Showing 30001 words to 33000 words out of 304903 words
Mai Martaba ya fadi ya mutu haka zamu tai zama cikin rashin hadin kai? Idan yau kika fadi kika mutu ni zan rika Nana ya kamata dai a gyara...”
Tana fadar hakan ta juya ta fice daga dakin rai a bace sai dai bacin ran na iya fuska ne be ka
i zuci ba. Ammy kuma ta ja dogon numfashi ta sauke ta lumshe ido. Ba tun yau indai ta hadu da abokiyar zamanta sai ta fada mata wata maganar marar dadi, me ya kawo maganar mutuwar Mai Martaba ko nata a nan? Kan abunda be kai ya kawo ba?
Sai da ta fic
e daga bangarensu sannan Shattima ya mike tsaye ya rufe system dinsa ya dauke ta ya nufi dakin Nana. Zaune ya same su ita da Zainab suna ta kyalkyalar dariya bakin kofar ya tsaya yana kallonta yana murmushi.
“Ya Shattima zo nan”
Ya karasa ya zauna d
ayan side dinta da ta nuna masa da hannunta.
“Me kuke kallo?”
“Comedy”
Ta amsa masa tana karbar wayar daga hannun Zainab ta mika masa. Kadan ya kalla ya mike tsaye.
“A sha kallo lafiya”
Ya juya ya fice, ita ma Zainab din ta mike tsaye.
“Bari naje mai wanka kamin na shirya kin gama”
“Okay”
Ta cigaba da kallon hankalinta kwance bayan Zainab ta fice. Shattima na fita daga dakin Nana ya nufi dakin da ya aje yaransa ya dauko su ya dawo da su dakinsu wanda Falmata tai masa tas sai kamshi
yake.
FALMATA POV.
Kamar wacce zata sanarda mutuwar wani haka ta shiga cikin gidan cikin tashin hankali da fargaba ga tsoron da ya cika mata zuciya har ya bayyana a fuskarta. Tun daga sallamarta zaka fahimci akwai damuwa da tashin hankali
a tare da ita balle kuma idan kai arba da fuskarka.
Kamar mai koyon tafiya haka ta karasa kusa da Tumba da ke aikin tsintar shinkafa ta risina kan ta ce komai hawaye ya fara isar da sakon abunda zata sanar.
“Umma dan Allah ki yi hakuri”
Umma ta a
je tray shinkafar tana mata kallon uku saura kwata.
“Ban gane na yi hakuri ba, me kika min macuciya?”
Ta fara yarfar da hannu.
“Sun kore ni daga aikin”
A take Umma ta saka, sam bata kawo kora daga aiki Falmata zata fada ba, a daukarta wani la
ifin tai mata na dabam.
“Amman wannan Ya kin iya bakinciki, dan kudin da zan samu kike wa Hassada? Ni zaki yi ma cuta?”
Da sauri Falmata ta girgiza kai tana wani irin kuka mai ban tausayi.
“A a Wallahi ba dan shi ba ne”
“To me kika yi ma wai
suka koreki? Taya za su kore ki haka nan kawai ba tare da kin musu komai ba?”
Bata boye komai daga abunda ta aikata ba wanda take kyautata zaton hakan ne yasa aka koreta, wato tofawa Luma Addu'a har mahaifinta ya gani.
“To uban waye ya kai ki yi mus
u addu'a ke ashibi yar neman yabo ko? Makira shegiya yar iskanka, ni za ki yi wa bakinciki? Bari Babanki ya dawo sai na miki wanda ya fi wannan”
Tana fadar hakan ta mike tsaye ta kai hannunta a kirjin Falmata ta fara murzar kirjinta iya karfinta. Wani i
rin kuka Falmata ta saka tana rike hannun Umma.
“Umma ciwo mutuwa dan Allah ki yi hakuri”
Bata saurareta ba har sai da ta murja iya yadda take cin zata cutarta da ita, tun da ta san idan aka murza kirjin burduwa mai tasowa ciwo take ji sosai. A rana
Falmata ta wuni da kirjin nata kamar dutse yana ta mata ciwo bayan nauyin da yai mata. Bayan sallah isha'i tana zaune saman tabarma ita da Naja sai dariya take mata, ita kuma ta takure guri daya tana ta tunanin abunda Umma zata saka Baba yai mata sai ta j
i sallamarsa, wani irin tashin hankali ta ji kamar ance mata ga mutuwarta nan. A yau Naja ce ta amsa sallamarsa taje ta karbo ledar hannunsa tana masa sannu da zuwa sai far'a take.
“Baba sannu da zuwa”
Falmata ta fada muryarta na rawa tana masa wani
irin kallon tsoro dan ji take kamar ma Umma ta mata sherin ne. Sai akai sa'a yana kawowa daidai inda take tsaye Tumba ta fito daga dakinta tana fadin.
“To Malam sai ka san abun yi, Fulani dai so take ta lalace, kama ta nai a kofar gida ita da wani da
ban san ko waye ba yana taba mata kirji”
A bala'in firgice Falmata ta mike tsaye tana kallon tana kallon Umma, a take Umma ta zaro mata ido.
