Showing 180001 words to 183000 words out of 304903 words
cup din.
“Sha lemu”
Ba karamin mamaki Zainab tai ba, sai dai ta alakanta hakan ta tausayin Fadime, domin bata sa ran ya santa. Sai da Fadime ta sha five alive ta ji sanyi har cikin kai da ruhu ta fara masa addu
'a, murya kasa kasa gudun kar Zainab dake kicin ta ji ta
“Na gode Allah ya saka maka da alheri, ya rabaka da iyayenka lafiya, kuma Allah ya tsare ka daga sherin mayu, da zuwa garin su Wasim, duk wata bakar mata ce ta jamin min, ta zo daga can wani gari
can nesa wai yola tasa na rakata a can garin, gashi nan ta tafi ta bar ni da bala'i, gashi nn na makance kuma an kawo ni gurin su mayu, Allah ya isa, da wani jikinta kamar yar tsana, wai hoto zata dauka, muguwa banzar Allah ya isa...”
Ta karasa da kuka.
Zainab ta hade wani numfashi da karfi tsabar bakinciki yasa shi kin wucewa har sai da ya dawo mata ta fitar da shi, mikewa tai tsaye da zimmar marin Fadime sai Shattima ya watsa mata wani mugun kallo, na me zaki yi? Hakan yasa tai tsaye cak tana hucin da
bata san ta ina yake zuwa mata ba.
“That's mean ke ce dalilin makantarta, and you're treated her badly”
“No ba ni ce silar makantarta ba she's lie, bata da hankali wannan yarinyar kuma kanta rawa yake”
Zainab ta fada tana kokarin kare kanta, uffan
Shattima be sake ce mata ba, irin yadda yake kallonta kadai ya isa ya sanar da ita irin bacin ran dake cikin idonsa, and the second thing he hate is argue, ta kuma san haka.
“Ka yi hakuri ka gafarce”
Ta furta cikin muryar dake nuna tana daf fa fashe
wa da kuka, domin numfashinta har wani sama yake yana kasa. Fadime na jin hakan ta aje kofin lemu ta kama kafar Shattima ta rike gam.
“Dan Allah dan Annabi karka bar ni nan, yauna shiga uku na, Wallahi yau farfesuna za su yi...”
Ta fashe da kuka, ko
ba a fada mata ba ta san Zainab ta ji abun da ta fada na zancen maita, domin shi kawai take tunanin zai bata mata rai, ba zancen wacan matar ba data raka zuwa garinsu Wasim, kuma ta san ba za su raga mata ba, baka taba maye ba ma ya ka kare balle kuma ka
taba, abu na mu dan kura da kallabin tsire
😂
A gafarce ni jiya ban samu na yi ba, bana jin dadi ne yau ma karfin hali ne, fatar za a min afuwa kamar yadda aka saba. Allah kara mana lafiya da abun da lafiya zata ci, ya tsare mu daga dukanin abun cuta
rwa.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sa
nyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren s
utura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku
iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
42
*Littafin nan na kudi ne biya ki
karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Yadda ta rike masa kafa sai ka rantse da Allah idan ta saki kafar wani abun ne zai sameta, ba zuciyarta ba har jikinta ba bakinta mai saki
n zance rawa yake. A take ta fara ruwan hawaye da majina, yana kokarin kwace kafarsa ta kai hancinta jikin wandonsa ta goge majinar.
“Ke Malama kafata ce kika share majina da ita”
Ta fada yana kallonta for the first time ta masa abun da ba a taba mas
a ba.
“To ina ruwana ko ba kai ka barni ina ta zuba ba, ba zaka fada min kace gata nan ta zo ba, kuma ka min alama kut”
Ta yi kwafa domin ta fi jin haushinsa yanzu fiye da kowa. Da me zan miki alama tun da ba gani kike ba? Ya furta a aransa a fili ku
ma sai ya kai hannunsa ya saka karfi ya banbanre hannayenta, wani irin hargagi tai kamar kyanwa ta kara kame kafar ta rike gam, daker ya yunkura ya mike tsaye, tana jinsa tsaye ita ta mike tsaye tana dafa shi har ta isa daidai kunkurunsa ta rike gam kamar
ta samu ice, ta dora kafarta ta dama akan kafarsa ta hagu, ta hagun ta dorata a kafarsa ta dama, ta yadda idan ya daga zai yi tafiya kafafuwanta na saman nashi.
