Showing 108001 words to 111000 words out of 304903 words
upstairs, be dade ba ya sauko rike da hijab green ya mikawa Falmata.
“Na gode Allah ya saka da alheri”
Falmata ta fada cikin muryar kuka.
“Amin Allah
yai miki mafita”
Momy ta fada tana jin wani irin tausayinta a ranta. Sannan ta sake kallon Ameer dake tsaye kusa da ita.
“Samo mata leda ta saka wannan”
“Momy na gaji fa”
Ya fada yan juyawa ya nufi hanyar kitchen, dan Murmushi Momy tai ta mai
da dubanta gurin Sirleem.
“Sirleem ya fadawa yarinyar gaskiya, saboda ta cire rai a aurenka tun yanzu, kasan Hajiya babu wanda take son ka aura sama da Nana idan har kana son farinciki a rayuwarka kuma dole ka bi umarninta”
Silently ya sauke ajiyar
zuciya yana kallon tsadadden agogon hannunsa kamar ba zai ce komai ba.
“Momy ba ki yi tunanin ya kamata ki taya ni wannan yakin ba?”
“Ba zamu zo ka auri karuwa ba...”
Ta bashi amsa kai tsaye sannan ta mike tsaye ta nufi upstairs ba tare da ta masa
sallama ba. Da kallo ya bita har ta haye sannan ya sauke kansa akan Falmata yana dan murmushin da be kai zuci ba? Ta ya zai fasa auren Mansura bayan yayi mata alkawari? Juyawa yai ya nufi kofar fita ba tare daya jira an kawowa Falmata ledar ba. Fitarsa da
minti daya Ameer ya fito rike da leda a hannunsa ya nufo inda Falmata take ya mika mata.
“Na gode”
Ta fada tana kokarin karba, ta dauki hijabin ta saka a ledar sannan ta mike tsaye ta nufi kofar ta bude, har ta fita Ameer kallonta yake. A entrance d
in ta tararda Sirleem tsaye yana jiranta, ganinta yasa ya sauka ya fara takawa ko kadan ruwan dake sauka be dame shi ba, ganin hakan yasa ita ma ta bi bayansa tana tafiya har suka fita gate din. Da kansa ya bude mata front seat ta shiga ta zauna sannan ya
zagaya ya shiga side dinsa ya mika mata hannu.
“Ina takardar da Momy ta baki?”
Ta mika masa, sai da ya karanta sannan ya kalleta da muryar da zata ji yace.
“Zan bi ta chemist na siye miki maganin”
Ta daga masa kai tana kara kama jikinta, sany
in ruwan sama sai ya hadu da na ac motar ga kuma ciwon da kanta ke yi sai suka sakar mata da zazzabi. Kallonta yai for few seconds sannna ya bude motar ya fita ya zagayo ta gefenta, bude side dinta yai ya kwantar mata da kujerar sannan ya mika hannunsa bay
an motar ya janyo jacket dinsa ya lulluba mata saman hijab dinta sannan ya rufe motar ya zagaya side dinsa ya shiga ya tashi motar sai da suka hau hanya sannan ya kashe ac, each and every three minutes sai ya kalli Falmata, rayuwarta yake tausayawa as her
age ace bata gida gaban iyayenta a irin wannan lokacin, yanzu idan shi wani mugun mutum ne me zai faru kenan? Gaban wani katon chemist ya faka motarsa ya fita ya bar Falmata a motarta, kamar fitarsa take jira bachi yai gaba da ita har ya siyo maganin ya da
wo cikin motar bata sani ba. Sai da ya kalleta sannan yai ma motar key suka hau titi.
“Heyy.... ”
Ya fada yana taba ta a hankali, sai ta bude ido ta farka a firgice, si ya kai bakinsa saitin kunnenta.
“Ina ne unguwarku ma?”
Ta fada masa, sai
ya gyada mata kai. This time around ita ce take ta kallonsa har suka isa cikin unguwar da be taba zuwa ba sai yau.
