Showing 18001 words to 21000 words out of 304903 words
ruwan da takardar ya koma, a zatonta zai ce yau ma sai ta biya kudin zaman dana bachi amman bata ji yace mata komai ba, sai dai ta
lura duk abunda yake idonsa na kanta.
“Ni nace ka kawo min ruwa ne”
Ya fada tana turo baki cikin sautin da ita kadai zata iya jin kanta, na kusa da ita ko kuma mai kallonta sai dai yaga bakinta na motsi sai hararar da take watsa masa ta isa ta sanar
masa cewar da shi take. Hannu ta kai ta dauki takardar ta jefar a kasa tana cigaba da turo baki ita ala dole ga shagwa6a66iya.
“Ba za a karanta ba”
Daga can inda yake zaune ya gwalo mata ido ya hade rai yana mata alamu da ta dauki takardar ta karant
a ko ya daketa, sai ta make masa kafada tana murguda masa baki, sai da ya unkura kamar zai taso ta karaso inda take sannan tai saurin kai hannu ta dauki takardar ta bude.
“Idan kina so zan iya kai ki wani guri inda zaki rika boyewa ba tare da kowa ya s
ani ba, amman nan ai public place ne kowa zai iya ganinki, idan kin aminta fita waje mu yi magana”
Da sauri ta dago ta kalleshi tana gyada masa kai alamar eh ta amince din, da ido yai mata alama da waje sai ta dauki school bag dinta ta nufi hanyar fita
tana waigensa. Sai da tai kusan minti biyar da ita sannan Sardauna ya fakaici idon mutane ya tashi ya fita. Can gefe ya hangota ta juya baya dan kar a ganta sai boye boyen fuska take.
“Ke”
“Ni ba ke ba ni Nana Aisha”
“To ina ruwana da wani sunanki
”
“To nima ina ruwana da kai”
Ita ta amsa masa ta shigar da yai mata maganar wato da fada fada, sai yai kwafa ya juya alamar zai tafi ya barta, da sauri ta riko hannun rigarsa.
“To akwai ruwana”
Ya sake yin kwafa sannan ya kalli security camer
a dake gurin ya kalleta.
“Idan kina so zan iya kai ki gidan ku sai ki boya a can idan lokacin da direban ki zai dauke ki yayi sai na dawo da ke”
“Ina zuwa”
Ta fada kai tsaye cike da jindadi, kallonta ya tsaya yi a ransa yana ayyana cewar idan shi
barawo ne sai ya sace ta salon alon.
“To ai zamu aro babur da zamu je can unguwar”
“To aro”
“Zaki hau?”
Ya tambaya da mamaki dan be dauka zata yarda ba.
“Eh”
“To ai kudi ake biya kamin a bamu aron babur din”
“Nawa?”
Tunani ya tsay
a yi kamin ya ce.
“2k kuma a can gidan da zaki zauna sai kin biya kudin zama”
Ta dan bata fuska.
“Nawa?”
“3k”
“Toh, ai dai ba zaka sace ni ba ko?”
“Eh shekararki nawa?”
“16”
“Amman dai ke wawuya ce”
Ya fada yana dariya a ransa
sannan ya juya ta nufi cikin restaurant din, abokinsa Mu'az yai ma magana ya karbi makulin mashin dinsa sannan ya fito ya same ta a inda ya barta.
“Ki fita can titi sai na zo na dauke ki”
Ba musu ta kama hanya a ranta tana jin zafin wawuyar daya kira
ta dazun, karasa yai gurin da suke aje abun hawan a gurin ya bude mashin din sannan yasa masa key yai tashi mashin din sannan ya fara tukawa ya fito da shi bakin titi can ya hangota ta boya a kusa da wani shago, karasa yai gurim ya faka mata ta hau yana f
ara tafiya ta rirrike shi gam ta boye fuskarta a bayansa, kusan sai ta rantse a rayuwarta bata taba hawan achaba ba, iyakarta keke shi ma tana yin wayo Ammy ta hana ta hawa saboda tana mace.
“Ke dallah sake ni kin wani rike ni kamar yar iska haka zan s
higa da ke a unguwar mu kina tabani, ni ba dan iska ba ne ba a saba ganina da mace ba balle kuma ta rike ni”
“To ni ba tsoro nake ji ba ko kuma ni aka ce masa yar iska ce, ni yar iska ce kai ne dai dan iska mai sato yarinyar mutane kaje ka kaita wani gu
ri ta boya”
Ta fada tana turo baki har lokacin bata yarda ta dago kanta ba. Tafiyar ba tai nisa ba ya faka mashin din gefen titi ya sauko ya fuskance.
“Ni ne ma dan iska mai sace yaran mutane? Ai ke ce stupid girl mai guduwa daga makaranta kina boya
a wani guri, kuma ba zan kai ki din ba na fasa”
Ya karasa yana dangwararta da yatsansa.
