Showing 15001 words to 18000 words out of 304903 words
ta fadi ta kasa tana gaisar da Ammy, Ammy ta amsa mata ba ya
bo ba fallasa sannan ta cigaba da danna wayar da take.
“Ranki ya dade zan gyara dakinsu Yan uku ne”
Ta fada muryarta kana ji kasan tsoro ne ya cika mata ciki fal, tsoron irin amsar da za a bata tsoron kallon matar sarki tsoron mutane da suke falon d
uka suka taru sukai mata tsaye a kai, kamin Ammy ta bata amsa har idonta ya soma cika da kwalla cikinta har murdawa yake kamar wacce tai wani laifi.
“To ai kin san inda dakin yake”
Ta yi saurin mikewa tsaye ta nufi corridor da zai sadata da dakin ya
ran, a nan ma wasu hadiman ne suke ta aikinsu, Falmata sai gaishe su take kowa ta gani sai tace nasa ina kwana da wanda ya kamata da wanda be kamata ba, ta kasa daga ido ta kalli kowa.
Sai da tai Bismillah sannan ta kai hannu ta tura kofar dakin ta shiga
har lokacin gabanta be daina faduwa ba, tsoron da take ji be gushe ba, haka take samun kanta a duk lokacin data shigo Masarautar, abun ka da wanda be saba shiga mutane sosai ba balle kuma manya kamar gidan Mai Martaba.
Wannan karon ba tai mamakin ga
nin Iya a dakin ba, daman ta saba ganinta a kullum idan ta shigo sai dai wani abun da yake bata mamaki yau kusan kwananta uku da fara aiki a gidan amman bata taba ganin yaran ba ko hotuna, a kullum kuma sai ta tararda Iya a dakin, haka ma a kullum sai Iya
ta saka dogari yai mata gadin dakin har Falmata ta gama gyaranta ta fita.
“Ka sa ido, irin wadannan yaran ba abun yarda ba ne”
Iya da fadawa dogarin tana wani yawo da manyan idonta akan Falmata kamar zata ciro su.
“To ranki ya dade”
Ya amsa
mata yana risinawa sannan ta fice tana ta wani shinshine². Falmata dai bata ce komai ba bayan gaisuwar da ta mikawa dogarin har da risina masa, sannan ta hau gyare gyaren dakin tana yi tana satar kallonsa domin gani take kamar wani abu zai mata.
Muhsee
n ne kadai zaune a dinning domin kowa ya karya a kama gabansa, wayar makkale a kunnensa yana ta fira da matarsa sai faman zuba murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin nishadi. Sai da ya gama breakfast din sannan ya yanke wayar ta taso ya nufo gurin Amm
y yana fadin.
“Wai har sun wuce ne?”
Da kallo Ammy ta bishi tana murmushi har ya karaso kusa da ita ya zauna a kasa.
“Ka dade kana bachi ne shiyasa”
“Gajiyar jiya ce, gashi kuma yau zan kama hanya shiyasa na tsaya hutawa”
Shiru tai na yan
mintuna kamin ta kalleshi ta ce.
“Yau zaka koma kenan?”
“Eh daman Mama Fulani kawai na kawo, ba dan ma yamma yayi ba ai da tun jiya zan koma dan ina da aiki yau”
“Ai ka kyauta shi Aliyu ya dauke mana kafa ko?”
Muhseen yayi murmushi kamar ba za
i ce komai ba sai kuma ya shafa kansa ya ce.
“Shi ma zai zo soon da Matarsa”
Ammy ta tabe baki.
“Shi dai ya sani, babu ruwansa da dangi daga Momy sai Fulani su kawai ya sani a rayuwarsa, ko da yakeba laifinsa ba ne laifin Fulani ne da bata nuna
masa ba”
Ammy ta karasa maganar tana aje wayar hannunsa.
