Showing 57001 words to 60000 words out of 304903 words

Chapter 20 - FULANI COMPLETE

yai magana da su sannan ta dago musu hannu suka fito suka karasa inda yake. Shine gaba suna biye ha

r suka shiga cikin magarin, sannan aka kawo musu motar jaki suka hau aka nisa cikin garin da su. Sai da aka isar da su gurin sarki suka gaishe shi ya san da zuwansu sannan aka wuce da su gurin boka, duk abunda ake Jarma be wani motsin kirki ko kallonsu be

son yi gudun kar yai laifi, shi a rayuwarsa be tana ganin mutane haka ba sai yau, you ashe akwai irin mutanen nan har yanzu. Amman kam garin akwai kyau ga manyan duwatsu da itatuwa ga kuma ruwa ta ko'ina gwanin burgewa kowa sai hada hadarsa yake.

A nan ma

sai da Jafaru ya shiga yai magana da su sannan akai musu iso, sun san Jafaru sosai dan ya saba kawo musu mutane kala kala kuma yana cikin irin mutane da suke bawa kudi ayi musu sako a burni ko daga wani gari zuwa wani gari.

A saman agalami suka samu m

utanen mai kama da munanan tsofi kansa da aski an masa tas idonsa kamar garwashin wuta, kana ganinsa ka san aka gawurtaccin ifiritai a tare da shi, yawanci mutane garin suna jin yaren hausa da fulatanci duk da kasancewar ba su cika mu'amala da kowa ba, sai

wanda suka yarda da shi, amman ban da wannan baya jin ko wane yare sai na su. Sai dai a kusa da shi akwai mai fassara musu komai.

Suna zama ya fara karaton musu abun da ya kawo su.

“Ka zo nan saboda a kawarda dan'uwanka, da matarsa da dansa ka hau

sarauta, kana son a kashe Shattima da Talba da sannan a nakkasa Zainabu da Balki”

“Wallahi haka ne”

Jarma ya fada yana kara gyara zamansa mamaki duk ya cika shi, ta dayan bangaren kuma yana jin kunyar jin sirrinsa da abokinsa Saminu yai.

“To ga t

afiya nan da ba dawowa, ga Fadime nan ga Falmata, ga Sardauna su za su lalata muku shiri”

Jarma ya nisa a cikin tunani yana ta neman gano waye Fadime waye Falmata? Kuma waye Sardauna? Sardauna na na Yola ko kuma wani sardauna nan dabam?

Wata kwarya

ya dauko mai ruwa ta aje gaban Jarma, ya fara karanta wasu abubuwa sai ga Mai Martaba ya bayyana a cikin ruwa, wani irin zabura Jarma yai ya matsa baya.

“A harbe maka shi? Yanzu nan za mu yi masa harbin kanko”

Jikin Jarma sai rawa yake yayi sauri ce

wa.

“Aa shi ai mun samu nasarar kwantar da shi, yanzu Shattima muke son a fara harbewa tukuna”

Mutumen ya fara karance karance yana kiran sunan Shatttima amman ya ki ya bayyana a cikin ruwan. Tun yana daukar abun da wasa har ya fara yi da gaske Shatt

ima ya ki bayyana a cikin ruwan sai sunansa.

“Akwai abun da ke kare shi, lallai shi ma be tsaya haka nan ba”

“Yanzu ba a iya harbe shi kenan?”

“Za a iya amman idan akai be same shi ba, zai dawo gurinka”

Jarma ya mike tsaye yana lalaba jikinsa.



“A a bari dai sai mun yi shawara tukuna”

“Ba a shawara a nan ku tafi can gari”

Jarma ya mike tsaye da sauri ta ciro kudin da za su kai dubu 30k ya aje musu, sai ya girgiza masa kai mutumen ya fassara masa.

“Kudin siyen dabba ake ba mu”

Ja

rma ya karo 50k ya aje musu sannan suka juya jikinsa sai rawa yake. Duk shige shigensa be tana shiga irin wannan gurin ba, ba tana ganin tsafi kararsa irin yau ba.

_________

Sauran page daya mu gama free pages.

*

🐄🐄

FULANI

🐄🐄

*

By Khade

eja Candy

*15 -Last Free Page*

Fadime ta kara lakkamo Ma'u tana dariya

“Wallahi kuwa”

Ma'u da rufe baki tana zaro ido.

“Kuma Wallahi da gaske koko na sa da safen nan, Fulani da gaske kin iya”

Wani kalar dadi ya kara rufe Fadime jin ta

canki abun da Ma'u ta karya da shi yau, bayan ta gama fada mata ita tana da aljannu kuma suna sa ta gane komai na mutum.

