Showing 60001 words to 63000 words out of 304903 words
ganta da tulu sama
n kai ga kan maciji ya leko, mutane sai gudu suke, kamin ta isa gida har ta canja kammani.
“Bappppa wayyo Inna na bani na taro aljalina”
Ta kasa tashi tsaye gani ba take idan ta mike macijin zai iya saukowa, mutane aka fara taruwa ana kallonta tai z
aure a kasa sai rusar kuka take fuska duk da bace da majina da hawaye zuciya kuma kamar ta fashe dan tsoro, ita gaba daya bata dauka ma da gaske yana iya yin tsafi ba sai yanzu.
“Mike tsaye ki zafar da tulun”
Kowa abun da yake fada kenan, ita kuma ba
bu kuzarin mikewar tsaye gashi yace mata idan bata isa gida bata sauke zai cijeta.
“Yace sai na kai shi gida, ku dauke ni ku kai ni gida, wayyo Bapppaa na wayyo Bapppaa”
Ta fada tana ta yarfe hannu, idonta har ya kumbura saboda kuka.
FAL
MATA POV.
Da tunani kala biyu Falmata ta isa gida, tunanin saukin kai da jindadin kadeta da M2 yai ga kuma kiranta da Ammy tai ta mata tambayoyi, ko miyasa tai mata haka oho. Sosai ta so ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta labarta mata yadda ta ga M2
sai ta tuna da Baba ya mata iyaka da gidan. Hakan yasa tai hanzarin cira kafa ta isa gida, da zimmar ta gama aikinta dan ta samu isa Islamiya da wuri ta labarta musu. Ko da ta isa gida har Gambo ta sanar da sakon Ammy ta bar gidan dan ita abun hawa ta hau
ba kamar Falmata ba da take tafiya a kafa.
Falmata na isa ta manta da wani kunci da tsoron fada ko wani abu, ta hau bawa Naja labarin yadda ta ga M2.
“Dan Allah matsa can mahaukaciya, hala M2 ne banza da zaki ganshi a bagas, sannu kakar farin jini
, dan kin ji ana cewa kina da farinjini shine kike wani karya kin ga M2 mahaukaciya”
Ko kadan bata ji abun da Naja ta fada ba, amman a yanayin yadda take harararta take jan tsaki tasan karyarta tayi, hakan yasa Falmata ta kara boye hular da ya bata a ci
kin jikinta ta mike tsaye cikin rashin jindadi ta nufi dakinsu. Tumba dake zaune bakin kofar dakinta ta bushe da dariya.
“Wallahi yarinyar can ta fara haukacewa, mugun son M2 da take ne yasa ta fara ganin mutane na zame mata haka”
Naja ta ja tsaki.
“Ko mai wankewa M2 takalmi ta isa ta gani balle M2, ita fa yadda ake fadar tana da farin jinin nan wani jin kanta take”
“Kira min ita”
Tumba ta fada tana dariya, daga inda Naja take zaune ta kwala mata kira.
“Ke kurma zo ana kiranki”
Falma
ta har cikin ranta ta ji sunan, wani abu na rashin jindadi ya ratsa zuciyarta, ta saka hular M2 can ciki bakkon kayanta sannan ta fito ta tsaya bakin kofa jiki ba gwari tun da babu wani abincin kirki a ciki.
“Ke yar kurma, dazun Gambo ta zo tace zaki r
ika wuni can kina rainon yara”
Tumba ta fada mata tana mata alama irin na kurame. Naja ta saka dariya.
“Ban cin kurmanta har da hauka na son kamaki, kin fara ganin mutane kina ce musu M2 ko?”
A nan ma Tumba ta saka mata dariya, a gurin Falmata ta
duka ta fashe da kuka, ba karyatata da suke take ji ma ciwo ba, kiran da kurma da suke a yanzu.
“Ji munafuka salon a shigo ace wani abu Umma tai miki kike kuka mu kuke dariya ko? Da shegen baki kamar zunubi”
Naja ta fada cikin tsawa, sai Falmata ta
mike tsaye ta shige dakinsu ta cigaba da kuka tana rufe bakinta dan kar sautin kukanta ya fito.
Sai da tai mai isarta sannan ta fito ta zuba surfe ta fara, sai da ta surfe tiya da rabi sannan ta shiga tai wanka ta saka uniform dinta na Islamiya ta dauk
o qur'ane ta da littafai ta fice.
Kusan kullum cikin rashin jindadi taje zuwa makaranta, saboda rashin jin da take a yanzu, idan akai karatu sai Khadija ko wata ta rada mata abun da Malam ya fada a kunne sannan ta ji, sai kuma idan Malamin yayi da karf
i, Falmata ba yarinya ce mai yawan surutu ba, amman hakan be hanata fadawa yan ajin su cewar ta hadu da M2 ba, most of them sun karyatata wasu na fadin dan dai tana son shi sosai ne yasa ta ga mai kama da shi.