“Ko karya na ke?”
Falmata ta girgiza kai da sauri.
“A a ba karya kike ba Umma amman Wallahi ba zan ka
ra ba dan Allah kui hakuri....”
Tun kan ta karasa Baba ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, yasa kafarsa ya shure kafafuwanta ta fadi kasa tana jin kamar babu naman fuska a fuskarta, ga kunnenta yayi wani dummmm jin tai yai dogon zango, kamar an
aiko shi haka ya hau dukanta yana fadin shi zata kawa abun kunya, gaba daya ta kasa kuka komai ya zo mata kamar a mafarki ga shi bata jin komai daga cikin abunda Baba yake fada kamar mai dukan Namiji haka Baba ya rika shurin Falmata yana dukanta har da sak
a kafarsa ya danne mata ruwan ciki sai da tai amai sannan Umma ta rugo da gudu ta rike shi tana kuka.
“Haba Malam daga fada maka abun dan ka mata fada sai ka hau yi mata wannan dukan, idan ka kashe ta fa, yarinya marainiya zaka mata wannan dukan”
Ku
ka take riri tana fadin haka iya karfinta wanda hakan yasa makonta su shigowa suna tambayar ba'asi, babu abunda ta rage sai ma kari da tai cewar wani ta gani yana taba kirjin Falmata. A lokacin ne Falmata ta ji wani irin kuka ya zo mata da karfi ta shiga a
mbaton Allah tana kiran mahaifiyarta da bata raye.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Mama Mama Mama Mama Mama, na shiga uku mutuwa zan yi, Bana jin komai Mama Baba Baba”
Ta unkura zata tashi ta ji ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ta kwanta a ka
san ta rike kunnuwanta tana wani irin kuka mai shiga zuciya. Tumba ta nufi inda take ta rika tana kuka kamar ba ita ta kitsa komai ba, kokarin dagata take amman Falmata ta kasa tashi sai kuka take. Mutane wasu na bata hakuri sai dai mafi yawa sun girgiza d
a jin dalilin dukan da mahaifinta yai mata, domin Falmata yarinya ce mai natsuwa da kamun kai wacce ake ganin kamar wata yarinyar matashi irinta a unguwar, wasu cewa suke sai dai idan saurayin ne yake son lalata amman Falmata ba halinta ba ne, wasu kuma su
n yarda wanda hakan bacin suna a gareta da kuma tarbiyarta, a yadda kowa yakr ganin Tumba tana rikon Falmata tana mata gatan da bata yi wa Naja ma da take yarta sai suka yarda da abunda ta fada a ganinsu ba zata mata sheri ba.
Har aka ci aka shude Falm
ata na kwance a gurin tana kuka, bata jin abunda mutanen suke fada har sai idan sun yi da karfi, fuskarta ya kumbura sosai kafarta sai ciwo yake kamar an cire mata shi, sai da dare ya raba sannan ta rarafa daker ta shige dakinsu bata ko karasa kan shimfida
rta ba ta kwanta a gurin a kasa tana kuka a hankali, babu komai a ranta sai kewar mahaifiyar ta kalaman da tai mata na bankwana.
“Zan tafi na barki ciki taradadi Fulani, Allah ya zama gatanki, na san za ki sha wahala kuma za ki ga banbanci da kiyayya,
amman ki rike Allah shi sai miki gata, kuma kar ki yi wasa da addu'a”
Mama..... Ta kiran sunan mahaifiyarta a hankali tana jin kamar ace tana kusa da ita, sai kuma ta fashe da matsanaicin kuka.
__________
Falmata baiwar Allah Iya ta ja miki
wahala yau
😭
Nana yar......
🤔
*
🐄🐄
FULANI
🐄🐄
*
By Khadeeja Candy
*8*
Da wani irin zazzabi Falmata ta farka, fuskarta ta kumbura gaba daya jikinta sai ciwo yake idonta ma ya kumbura sosai sakamakon kukan da ta kwana tana yi.
Babu abu
nda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai.
Tumba ce ta shig
o dakin tana kare mata kallo.
“Ba za ki tashi ki je gurin aikin ba?”
Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi.
“Ban ji komai ba Umma”
Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake
rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata.
“Ni za ki fara yi wani sabon siyasa?”
Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a ji
kinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada.
“Wallahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai”
Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa y
a sanar da gaskiyarta.
Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura.
“Cewar nai ki tashi ki tafi aikin”
Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata t
a yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa.
“Ba za ki je, ki ba su hakuri ba?”
Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai
maganar.
“To”
Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana s
hirin tafiya.
Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa.
“Kar ki karbi abincin nan
, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....”
Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya s
uke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali.
“Haba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro”
“Ni dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da k
aruwa ba”
Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya.
“Wallahi da na san haka abun zai zam
a da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu”
Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan
ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko
? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta.
Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin.
“Innalillahi ke lafiya me ya same ki?”
Bata ji abunda Khadija tace ba amman tabbas ta ga bakinta na motsi. Hakan yasa Falmata ta fashe da kuka, ta sani an nakasata kenan.