“Ko da yake ga Shattima ne nan muna fama da shi, idan na ce yaje gurin yan'uwa kamar na kira masa mutuwa, sai dai azo a iske shi, wani irin jin kansu suke kamar wasu Sarakuna”
“Ammy ai kara
ma Shattima da Aliyu, tun da shi zai zauna ayi fira da shi kuma zai sakewa kanensa Fuska, Aliyu kuwa idan kika ga yana fira to da Mama Fulani ne ko matarsa ko Momy sai kuma Abba”
Ammy ta tabe baki.
“Uhm Abunda yai Aliyu shi yai Shattima idan ya gank
a ne yake nuna shi na kwarai ne”
Har Muhseen ya bude baki zai yi magana sai ga Iya ta shigo falon fuska daure.
“Ranki ya dade wai yarinyar nan za a bari tai ta kula da dakin yan uku?”
Ammy ta mata wani kallo cike da kasaita.
“Akwai wata matsa
la ne?”
“Ranki ya dade ni kam sam ban yarda da ita ba, kuma yarinya ce karama ina zata iya wani abun kirki, yanzu ga masu aiki bila'adadin a gida amman ace sai an dauko wata daga can waje ta zo gyara dakin jikokin Mai Martaba?”
Kallonta kawai Ammy ta
ke na wasu yan dakiku kamin ya bude bakinta cike da kasaita ta ce.
“To yanzu challenge dina kike yi Iya? Ko umarni kike ba ni?”
Da sauri iya ta risinar da kai.
“Ba ko daya ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya, shawara ce kawai ni kaina idan a
ka bar ni zan iya kula da su”
“To Mahaifinsu yace baya bukatar kowa ya kula masa da su a nan sai daga waje, kuma shi yace baya son tsohuwa ko mai ƴaƴa, sai ki same shi ki bashi shawara”
Kasa kasa Iya ta watsawa Ammy harara tana wani kashe ido.
“R
ana na zuwa Zainabu”
Ta fada a ransa sannan ta juya ta fice bayan ta bawa Ammy hakuri. Sai da Iya ta fice sannan Ammy ta daga kai ta kalli Katuwar kofar ta dauke kai ta mike ta nufi hanyar dakinta.
Tsab Falmata ta gyara dakin yaran daman can ba datt
i yai ba sai dai kullum sai ta tisa gyaran ne ta goge ta saka turare ta canja sanin gadon yaran, tana gamawa ta fice ba tare da ta yi ma kowa sallama ba. Sai da ta fito daga Masarautar gaba daya sannan ta samu sallama da natsuwar zuciya domin a yanzu har n
umfashinta take jin ya daidaita tsabanin idan tana gida bata son yin numfashi da karfi wai kar su ji ace ta yi laifi. Ta mika kafa sai tafiya take ita kadai a titin da babu mutane sosai, idan ka cire kofar Masarautar da a kullum take cike da mutane sauran
makotansa kowa yana cikin gidansa sai idan fitar ta kama, unguwar manyan mutane ce mai kama da GRA, ko'ina manyan gidaje ne gwanin sha'awa.
Sai da ta shigo cikin gari sannan natsuwarta ta kara daidaita domin ta fi son unguwarsu fiye da wacan da take ga
nin kamar wata rana za a iya sace ta a can, da ganganta ta rage tafiyar da take ta soma tafiya kadakadan tana saurarin wakar Sirleem dake tashi a shagon wani mai charji, cikin zuciyarta take bin baitin wakar tana jin muryarsa na shiga har cikin kanta.
*
🐄
🐄
FULANI
🐄🐄
*
By Khadeeja Candy
*Fadime dabam ta kauyen Katsina ita ce take jin busar sarewa. Falmata dabam ita ce ta Yola mai aikin raino a gidan Sarki, sai dai dukansu ana musu inkiya da Fulani. Fatar kun gane za ku daina rudewa
😀
*
*4*
SIRLEEM POV.
“Hajiya ina jin kamar ba zan iya jira har Nana ta kare Karatu na aureta ba....!”
