Showing 225001 words to 228000 words out of 304903 words
sai ta fito ta tsaya daga bakin kofa.
“Waye ne?”
“Hajiya, wai wasu ne s
uka zo, dogarawa a mota, wai sun ce na sallamo ki”
“Ni”
Ta nuna kanta gabanta na mugun faduwa, ko ba a fada mata ba ta san daga inda suke, sai dai ba kiran ba ne abun tsoro, dalilin kiran ne abun firgitarwa, what if Fadime ta fada musu wani abu ne su
ka nemi a kirata? Ko dai minene bata isa ta hana kanta zuwa ba, hakan yasa ta share gumin daya karyo mata ta koma ta dauko mayafinta ta fito tana tafiyar kamar bata son fita yadda gabanta yake faduwa sai ka rantse da Allah zuciyarta zata fasa kirjinta ne t
a fito, sai da ta kai bakin kofar fita sai kuma ta ji kamar fitsari ya cika mata mara ta juyo ta dawo dakinta da sauri ta shiga bandakin tai fitsari, sannan ta fito cike da tunani kala kala ta fita. Bata raina kanta ba sai da tai arba da dogaran tsaye jiki
n wata 406 su biyu suna jiranta, abun ka da an saba sai ta sakar musu murmushin karfin hali tana sama gaisuwar da suke mata.
“Lafiya dai?”
“Inshallahu lafiya kalau ne, Jekadiya ta ce mu dauko ki Ammy na son ganinki”
“Ikon Allah Ammy da kanta? Ya a
kai kuka gane gidan?”
“Jekadiya tai mana kwatanci, duk da haka ma sai da mu ka yi tambaya sannan muka gane”
Dayan ya bude mata kofa sai ta nufi motar ta shiga kamar ba komai, sai dai zuciyarta na ta zillo gumi sai karyo mata yake, babu abun da take h
ararowa sai Fadime, gashi gidan Sarauta ne asirinta na tonuwa kowa zai ji. Take ta nemi natsuwarta da dakiyar zuciya ta rasa, suna isa cikin masarauta ta sake jin mararta ta cika da fitsari, sai dai bata iya cewa komai ba ta nufi bangaren Ammy tana tafiya
kafafuwanta na mata nauyi ga wani uban naso ta da saka fuskarta a gaba. Ta dade a tsaye bakin kofar kamin tai jihadin kai hannunta ta kwankwasa kuma, kamin a bude mata ta share gumi ya kai sau hudu, da ace tana da hawan jinin da tun a lokacin yayi azalinta
. Jekadiya da kanta ta bude mata kofar falon, tana ganin Iya ta washe mata hakora tana dariya kamar ba komai.
“Aa Iya har an iso, shigo Ammy ke son magana da ke”
Ta wangale mata kofar dakin, Iya ta yi mata murmushin yake tana cira kafarta ta nasa cik
in falon, babu kowa a falon sai tv taku daya biyu Iya ta ji wanin abun da ke hana mayu da macizar da aljanu zama lafiya, wato hantiti da tsakin kuka da kuma ƙashi, a rikice ta juya da wani irin sauri ta fice daga falon tana toshe hanci.
“Kai kai yau dak
in Ammy ne yake wannan warin haka?”
“Me kika ji?”
Jekadiya ta tambaya tana mata kallon mamaki domin Ammy ta fada mata komai. Tambayar da Jekadiya tai mata yasa ta dawo hayyacinta har ta tuna abun da ta furta, gaba daya sai ta ratsa natsuwarta, ta rik
a jin warin yana biyota har waje, daman maye baya zama idan irin wannan hayakin yake.
“Jekadiya ki fada Ammy zan je na dawo”
Kamin Jekadiya tace komai Iya ta juya da sauri ta fara sauko kasa sai wani abu take kamar mahaukaciya gaba daya notin kanta y
a kwance, duk yadda Jekadiya ta so tsayar da ita sai ta ki saurarenta, gaba daya jin tai bata bukatar zama a cikin gidan ma, sai da ta fita waje ta tari napep ta hau sannan hankalinta ya so ma kwanciya jin ta fara shakar iskar unguwarsu, sai a lokacin ne w
ani tunani ya zo mata, wata kila Ammy ta yi haka ne saboda ta gasgata zancen Fadime, saboda ta gano idan da gaske ita din mayyace ko kuma a a, kuma yanzu ta san dole ne zata yarda tun da har ta kasa shiga cikin falon balle har ta isa dakin Ammy.
