Showing 210001 words to 213000 words out of 304903 words

Chapter 71 - FULANI COMPLETE

sauran yan biki suna ta guda, abun ka da Amarya mai farin jini.

A lokacin da suka isa bakin titi sai kallo ya koma sama, Tumba ta saki ido tana kallon mayan motocin da aka jera na alfarma har kusan gud

a goma sha biyu.

“Jama'a ina motar mu?”

Ta tambaya gabanta na faduwa, Sai yan bikon su ka ce

“Su ne nan ai, amman ga motar da Amarya zata shiga can”

Sun nuna wata kafirar mota mai kyau fara sol kana ganinta ka ga sabuwar mota, a take kallo ya

koma sama, daga Tumba har yan biki suka koma mamaki, ba ma kamar ita ta take ganin kamar mafarki take. Fitilar hannunta ta haska fuskar matar da ita dan kara tabbatarwa.

“To”

Ta fada cikin kunya, da tsoro, wata zuciyar na raya mata cewar wata kila ar

osu yai ko kuma abokansa ne manyan mutane suka yi masa kara. Kamar hawainiya haka ta nufi motar da aka bude musu ta shiga sannan aka shigar da Falmata da kawarta Khadija wanda ita ma mamaki ya kusa kashe ta.

“Shiyasa Tumba ta dage sai an yi, ashe saboda

ta san mai kudi ne ta ci duniya”

Khadija ta raya a ranta, haka aka cika motocin har wadanda ba da su ba a bikin sun samu gurin shiga, unguwa ta dauka cewar Falmata ta auri wani hamshakin mai kudi, wasu na fadar wai ai hakurin da tai ne wasu kuma su ce

Allah ya sa na kwarai ne. Tumba kam ciki ya duri ruwa ta rasa wane tunani zata fara yi. Ita dai tana ciki motar ana tafiya har suka shiga wata sabuwar unguwa ta manyan mutane, a zatonta wucewa za ayi, ba ta ankaro ba ta ga an kunna kai cikin wani katon gid

a. Mai bala'in kyau da daukar hankali, fentin gidan fari sol ga haske kamar rana, idan sama ne mai hawa daya an kawata ko'ina da fulawoyi.

“Kai malam gidan Malam Mu'azu za ku kai mu fa? Ya muka ga nan kuma?”

Tumba ta sauko daga motar tana fadar haka,

gabanta sai faduwa yake.

“Nan ne gidan ai Inna”

Daga daga cikin matan da suka zo biko ta amsa ta.

“Ke Ta dela wannan ne gidan da kuka he kuka gani?”

Wacce aka kira da Dela ta girgiza kai.

“Aa ba wannan ba ne”

“Inna an canja wacan ne shiy

asa, daman saboda ga a yi ma wannan fenti ba ne yasa aka ce a akaita can, sai gashi kuma an gama kamin lokacin”

Numfashim Tumba ne ya fara rawa ta ja kafa kamar wata marar lakka suka doshi cikin gidan dake ta kamshin turare. Bata raina kamta ba sai da s

uka nas kafarsu cikin falon da za a iya kira da aljannar duniya. Sanyi ac da katon tv ga manyan kujeru farare masu kawata ido da rudarda makiya suna musu marhabun...

48

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza

Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Tumba ta ja da baya da sauri tana rike da hannun Falmata.

“Aa indai Malam Mu'azu ne da aka daurawa aure dazun tare da Falmata ba wannan ne gidan ba”

“Inna nan ne gidan fa”

“Aa”

Tumba ta jata ta tsaya a waje ita ala dole ba gidan ba ne, domin a iya ganinta tsohon da aka aurawa Falmata be da tarin wannan arzikin, mutumen da yake kamar maroki ma taya ya samu wannan uban arzikin kato gida haka komai a tsare falon ma a kawatashi kama

r na yar minister, sai da ta gama kallon ko'ina harabar gidan. Sannan ta ciro wayarta ta kira line Baba, wayar bata dade tana ringing ba ya dauka yana sallama. Ko amsawa ba taba tsaya yi ba ta ce.

“Malam ka kira mutumen ka tambaye shi ina za a kai Falma

ta, motocin da ya aiko sun dauko mu sun kawo mu wani katon gida da ni na san ba na shi ba ne”

“Wani gida kuma?”

“Eh ba gidan da muka je muka gani ba, wani gidan ne na dabam, ka kira shi ka tambaye shi inda za a kai yarinyar”

“To shikenan”

Ya ka

she wayar, Tumba ta saka wayar a cikin zanenta tana kallon yan'uwan Baba da sukai cirko cirko.

