa yana ganin kamar Umma ba za tai cuta ba, mutanen da suka yarda da ita kalilan ne, ita da kanta ta saka na kira

mata Umma, ta rika hannun ta saka a cikin na Umma tana fadin, Tumba ga amanar Fulani nan n baki, ki rike ta amana ki ji tsoron Allah kanenta ma na baki amanarsu idan kin cutar da su ke da Allah, a lokacin ne Umma ta saka fada tana cewa ita ba zata karbi am

anar kowa ba, Mama ta kama hannuna tana kuka, tace Fulani ki yi hakuri zan tafi na barki cikin kunci, ki yi hakuri Allah yana tare da ke, ki kula da kanenki kuma ki yi hakuri da rayuwa, n yafe miki na yafe muku ku duka Allah yai muku albarka, karki watsar

da tarbiyar dana dora ki a kai, kuma ki yi hakuri da rashin uwa wata rana zaki zama uwa ke ma, Allah yai muku albarka”

Ta kasa karasawa sai fashewa tai da kuka ta duke a gurin tana jin kamar a lokacin ne Mama ta rasu. Sirleem ma dukawa yai gabanta yana

kallon fuskarta zuciyarsa ta cika da tausayinta.

“A ranar muka wuni kuka n da ita, sai tace min nai hakuri na yi shiru, na daina kuka, amman ita ba rayuwa za tai ba, ashe da gaske ne ta rasu ranar juma'a kowa na mata kyakkyawan shaida, ta tafi ta bar n

i ni kadai, bayan rasuwarta Umma tace ba zata iya rikon kanena ba, sai Baba ya dauke su ya kai su kauye gurin kannen mamana, aka bar ni ni nake aikin komai a gidan, ko ban yi laifi ba zata iya cewa na yi baba ya doke ni, wannan aikin ma saboda na samo mata

kudi nake yi, gashi ba a ba ni abincin a gidan saboda Baba ya hana.... Kuma kullum kasa nake zuwa na dawo kasa...”

Ya karasa cikin wani irin kuka mai taba zuciya, mikewa Sirleem yai tsaye ya fice daga garden din wanda hakan ya bawa Falmata damar kuka t

a tausayawa kanta. Kara matsawa Shattima yai jikin window yana hango Falmata, he feel her feel shi da Mai Martaba yake masa wasiya ma ya yaji balle ita data rasa uwa at her age ga kuma kuncin rayuwar data fuskanta, wani irin tausayinta ne ya cika masa zuci

ya.

Sirleem be dade ya dawo gurin rike da tissue da ruwan gora, tissue ya fara mika mata ta karba ta goge idonta ta hancinta sannan ya bude ruwan gorar ya mika mata. Hannu biyu ta saka ta karba ta kai bakinta ta sha.

“Na gode”

Ta furta bayan ta s

ha ruwa idonta har yayi ja ya soma kumbura.

“Rayuwarki abar tausayi ce Falmata, zan yi magana da Ammy if possible a rage miki time din dadewar da kike, kuma ki samu wani mai napep ki masa magana zan rika biyansa sai ya rika kai ki gida kullum yana dawa

wa da ke”

Tun da ya soma maganar take masa wani irin kallo mai wuyar fassara.

“Na kasa yarda kai ne Sirleem M2, ni ka gama min komai tun da har ka tausaya min, sai yanzu na yarda ban maka soyayyar banza ba, har yanzu ina ganin kamar mafarki na ke, b

an san me zan ce”

Ta karasa tana fashewa da wani sabon kuka, sai yai murmushi ya bude mata hannayensa.

“You deserve a hug”

Shattima na ganin haka ya bar jikin window da sauri.

‘Bad guy’

Ya fada a ransa kamin ya mika hannunsa ya bude kofar

dakin ya fita. Jekadiya ya tarar a falon, tana ganisa ta risina tana gaishe shi.

“Jekadiya a fadawa yarinyar can Baba Adamu zai rika kai ta gida kullum kuma ya dauko ta, ki hanzarta kiranta tana Garden”

“An gama ranka ya dade, Allah kara maka lafiya



Ta mike tsaye da sauri ta nufi kofa, shi kuma ya karasa dakin Ammy ya tura kofar ya shiga da sallama.

“Wa'alaikassalam”

Ammy ta amsa masa tana duba wasu manyan laces dake kasan gadonta.

“Na shiga gurin Mai Martaba ne?”

“Eh mun gaisa”

Daga haka be sake cewa komai ba, Ammy ma bata ce masa komai ba ta cigaba da duba laces din. After like 5 minutes Sirleem yai knocking kofar dakin.