“Wallahi dole ne ka tafi da ni, ba zan zauna ba, ai kai ka bar ni ita ta zuba, baka ko min a
lama ba, duk ta ji komai, shikenan sai na zauna su cinye ni, ga makanta ga mutuwa aa Wallahi ba zan yarda ba”
Ta fada har da girgiza kai tana kara rike shi, be san lokacin da murmushi yai ma kansa muhalli a fuskarsa ba, murmushin da ya bayyana hakoransa
.
“Ina zan kai ki?”
“Ka kai ni garinmu”
“Garinku ba nan kusa ba ne”
“To ka kai ni gidanku gobe sai ka kai ni garinku, ai gidan ku ba mayu ko?”
Yayi shiru sai kallonta yake cike da nishadi. Ya cira kafar daya ya taka tana saman kafafuwansa.
“To sauka”
“Aa Wallahi ba zan sauka kana ganina haka idan na sauka wayo zaka min, sai dai mu tafi a haka”
“Ya za yi na fita dake haka? Kin san waye ni kuwa?”
“Ina ruwana da kai ko waye, kai ka san wacece ni? Hmmm”
Ta kara kankameshi, seriousl
y be san yadda zai yi tafiya da ita ba a haka kafafuwanta saman na shi. And what he hate the most is ka take shi amman ji yadda ta dora duka kafafuwanta saman na shi.
“Ba zan iya tafiya a haka ba”
Yadda yake amsa mata kadai abun mamaki a gurinsa, do
min ya tabbatar da ba ita ba ce ta yanzu ya dauke ke ko waye da mari. Jin ya fadi haka yasa tayi kasa da hannunta ta kama rigarsa ta shadda ta rike gam, sannan ta sauka kan kafafuwan nasa.
“To mu tafi...”
Sai da ya kalli rikon da tai masa sannan ya k
alleta.
“Ban san inda zan kai ki ba Wallahi”
“Ko ma ina ne ni ka kai ni”
Ya hade yawu a hankali sannan ya fara takawa tana rike da shi kamar wanda yai mata sata gefen shaddar data rika har ta tamuke. Yadda ya fito cikin falon ba zaka ce shine ya s
higa dazun fuska a hade ba, domin a yanzu murmushi da nishadin da be san ta ina yake zuwa masa ba ya wanke masa fuska da zuciya. Har gaban motar ya karasa da ita ya bude front seat.
“To shiga ki zauna”
“Aa idan na shiga wai wata motar ce zaka saka ni
sai ka shiga motarka ka tafi ka barni”
Ya sake yin murmushi.
“No motata ce”
“Ce Wallahi?”
Ya zaro ido kamar tana ganinsa, a rayuwarsa ba a taba bashi rantsuwa ba. Shiru yai mata a gurin sai kallon kyakyawar fuskarta yake. Jin shiru yayi yawa y
asa ta kai dayan hannunta tana taba kirjinsa.
“Kana nan ai”
“Idan ba zaki shiga ba, sake ni na tafi”
“Sai ka rantse”
“Ba zan rantse ba”
“Ni kuma ba zan sake ka ba”
Ta kara gyara tsayuwa yadda zata ji dadi dadewa a gurin. Kansa ya daga sa
ma ya sauke can kuma ya kalli gate yana mamakin yadda akai be dauke ta da mari ba tun dazun.
“Sai dai mu yi ta tsayuwa a nan har dare, Allah yasa ma ayi ruwa”
Ya wara idonsa yana kallonta like serious ya fada a ransa, ya sake yin murmushi.
“Okay
i swear”
“Ka ce Wallahi Motata ce kuma ba zan tafi na barki ba?”
Ya kara zare ido, wai yarinyar nan kuwa ta san waye shi? How on earth zata saka shi rantsuwa again kamar kotu?
“Ka ce”
Ya mata shiru kamar shekararen ice.
“Ya ma sunanki?”
“
Fadime”
“Okay, ki tsaya mu yi maganar hankali ni ba zan sake rantse miki ba, idan kin yarda da ki ki shiga kawai bana karya, kuma har garinku zai maida ke saboda iyayenki suna can suna nemanki idan ba su gan ki ba zasu saka ni kotu”
“A ina suka ganka
?”
Ta ina zai bata labarin suna tsaye a rana?
“Shiga mota”
“Sai ka rantse kamar yadda na ce ka fada sannan”
“Wallahi motata ce kuma ba zan barki ba”
Tana jin ya fadi hakan ta sake shi ta lalaba ta shiga motar, shi kuma ya rufe yana murmushi
sannan ya zagaya dayan side din. Kamin ya zagayo ya shiga motar har ta tsawwala, sai ta taji ya shiga ya zauna har yayi ma motar key sannan hankalinta ya kwanta.
“Kika sani ko ni ma maye ne?”