“Ni sam ban yarda gidansa ba ne, domin be da irin wannan arzikin da zai samu wannna katon gida, idan ma yana shi to boye mana yai kuma ba na halal ba ne, wann

an irin abu haka”

Ana nan dai wasu suka saka na su baki, suka taya ta wasu kuma su ka kama bakinsu su kai shiru, Inna laure dai na tsaye da tunani biyu a ranta, domin a yanzu ta gane dalilin kukan da Falmata take yi, bata son auren ne, ita kuma Tumba ta

tsaya mata akan auren ne saboda ta sha wahala sai gashi ta ga abun da ba tai zato ba hakan yasa ta rudewa tana fadin wani ba gidan ba ne. Suna nan tsaye Baba ya kira Tumba jiki na rawa tai picking.

“Tumba yace nan ne za a kaita indai Unguwar 300 House'

s ne”

“Unguwar ne Wallahi, amman Malam ba wacan gidan da muka je muka gani ba ne”

“Babu komai tun da har yace nan ai sai ku kaita kawai”

“To Amman Malam baka ga gidan ba, abun tsoro ne kar sai mun bada baya ya yanke mata kai”

Inna laure na jin

haka ta kada baki ta ce.

“Wane irin magana ne wannan Tumba? A maimakon ki jidadi ki yi mata fatan alheri sai ki fara wani magana marar dadi”

Ta fisge hannun Falmata ta jata zuwa ciki.

“Zo mu je, mu da zuciya daya muka aurar da ke, kuma muna miki f

atan alheri fatan na gari, yi bismillah ki shiga da kafar dama”

Falmata ta yi bismillah sannan ta shiga da kafarta ta dama kamar yadda Inna Laure ta umarta, Inna Laure ta shiga da sallama mata biyun da ke ciki suka amsa mata.

“Mashallahu”

Ta fada

sannan ta kai Falmata saman doguwar kujera ta zauna. Sauran yan'uwa da yan unguwa suka shiga sauran dakunan da kitchen suna dubawa, dakuna uku ne a upstairs din na farko ya bi na biyun kyau na biyun kuma ya fi na ukun kyau, sai dai kowane daki fararen kay

a ne, kicin din ma an cika shi da kaya ga abinci kala kala a store din. Khadija ce ta zo ta zauna kusa da Falmata ta kama hannunta ta rike, tana ta murmushi kamar ba ita ce ta gama kuka ba a dazun, ganin gidan da irin kayan dakin da aka zuba a gidan ga gid

an ya hadu iya haduwa. Nasiha sosai Inna Laure tai mata ciki har da ta addu'a.

“Karki kuskura wasa da addu'a kuma kar wani ya kawo miki wani abu yace ki baw mijinki ko ki amfani da shi da sunan kayan mata ki karba, kin ga Tumba nan ki yi hankali da ita,

ki san abun da zaki fada ko ta baki ki karba, sannan ki yi ta hakuri zaman aure sai da hakuri, idan kin samu ki taimaki babanki mamanki kuma ki bita da addu'a da sadaka Allah ya ba ku zama lafiya”

Khadija ce ta amsa da Ameen, sannan Inna Laure ta saki

hannunta ta hau sama ta duba dakunan ta sauko tana ta sanya albarka. Tumba dai na tsaye bakin kofar dakin ta kasa shigowa, gaba daya kanra ya dau zafi ga zuciyarta kamar zata fashe take sai tukiki take mata, gaba daya ta rasa ma kalar tunanin da za ta yi,

cikinta har murdawa yake.

Tana a bakin kofar har su Inna Laure da matan da suka musu rakiya suka fito sannan ta juya ta bi bayansu ta kasa cewa komai har suka shiga motar aka juya da su, sai gidan ya rage daga Falmata sai Khadija sai kuma sauran kawayen

ta da yan'uwa da suke sa'aninta. Khadija ta bude mata mayafi.

“Bude fuska ki ga gidanki, duba ki ga inda Allah ya kawo ki Falmata”

Falmata ta dago kadan tana kallon falon, sai ta ji kamar ba gaske ba daman ranar yau ta zame mata kamar a mafarki. Jan

mayafinta tai ta rufe kanta, a yanzu bata sna me zata yi ba kuka ko murna? Idan murna ne anya ya dace tai murna da auren tsoho ko da ace ya tara mata wannan uban dukiyar. Sai da aka maida su Inna Laure da Tumba sannan motocin suka je dauko ango.

Kawayen

Falmata na jin tsayawar motoci suka fara gyare gyaren jiki, Falmata kuma ta kara maida kanta kasa.