“Yanzu kenan za ki iya fadawa mutum abun da zai same shi”

“Eh amman sai na yi bachi, amman dan Allah Ma'u karki fadawa ko sai w

anda kika yarda da shi, idan Bappa ya ji zai min fada ko ya doke ni ma”

“Ba zan fada ba”

Fadime ta yi dariya.

“Inna tace masu irin wannan abun kudi ake ba su, idan kina ga wani na son a masa ya bada kudi ki kawo shi zan masa amman a boye”

“Aik

o zan ta kawo miki mutane Wallahi, sai ki sammin wani abu ni ma”

Sai da hantsi ya bude sosai sannan Fadime ta bar kofar gidansu Ma'u ta dawo gida. Kai tsaye ta nufi bukkatarta ta dauko biro da littafinta ta fara rubuta hau Amo tace zata kawo mata miji,

kuma ta fadawa kawarta Ma'u cewar tana dubi.

Gaba daya wunin ranar wuni tai cikin farinciki da jindadi kana ganinta kasan dadi take ji tana murna wai Amo ta mata miji kuma a bunni.

Amo dai sai kallonta take a ranta tana fadin

‘Zaka si ubanka idan

ka aureshi mutuwa za kai, idan ka gagaran ci ai ba ka gagari wani ba’

Ta fada tana dan murmushi sai da Fadime ta mike tsaye tana kora shanu zuwa daji Amo ta lura yau wutar nan bata biye da ita, a razane ta mike tsaye tana bin bayanta da kallo.

Inna ma

ta mike tsaye daga can cikin bukkar da take zaune tana kallon Amo, wacce razanar ta bayyana, Inna daman can ta dade tana zargin Amo da maita ba tun yau ba, tun daga lokacin da ta bata labarin cewar suna da maitar gado wacce ake bawa yara tun suna kanana a

mman ita Allah ya tsareta ba a bata ba, ga yayan wabin da Inna tai ta yi a duk inda take neman magani sai ace manya ce take cinye mata yaya, wani cikin ma tun kan ya zo duniya zata yi barinsa, Fadime ce kawai ta rayu ita ma daker dan babu kalar ciwon da ba

tai ba, Allah ne dai ya rata ta da kuma addu'oin da take yawan yi mata, Bappa ma yana mata sosai har rubutu yake mata ya bata ta sha, tun a wacan lokacin idan Inna ta fada masa tana zargin Amo sai ya karyarta yace baya son tashin hankalin, har yake ganin

kamar kamar Inna tana haka ne saboda Amo kishi, bayan kuma ita ta zo ta tararda Amo.

Sunsunsun Amo ta shige bukkarta da mugun mamaki, ta sani wani sa'in ana samun akasin abun da tai mata, sai dai ba ko yaushe ba, domin Fadime babu ruwanta da addu'a sa

i dai idan yi mata akai, kuma wannan wutar ta dade da saka mata ita tun Fadime na karama, taya yau rana daya za a wayi gari babu ta? Ko dai Inna ta karbo mata wani maganin ne? Idan ba haka ba gaya wutar ta bar binta? Adakin ta kasa zaune ta kasa tsaye sai

safa da marwa take gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya.

A kullum idan Fadime zata je kiwo sai ta saka shanun gaba tana binsu a baya, ban da kwana biyun nan da take son sake ganin Wasim, kullum baya take baro shanun sai idan sun kawo kansu. Tana isa ta

haye saman dutsen ta fara kiransa.

“Mai busa”

Haka take kiransa a duk lokacin da ta iso gaban dutsen, duk kiran da zata masa kuma ba zata ganshi ba, ba zata ji busar ba, bata kuma fasa kiran ba. Sai dai shi yana saukowa kasa ne ya boya jikin dutsen

yana kallonta har tai abunda za tai ta gama.

Sai da ta sauko saman dutsin sannan ta ganshi kasa tsaye ta inda zata ganshi yana kallonta fuskarsa da murmushi, dan tsoro ta ji.

“Kenan shi aljanin dutse ne?”

Ta raya a ranta, a fili kuma sai ya kara

hayewa saman dutson alamar ba zata sauko ba. Ganin hakan yasa ya fara haurowa saman dutsen still yana mata murmushi.

“Ka yi hakuri ni ba dan wani abu na kira ka ba”

Ta fada tana kokarin sauka ta dayan bangaren, ganin hakan yasa shi ma ya juya ya sa

uka. Sai suka koma kallo kallo ita da shi, ta kira shi ne kawai ba dan tana da abun cewa ba, kuma bata san zai ji ta ba, tun da ta saba kiransa kwana biyu bata ji shi ba. Da hannu yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, ta girgiza

masa kai. Zaunawa yai a gurin ta dauke kai daga barin kallonta. Hakan yasa zuciyarta ta raya mata cewar ko aljani ne shi ba zai cutar da ita ba tun da har mafarkinsa take. A da idan Inna tace mata tai addu'a sai tace mata wuya take ji, amman a yau da take

son zuwa kusa da shi sai da ta tsaya ta karanta addu'oin data iya sannan ta tunkareshi tana takawa kadankadan kamar mai tsoron ya ji takunta, kansa na kasa har ta kawo kusa da shi ta risina ta leki fuskarsa, sai ya sakar mata murmushi ita kuma tai masa da

riya irin dariyar nan ta dole kuma ta tsoro wacce mutum ke yi a rikice.