“Ina gidanku yake?”
“Ina gidanku yake?”
“Yana can ciki mota bata shiga”
“Okay, bari ruwan ya rage sai ki sauka”
Daga haka ya k
unna wutar motar ya soma nuna mata yadda zata sha maganin.
“Na gode Allah ya saka da alheri”
“Gobe misalin uku na rana ki dauki permission a gurin aikinki sai ki same ni a gidanmu na kai ki Momy ta duba kunnen ai kina so ko?”
Ta gyada masa kai al
amar tare da dagowa da sauri.
“Eh ina so sosai”
“Okay gobe ki musu magana sai na kai ki asibitin da take aiki a duba ki”
“Ina ne gidanku?”
“Gidan da kike aiki, amman b bangaren Ammy ba bangaren kishiyarta”
Shiru tai kamar mai tunani, sam bat
a dauka Ammy na da kishiya ba, sai yau.
“Oh ki fito bakin gate din ku ki tsaya idan uku na rana yayi zan same ki a gurin okay”
“Tau...”
Ta fada tana kallonsa sannan ta shiga kokarin bude motar.
“Ba zaki bari ruwan ya gama sauka ba”
“Zan iya
tafiya a haka, idan aka fadawa Babana an ganni a mota zai iya kasheni”
Kallon tausayi yai mata sannan unlock din motar ta bude ta fita sai kuma ta duko ta mika masa rigarsa.
“Gashi na gode”
Ya mika hannu ya karba, ita kuma ya juya ya nufi hanyar
da zata sadata da gidansu jikinta sai kamshin turarensa yake.
HAJIYA BABBA POV.
Ta kasa zaune ta kasa tsaye sai tunanin yadda zata bullowa lamarin Falmata take, ba Falmata kadai ba har Fadime da Sardauna so take ta sani, ganin abun da mutanen
suka fada ya fara tabbata yasa ta fara jin tsoron.
Wayarta ta dauka ta kira amiyarta Hajiya Talatu, bugu daya ta dauka da far'arta, sai da suka gaisa sannan ta labarta mata halin da take ciki.
“Kin san me Hajiya? Mataki zamu dauka tun yanzu, waya s
ani ma ko wani hadin kai ne da ita Ammyn?”
Hajiya ta dan yi shiru tana nazari.
“To ni yanzu ya zanyi? Tsoro nake kar mu mata asiri ta tona mana asiri”
“Ai dole shi za'ayi idan ba haka ba taya zamu koreta a gidan? Dole sai da asirin nan”
“Kika
sani ko abun da zai saka aikinmu ya wargaje kenan? Ni fa tsoro nake ji, ki samu lokaci ki shigo gobe mu yi shawara abun da ya kamata wannan maganar bata waya bace”
“To kenan Hajiya zan shigo gobe idan Allah ya kaimu”
Daga haka ta aje wayar, zuciyarta
na raya mata yi ma Falmata asirin da zata bar gidan ta dayan bangaren kuma tana jin tsoron kar ya zama na ko tana da aljanu da za su tona mata asiri su fadi abun da tai. Mikewa tai tsaye ta fara safa da marwa, tunanin yadda zata bullowa lamarin take, wann
an karon sai da ta kai karshen dakinta sai kuma ta juyo da sauri ta dauki wayarta number yarta ta lalabo ta aika mata kira, Jurry dake kwance saman gadonta ta mike tsaye tana kallon kiran mahaifiyarta.
“Hello Hajiya”
“Juwairiyya kina ina?”
“Dakin
a, lafiya dai”
“Dakina lafiya dai?”
“Ba lafiya ba, zo ki same ni yanzu nan”
“Okay”
Ta aje wayar tare da mikewa tsaye gaba daya ta fito daga dakinta ta nufi dakin mahaifiyarta, daf da zata shiga dakin Sirleem ya turo kofar falon ya shigo tufafin
sa a jike shakaf da ruwa.