Abun da ya bawa mutane mamaki ganin abokan ango yara amman angon tsoho da har da hurhura, yana sanye da mayan kaya har da babbar riga shaddaraa sai shinn

ing take. Kusa da Falmata ya zauna yana ta kamshin turare kan ganinsa ka ga sabon ango. Duk wani abun da ake fada be ce komai ba iyakarsa murmushi, abokansa ne suka bawa yan matan da suke tare da Falmata kudin siyen baki har 200k, ba karamin mamaki ne ya c

ika su ba, har tsoron karbar kudin suka yi, sai Khadija ce ta karba har tana fadar wai a karo amaryar mai tsada ce, ita ce ta fara yin addu'a tana bada shawarwarin zaman lafiya, wani abokin ango ma yai nasa sannan suka Fita tare da kawayen amaryar domin aj

e su gidansu, sai da suka fice sannan ya mike tsaye ya isa bakin kofar falon ya rufe ya shiga kicin ya dauko cup da plate ya dawo kusa da ita ya aje a kasa.

“Amarya...”

Ya furta ta ainahim muryarsa, dan dagowa Falmata tai jin kamar irin muryar Sirle

em, sai dai bata dago ba.

“Dago ki kalli angonki mana”

Ya sake fada yana murmushi, hannu ta saka ta dafa zuciyarta ta lumshe ido tana kara jin kamar mafarki take. Zaunawa yai kusa da ita ya kai hannunsa ya dage mayafinta yana kallon fuskartaz fuskars

a dauke da murmushi, janye mayafinta yai baya ya sauke shi kasa, ya kai hannunsa ya dago fuskarta, har lokacin idonta a rufe ya ke. Matsawa yai kusa da fuskarta ya hura mata iska a idon.

“Bude idonki Teema”

Jin irin sunan da ya kirata da shi yasa tai

saurin bude idon zuciyarta na bugawa da mugun karfi. A zatonta za ta arba sa Sirleem ne sai tai arba da tsohon nan, sai dai a yau yana da haske sosai ga shaddar jikinsa sai kyalli take, tsabanin ganin da tai masa na farko da yake sanye da tufafi masu datt

i kuma da dauda a jikinsa.

“Teema...”

T kasa amsawa kuma ta kasa ce masa komai kana ta kasa dauke ido a akan fuskarta, wadansu siraran hawaye ne suka sauko mata, ta hade yawu ta sake hadewa.

“Teema... ”

A nan ma ta kasa amsawa. Mikewa yai tsa

ye yana murmushi ya cire babbar rigar jikinsa ya aje gafe, sannan ya kai hannu a fuskarsa ya fara cire furfurar dake fuskarsa. Mikewa tai tsaye da sauri ta zaro ido tana girgiza masa kai.

“Aa”

Ya sakar mata murmushi yana kokarin kai hannunsa ya rikat

a sai tai saurin ja da baya hawaye na sauko mata sosai.

“Aa”

Ta sake furtawa tana kara yin baya. Can kuma ta kai hannu ta fara murza idonta, domin gani take kamar mafarki take, matsawa yai kusa da ita zai taba ta sai ta fashe da kuka ta kara ja da ba

ya tana kuka mai karfi.

“Ohhh.....”

Ya furta yana kallon yadda hawaye ke sauko mata. Ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tana kuka mai karfi.

“Teema...”

Ya sake kiranta a karo na hudu yana matsawa kusa da ita. Bata amsa ba sai kuka take, hannay

ensa ya saka janye hannun da ta rufe fuskarta da shi yana kallon fuskarta.

“Falmata kukan ya isa haka”

Ta bude idon tana kuka.

Sai ya jata jikinsa zai rumgume tai saurin juya masa baya tana kuka gaba daya ta kasa gane komai duniyar ma gaba daya ju

ya mata take. Rumgume ta yai ta baya.

“Kina mamaki ne?”

“Ni ba kai aka aura min ba”

Ta fada daker saboda kukan da ya ci karfinta, sai yai murmushi ya juyo da ita ta rumgume ta.

“Ni aka aura miki, ta sigar da babu wanda ya san ni din ne”

Falm

ata ta dago kai ta kalli fuskarta sai ta ga shi din ne dai ba wani ba. Take ta girgiza kai.

“Ta ya? Ya ya? Ko dai mafarki na ke?”

Dogowa yai ya hade hancinsa da nata ta saita bakinsa saitin nata ya kama lip dinta na kasa ya fara sotsa a hankali sai t

a lumshe ido tana kokarin baya amman yaki bata dama, sai ma hannunsa daya da ya saka ya tallafo kunkurunta tai sama.



“Wow...”

Ya furta bayan ya cire bakinsa daga nata yana kallon fuskarta, ita kam ta rufe ido sai sauke numfashi take a hankali har lo

kacin zuciyarta bugawa take da karfi, ga jikinta sai wani yanayi yake bata na dabam.

“Yanzu kin yarda ni aka aura miki?”

Ta girgiza kai alamar no, sai yai murmushi mai sauti ya ja zuwa kan kujera suka zauna, ya rumgumeta jikinsa tsantsan.