Ba Hajiya kadai ba gaba daya kanensa kallonshi su kai. Da Mamaki Hajiya tace.
“Ban gane ba?”
Ya cika ma bakinsa iska ya busar sannan ya shiga murza h
annunsa kamar mai shafa mai.
“Kawai dai bana iya jira, tana kula wasu bayan kuma kowa a Masarautar nan ya san ni zata aura, sannan ina ganin kamar yan gidansu basa son hadin nan nawa da ita idan abun ya kai wani lokacin za su iya lalata shi”
Ajiyar
Hajiya ta sauke.
“Gaskiya ne, za su iya lalatawa amman zancen tana kula wasu kar ya dame ka kai auren a haka ai zata daina kuma idan ka gani ka rika magana”
“Na ganta da Deen din nan da yake zuwa duba yaran Shattima, na je har Part din su na yi maga
na babu wance komai karshe ma Hajiya Karama ta taso tana fada ni wai ina takurawa Nana kamar wani ubanta”
Hajiya ta yi murmushi mai kama da dariya.
“Kar hakan ya dame ka Sirleem kai dai ka aureta kawai komai zai wuce”
Ya kalleta cike da gajiyar j
in abunda take yawan nanata masa idan yai mata complain akan Nana.
“But Hajiya miyasa dole sai Nana? Tsakanin da Allah neman auren nan na saka kaina ne kawai saboda kin tirsasa ni amman ni kaina yarinyar nan bata kwanta min ba, ni kuma na fara gajiya g
askiya ba zan jure daukar wulakanci a gurin kowa ba na fi karfi haka, dan kawai tana yar sarauta ubanta yana sarki mahaifiyarta tana matar sarki yayanta yana dan sarki ba zan dauki wannan wulakanci ba na fi karfin wulakanci a gurin kowa ni”
Ya fada yana
daga kafadunsa, Rima ta tabe baki tana ture kofin tea dake gabanta tare da kallon yayan nata.
“Ni kaina ba son auren nan nake ba, dan dai kawai Hajiya ta matsa ne akan ayi, amman miye amfanin hada alaka da makiyi alakar ma ta aure haba dai...”
Murm
ushi Hajiya tai ta taso daga kujerar da take zaune ta dawo bayan Sirleem ta tsaya.
“M2 ba haka duniya ta sanka ba? Kai a yadda kake Celebrity sai kaje ka auri wacce bata kai ba? Ga yar sarauta yar masu naira kuma kyakkyawa yarinya mai kurciya a gidanku
? Ba ka lura ba? Maran manyan mutane suna auren yar manyan mutane? A yadda kake sannen a duniya ai kamata yai ace ka auri yarinyar da ta isa gaba da baya, taya za a tashi maganar da kasan zata iya saka Mai Martaba a cikin wani hali bayan gashi kwance ba la
fiya? Baka tunani ya takama mu sakawa Mai Martaba da irin hallacin da yai mana? Idan mahaifiyarta matar sarki ce kai ma taka uwar matar sarki ni da Zainabun Jirgi daya ya dauko mu domin dukanmu Mai Martaba muke aure. Ke kuma Rima da kike fadar hakan ai kya
utatawa ce wanda yai maka sheri sai ka saka masa da alheri, ba ni da burin da ya wuce na ga Sirleem ya auri Nana a yanzu ku karfafawa dan'uwanku guiwa ba wai ku sare ba”
Ta karasa tana kallon Rima. Sirleem ya juyo yana kallon mahaifiyarsa tasa.
“Amma
n Hajiya ai ba Nana ce kadai yar sarauta ko yar masu arziki ba, akwai da yawa mi yasa ba zaki bar ni naje da kaina na zabi wacce tai min ba?”
