Showing 45001 words to 48000 words out of 304903 words

Chapter 16 - FULANI COMPLETE

da suka haska samaniya su kai mata ado, ga iska mai sanyi sai kadawa yake.

FADIME POV.

_A yau ba mafarki nai ba a fili na ji busar, amman ban ga kowa ba_

Bayan ta rubuta wannan ta sake buge wani fegin ta rubu

ta.

_Kuma yau ma naggen Bappa ta mutu, kuma kadangaren dake bandaki ya biyo ni_

Bayan ta rubuta ta rufe littafin ta aje a inda ta saba ajeshi tare da biron, haka take duk abunda ya faru a wunin ranar sai ta fada, idan tai mafarkin busar sarewar nan

ko mutumen nan da yake bayanta ma rubutawa take, ita ala dole ga yar boko.



“Fulani”

“Inna”

“Warre”

Ta mike tsaye ta fito daga dakin zuwa inda mahaifiyarta take zaune tana kiranta.

“Gashi nan an gama dauki ki je”

Sai ta gama kirga gidar

ko ta nawa ce sannan ta dauka ta dora saman kai, ta koma can kusa da dakinta ta dauki wani karen zana ta fice daga gidan. Dandali ta nufa tana tafe tana rera wakar da ake a dandalin ta Fulatanci, tun kan ta isa ta hango yadda dandali ya cika da mutane mas

u sana'a sun baza, masu samari kowa ya ja tashi gefe suna fira, masu rawa da wasar dandali na yi. An kunna wutar kara ta kama sosai ta haske ko'ina na gurin. A gurin da ta saba zama ta zauna ta aje gidar dake kanta a gabanta tana bawa idonta abinci.

Sa

i kusan sha daya sannan kowa ya watse wadanda sukai ciniki sun yi, masu samari kuma akai sallama kowa ya nufi gidansu. Ita ma kanta a gajiye ta dawo gida tana hamma, ko da ta iso Inna ta gyara mata gurin kwanciyarta sai kawai ta shige dakinta ta kwanta. Mi

salin karfe biyu suka fara jin tafiyar jakuna a rufin dakin na zana, can kuma ta fara kukan mage, kamin ta koma kiran sunanyen mutanen gidan. A take Fadime ta tashi zaune ta kwala wani uban ihu tana kiran sunan Babanta.

“Bappa Bappa Bapppa.......”

K

amar jira ake sai ta fara jin kokan magen a bakin bukkatar tana koyonta da sautin kukan magen.

“Bapkwau Bapkwau”

Sai kuma ta ji tafiyar dakuna a tsakar gidan, har da wani tuma suke suna direwa, sai kuma ta ji kamar kukan kare, a lokacin ne tai ihun

na gaske wanda ya farkar da Bappa daga bachin da yake domin shi idan sabo ya saba da irin wannan abun, dan haka baya hana shi bachi ita din dai ce da ta kasa sabawa kuma a duk lokacin da ta ji sai ta yi ihu ta kirashi. Da sauri ya budewa zagen da suka sako

wanda shi ne murfin bukkar ya fito, sai yai arba da bakar mage tsaye a kofar bukkar Fadime, cikin kuzari ya nufi inda tabaryar gidanta take ya dauk ya jefeta da ita da sauri tai tsalle ta haye saman bukkar tana masa kuka sannan ta sauka da can baya.



Bappa....”

“Kone Fulani addu'a akai idan kajji haka haba, kai kullum in zaka kwanta baka addu'a Fulani”

“Ni addu'ar wuya take ba ni”

Ta fada bayan ta ga mahaifinta a cikin bukkatar yana lalaben inda take ya riko hannunta suka fito, komawa yai da i

ta dakinsu ya saka ta a ta su bukkar, ya kunna ashana ya lika a kyandir yai mata shimfida a kasa, shi kuma ya hau saman gadon karan ya kwanta, mahaifiyarta na daga gefe kwance sai kwasar bachinta take.

*

🐄🐄

FULANI

🐄🐄

*

By Khadeeja Candy

*12*

SIRLEEM POV.

“Tun kwanan baya nai maka maganar, ya kamata mu fara hada lefe ba ka ce min komai ba”

Ya daga kansa ya kalli Mahaifiyarsa, kamin ya sake kallon Jarma wanda tun da suka gaisa be sake ce masa komai ba, sai kuma ya sake kallon mahaifiy

arsa.

“Yarinyar da aka ce sai ta gama makaranta, idan mu ka ce za mu hada lefe yanzu ai mun yi sauri”

“Ba dole sai ta gama makaranta za ayi auren ba, ba zan iya jira har lokacin ba, idan muka hada komai mu kai musu su ce ba za su karba ba”

“Amman

already an yi wannan alkawarin ai, be kamata mu tayar ba”

“To ni na tayar sai ya? Malam ka fara bada kudin da za a hada maka lefe kaji”

“To In-Sha-Allah”

Ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fice daga dakin. Da wani kallo mai kamar harara ta bishi

har ya fice, sannan ta kalli Jarma.