“Ai Wallahi ba zan sauka ba, zan maka ihun ka yi satar mace”
Yadda ta daddage kan mashin din kamar na gidansu tana watsa masa wani kallo ya sani sarai zata iy
a iya masa ihun abunda ba halinsa ba, kwadayi yaja masa bala'i, ya san ma it's risk tsayinsu a gefen hanyar dan wani wanda ya santa zai iya ganinta da shi, ba shi da wani option da ya wuce kaita gidansu din ko kuma maidata inda ya daukota. Da farko yayi ku
dirin maidata inda ya daukota sai dai zuciyarsa na son kudin nata da yake gani kamar na banza a dole ya daure ya cije ya cigaba da tafiyar idan ta riko shi ya buge hannunta har suka kusa isa unguwar sannan yai mata dabara da ta rike karfen mashin din ta sa
ke shi.
Bata yarda ta dago fuskarta ba sai da ya faka mashin din kofar gidansu ya sauka sannan ita ma ta sauka tana wani kyankyamin unguwar balle kuma da aka shiga cikin gida har wani dage kafa take sama sama kar ta taka kasa.
Shi yai sallama Anti Rabi
dake aikin hada kwado ta amsa masa, ita kam banda aikin bata fuska da karema gidan kallo babu abunda take. Anti Rabi ta bishi da kallo har ya shiga dakinsa Nana na biye da shi ya dauko tabarma ya shimfida mata bakin kofar Anti Rabi.
“Zauna a nan”
Ta
karewa tabarma kallo tana kyankyami.
“Wallahi ba zan zauna ba, wannan gida duk kazanta ni ba na son nan”
Ya zaro ido
“Kan uban gidan na mu ne duk kazanta? Idan ba ki zauna ba zan bata miki rai”
Ya fada a tsawace amaimakon ta ji tsoro kamar ya
dda yaran Anti Rabi suke idan yana musu fada ita sai ta make kafada.
“Wallahi ba zan zauna ba, gida duk datti gidan dokin mu yafi wannan”
“Zan zane ki zan miki bulala”
Ya fada yana nuna mata icen dogon yaron dake gidan, sai ta sake make kafada.
“Wallahi ba zan zauna ba, kuma ba zan koma can ba, kuma ba zan biya kudin ba”
“Na rantse da Allah karya kika sha”
Ya fada yana buga kafa a kasa dan kudin sune damuwarsa. Anti Rabi ta tashi ta shiga dakinta jikinta na bari ta kwalowa kanen nata kir
a.
“AA...”
“Tsaya nan sai na fito”
Ya fada mata bayan ya amsa kiran Anti Rabi, sannan ya nufi dakin ya cire takalminsa ya shiga cikin rada Anti Rabi ta fara masa magana har lokacin jikinta rawa yake dan tsoro ya gama kamata.
“Ina ka dauko wan
nan yarinyar?”
“Ita ce wanda na baki labari jiya”
“To miyasa zaka dauko ta ka kawo nan? Kidnapped dinta zaka yi?”
“A'uzubillahi haba Anti kamar dai baki san ni ba? Ce mata zan kaita inda zata boya sai ta biya kudin”
Hannu biyu Anti Rabi ta hada
tana rokonsa.
“Dan Allah dan Annabi ka rufa min asiri ka maida yar mutane, karka jamin masifa ka jawa kanta, daga ganin yarinyar nan yar manyan mutane ce, ka duba kaga irin kallo da ake mana a unguwar nan na masu rufin asiri amman ita kallon kazamai ma
take mana har da cewa gidan dokinsu ya fi gidan nan kyau ka rufa min asiri ka maida ta karka sake kallonta ma kar sheidan ya sake raya maka wani abun”
“Anti Rabi.... ”
“A a bana son jin komai indai kana jin maganata ka maida yarinyar nan inda ka dau
ko ta dan Allah”
Juyawa yai ya fito daga dakin, sa cin karo yai da Nana tsaye a kofar dakin da alama labe tai musu.
“Wallahi ba zan koma ba, sai direbana ya zo kuma ba zan zauna a nan ba”
Anti Rabi ta fito da sauri ta hade hannayenta ta risina ha
r kasa tana rokonta.
“Dan Allah dan ma'aiki ki rufa mana asiri yarinyar nan ki koma inda ya dauko ki”
Ta make kafada daya lallai ita ba zata koma ba.
“Sai idan direbana ya zo”
“Haba Anti ya zaki duka kina rokon yarinya kamar wannan dan Allah ta
shi”
AA ya fada cike da jin haushin yadda yayar tasa ta risina tana rokon Nana, wanda hakan ba karamin dadi yai ma Nana ba domin ko a gidansu aka risina mata dadi take ji tana ganin an bata girma yadda ya kamata tun da Mai Martaba ba ma haka ake masa. A
nti rabi bata bi ta kansa ba ta ce.