“Ya Sirleem ina ka fito haka?”
Ta tambaya ganin yadda ya jike bayan ta fi kowa sanin yayan nata baya son ruwan sama ya taba shi.
“Somewhere...”
Ya amsa mata ba tare da ya kalli inda take ba, ya nufi corridor da zai s
ada shi da dakinsa. Tsayawa kallonsa tai sai da ya shige sannan ta tura kofar dakin Hajiya Babba ta shiga. Bakin gado ta samu Hajiya zaune tana ta faman sauke ajiyar zuciya.
“Hajiya lafiya dai?”
“Ina fa Lafiya? Juwairiyya muna cikin matsala, abun da
mutanen nan suka fada ya fara tabbata”
Jurry ta zauna tana yi ma mahaifiyarta kallon rashin fahimta.
“Ban gane ba...”
Sai da Hajiya ta tunasar da ita abun da bokan nan ya fada n cewar Falmata Fadime and Sardauna za su lalata musu shiri sannan ta
dora da..
“Kuma yarinyar nan tana cikin gidan nan tana aiki, ita take rainon yaran Shattima...”
“Bakuwa ce amman ko?”
“Nima haka nake tunani bata dade da fara aikin ba”
“To yanzu ya kenan?”
“Mafita nake nema na rasa yadda zan yi, gana daya
kaina ya kulle, tsoro nakr kar na shiga malamai ta tona min asiri ban sani ba ko tana da aljanu ne, gaba daya hankali ya kasa kwanciya, gashi a ba a bangaren nan take ba balle na koreta”
Hajiya ta karasa tana dauke numfashi kana ganinta kasan a tsora c
e take sosai.
“Ko ba a nan take ba, zamu iya yin abun da zai saka a koreta mana”
“Me zamu yi me zamu yi Jurry ace mun saka ido akan yarinyar da bangarena take ba? Daga nan ai wani tsonon asirin ne kuma”
“Ni na san abun da zan yi Hajiya, yanzu yar
inyar tana ina?”
“Tana bangaren Ammy zaki ganta wata baka haka bata ji sosai ba zata wuce sa'ar Nana ba”
“Bana shiga bangaren Ammy amman zan ganta gobe inshallah, na san abun da zan yi”
“Me zaki yi?”
“Na san me zan yi Hajiya ai ba komai ne za'a
tsaya ace sai an yi asiri ba, sometimes we need to work with our brain”
“Kar ki yi abun da zai kara jefamu cikin matsala fa”
“Ki yarda da ni Hajiya bari dai, na fara ganin yarinya yanzu”
Hajiya ta sauke ajiyar zuciyata ba dan ta natsu da abun da
Jurry take fada ba duk da bata san abun da zata aikata din ba.
SHATTIMA POV.
Ya sauke wayar daga kunnensa yana jin wani iri, he don't know why Baba Waziri ke son ganinsa, ya san mo ma minene Magana ce mai muhimmanci tun da har ya bukaci ganinsa, kam
ar yadda ya kira shi a yanzu ya sanar masa cewar yana dakin Ammy yana jiransa. Mikewa yai tsaye yana busar da iskar bakinsa, iskar backyard din da yake tsaye yana bugunsa yana ratsa ko'ina na jikinsa. Juyowa yai ya turo glass door din ya shigo cikin falon,
kai tsaye ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin yayansa, he just want to make sure suna lafiya kamin je ga kiran da Baba Waziri yake masa, a hankali ya tura kofar dakin ya shiga, sai ya samu wutar dakin a kashe sai bedside lamp dake haska su, ac kuma an
kunna shi kadan ya lullube su kamar yadda yake bukata, karasa yai kusa da su yai musu addu'a ya sumbance su sannan ya mike tsaye a hankali ya fito daga dakin. Kai tsaye ya nufi dakin Ammy gabansa sai faduwa yake, sai da ya kwankwasa sannan ya tura ya shig
a, Ammy na zaune kan prayer mat Baba Waziri kuma na zaune a saman kujerar dake facing din gadon Ammy. Sai da ya gaisa da Baba Waziri sannan ya zauna kusa da shi yana kallon fuskar Ammy, domin ta fuskarta yake gane komai idan irin wannan ta taso a tsakanins
a da Baba Waziri ko da Mai Martaba, sai dai wannan karon ya lura kamar Momy ma da kanta bata san komai ba. Baba Waziri yayi gyaran murya sannan ya ce.