“Kai aljani ne?”

“Aa”

Ya amsa mata yana dagowa ya kalleta da kyau.

“To miyasa na ke mafarkinka?”

Kallonta kawai yake irin kallon nan na son tantace gaskiyarta. Kamar t

asan irin kallon da yake mata sai tace.

“Wallahi ba karya na ke ba, ina mafarkin, da wani mutum kuma da wani kana rike da wannan abun busar kana busa amman kullum baya kake bani, shiyasa lokacin da na ji busarka na zo har nan dan gani idan da gaske ne,

kuma busar iri daya ce”

“Ni ba aljani ne bane”

Ya fada cike da mamakin mafarkinsa da tace tana yi.

“Kuma tun lokacin nan nagge bata sake mutuwa ba, miyasa kake saka wannan abun”

Ta nuna warkin dake kugunsa, sai yai murmushi.

“Haka muke, k

ayan garin mu”

“Ina ne garin ku?”

“Garuk”

Ta gwala ido tana matsowa kusa da shi, sai a lokacin ta tuna da taba jin labarin garin ance mutanen ciki basa saka tufafi kuma matsafa ne.

Ta zauna a kasa tana kara kallonsa.

“Kai kake min tsafi nake m

afarkinka kenan?”

“Aa”

“Ya za'ayi na tabbatar da kai mutum ne?”

“Idan kika taba jikina za ki ji shi kamar na ki, idan na aljanine za ki jishi da sanyi ko taushi ko gashi ko kiji kamar ba hannun mutum ba”

Dan matsawa tai kusa da shi, sai ya miko

mata hannunsa ta taba sannan ta taba nata, sai ta ji shi normal kamar ita. Amman hakan be sa ta gansu ba.

“Ka yanke kanka na ga jini sai na yarda”

Wannan karon dariya yake, a ransa yana mamakin wauta irin nata taya zata ce ya yanka jikinsa.

“Sa

mo min kare ko dutse mai tsine”

Ba musu ta tashi taje ta samo masa, ta kawo ta zauna kusa da dan tabbatarwa idan da gaske yankawan zai yi ko a'a.

“Miye sunanki?”

“Fadime”

Ta amsa mashi tana kallonsa da manyan idonta masu haske da daukar hankal

i. Murmushi yai ya mike hannun na dama ya saka hannunsa na hadu ya karkari hannunsa na dama kadan jini ya dan fito. Da sauri ta rufe ido tsigar jikinta na tashi.

“Innalillahi, da gaske ka yanka ni wasa nake maka fa”

“Ba hakan zai sa ki yarda da ni b

a”

Ya fada yana kallon gashin kanta.

“Na yarda”

Ta fada bayan ta bude idon.

“Miye sunanka?”

“Wasim”

Haka ta fara masa tambayoyi kala kala yana bata amsa, duk abun da ta tambaya sai ya bata amsa, tun tana da sauran tsoron har ta sake jik

i da shi.

Har da karbar sarewarsa ta busa, sai nata busar bata fita saboda bata iya ba. Har sai da ya karba da kansa ya fara busar tana ta kallonsa cike da burgewa.

“Waya koya maka?”

“Wani tsoho”

“A ina yake?”

“Garinmu”

Ya amsa yana kallo

nta, mugun burgeshi take, ko wane motsi nata the way da take tambayarsa yadda take sake jiki da shi far'arta kyauta and everything. Ta gyada kai tana murmushi, da yamma lis ta koro shannun ta sako su a gaba ta jeru ita ta shi suna tafiya, sai ya rakota har

kusa da hanyar gidansu sannan ya tsaya ita kuma ta daga masa hannu, shi ma ya dago mata sai ta juya ta cigaba da tafiya sai kwasar dariya take.

Daman tun dazun take jin dariyar take son ta yi ta kasa, wai basa saka rika kuma basa son shiga cikin mutane

n da na nasu ba, gaba daya kallon mahaukata take musu.

Sai ta kai shannun gida ta shigarda da su gurin da aka saba ajesu, sannan ta sunsuda ta fita, sai da ta kama hanya sannan ta hango Bappa tafe tare da wani makocinsu, da sauri ta boya bayan wata bis

hiyar dogon yaro. Kasancewar bishiyar katuwa yasa Bappa da mutunen ba su lura da ita ba, domin gaba daya hankalinsu baya gurin yana kan abunda suke tattaunawa ne.