“Yaron nan idan ba mu yi da gaske ba, zai iya ba mu kunya”

Jarma yayi murmushi.

“Karki ji komai Hajiya, ai yana da biyayya ba zai tsaba miki ba, yanzu matsalarmu guda biyu ce, Mai Martaba da kuma Shattima, kum

a na sama mana mafita”

Hajiya ta mike tsaye duk da isar da take ji da kasaitarta ta isa bakin kofar ta saka mata key sannan ta dawo ta zauna.

“Wace mafita ce?”

Jarma yayi murmushi a karo na biyu sannan ya ce.

“Akwai wani gari can yamma da Kat

sina, garin wasu matsafa manyan arna, ance aikinsu kamar yanka wuka yake”

Hajiya ta dauke kai cike da kasaita.

“Na saba jin irin wannan daga bakinka, sai mun gwada kuma mu ga ribar yar adan ce, ni yanzu masu yi da gaske na ke nema”

“Wannan karon

masu yin da gaske ne Hajiya, domin su ba a musu aike sai dai mai sako ya isa da kansa, bari ki ji na fada miki a yadda aka ba ni tarihin garin basa bako, sai da sanin manyan gari gudun kar rayuwar bakon ta shiga hadari, wanda ba jinin garin ba baya zama ga

rin. Sannan aikinsu kamar yankam wuka ne, sha yanzu magani yanzu, tun kan ki fadi bukatarki za su sanardar ke dalilin zuwanki da inda mafita take, ke bari na baki wani labari gaba daya jama'ar garin ba su yarda da wani abu wai cigaba ba, na zamani ko mai m

oriyarsa, in yanzu kika ce a kashe miki Shattima take za su masa harbin kasko su aika shi lahira, mayan yan siyasa da masu kudin garin nan ance can suke yada zango dan biyan bukatunsu”

Cike da gamsuwa Hajiya take kallon Jarma, yadda ya koda mata mutane

da ace ba a gaske haka suke ba, zata iya yarda domin ta ji abunda ta dade tana nema.

“A ina ka san su Jarma”

“Wani abokina Malam sa'idu ne ya fada min su, shi mutumen Bandalo ne wani kauye da ke Katsina, sai dai cirani yake a garin nan sai dai shi d

in amintaccen na ne”

“Mutumen da zai iya rike mana sirrinmu ne?”

“Idan ma zai tona mana asiri, sai dai ya fadi cewar ina nemawa yata maganin aure ne, domin na fada masa yata Nafisa ce take fama da bakaken aljannu da suka hana ta lafiya kuma suka hana

ta, sai ya bani shawarar cewar da zan iya da naje can zan samu gani a take”

Murmushi mai kyau Hajiya tai tana kallon tv dakinta kamar da gaske hankalinta yana can.

“Jarma sarki wayau”

“Hajiya kenan, wani ai be isa ya san sirrin mu ba, sai dai zu

wan ne da kamar wuya a yanzu”

“Zuwa ba shi da wahala duk inda samu yake zan iya kai kaina, ba ni da kowa a katsina amman zan iya karyar zuwa wani gurin sai mu je can, matukar zan samu biyan bukatata Jarma, bana tsoron ratsa ko'ina zuciyata a bushe take”

“Zan neman takamaimen inda garin yake, da inda ya kamata mu sauka da kuma wanda zai magana jagora a cikin garin”

“Ka nemo Jarma amman ka tabbatar idan muka tafi ba zuwan banza za mu yi ba, za mu samo maganin ciwon mu”

“In-Sha-Allah”

Daga haka

yai mata sallama ya fice daga dakin, ita kuma ta mike tsaye ta isa gaban windows dakinta tana kallon bayan gidan, ji take kamar ta runtse ido ta ganta a garin.

FADIME POV.

A yau ma sai da ta rubuta domin ta yi mafarkinsu, sai dai a yau mutum bi

yu tai mafarki da nai busar sarewar nan da kuma dayan da yake tsaye a gefensa dukansu sun bata baya ne.

Daga bukkatarta ta fito ta nufo inda Inna da Amo suke zaune suna maganar sarautar garin.

“Ni ina ganin kamar abun nan zai zama rigima ne, tun da

duka yayan suna son sarautar fa”

Amo ta lashi baki da wata uwar tsaga da ta bata mata fuska tace.

“Mu dai na mu ido, ban da rashin hadin kai, yayan uku ba za su hakura su bar wa daya ba? Wannan ai ba burgewa ba ce”

“Ni ma dai haka na ce”

Fadim

e na zuwa ta zauna kusa da mahaifiyarta ta kwanta jikinta.