“Khadija Umma ta min shari ta ce Baba ta ga namiji yana taba ni, Baba ya min
mari biyu kuma ya doke ni, ya ce kar a sake bani abincinsa, Khadija bana iya ji yanzu sai an yi magana da karfi na shiga uku”
Wani irin rirrike Khadijar take tana fadin kukan kan ya samu hanyarsa, a take Khadija ita ma ta fashe da kuka ita da kawarta a
ka rasa nai rarrashi wani. Mahaifiyar Khadija ta saki tsintsiyar hannunta tana hawaye.
“Wai me kika tarewa matar nan ne? Wani irin zallumci ne wannan?”
“Allah ya isar miki Falmata Allah ya saka miki”
Khadija ta fada cikin kuka, kamin ta kama kawa
r tata su nufi baranda su zauna. A gidan Falmata tai wuni Maman Khadija da Khadija suka kitsa mata idan ta koma ta ce wa Falmata taje gurin aikin ta ba su hakuri sun maida ta.
“Kullun idan ta tura ki aiki ki dawo nan ki zauna sai lokacin komawarki gida
yayi sannan ki koma, abinci kuma ki zo nan ki rika ci kullum”
Maman Khadija ta fada mata a kunne cike da tausayawa, domin idan bata mata rada ba ba zata ji abunda tace ba. Falmata ta gyada kai.
“Na gode”
“Babu komai ai yiwa kaine, wannan rashin
imani na Tumba yayi yawa, ko dan tana ganin bata haifa ba ne take haka? Wannan wace irin zuciyata ce?”
“Allah zai saka mata In-Sha-Allah”
Khadija ta fada tana sharewa Falmata hawayenta. Sai da Falmata ta auna lokacin komawarta sannan ta fita daga gid
ansu Khadija ta kama hanyar gida tana ta jin tsoro domin gani take kamar asirinta zai tonu Umma ta gano bata je aikin ba.
AA POV.
Tun shekaranjiya da yai hadari da Nana be sake fita aiki ba, ba dan kuma baya iya fitar ba, sai yai amfanin da acc
ident din da yai yace musu ba shi da lafiya zai dauki sati yana jinya, tsoro ya cika masa ciki yana ganin kamar idan yaje zai iya haduwa da Nana ta kira wani tace gashi nan a kama shi wata kila ma Babanta Soja ne ko Alkali a masa daurin goro. Anti Rabi kam
ba a magana domin ko kofar gidan aka taba sai ta ji kamar zuwa za ayi a tafi da ita da AA.
“Babu irin gargadin da ban maka ba, amman baka ji ba, gashi nan ka je ka kwaso mana abu kai baka cikin natsuwa ni bana ciki”
Kallon Anty Rabi yai yana murmus
hi, duk irin tsoro da fargabar da yake idan ya tuna Nana da yadda take wasu dabi'un sai ya samu kansa da annashuwa, ba laifi tana da wauta and he likes that ko dan kudin da take sake masa.
“Babu fa wani abu Anti, da za su kamamu ai da ba za su kai yanz
u ba a nemo inda nake ba, ina tunanin bata fada ba ne saboda ita ma bata da gaskiya ai”
“Hmm ka sani ko ana can ana nemanka?”
“Idan nemana ake ai ta san gidan nan, kuma ta san inda na ke aiki”
Ya fada har lokacin murmushi yake.
“Maybe yar fari
n ce tana da wauta sosai”
Ya fada a fili sannan ya mike tsaye, da gaske he miss her, Allah ka dai ya san irin karyar da tai, da kuma irin sakin da za tayi, no wait ta ma isa gida? What if inda ya barta wani abun ya same ta? Ko ta bi wani kamar yadda ta
bishi, ai ba kowa ne na gari ba right? Idan ta nunawa wani kudi zai ma iya kidnapped dinta. A take hankalinsa yai mugun tashi wayarsa dake aljihunsa ya ciro ya chiga contacts sai a lokacin ya tuna ai shi ya bata number sa kuma bata kira shi ba.
Gaba daya
sai ya ji ba shi da natsuwa tunaninsa be kawo masa haka ba sai yanzu, and if wani abu ya same ta shi ne sanadi, domin shi ya barta a gurin kuma ya san abunda yai be kyauta ba. Gaba daya sai ya ji hankalinsa yai mugun tashi, be bari Anti Rabi ta fahimci ko
mai ba ya shiga dakinsa ya cire vest din jikinsa ya dauki wata bakar t shirt ya saka ya fito.
“Anti bari na leka nan waje”
“To Allah dai ya tsare idan ka ji baka natsu ba ka dawo gida dan Allah”
“Okay In-Sha-Allah”
Sai da yai addu'ar fita daga
gida sannan ya fita gidan. Kai tsaye gurin aikinsa ya nufa duk da ya san ba lallai ne ya ganta ba, sai dai sanin cewa tana yawan zuwa gurin wata kila ma an zo nemansa.
SHATTIMA POV.
Ya saba every end of the week yana ziyartar dakin motsa jiki, b
ut wannan karon sati biyu be je ba saboda be samu zama ba. Hakan yasa yake jin jikin kamar ba nasa ba, tafiya yake a hankali kamar wanda baya son taka kasa da daidaiya yake bin