“Daman n

a san ba lallai ne ki yi aurin yarda ba, domin ba ki zato ni ne wannan tsohon ba right?”

Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai y sake yin murmushi ya rumgume ta da kyau yana jinta har cikin ransa.

“Ban taba haduwa da wata halitta da nake tausayi ba,

kamar ke kin shiga taskun rayuwa kala kala, abun da nake miki fata shine ki samun jindadi”

Yayi shiru yana shafa bayanta a hankali.

“Na san idan na je neman aurenki a matsayin da kike ba za a bani ke ba saboda ba a son ki huta, hakan yasa na samu ma

i kwalliya ya lalata min jiki, na saka furfura kuma na je har kofar gidanku na yi sallama da step mother dinki, na fada mata na ganki a hanya kuma na bincika ance nan ne gidanku”

Yayi murmushi yana kokarin dago Falmata ya kalleta.

“And i got lucky in

a rokonta da neman ta shige min gaba sai ta amince tana ta jindadi, na bata number wayata akan ta kirani idan mahaifinku ya dawo sai ta karba tana ta murna, daga lokaci ne ma kara gane cewar baki da gata, sai tausayinki ya kara kamani”

Ya karasa yana ja

n hancinta.

“Babanki ya tambayi waye ni sana'a sai na fada masa, ina cin kasuwar kauye ne, ina siyo dabboni na siyar a kauye, kuma matana da yayana suna can, amman ke idan na aureki a nan zan aje ki, sai ya fada min na nemi so a gurinki, bayan mun yi ha

ka sai na kirata a waya na fada mata, sai tace kar na damu an bani yarinyar, haka ya kara tabbatar min cewar baki da gata, i tot ko wasa take sai gashi mahaifinku ya kira yace ya bani ke, kin san irin dadin da na ji a irin wannan lokacin?”

Ya saka hannu

nsa ya cire dankwalin da ke kanta ya sumbanci kitson dake kanta.

“Na yi murna sosai, irin murnar da ban yi zato ba, kuma idan aka tambaye ni a wannan lokacin ba zan iya fadar dalili ba, maybe saboda ina jin zan taimaki wata ne, ko kuma saboda ban tana n

eman aure da kaina an ba ni ba ne i can't tell”

Ta sake dagowa ta kalleshi har lokacin ji take kamar mafarki ne. Bakinsa ya kai ya sumbanci hancinta.

“I cant believe halalina nake tabawa, ashe abun yake da farinciki, so haka angwaye suke ji, ina jind

adi sosai, tun da aka daura aurena na samu kaina cike da farinciki, duk da yake Hajiya ta bata san na yi auren nan ba”

Falmata ta tashi zaune tana raba jikinta da nashi.

“Ban gane ba? To mutanen da ka tura fa?”

Ido ya kura mata yana ta kallon kyak

kyawar fuskarta.

“Biyansu nai, da mutanen da na gabatar a matsayin iyayena da yan uwana duka siyensu na yi, just saboda na tsirarta dake dga halin da kike ciki, da kuma halin da Momy take kokarin jefaki”

“Ni...?”

Ta nuna kanta, sai da ya sumbanci

goshinta sannan ya ce.

“Ke fa, ke ba zaki sani ba ne, amman na ji abubuwan da Momy take fada a lokacin da kuke kicin, zuciyata ta raya min cewar Momy zata iya miki dashe, saboda haihuwa ne abun da kadai take nema a yanzu, idan ba shi ba miyasa zata ce

wai tana fatar idan ta bukaci wani abu daga gareki ba zaki hanata ba, and zargina ya kara tabbata ne a lokacin da na ji tana kokarin inganta rayuwarki.

I know Momy tana da kirki da karamci, amman miyasa zata miki duk wannan cikin kankannen lokacin da b

ata gama shakuwa da ke ba, and na ga irin tashin hankalin da ya same ta a lokacin da na sanar mata aure za a miki, har take so hadaki da Ameer? Why? Maybe saboda ta samu cin ma burinta, a iyakar tunanina ya bani cewar idan ban aureki ba, rayuwarki zata shi

ga matsala, wa zaki aura? Me zai faru kamin aure duk babu wanda ya sani, domin a lokacin da naje neman aurenki da ace wani ne ba ni ba haka za a aura masa ke, a jefa rayuwarki cikin matsala, kowa burinsa yayi amfani da ke, ke kuma abun da kike bukata a yan

zu shi ne kulawa karatu da kuma ingantacciyar rayuwa, na daukarwa kaina alkawarin aurenki, sai dai bana da tabbacin kina so na ko akasin haka, iyakar abun da na sani shi ne auren zai fitar da ke daga kangi kuma zan tallafawa rayuwarki, sai dai na miki wani

alkwari guda daya”

Sai yai shiru har sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login