“Shattima dalilin kiran abubuwa ne guda uku, masu muhimmanci a gare ni kuma a gareka, ban fadawa kowa
wannan ba, ciki har da mahaifiyarka, ni na yanke wannan shawarar da kaina, kuma bana fatan zaka saba min”
Shattima yayi sunkuyar da kansa yana sauraren Baba Waziri. Shiru Waziri yai na wani lokaci sannan ya cigaba.
“Abu na farko, ina son ka yi aure
, domin zaman ka a haka ba zai yiyu ba, ba zamu zuba maka ido kana babba a cikin gidan nan ba, kuma ace kana zaune babu mata”
Da Sauri Ammy da Shattima suka kalleshi, kamin Shattima ya maida dubansa gurin Ammy.
“Amman Waziri kasan matsalar Shattima
ba tun yau”
Cikin bacin rai Baba Waziri ya daga mata hannu.
“Karki sake min wannan maganar, ya kike kokarin maida shi ya zama wani abun tsoro, kai kana da wacce kake so?”
Baba Waziri ya karasa yana kallon Shattima da yai mutuwar zaune a gurin.
“Aa ba ni da ita Baba”
“To kaje gidana ka duba, Jayyada ko Maijidda gidan daya daga cikinsu tana maka”
“Baba ka san matsala ta fa, ni kaina yanzu tsoron kaina na ke”
“Idan baka son su ka fada min yarinyar da kake so, ko yar waye ce zan nema maka
aurenta, idan kuma nemowa zaka yi zan baka dama”
Cewar Baba Waziri with serious face. Shattima ya aje numfashi a hankali sannan yace.
“Baba babu matar da zata yarda ta auri a halin da nake ciki, da dai mun dan jira n wani lokaci”
Kamin Baba Wazir
i yace komai Ammy ta ce.
“Jayyada ai ta yi kankanta Nana ma ta girme ta ai, sai dai Maijidda kuma bana tunanin Hajiya Talatu zata yarda a aurawa ƴarta Shattima”
“Talatu ke da ikon Maijidda ko ni? Ya in magana kina kawo min wata magana Ammy? Ni nai r
a'ayin aurawa Shattima yata, ko ke baki isa ki hana ba, balle kuma Talatu da take karkashina, idan kika ga abun nan be yiyu ba, Shattima ne da kansa be amsa tayi na ba, amman ni haka nai fata”
Baba Waziri ya karasa da muryar dakd amsa sunansa na cikakke
n namiji mai magana daya. Shattima ya hade yawu a hankali ba tare da yace komai ba, ya san yadda Hajiya Talatu ta tsani Ammy balle kuma ace yarta ta aure shi bayan idan mace ta aureshi mutuwa take, da ma ace abokiyar zamanta ce Hajiya Mairo, duk da yasan i
ta ma ba zata so rasa yarta ba, shi kansa ya san karfin hali ne kawai irin na Baba Waziri b dan bayan son Maijidda ba balle kuma Jayyada da take karama.
Ammy ta aje carbin hannunta ta fuskanci Baba Waziri.
“Ba ina son hana hada auren Maijidda da Sh
attima ba ne, ina duba makomar Maijidda ne, lamarin Shattima kullum gaba yake ba baya ba, ko a kwanaki baya sai da na tutube abokinsa Ra'ees daya nema masa aure a can Katsina ko da yar kauye ce ba tare da sanin Shattima ba, amman abun ya gagara karshe kira
na yai ya fada abun da ya faru na rashin dadi kuma yace shi ya cire hannunsa a ciki”
Baba Waziri yayi mata wani kallon Mamaki.