Haka dai ta bar Islamiya cikin rashin jinda
din yadda suka karyarta daman ta san ba za su yarda ba, ita ma dai a lokacin ta fara kwankwanto da gaske M2 ta gani ko mai kama da shi?
Ko da ta iso gida sai ta tararda wani tashin hankali, yaron da aka aiko yana tsaye yana jiran dawowarta Tumba kuma ta
yi wani shegen zama tana rawa da kafa. Ta shigo da sallama Tumba ta hau ta da matsifa.
“Ashe Falmata zuwa kike kina cin bashin garin kwaki a shago da sunana?”
Dakan shida-shida gabana yai, ta sani yau asirinta ya tonu, tabbas tana zuwa karba kuma i
dan ta je Tumba take cewa saboda tana jin kunyar tace ita zai bawa bashin gari.
“Saboda asan ba a baki abinci ko kuma dan ki bata min suna ni da ubanki? To ya aiko yace a bashi kudinshi bari ubanki ya dawo sai kin fadi dalilinki na bata min suna”
Ka
mar an tureta haka ta fadi gaban Tumba kamar mai neman gafara hawaye sai sallama suke a fuskarta.
“Dan Allah dan darajar Annabi karki fadawa Baba Umma, ki rufa min asiri, zan samu kudinsa yanzu na bashi, ki yi hakuri Umma ba zan, idan na sake ki kashe n
i, Umma wallahi yunwa take damuna shiyasa na ci bashin amman daga yanzu ko zan mutu ba zan sake ba, na rantse da Allah Umma, dan manzon Rahama ki rufa min asiri Umma ba zan sake ba har abada”
Tumba ta fisge kafarta tana kallon.
“Tafi idan Babanta ya
dawo za a fada masa”
Yaron ya juya ya fice, sai Falmata ta mike tsaye da sauri.
“Na bani na lalace na shiga uku wayyo ni Allah na Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ta furta ta karfi kuka na subuce mata, sai ta saka hannunta da sauri ta rufe bak
inta, da gudu ta shiga dakinsu ta fada kan shimfidar da take kwana.
“Wayyo ni Allah na yau asiri na ya bonu, wayyo Mama Mama ina ma ni na mutu ba ke ba, Allah ka karbi raina kamin Baba ya dawo Allah na shiga uku”
Ta fada tana yarfe hannunta hawaye s
ai zubo mata suke kamar ba gobe.
ZAINAB POV.
Ta dan yi shiru sannan tace.
“Na ce mishi ya bari har na dawo daga tafiyar da zan yi”
Ammy ta kalleta.
“Ni fa ina tsoron lafiyar nan Zainab, kin san kasar ba wani tsoro kuma ki ce za ki je g
arin cikin mutanen da ake fadar basa saka tufafi? Kina ganin ma za su aminta ki dauke su hoto ne?”
“No ba wai kai tsaye zanje can ba, zan sauka garin dake kusa da su ne, nai magana da mutanen tukuna sai na isa garin, kuma ko ban samu zuwa can ba ai ance
akwai manyan duwatsu a kusa da su da ruwa, kuma ance akwai Fulani irin masu yin bukka da gidan zana su zauna a kusa da su, ko da ban samu isa can ba na san ba zan sara abun dauka ba”
“To Allah dai ya tsare”
“Amin, Ammy dan Allah ki mata magana, ban
zan abun da mutunen nan yai mata ba, ta ki ta saurare ni, ni kuma ina son shi, shi yanzu yace yana son ya turo kuma ya sanar a gidansu amman sai ya samu tabbaci daga gareni”
Ammy ta yi murmushi.
“Karki samu damuwa, zan yi magana da ita, idan ta amin
ta sai a sanarwa yan'uwan mahaifinki”
“Na gode Ammy”
Mikewa tai tsaye tana sanye da riga da wando English wears, kanta sanye da dankwalin nan da ake yayi blue.
“Bari na duba dakinta idan tana nan sai na turo miki ita”
Kai kawai Ammy ta daga mat
a, ta maida dubanta gurin tv dake dakinta, kallon kawai take amman hankalinta baya can, bata da damuwar da ta wuce ta Mai Martaba a yanzu, a iya tunaninta ta rasa gane abun da yake damunsa, gashi idan an gwada yi masa na hausa sai abu ya karu a maimakon ra
guwa. Kiran wayarta nd ya katse mata tunanin da take, sai ta mika hannu ta dauka.
“Assalamu Alaikum”
Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren.
“Wa'alaiki-Assalam, Ammy barka da yamma”
“Yauwa Ra'ees ya gida”
Ta fada cike da kasaitar da ta zame mat
a jiki.