“Gaskiya ina baka shawarar ka kara aure kawai”

Shine kawai abun da ta ji, duk da bata

san abunda ake tattaunawa akai ba, amman tabbas ta ji Bappa na ce masa ya kara aure, a gurin tai ta tsayi har sai da suka karyar kwana sannan ta fito yana girgiza kai tana dariya.

Juyawa tai ta canja hanya zuwa gidansu Ma'u, ko da ta shiga ta samu Ma'u

na alwala sallah magariba, sai ta risino kusa da ita.

“Ma'u nan da kwana biyu mijin Ande Hanne zai fara maganar aure ce ni na fada miki”

Ma'u ta kalleta da sauri.

“Aljanin ne ya fada miki?”

“Eh, yau da naje kiwo ma a fili ya ganshi yace zan r

ika ba da magani zan rika fadawa mutane komai”

Ma'u ta kara zaro ido gaba daya ma sai ta ji tsoron Fadime ya fara kamata.

“Da gaske?”

“Allah amman karki fadawa kowa”

“Ba zan fada ba”

Gaba daya tsoro ya gama kama Ma'u, Fadime ma ta lura da ha

kan kuma ta jidadi, ita gaba daya tun da Inna ta fada mata masu magani kudi ake ba su su fadawa mutum matsalarsa ta ji tana sha'awar abun. Haka ta kwana da tunani kala kala na irin karyar da za ta yi ma Inna ta yarda ta fara bada maganin.

Sai da Fadime

ta gama karyawa da fura mai tsami sannan ta zauna saman tabarmar da Inna ke zaune tana gyaran gida.

“Inna na sake mafarkin aljanun nan sun ce zan bada magani fa”

Inna ta daka mata tsawa.

“Fulani kar na sakd jin maganar nan a bakin ki, da kin sak

e maganar nan sai na fadawa Malam”

Da sauri tace.

“Na bari”

“Gashi kije ki debo ruwa”

Ta tashi da sauri ta nufi inda tulun daukar ruwan yake ta dauka ta fice da sauri ta nufi gurin deban ruwa, tasan Bappa sarai be son irin abubuwan nan. Tana t

afe tana wakewaken har ta isa, sai da ta duka ta fara cikon ruwa sai ta ji a na kirata.

“Fadime”

Da sauri ta juyo suna hada ido ta sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake mata murmushi. Tsaye yake nesa da ita.

“Ashe kana zuwa nan da safe”

Y

a gyada mata kai yana karasowa kusa da ita, har yanzu bata daina jin tsoro ba sai dai ba kamar na da ba.

“Ruwa kike deba?”

“Eh”

Ta fada tana dariya sannan ta duka ta cigaba da cikon, sai kuma ta juyo ta kalleshi.

“Dan Allah ka taimaka min ka

min wani abu”

“Minene”

“So na ke idan na cika tulun nan, ka masa tsafi tun da ku matsafa ne ai zaka iya ko?”

“Saboda me?”

“Saboda Inna ta yarda cewar ina mafarkin aljanun, so na ke ka masa tsafi sai na je gida na aje tulun sai ruwan su zama mac

iji”

“Ba ki jin tsoro?”

“Ai ba anan ba sai na je gida, amman ka min alkawarin ba za ka cutar da ni ba”

“Ko wani ba zan bari ya cutar da ke ba”

“To ka min ka ji”

Ya daga mata kai. Sai da ta cika tulun dam sannan ta matsa tace yai mata ita dai

burinta kar Inna ta karyartata, burinta Inna ta bata hadin kai ba sai Bappa yaji ba. Matsawa yai kusa da tulun ya saka hannunta yana ta kallonta be wani dade ba ya cire sai ta zaro ido.

“Yanzu shikenan da naje gida zan ga ruwan ya zama maciji?”

Ya

daga mata kai alamar Eh yana ta kallonta, sannan ya tallaba tulun ya dora mata saman kai, tsakanin dora mata tulun da fara jin motsin abu mai rai a cikin tulun be yi minti 1 ba.

Yana kallonta sai ta fashe da kuka.

“Ba yanzu na ce ba, Wayyo Bappa wayyo

Bappa wayyo Bapppa”

Sai fitsari, ta fara kukan da gaske gasken hawaye kamar ruwa.

“Idan kika sauke tulun macijin ciki zai cijeki, karki sauke sai kin isa gida”

Ya fada yana dariya. Gaba daya jikin Fadime rawa yake kafafuwanta sai lankwashewa suke

kamar zata fadi, numfashinta ya fara sama sama, faduwa tai kasa ta fara rarrafe dan bata ma iya tafiya, haka nan ta isa gari duk da bata zanenta da zawo sai kuka take tana kiran Bapppaa, ga tulun saman kanta. Duk wanda ya kalleta sai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login