“Har yaushe ke da kanki zaki. zauna kina chaf danki? Wallahi da ba ke bace kika fada min wannan maganar a yau akan Shattim
a jinina Wallahi da sai n baki mamaki, wannan dai umarni ne B shawara ba, dole ne Shattima ya sake aure”
Shattima da uffan be ce ba, sai tunanin Fadime ya fado masa a rai, daman shi aka je nemawa aurenta? Ita kuma ta zo tana ta neman Ra'ees, shi kuma ya
na ta boye, sai ya yanzu ya tuna maganar Ra'ees na cewar wani abokinsa yaje nemawa aure. Ban ankaro ba ya ji Baba Waziri na dora masa wani umarnin.
“Abu na biyu zan mu kara fitar da Mai Martaba waje, domin a kara duba lafiyarsa ba mu san abun da Allah z
ai yi ba”
“Bana son na shiga tsakaninka da dan'uwanka, amman shi kansa baya son fita yanzu, kuma na dora shi akan magani da mun jira muga abun da Allah zai yi, kuma na ga an fitar da shi ba sau daya ba, amman kamar yafi samun sauki a gida”
“Kai kwara
ren likitan zuciya ne, mu bari kwararen likitan kwakwalwa ya ganshi pls, idan ina maganar dan'uwana ku daina saka min baki, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan nasa, kullum da abu na ke bachi nake tashi, be kamata mu saka masa ido haka ba”
“Haka n
e ni kaina abun na damuna, kuma ina son ka saka har saukar qur'ane ayi masa, ba a san inda rabo yake”
Cewar Ammy cike da damuwa. Sai Baba Waziri ya amsa mata da cewa.
“Duka za ayi da yarda Allah”
Ya sake fuskarta Shattima yana fada masa abu n kar
she.
“Abu na uku kuma na karshe, dole ne ka nemi transfer ka dawo nan da aiki, ba zai yiyu ka zauna a can ba bayan kai ne babba a masarautar nan, Ammy na bukatarka Mai Martaba na bukarta, wasu abubuwan za su iya tasowa sai ace sai na jira ka ka zo ko k
uma ace kana ina ace Katsina kake aiki? So this one ma Umarni ne dole ka dawo garin nan da aiki”
Shattima ya kalli Ammy wacce ke murmushi dukan abubuwan da Baba Waziri ya fada sun mata 100% musamman dawowarsa a nan daman ta dade tana son ya nemi transfe
r sai yace mata baya son yana kusa da masarautar nan saboda abubuwan da suke faruwa. Ko kadan umarnin Baba Waziri ma dawowa garin Yola da aiki be yi ma Shattima dadi ba, amman be isa yace a a ba tun da har ya furta masa cewar umarni ne.
“Zan iya baka da
ma kai tunani akan yarinyar da kake so, domin ba zan maka dole ba, ban ce dole ka so yar wajena ba, amman aure dole ne you can go...”
Shattima kamar mai jira ya mike tsaye da sauri ya fice daga dakin yana cikawa bakinsa iska.
FADIME POV.
Was
he gari tun da farar safiya Fadime ta dauko littafin da biro, duk abun da ya faru sai da ta rubuce shi tsaf sannan hankalinta ya kwanta. Bayan ta gama ta fito waje tana lekon dakin Amo, sosai take jin kamar ta labarwa wani a sanadinta komai ya faru kuma ta
na tsoron kar Bappa ko Inna su ji, kusa da Inna ta zo ta tsaya tana gaishe ta kamar ba ita ba.
“Inna naje na debo ruwa?”
“Eh amman kamin ki fita ki yi addu'a dan Allah”
Inna ta amsa mata da halshen fulantanci, da sauri Fadime ta nufi inda tulun y
ake ta dauka tana fadin.
“Ai na yi addu'a kuma