“Al-hamdulillah Ammy an samu wata, amman dai ba mu je, sai dai marikiyar yarinyar tace zata iya aura masa ita”
“Ka fada mata matsalar sa ne?”
“Eh ta ji komai, firar ma ta ji muna yi shine tace tana da ƴa zata ba shi, amman dai ba mu je ba
tukuna”
“To yayi kyau, amman fa ba sai kun bayyana dan wane ba, kuma ka yi duk abun da ya dace, karka bari Shattima ya ji komai, sai an kammala yadda ba zai iya ce mana aa ba”
“In-Sha-Allah Ammy”
“Na gode Allah ya maka albarka”
“Ameen”
Tana
kokarin aje wayar aka kwankwaso kofar dakin kamin a turo a shigo. Hajiya Balki ce Nana na biye da ita a baya, a baki kofa ta tsaya tana kallon Ammy sai cika take tana batsewa.
“Yanzu an kyauta kenan? Sai a dauke yarinya akaita gurin Waziri bayan kin s
an ita da Waziri ba jituwa suke ba?”
Ammy ta kalleta da mamaki kamar ba zata ce komai ba.
“An kaita gidan Waziri kamar wacce aka kai gidan yari? Kanen ubanta ne fa”
“Na san kanen ubanta ne ai, amman tun da bata son zuwa ai sai a kyaleta”
Ammy t
a dauke kai bata sake ce mata komai ba. Ganin hakan yasa ta juya ta fita Nana kuma ta zauna saman kujera tana matsar yatsun hannunta tana kallon Ammy. Ko da wasa Ammy bata kalle inda take ba har ta gaji dan kanta tace.
“I'm sorry”
Ammy ta watsa mata
wani mugun harara.
“Dakinki dai kike so ko? To gashi can idan kin mutu a haka rame a saka ki a ciki, tashi ki fata”
“Ammy ki yi hakuri....”
Bata karasa ba Ammy ta daka mata tsawa.
“Get out”
Ba shiri ta mike tsaye jikinta na rawa ta fice da
ga dakin tana fashewa da kuka.
_________________
Al-hamdulillah, a nan na kawo karshen free pages, duk mai son cigaban wannan labarin ya biya 300. Pages din da za su biyo bayan wannan na kudi ne ba kyauta ba, ko kun ganshi a waje na sata ne.
Patronize me if ku masoyana ne na gaskiya, show me that love.
Son so Fisabilillah.
*FULANI -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence to 08036126660 ƴan nijar za ku tura 500cf to +22790165991*
Wadanda ba su ac
count za su iya turo mtn card ta 08036126660 bana karbar transfer.
16
A gaban wani madaidacin gate ya faka motar, budurwar ta bude ta fita sannan ta budewa Falmata tana mata alama da ta fito.
Cikin rashin kuzari Falmata ta sako da kafafuwanta sannan
ta fito daga motar tana jin sanyin ace motar na saukar mata da mura, sai kokarin boye ledar hannunta take tana karewa na unguwar kallo, ba unguwar masu kudi bace haka kuma ba za a kirata da unguwar talakawa ba, irin unguwar nan ce mai kama da sabuwar unguw
a wance mutane ba su gama dawowa ba, domin akwai gine gine da yawa da ba a karasa ba, ga kuma ciyawa da tai yawa a ko'ina, tsakanin wani gidan da wani kuma akwa tazara mai tsawo ta filayen wasu mutane. Hannu ta saka a jakarta ta ciro makulli tana kikarin s
akawa sai gate din ya bude, ta dan bude ido da far'a sannan ta tura ta shiga.
“Shigo”
Bayan Falmata ta shiga ta rufe kofar gate din, arba da tai da wata hadaddiyar mota yasa murmushin fuskarta ya kara fadada da sauri ta nufi entrance har tana hadawa
da gudu, hakan kuma ba karamin tsoro ya ba Falmata ba, tana a wani gari da ba na ta ba, a wata unguwa kuma a sabon gida da matar da bata sani ba.
“Karaso mana ko kina jin tsoro ne?”
Matar ta fada ganin Falmata ta tsaya daga can kusa da gate din tan
a karewa madaidacin gida kallo. Sai da ta tura kofar falon sannan Falmata ta karaso kusa da ita
“Shiga”
Cikin tsoro da fargaba ta nasa kafarta a cikin falon, bayan ita ma ta shiga ta maida kofar ta rufe.
“Zauna a nan”
Ta nuna mata kujera, ciki
n rashin natsuwa ta zauna saman kujerar dake kusa da kofa.
“Mansura daga ina kike?”