Wani iri
n bakinciki da bacin rai ne ya kusanceta, bakincikin da ko mutuwa bata kai shi
ɗ
aci ba a gurinta.
“Ammy ta yi haka ne saboda ta gane ko?”
Ta furta a fili tana jin wani tukikin bakinciki na ta so mata. Mai Napep din ya juyo ya kalleta a zatonsa ko ma
gana take masa ne, sai kuma ya ga wani gurin take kallo rai a bace. Kunya ta zame mata biyu, ga ta abubuwan da ta aikata wanda ta san izuwa yanzu Fadime ta fada musu komai ga kuma wata karin kunyar kasa shiga falon Ammy da tai.
“Ba ki tabbatar ba, yanzu
zan tabbatae miki, kin yi wauta na kokarin kama ni ta wannan hanyar, dole ne na yi abun da zai dauke mu ku hankali kuma kamin a kara wani abun ya kamata wannan kam na zanja salo”
Wannan karon a cikin fai furucinta tana sauke kafarta kasa daga kam Napep
din.
“Hajiya kudinki 500 ne”
“To jira ni ina zuwa”
Ta juya ta shiga cikin gidan domin bata fita da komai ba, kana ganin tafiyarta kasan ba lafiya ba kamar an korota haka ta shiga cikin falon ta, ko ta can Zainab dake kwance kan doguwar kujera tan
a waya bata bi ba, ta wuce dakinta ta dauko jakar kudinta ta ciro 1k ta fita sai sauri take kamar zata tashi sama.
Bata ma isa gate din ba ta kira mai gadi ta mika masa kudin.
“Ka bawa mai Napep yana nan waje, ka karbo min canjina”
Yana karbar kud
in ta juyo da sauri ta dawo cikin gidan. Fuuuu ta wuce dakinta Zainab dai sai binta take da kallo, da ada ne zata iya tambayarta mi yake faruwa amman a yanzu iyakarta da ita ido, duk da tana ganinta cikin rashin natsuwa.
Iya na shiga dakinta ta maida ko
far dakin ta rufe, ta zauna bakin gadonta tana mamakin abun da Ammy ta shirya mata.
“Tun farko ita ya kamata ace na fara kamawa, da yanzu bata samu damar yin wannan abun ba, na yanzu tana can kwance tana jinya kamar mijinta, amman saboda na kyale ta har
ta samu damar yi min haka? Ta tona min asiri a cikin Masarautar nan?”
Ta mike tsaye tana jin kamar ana sukanta a zaunen da take.
“Ko da yake ba laifin Ammy ne kadai ba, har da laifin yarinyar nan Fadime? Amman na san maganin abun”
Ta fada zuciya
rta na raya mata ta yanke kurwar Maijidda tun a yanzu ba sai biki ya matso ba ko kuma an yi aure kamar yadda take yi ma sauran, domin idan tai tun a yanzu babu wanda zai zargeta kuma hankalin Ammy zai koma a can, sannan bata san abun da aka shirya mata ba
a nan gaba.
FADIME POV.
Wata hadimar ce ta shigo falon da su Bappa suke tana sinne kai kasa ta ce.
“Shattima ya turo na tafi da Fadime idan kun kallama”
“Ki tafi da ita ina zaki kaita?”
Bappa ya tambaya, kamin hadimar ta amsa Fadime t
a mike tsaye tana fadin.
“Cikin gida can gurin matar sarkin, ai a can nake zaune”
“To yayi kyau, kuma idan kin je ki yi musu shirme da kika saba, Wallahi ki kwantar da hankali ki san irin abubuwan da zaki fada ko ki yi, kina yin wasa Wallahi za su da
ure ki, kuma Wallahi kin dauro har abada, dan sarki babu ruwansa da makantarki”
“Bappa wai sarki ne babba?”
Fadime ta tambaya jin yadda Bappa yake tsoratata.
“Sarki ne babba, garin Yola fa gaba daya, kamar ace sarkin Katsina”
Ta zaro ido tana j
in wani irin kimar Shattima da kwarjininsa suna kankwaro mata, sai a yanzu ta gane ya sarautarsu ta ci uban ta su Wasim da take gani da girma, sai a yanzu ta gane dalilin da ya saka baya son yawan magana kuma yake dadewa kamin ya bata amsa wani lokaci.
Ta mika hannunta ta inda take zaton hadimar na gefen.