Ya fada yana murmushi tare da kai hannunsa ya kara gudun
ac motar. Cak Fadime ta tsaya.
“Kuma fa?”
Take wani tsoron ya kamata, nan da nan sai kuka kamar ba ita ce ta gama rigima ba yanzu. Da gangan Shattima ya kyaleta tana ta rusar kuka a motar har sai da suka bar gidan suka hau babban titi.
“Wasa nake
miki”
Ta ki daina kukan, shi kuma be fasa murmushin daya kusan zame masa dariya ba.
“Haba wasa fa nake”
“Rantse to”
Ta fada cikin kuka, sai ya kalli fuskarta.
“Me zan ce?”
“Ka ce Wallahi wasa na ke”
“Kina ta saka ni rantsuwa fa ba a ta
ba sani haka ba”
“Ni ma ba a taba min haka ba, ka taba ganin an bawa maye ajiyar nama? A kawowa maye mutum har cikin gida ace wai ya aje? Kaddarorine suke ta bina, daman sai da Inna tace Fulani karki je garin nan karki je, amman ban ji ba na tafi, gashi
nan naje na ci wuya, kuma na dawo na makance, har an kawo ni ajiya gurin mayu”
Shattima ya bushe da wata kalar dariya da ya manta when last yai irin dariyar, dariya sosai har yana buga sitiyarin motarsa.
“Oh my god”
Ya furta yana kokarin takaita
dariyarsa. Kana ya kalleta.
“Waya fada miki cewar mayu ne?”
“Wasim mana”
“Waye Wasim?”
Sanin labari zata bayar yasa ta share hawayenta, ta gyara muryarta dake da kufan kuka.
“Saurayina ne, a lokacin da ya kawo ni sai yace ga ajiya na kawo id
an kin ga dama ki cinye idan kin ga dama ki aje, kuma yace mata kin ki amayarda kankarar maitar nan ko? Kin zama daman cikin mutanr kina cin mutane yan uwanki, sai ta ce aa ni banci kowa ba, duk mutanen da nake ci masu shiga ganyata ne su tare min cikar bu
ri, wani mutum nake bibiya, na cinye masa mata yanzu kuma yayansa na ke bibiya, kaga kenan mayya ce ko?”
Shiru Shattima yai yana tunani rage gudun motarsa.
“Waya fadi haka?”
“Ita wannan tsohuwar mai magana kamar gere kyankyankyan...”
Fadime ta
kwaikwayi muryar Iya tana matse baki kamar tsohuwa. Shattima yayi murmushi duk da kasancewar yana cikin rudani da tunani. Sai a lokacin tunani ya zowa Fadime, what if shi ma danta ne? Ko Kuma yana da alaka mai karfi da ita?
“Wannan tsohuwar mamanka ce?
”
“No”
“Kakarka ce?”
“No”
“Kanwar mamarka ce?”
“Oh...No”
“To miye alakar da ita?”
“Tana zama a gidanmu ne kawai kamin ta dawo nan”
“To yarta fa? Ita ma baka da alaka da ita?”
“Yes”
“Ko dai budurwarka ce?”
“No kin cika tamba
ya”
“To ina zaka kai ni?”
“Ina na sani, kin zame min kaya”
Can kuma ya kalleta yana murmushi yace.
“Bakin titi ki yi bara”
“Lalala ai ni ba makauniya bace makafi da nakasassu sune suke yin bara Allah ya tsare ni nikam”
Shattima ya faka mo
tarsa gefen titi yana tintsirar dariya kamar ba shi ba.
“To ke micece?”
“Ai ni ba haka aka haife ni ba, kuma idona zai bude, kuma maganar nan ta min zafi”
A take idonta ya cika da kwalla domin har ga Allah ta ji zafin da ya kirata da makauniya har
ta furta kalmar bara a gareta.
“Duk matar nan ce da ja min shiga wannan hali, da bata je garin ba da ban bita ba, ni Wallahi yanzu idan na ga wani zai je ma hana shi zan yi, duk bakina na yaje min nace mata na san wanda zai kaita, salo gareni Allah ya
yi min shegen salo (Banbandanci)”
Shattima ya jingina da jikin kujerAR motar yana dariya.
“Wace mata kuma?”
Ta fara bashi labarin abun da ya faru tun daga farko har karshe.
“To ai ita ce wannan matar wacce muka baro gidanta yanzu, ba a motata
kuka hadu ba kika ce mata kin sa gari”
“Haka ne haka ne...ita ce?”
Ta daki kirji.