“To mage sarkin son jiki daga ni”

Da sauri Fadime ta dago ta kalli Inna wacce tai mata maganar.

“Inna jiya ma sai da mage ta zo”

Hanzarin tashi tsaye Amo tai ta dauki kwayar danyen ma

nshanunta ta dora saman kai.

“To muka zamu bunni sai wada hali yai”

Bata ko tsaya jiran abunda Inna zata ce mata ba ta saka kai ta fice daga gidan da saurinta, har kusan karo su kai da wata makociyarsu wacce ta kunno kai cikin gidan rike da takarda

hannunta.

“Maraba da Nene”

“Na yalle dam Inna Fadime”

“Janfelen”

“Na sukka

ɓ

e?”

“Janfelen, na wurinde?”

“Janfelen”

Ta zauna inda Amo ta tashi tana mikawa Fadime takardar hannunta.

“Fadime karanta mini injiya minana Mai samari yak a

iko min”

Fadime ta karbi takardar ta bude tana karanatawa, gaisuwa ce farko sai tambayar lafiyar mahaifiyarsa sannan ya sanar da ita sakon kudin da ya aiko mata dubu bakwai ta hanyar abokinsa, dan rani.

“Munafwuki amman be ba ni komai ba, sai wasika

, yalla ya aza babu me karanta min ita, bari naje yanzu na iske shi, mugun ba'adare”

Inna ta saka dariya ita da Fadime dan sun san halin Nene da kudi bata jin has. Nene ta fita daga gidan sai fada take ko sallama bata tsaya yi ma Inna ba.

“Fadime ta

shi ki tahi rahe ki samo mana diyam”

A take ta bata fuska ta fara shura kafafuwanta.

“Inna ko hutawa ban yi ba, yanzu na farka daga bachi ai”

“Wallahi ina sa miki sanda yanzu, wa zai dauko ruwan ni?”

Ta tashi tana zabure zabure ta dauki tulun r

uwa ta fice daga gidan, tana sanye da kayan fulani riga da zane cigiyarta a sake kanta kuma babu dankwali sai dan xaren kwaliya da suke daurawa akai ta raba gashinta gida biyu ko wane tsoro ya sauko bayanta.

A maimakon ta taje zafin da ta saba diban ruw

a sai ta nufi babban gulbi garin da ba kowa yake zuwa can ba, saboda nisansa da kuma girman da gurbi yake da shi domin gulbi ne da ya hada mayan jihohin yanki.

Baki baki ya tsaya ta saka tulunta cikin ruwan ya cika ta cire ta aje, tana waige waige ko z

ata samu wanda zai dorata kasancewar safiya masu kamun kifi sun gama sun tafi sauran mutane kuma ba su fara hada hada a gurin ba.

“Kai kado, ware”

Ta kwalawa wani bahaushen mutum da ta hango can nesa da ita. Amman ko kula ta be yi ba. Zaune tai a gu

rin tana ta wasa da ruwa da kafafuwanta, kamar ance saurara ki ji sai ta fara jiyo busar sarewar nan can nesa da manyan duwatsun da suke gefen gulbi, da sauri ta mike tsaye, ta fara waige waige sai kuma ta fara gudu tana nufar inda duwatsun suke, gudu take

sosai kafafuwanta babu talkami domin a can ta baro su gurin da ta cika tulun, manyan duwatsu ne wanda hanyewa samannsu ma wani sabon aiki ne amman a haka ta rika dafa tana rarrafe kamar dole har ta haye sama, mikewa tai tsaye tana kallon mutumen da take h

ange a saman wani dutsen da ke can nesa da ita yana busar, jikinaa babu riga sai walki sanye a kugunsa, ba zata iya tantance fuskarsa ba domin baya ya bata kamar yadda ta saba mafarkinsa, wani irin gwalo ido tai waje ta hangame baki tana kallonsa, ya mata

nisa sosai bare ta jira shi ya jita ko kuma ta jarasa kusa da shi, sai dai busar da yake ya karade ko'ina saboda yau a saman dutsen yai ta sabanin a da fa yake yinta a kasa ko a saman ice.

Sai da ya gama busar sannan ya juyo ya fuskanci inda ya bawa baya

, sai ya hango wata yarinyar da be tana gani ba ba kuma zai iya tantancewa ba tana kallon inda yake. Gangarawa yai ya sauka daga saman dutsen yana kallonsa tun tana hangoshi har ta daina ganinsa, a lokacin ne ita ma ta sauko da wani irin gudu kamar sabuwar

mahaukaciya, tana isa gurin tulunta ta zubar da rabin ruwan ta dauki tulun ta dora a kai ta saka talkaminta ta nufi gida da sassafar zuciyarta na bugawa da karfi kamar zata fito daga kirjinta, numfashin ma daker take yinsa. Ta kasa yarda cewar abunda take

gani a mafarki shi ta gani a zahiri, mutum ne ko aljanani? Miyasa yake zo mata a mafarkinta? Kuma a irin busar da ta ji yana yi a yau? Why ba shi da tufafi a jikinsa? Why yake busar a kusa da inda zata iya jinsa? Wanene shi? Duk tana bukatar wadannan amso

shin a yanzu. A bakin bukkar Inna ta aje tulun ta shige bukkarta, ta dauko littafinta ta fara rubutawa abun ya zame mata kamar wajibi.