“Yanzu ya kike so a yi?”
“Sai ya duka ya roke ni yadda kikai”
“Ni din? Ashe ko zaki tsufa a tsaye”
AA ya tambaya yana kallonta da mamaki ganin take kokarin zame masa kashin wuya.
“Ba zan zauna akan wannan
ba”
Ta nuna tabarma sai Anti tace.
“Idan na dauko miki katifa na shimfida miki a waje zaki zauna?”
Tayi wani abu da kai kamar mai yanga sannan ta amsa da eh. Abun ka da mai nema cikin sauri da kuzari Anti Rabi ta dauko katifar dake kan gadonta ta
aje a waje ta dauko zanin gadon data wanke ta ninke ta shimfida mata har da su filo. Sai da Nana ta karewa katifar kallo sannan ta cire takalminta ta hau ta zauna tana kara karewa gidan kallo.
Anti Rabi ta kuma ta cigaba da hada kwadon da take cikin ras
hin natsuwa dan ita tsoro ma take kar wani wanda ya santa ko ya san yan gidansu ya shigo ya ganta a gidanta.
Bayan ta gama ta zubawa AA ko da wasa batai ma Nana ta yi ba dan ta san ba zata ci ba, ita dai tana zaune tana kallon yadda AA yake aikin auna kw
adon a bakinsa kana gani kasan yunwa yake ji.
“Gashi nan ba kiba sai mugun ci”
Ta fada a ransa, kamar ya san ta yi maganar sai ya juyo ya kalleta.
“Za ki ci?”
“Allah ya tsare ni da cin ragin abincinka kazami da kai ma”
Ta fada tana dauke ka
i, har cikin ransa ya ji zafi ya kalli Anti sai tai masa alama da yai shiru, a iya tunanin Anti Rabi yarinyar tana neman rigima ne ayi mata wani abu taje tace an taba ta babanta yasa a dauresu ita da AA duk kuwa da kasancewar bata san waye uban nata ba.
Sai karfe daya da yan mintuna direbanta ya kirata ya fada mata cewar zai zo ya dauke ta yanzu, sannan ta tashi wanda yai daidai ta dawowar yaran Anti daga makaranta.
“Ki ce masa ya maida ni”
Ta fada ta sigar Umarni kamar yadda take wa bayin gidansu
. Anti Rabi ta kalli AA dake aikin danna karamar touching dinsa tace.
“A-A tashi ka kaita”
Ba musu ya mike tsaye ya saka wayar aljihu.
“Ina kudin zaman da kika yi dana katifar duk sai kin biya”
Ta bude jakarta ta kirga kudin da za su yi 8k y
a mikawa Anti.
“Gashi na zaman da nai da na katifarki, ai ba gidanshi ba ne ba katifarshi ba ce”
AA ya saki baki yana kallonta.
“To waya kawo ki gidan? Ki bani kudina malama”
Ta maida ragowar kudin.
“Wallahi ba zan bayar ba, kai da kace min
ma kai dan iska”
Anti ta zaro ido.
“Subhanallahi AA”
“Na rantse da Allah karya take wannan yarinyar munafuka ce”
Ya karasa yana kara dangwararta a karo na biyu bayan wanda yai mata a titi.
“Kin gani ko haka dazun yai min a titi dan yace
na taba shi na ki wai sai dai na rika taba shi idan muna kan babur din hadda cewa yai zai sace ni”
Bayan kallon Anti Babu abunda AA yake, gaba daya kunya ta gama rufe shi shi da ko budurwa be taba yi ba yau ace wai yana neman mace ta taba shi, ji yai ka
mar kasa ta rabi biyu ya shige ciki, Anti ta kasa cewa komai sai kalloshi take da mugun mamaki.
“Kaje ka aje ta inda ka dauko ta”
Ta masa maganar da sigar da shi kansa ya san ba da wasa take ba.
“To”
Ya juya sululu ya fice, Nana ta risina ta
aje kudin da Anti ta ki karba saman katifar sannan tai mata sallama ta fice. Ko da ta fita har ya tashi babur din ita kawai yake jira, kamar dazun yanzun ma tana hawa ta sake rike shi sai da ya buge mata hannu sannan ta maida kan karfen baya ta boye fuskar
ta a bayansa.
Tun da suka kama hanyar bata ji yace mata komai ba, a tunaninta zai mata magana ko yai mata fadan karyar da tai masa a gurin yar'uwarsa amman sai taji shiru.
“Ni ba zan sake biyoka ba”
“Ki ga ma Uban da zai sake zuwa da ke, ko a rest
aurant din nan na sake ganinki sai na fadawa shugaban mu yasa an koreki”
Ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ba.