Budurwar ta juyo da sauri tana kallon kofar kitchen din. Sirleem ne tsaye jikin kofar rike da gorar ruwa yana kallonta. Cikin murna ta karasa kusa da shi ta rumgume
shi.
“Oyoyo ban taba expecting zaka zo yau ba, what a surprise”
Ya dan kawar da fuskarsa daga kiss din da take kokarin yi masa yana kallon Falmata, juyawa ta yi ta kalleta sannan ta sake kallonsa tana kokarin kai hannu ta taba sajen fuskarsa, sai y
a rike hannunta ya tureta gefe ya dawo falo ya zauna.
“Na hadu da ita ne a tasha, an kawo min sako daga kano shi ne na je karba sai na hadu da ita, tun cikin tasha tana kuka har waje da na tambaye ta sai tace bata san kowa ba a nan gudowa tai”
Tun d
a ta fara maganar yake kallon Falmata yana jin kamar ya taba ganin fuskarta but zai iya tuna a ina ba ne. Ya kalleta a natse irin kallon da ita ta san me yake nufi. Sai ta nufo shi tana cire Veil din kanta.
“You know idan na ga mutum a damuwa ina son n
a taimaka masa, because ni ma na taba shiga a irin wannan matsalar”
Ya sake kallon Falmata da tai mutuwar tsaye tana kallonsa. Shi din ne ko kum har yanzu idonta gizo yake mata? Ko kuma masu kama da shi ne take gani? Ai ta baro yola ya akai ta ganshi a
nan?
“Me yasa ta gudu daga gidansu?”
Ta zauna daf tashi har jikinta na gogar nashi.
“Ya za a yi na sani yanzu yanzu fa na hadu da ita ban tambaye ta ba”
“And kika bata masauki, what if karya take? Kika san abun da ya rabota da gidan?”
“Ban
sani ba, amman zan sauketa a nan zata zauna tare da ni, tana bukatar taimako”
“This is my own house not yours, hope kin san da wannan?”
“And that mean?”
“Ba zata zauna a nan ba”
Ya fada mata kai tsaye yana kallon cikin idonta, fuskarsa babu an
nuri.
“Fine idan baka son ta zauna tare da mu, zan sallame ta, amman rayuwarta zata iya fadawa a hadari ka sani”
Ya mike tsaye yana shafa kansa.
“Idan rayuwarta ta fada a hadari ina ruwanki? Kin santa ne? Idan kina tsoron ta fada a hadari then t
ake her to her parents house”
“Amman ka san abun da yasa ta baro gidansu? Duk ba mu sani ba bata son zama kusa da kowa na ta that's why she run”
“Kin fi kowa sanin hali da mace take fadawa idan ta rubu da iyayenta, uhmmm?”
Ta yi shiru tana kallons
hi.
“Lokacin da kika gudo daga gidan iyayenki da kika fada mugun hannu ba karuwanci kika fara ba? So on kika bata future dinki that's why Hajiya ta hana na aureki, kowa kallon karuwa yake miki kina son ki koma cikin familynki kin saka saboda kin lalata
alakarki da su, look at her bata wuce 15 ba, and if you want to help her take her back to her parent house”
Hawaye ne masu zafi suka fara sauko mata, ta kalli Falmata a tsawa ce tace.
“Ke tashi ki fita”
Falmata ta kasa motsi balle ta mike tsaye t
a fita kamar yadda ta umarta, bata ji duka kalmansu ba amman ta ji wannan tsawar kuma ta ji turancin da Sirleem yai mata a karshen maganarsa da ya karasa a fusace, and now hawaye Mansura take, hakan na nufin matsala ta samu da mijinta a dalilinta.
“As h
ow? Ki kawo ta unguwar da bata san kowa ba kuma ki ce ta tashi ta tafi idan aka tambaye ina ta fito tace a nan gidan ko?”
“To ya kake son nai mata?”
Ta fada a tsawace tana hawaye, tass ya wanke mata fuska da mari.
“How dare you, dan ina son ki ba
shi zai baki damar yin duk abunda kike so da ni ba, kamar yadda so na be hanaki kula wasu mazan ba”
Sai a yanzu ta gane fushinsa ba na shigowa da Falmata kawai ne ba, har na fitar da tai da Yasir, durkushewa tai a gurin ta fashe da kuka. Falmata dake r
ike da fuskarta sakamakon marin da akai wa Mansura ta mike tsaye ta sauri ta nufi kofa.
“Ke....”
Ya kirata a watsawa sai ta juyo jikinta na rawa ta fashe masa da kuka tana girgiza kai. Kallonta kawai yake kamin ya nuna mata kujera alamar ta zauna, s
ai ta dawo kusa da kujerar ta zauna a kasa tana hawaye. Ganin tana ta boyon hannu a hijab ga hawaye sai sauko mata suke yasa