AA POV.

Ba karamin dadi ya ji ba kudin da Nana ta saka masa a account, sai dai ko kadan hakan be bashi natsuwar

ya cigaba da zama a unguwar ba, domin a ganinsa kamar ana dana masa tarko ne, line ma cire shi yai ya aje ya daina kira da shi ya dauko wani tsohon line sa ya saka a wayar.

Baya tafiyar da zai yi nisa da gidansu, ba dan komai ab sai dan ganin yake kam

ar idan ya bar unguwar za a iya kama shi, ita kanta Anti Rabi ta lura da rashin natsuwarsa har take ganin kamar ma ya fita tsoro.

“Idan kana jin zaman ka a nan ba zai yi ba, ka koma cikin gari gurin Kawo ka zauna na kwana biyu tukuna, duk da dai na ga k

amar ba za a maka komai ba”

Ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta.

“Anti bayan faduwar da mu kai yarinyar ta sake ba ni kudi fa”

Anti ta zaro ido.

“Yaushe ka hadu da ita har ta baka kudi”

A dolen dolensa ya labarta mata yadda komai ya gudana da

kuma irin tsoron da yake ji da kuma zargin an dana masa tarko da yake.

“Ai Allah ya kara maka, AA wani irin mayen kudi ne kai? Sai ka jawa kanka fitina ko? So kake azo a kulle mu gaba daya kuma kasan ba mu da gata sai Allah, idan ma ba tarko ne ta dan

a maka ba, wata kila yarinyar sato kudin take ko kuma tana samo su ta hanyar da be dace ba, duk ranar da dubunta ya cika kai zata nuna”

A take AA ya ji kamar ya saki fitsari domin shi be kawowa kansa tunanin tana samun kudin ta hanyar da be kamata ba ne

, sai yanzu da Anti ta fada.

“Anty yanzu ya za ayi?”

“Ina na sanar maka? Ai kara ka koma can unguwar Waziri gurin Kawo Bala, idan ma wani abun za maka kara ace kana kusa da wani babba namiji”

Shiri yai ba dan yana so zai bi shawarar tata ba sai d

an be da yadda zai yi, idan har sata take tabbas zata jefashi a cikin matsala kara ma ya koma unguwar da bata sani ba ko da ta zo gidan ta tararda baya nan. A take ya shiga cikin dakinsa ya hada kala biyar ya saka a jakarsa ya fito.

“AA ka rika hakuri

da rayuwa, rashi ba hauka ba ne, kai maraya ne kana ta neman jefa kanka a cikin matsala, kai kawarda idonka daga neman kudin nan dan Allah, idan kai hakuri sai ka same su cikin sauki, amman wannan bude idon da kake sai ka ga ka samu kudin ta hanyar da be d

ace ba, idan kai hakuri zaka samu duk abunda Allah ya rubuta maka cikin sauki”

Anti ta fada cike da damuwa, ta san kanenta ba irin yan iskan samarin nan ba ne, ba zai aikata wani abu dan neman kudin ba, amman tana tsoron shedan da zuciya, domin son kudi

n AA ba na wasa ba ne ita kanta ta sani.

“Shi ma wannan yana cikin rabo na ne Anti, yarinyar Allah ya kawo ta ne dan na yagi rabona”

“Ko kuma ka yagi rabon wahala ba, gashi nan ai ka fara boye boye ka kasa komawa aikinka, ka kasa natsuwa”

“Ke dai

ke yi ta min addu'a kawai, Allah ya sa kar ta tona mana asiri, amman fa ko gobe ta bani sai na amsa”

“Idan an kama ka kar ma ka fadi sunana Wallahi”

Ta fada a fusace sannan ta shige dakinta, shi kuma yai murmushi ya fice daga gidan.

HAJIYA KAR

AMA POV.

“Abun da kike yi be dace ba Zainab, taya Shattima zai yi magana ki musa masa, a iya tunani Shattima ko cewa yai ki dauki wuka ki yanka ni za ki iya”

Da mugun mamaki Zainab ta kalli Iya.

“Iya kin san abunda kike fada kuwa?”

“Na sani,

biyaya ya kama ace kina musu ta kowane hali kamin ki gina kanki”

“Ba ki wulakanci da akai miki ba ne”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login