“Ammy”

Jin muryarsa yasa Ammy ta masa izinin shiga, sai ya shigo da kuzarinsa sai dai ganin Shattima ha

kimce saman kujera ya katse masa hanzari, ko da wasa Shattima be kalli inda Sirleem yake ba, ji yake shi ne gaba da shi saboda yana son Nana ko ba komai dole ya girmama shi. And Sirleem did that ya karasa har inda yake ya mika masa hannu, sai a lokacin Sha

ttima ya kalleshi, ya mika masa nasa hannun suka gaisa, sannan Sirleem ya karasa kusa da Ammy ya zauna, daman can haka yake da ita be taba daukar kansa a matsayin ba dan gidan ba, ko kuma kallonta a matsayin kishiyar uwarsa ba duk kuwa da kasancewar Hajiya

Babba bata son haka. Sai da suka gaisa sannan ya gabatar mata da abun da ya kawo shi.

“Ammy akan yarinyar nan ne mai reno, i think tana dare sosai gata mace, why not ta rika zuwa gida 6pm”

Kamin Ammy tace komai Shattima ya kalleshi yace.

“Daga

yanzu sai 10 zata rika zuwa gida, kana da matsala da hakan ne?”

Sirleem ya kalleshi kamar zai yi magana sai kuma ya mike tsaye.

“alright All the best, but it's someone's daughter remember!”

Shattima dai be ce masa komai ba, ko inda yake ne sake ka

llo ba.

“Sirleem you can go zamu duba”

Uffan be sake cewa ba, ya nufi kofa. Shattima ya bishi da kallo zuciyarsa n raya masa yana son yai hakan nan saboda ya samu damar shigewa jikin Falmata da kyau.

_________

Ina mata matan kwalisa Mata

n da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mal

lakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki d

a na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169

311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

30.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abub

akar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

FADIME POV.

kamin su karaso ya Wasim ya kalli Fadime ya ce.

“Karki yi magana kuma komai aka baki karki ci”

Ta daga masa kai wasu hawaye masu zafi na sauko mata. Ganin hakan yasa y

a kai hannunsa ya rika wuyan hannunta. Mutane na karaso kusa da shi suka risina masa alamar girmamawa.

"Erregeak zure ahoarekin ikusi behar du"

_Sarki na bukatar ganin tare da bakinka_

Be ce komai yaja hannun Fadime ya fita daga cikin runfar, Zai

nab na ganin haka ta bi bayansu da sauri, mutanen da suka zo kiransa suka rufa masa baya. Ta inda mutane suka fito ya nufa rike da hannun Fadime wanda ta kasa daina hawayen da take. Ta bayan wani guri wanda yafi kama da kasuwa suka bullo, duk inda Wasim ya

dora kafarsa sai an risina masa an dauke ido daga barin kallonsa alamar girmamawa da biyaya. Sun yi tafiya mai dan nisa a kafa kamin su isa bakin wata babbar kofa ta itace an mata gate har da masu gadinta. Wasim na isowa gurim kofar aka bude masa suna ris

inawa har sai da ya wuce sannan suka tashi. Hakan yasa Fadime ta ji wani girma ya kamata, ko ba komai ta ci alfarmar Wasim ita ma an risina mata, a nan ta kara yarda babu wanda ya isa ya taba ba, kimar Wasim da sonsa suka kara ninkuwa a ranta. Shiga cikin

gurin yasa daga Zainab har Fadime suka manta da abun da ya kawo su gurin, wata sabuwar duniya ce, kuma babbar daula mai zaman kanta, babu komai a dayan bangare sai katuwar gona mai cike da manyan itace wanda har baka iya hango cikinta saboda hudu, ta gafe

daya kuma kana jin kwarar ruwa alamar akwai korama a gurin. An bi ko'ina na harabar an haska shi da wutar ice wanda hakan ya bawa Zainab da Fadime damar ganin irin kwaliyar da aka yi ma gurin da koren ganye mai yanayi da ganyen ayaba. Sai da suka isa gaban

wata kofa sannan Wasim ya cire talkaminsa na fata, ya nasa kafarsa a gurin, Zainab da Fadime kan daman ba su shigo garin da talkami ba. Wata katuwar fada ce da aka shimfida mata gashin farar damisa, tun daga bakin kofar har zuwa inda Sarkin yake zaune kan

wata kasaitacciyar kujera da zaka iya rantsewa ba itace ne aka saffara ba. Daga hannun kujerar har jikinta an masa kwaliya da farar azurfa. Ginin fadar kuma an masa kwaliya da fatar zaki inda Sarkin zai dora kafarsa da hannunsa ma kan Zaki ne a gurin. Tsi

rarun mutane ne a cikin fadar ciki har da Liya dake tsaye gefen Sarkin dake hakimce saman kujera fuska babu annuri.

Nan da nan jikin Fadime ya fara rawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login