“idan zaka auro yar sarkin Makka, dan arzikinsu da Sarauta ba ka cika min burina ba matukar baka auri Nana ba,
idan kuma zaka auri yar sarkin talauci na duk duniya bayan ka auri Nana to ba zai tana damuna ba, ni dai burina Nana ta zama uwargidanka”
A hankali ya aje numfashi yana kallon kanensa wanda shi ma kallonsa yake suna mamakin furucin mahaifiyar tasu. Talb
a ya ce.
“Amman Hajiya miyasa?”
“Saboda ta wannan hanyar ce kawai zan iya sakawa mahaifinka da abunda yai mana”
Gaba daya kanensa mata su uku tashi sukai daga dinning, kaf a duniya basa da makiyiya irin Ammy wato uwargidan Mai Martaba, su kam ba
su da dalilin na cewa ala dole sai yayansu Sirleem ya auri Nana ba bayan shi kansa ba sonta yake ba. Da kallo ta bisu tana murmushi kamin ta kalli Talba ta ce.
“Raheen a kira min Kulu”
Tana fadar hakan ta nufi hanyar dakinta cikin wani irin taku kam
ar wacce ba zata mutu a saka a kasar ba, tsadadar shaddar dake jikinta sai motsi take tana wani maiko. Tashi Talba yai ya fita domin zuwa kiran Kulu kamar yadda ta Umarta, Sirleem kuma ya ciro wayarsa daga aljihu yana kallon kiran Mansura da ke shigowa way
arsa.
Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta fuska babu annuri kamar ba ita ce dazun ta gama dariya ba, a zahirin sarkar gold din dake wuyanta wacce ta sauko har saman kirjinta take kallo a badini kuma zuciyarta na can wani gurin tana wani tunani na d
abam, stool din madubin ta ja ta zauna tana cigaba da kallon kanta abubuwan da suka faru a baya take tunawa, ta dayan bangaren kuma tana kitsa yadda wasu abubuwa za su tafi a nan gaba. Yanayin yadda take motsa bakinta kadai ya isa ya sanar da cewar zance
zuci take.
“Shigo”
Ta fada tana dauke kai bayan an kwankwasa dakin minti uku da suka wuce. Kulu ce ta shigo dakin tana sanye da doguwar riga ta atamfa an mata irin dinkinsu na tsohu kanta lullube da mayafi, gaban Hajiya Bilki taje ta zauna tana mika
mata gaisuwa.
“Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya, Sardauna yace kina nemana”
Tashi Hajiya tai daga kan Stool din ta koma saman shimfidarta da ke gefen gado ta kishingida tana kallon Jekadiyar ta ta.
“Kulu wane Likita ne yake zuwa duba yar
an Shattima?”
“Wallahi ban san shi ba ranki ya dade”
Wani kallo Hajiya tai mata.
“Taya za'ayi kina cikin masarautar ace baki san masu shiga da fita a ciki ba?”
“Ranki ya dade na ga kamar bangaren Ammy ne, ni kuma na fi kula da abunda ya shafi
bangarenki ne Allah kara miki lafiya”
“This is nonsense, Ammy da bangarenta ba a cikin masarautar nan suke ba?”
Hajiya ta fada a tsawace har tana tashi zaune fuska babu annuri.
“Ciki suke Allah ya baki yawan rai, tuba nake”
Cewar Kulu tana kar
a noce kai kasa.
“Kina da matsala Kulu, duk abunda ya kamata ki saka ido akai ba kya yi”
“Zan bincika ko waye shi Allah ya huci zuciyar ki ya kara miki lafiya”
“Kira min Jarma”
“An gama ranki ya dade”
Kulu ta mike da sauri ta fice daga daki
n ganin yadda Hajiya ta hade rai kamar bata taba dariya ba. Ba a dauki dogon lokaci ba Jarma ya shigo dakin yana sanye da babban riga ga wani uban rawani a kansa, inda Kulu ta zauna ya zauna tana kallonta hankalinsa kwance sai dai har ya zauna ta kira shi
ya amsa ta kora masa bayani bata kalleshi ba.