“Ka yi hakuri ba zan sake ba”
Be ce mata komai ba har suka kusa isa, sannan ya faka gefen hanya ya sauka kan babur din ya kalleta.
“Ba ni 5k dina, kin ga dai taimakonki nai ko? Dan Allah ki bani kudina dan Allah”
Bata ce komai ba sai kallonshi take. Hakan yasa ya koma rokonta ta sigar tausayi yana mata magiya a iya ganinsa idan ta tafi ba ta bashi kudin nan a yayi aikin banza ken
an.
“Haba baiwar Allah, ki ji tausayina kin ga nan ni maraya ne ba uba ba uwa komai ni nake yi ma kaina kuma gashi ba wani aiki sai na restaurant dan Allah ki ba ni kudin kinji?”
“Ba kace ba zaka sake kawoni ba”
“Zan sake kawoki, mota ma zan aro b
a babur ba kin san ya fi sirri”
Ya amsa mata da sauri.
“Ka iya mota?”
“Eh”
“Idan kana zo zan iya maida kai direbana sai ka rika kawo ni nan kullum idan lokacin tashina yayi sai ka maida ni gida”
“Da gaske?”
Ya kara masowa kusa da ita.
“Eh yau zan ce ma Ammy bana son driver din ta canja min wani”
“Kuma zata amince?”
“Eh”
“To kawo wayarki na saka miki number ta idan ta amince sai ki kirani”
Ta bude jakarta ta dauko iPhone yar yayi ta kunna sannan ta mika masa.
“To sa min
a nan”
Da mugun mamaki da kuma dan tsoro ya karbi wayar, how yarinya karama kamar ita ace tana rike irin wannan wayar? Lallai babanta ba karamin barawon kasa ba ne.
“Waya saya miki wayar?”
Ya tambaya bayan ya saka mata number.
“Ammy na ce ta
siya min bata siya min ba, Ya Shattima idan na masa maganar baya sai ya ce sai na gama makaranta, Hajiya Karama ce ta siya min?”
“Wacece Hajiya Karama?”
“Yayata ce”
“Waye mahaifinki Nana?”
Ya tambaya mamaki na kara bayyana a fuskarsa, har ta b
ude baki ta bashi amsa sai kuma ta fasa bata son ya san asalinta gudun kar ya tona mata asiri ko kuma ya sace ta.
“Wani ne ba shi da lafiya ma, baya son mutane idan an yi taro da yawa sai ya rika jin tsoro shiyasa baya fita muma ba kullum ake bari muna
shiga ba, ance wai sammu ne wasu kuma su ce jiface amman dai Ammy tace mu daina cewa haka mu rika cewa be da lafiya kawai”
Ya maida wayar a jakarta bayan ta kashe, wannan karon kallon tsoro yake mata sai a yanzu yake fahimtar yaren da Anti Rabi take ma
sa, wata nawa yana kokarin ganin ya canja wayar hannunsa ya siye ko ta 50k amman abun ya gagara, yau sai gashi yaga karamar yarinya da wayar 500k lallai mayan kasar nan ba karamin dadin rayuwa suke ji ba, ya raya a zuciyarsa a take sai yaji ya ba kansa tau
sayi matuka.
“How babur na maida ke”
Bata ce komai ba ta bude jakarta ta ciro 7k ya mika masa.
“Gashi”
Ya kalli kudin be karba ya ce.
“Wa yake ba ki wadannan kudin?”
“Hajiya Babba”
“Mahaifiyarki?”
“A a Step mother dinta, wani lok
acin kuma Hajiya Karama ma tana ni kudi sosai idan ta samu Ya Shattima ma yana bani amman ba sosai ba, sai Ya Sirleem shi ma yana ba ni sosai, ka karba”
Ya kara mika masa, ya dade yana kallon kudin da mugun mamaki sannan ya karba yana tunanin anya ma mu
tum ce? Ko dai garin shegen son kudinsa ya kwaso aljana? Yanzu akwai yarinya karama mai rabon kudi haka dan bata san zafin su ba?
Ya hau babur din ita ma ta hau baya suka cigaba da tafiya, be yarda ya isa har cikin restaurant ba ya sauke ta a titi ya shig
a ciki, ita kam bata ma shigo ciki ba sai ga direbanta ya zo daukarta sai kawai ta shige mota suka kama hanyar gida.
*
🐄🐄
FULANI
🐄🐄
*
By Khadeeja Candy
*5*
HAJIYA KARAMA (Zainab) POV.
Ta bude motar ta fito tana karewa gidan kallon ka
mar wani bakonta, ko da yake kusan gidan bakonta ne domin tun zuwanta na farko ba ta sake ba sai