“Har take min wannan wulakancin? Har take ce min na sauka a kujera? Har take min tsawa? Har take min fada? Lallai dan adam butulu ne, lallai wannan matar ba zata ga
annabi ba, mayya kawai yar mayya, masu bakin hali da mugun nufi, Allah yasa idanuwana suna budewa nata su rufe, amman ba zan taba yafe mata ba, ai wannan zallumci ne, ko tausayina bata gani? Wayyo Allah”
Kuka take sosai tana jin zafi abun da Zainab tai
mata.
“Allah ya saka min a gareta da duk wanda yai sanadiyar haduwa ta da ita”
Shattima ya dago ya kalleta.
“Har da ni kenan?”
Ba dan tana tsoron kar ya sauke ta a hanya ba, da ko amsa masa ba za tayi ba.
“Aa bacin rai ne ya kawo haka, na y
afe maka”
Ta fada cikin kuka, ba dan ta yafe masa a zuciyarta ba. Murmushi yai ya ja motar suka koma kan titi. Maganarta ta dazun ce ta dawo masa a rai, cewar wani mutum take bibiya ta cinye matansa kuma tana bibiyar yayansa, me hakan yake nufi? Baya so
n ya munana tunaninsa, amman har ya fadada tunaninsa mutumen daya fada ba yi kama da kowa ba sai shi! And lastly Ammy ta fada masa cewar ta talla Zainab, miyasa bata ji tsoron kar Zainab din ta mutu ba?
“Bayan haka kin ji wani abu?”
Ya tambaya yana
kallonta, sai ta girgiza masa kai domin ba zata iya amsawa ba saboda kukan da take na bakincikin abun da Zainab tai mata.
“Wallahi da na san ita ce, ko tace na sauka a kujerar nan zan ce mata ba zan sauka ba, idan tace matsa can n ace ba zan matsa ba, h
ala ba saboda ke na samu matsala ba? Wallahi na fita iya iskanci yar daba ce ni idan bata sani ba, har ta isa?”
Shattima ya saka dariya, yana mamakin yadda ta rike abun a ranta ta kasa sakinsa.
“Dan Allah ki bar ni nai tunani, i need to think”
“T
o think Mr thinker...”
Ta fada cikin kuka, sai yai murmushi ya kai hannunsa yaja dogon hancinta.
“I like you idan ba ke ba ba zai miki haka duk a garin Yola?”
Ya saka dayan hannunsa ya dauki wayarsa ya nemo number Jekadiya. Bugu daya ta dauka tana
rangada masa kirari.
“Jekadiya, dan Allah a nemo yariyar nan gobe”
“To an gama ranka ya dade”
Ya aje wayar kamar yadda ya saba ba tare daya kashe ba. So yake yayi ma Falmata wasu tambayoyi he need to confirm something. Ya kalleta har lokacin kuka
take.
“Baki gajiya da kuka?”
“Baka san yadda nake ji ba, na taimaki matar nan amman shi ne zata saka min da haka? Ai ko bata san ni ba be kamata tai min haka ba, dan'adam yana da daraja, mu mutanen kauye ba mu san mu wulakanta mutum ba”
“Bata kya
uta ba, sorry amman ba ganina nan ba? Zan kai ki gida gobe inshallah”
Ya zari tissue ya dora mata a cinya.
“Share hawayenki da wannan”
Ta dauka ta share ta goge majinar ta mika masa.
“Gashi”
“No kefa shi can”
Ya sauke gilashin motar na si
de dinta.
“Ina?”
“Gefenki ta gurin da kike jin iska”
Ya mika hannunta ta jefar.
“Ina zaka kai ni?”
Ya daga kafadunsa alamar be sani ba duk da ya san bata ganinsa, not knowing where to take her, yadda take da yawan surutu ba zai iya kaita mas
arauta a yanzu ba, domin zata je ta basu labarin maita na Iya, and if Ammy ta san yaje gidan Zainab she won't be happy. Bashi da zabin daya wuce ya kaita gidansa kamin gobe, ya sake dauko wayarsa ya kunna data da kansa dan siyen ticket din mutum biyu, shi
da ita na zuwa Katsina gobe.
FALMATA POV.
Sai da tai kamar ta koma cikin gidan ta fadawa Jekadiya cewar tana son ta cigaba da aikin kamar yadda ya bata dama, sai kuma wata zuciyar ta hanata, sai ta nufi gate din kai tsaye da zimmar ficewa, a
tunaninta cigaba da aikin karin wata barazanar ce a gurinta, domin zata iya shiga wata matsalar kuma bata san abun da zai kara biyowa ba, wata kila ma yafi wanda ta shiga a baya. Bata karasa gate din ba motar Sirleem ta kunno kai cikin gidan, yana kawowa d