“Jarma”
“Hajiya”
“Akwai wanda ke son shiga tsakanin Sirleem da Nana”
“A cikin masarautar nan yake?”
Jarma ya tambaya cike da mamaki, sai a lokacin ta kalleshi.
“Bare ne, yaron da yake zuwa d
uba yaran Shattima”
Jarma yayi murmushi.
“Doc Deen? Kar hakan ya damu Salim, wayayyace kawai irin ta yan zamani ke kinsan ai ba zan bari wani ya dauki hankalin Nana ba”
“Idan ma ka ga zai kawo mana matsala ko wasa, aka yi masa sanadi da gidan nan
”
“Baki da matsala da wannan Hajiya Salim ya cigaba da neman yarinya babu abunda za a fasa”
Ta dan yi murmushi tana kallon wata doguwar Fulawa dake gabanta.
UNCLE A A POV.
Ya yamutsa shinkafa da waken dake gabansa a kwano yana bata fuska.
“Anti Rabi sai ayi ta mana wake da shimkafa ba wani canji”
Anti Rabi dake aikin damawa dabbobinta kasari ta yi dariya.
“Hmm Unclen dinsu wani lokacin iskancin ka yawa yake, wani na can be samu kamar wannan ba amman kai ka raina, da alama dai kana d
a kudin cin wani abinci shiyasa”
Ya shafa kansa yana yar dariya.
“Wallahi kuwa wata yar marasa sanin darajar naira na samu nai mata na yan talakawa na ci kudinta”
“Ban gane yar marasa sanin darajar naira ba”
Yayi dariya a karo na biyu sannan ya
labartawa Antinsa yadda ya yaudareta.
“Amman dai Uncle din yara baka da tausayi”
“Wane irin tausayi kina ganin yarinyar nan kin san yar masu abunce ce karamar yarinyar yar secondary school ta ciro kudi sun kusan 50k ta bani 5k ya maida saura, uwayen
su ne barayin Jihar mu ai”
Ya mike tsaye yana ciro kudi, 2k ya cire a ciki ya mikawa Yayar tasa sannan ya maida sauran aljihu.
“Ni bari naje waje na ci abu mai kyau”
“Ni wannan aikin na ku yana bani mamaki kuma aiki a restaurant amman ba zaku iya
cin abinci a ciki ba?”
“Ai wannan mutumen be da kirki ko ruwansa ka sha sai ka biya shi, zaka ci idan kana so amman zai cire a cikin albashinka”
“Allah dai kyauta ni kam ban taba gani ba”
“Ai ina samun wani aikin zan bar na shi Wallahi”
“Allah
dai ya kawo rabo mai amfani”
Da amin ya amsa sannan ya fice daga gidan. Abun ka da unguwar mai mutane yana fita abokasa suka fara dago masa hannu.
“Sai Sardaunan samarin Yola”
Ya nufe su yana dariya.
“Amman na talakawa”
Ya karasa ya basu
hannu suka gaisa sannan ya kara gaba ya siye alalen gwangwani gurin wata ya cika cikinsa a titi.
Washe gari ma fa yaje restaurant din sai da ya sake tararda Nana a inda ta saba zama, wannan karon ba bachi take ba idonta biyu suna hada ido ta watsa masa
harara ta kawardar da kai, a iya ganinta da yake yi a yanzu kam ya tabbatar karya take da tace yayanta ne yake cewa ta jira a nan, ya lura idan ta ga mutane sai ta boye fuskarta kar a ganta haka yai ta aikin raba ma jama'ar da suke shigowa abinci yana kal
lonta zuciyarsa na karantarta tana tsara masa yadda zai sake samun wasu kudin a gurinta.
Sai da ya koma gurin zamansa ya zauna sannan ya dauki biro da takaradar yai rubutu a kai ya dauki bottle water ya nufi inda take ya aje mata takardar a saman tebur
din tare da ruwan ya koma ya zauna yana kallonta.
Tun da ya nufota take turo baki tana harararsa har ya karaso ya aje mata