“Mu tafi”
Hadimar ta kama hannunta suka fice daga falon Bappa sai nanata mata yake ta bi a hankali da yaren fulatanci. Suna tafiya Fadime na tuna abubuwan da suka faru tsakaninta da Shattima, ita
ma ai ya kamata ta gane babbar Sarauta ce tun daga jin gidan sama da suke da kuma yadda suke da yawan hadimai, kuma ga sanyi ac da kayan dadi a ko'ina.
Har cikin fadar Ammy Hadimar ta shiga ta ita sannan ta saki hannunta.
“Ina za ki je?”
Bata samu d
amar amsa mata ba sakamakon hannun da Shattima ya daga mata sai tai saurin ficewa ta tare da tace da Fadime komai ba.
“Ke ina kika kawo ni”
“Wani guri”
Ta ji muryar Shattima daf da ita, shiru tai kamar ba ita ba tana jin girmasan da kwarjininsa n
a kamata, sai ta ji ta kamar yar wata kudan zuma a wata duniyar babbar duniya, gabanta ya shiga bugawa da karfi abun da bata saba ba.
“Kin ga Babanki?”
“Eh Ranka ya dade”
Ya wara yana murmushi.
“Ni ne ranka ya dade a yau kuma?”
“Dan Allah ka
yi hakuri da duk abubuwan da na yi maka”
Ya juyo da ita tana fuskantarsa duk da kasancewar bata ganinsa.
“Me kika min?”
“Abubuwa da yawa ba za su kirgu ba”
“Baki min komai ba, na san ai ba ki san komai ba, kuma ko kin sani rayuwarki ki simple
ba lallai ne komai ya burge ki ba”
Shiru tai ta natsu sosai tana saurarensa kamar ba ita ba.
“Ina son nai miki sallama ne, na siya muku ticket jirginku zai tashi 7am ba lallai ne na shigo gida kamin lokacin ba, so i wanted to say goodbye”
Ta yi sh
iru tana wani abu na rashin jindadi yana ziyartarta duk da kasancewar tana son gida kuma tana son kasancewa tare da Bappa da Inna da kauyenta, sai dai a yanzu da Shattima yai mata wannan maganar sai ta ji kewarsa da dan sabon da tai tare da Nana ga dadin d
a take ci kullum.
“Ranka ya dade, yanzu shikenan ba zan sake ganinka ba?”
Ya lakace hancinta yana murmushi.
“Daman kin gan ni ne?”
“Ina nufi ba zan sake jin muryarka ba?”
“Yes ni ma ba zan sake ganinki ba, zai je ki cigaba da rayuwarki kamar
yadda kika saba, kuma i hope idonki zai bude soon i mean very soon”
Ta kasa cewa komai sai saurarensa take tana jin kamar ta fashe da kuka. Ya cire agogon hannunsa ya kama hannunta ya saka mata.
“Ga wannan ki rika tunawa da ni, ban taba haduwar da m
acen da na ji bana son rabuwa da ita ba irinki, tun a ganin farko da na yi miki a Katsina kika kwanta min a rai, to be frank komai na ki yana burgeni i like you”
Ya fada yana kallon cikin idonta dake cike da kwalla. Ya dade yana kallonta kamin ya kai ba
kinsa saitin kunnenta ya rada mata.
“Bye Allah ya tsare hanya”
Lumshe ido tai hawayen idonta suka sauko, kashe kunne tai tana sauraren sawun kafarsa har ya fice daga falon, sai ta rage tsawonta ta zauna a gurin ta share hawayen da bata san dalilin zu
barsu ba. After like 5 min ta ji sallamar Jekadiya ta shigo gurin sannan ta kama hannunta.
“Ta so mu je yace za ki yi ma Ammy sallama, sai na maida ke daki”
Fadime ta mike tsaye tana jin kamar a barta tai ta zama a gidan duk bata iya shaidar fuskar k
owa a gidan saboda bata gani. Babu abunda take sai saurare har suka isa dakin Ammy, tana Jekadiya ta rage tsawo ita ma ta rage ta zauna kasa.
“Ammy Shattima ne ya ce na kawo ta ta yi muku sallama”
Ammy dake kishimgide ta dago tana dubanta tare da cir
e gilashin idonta tana murmushi.
“Yarinyar mai abun al'ajabi, ki zo mana da abubuwa zuwanki ya zama mana alheri, yaushe za ku tafi?”
“Gobe ya ce, da karfe bakwai za mu hau jirgin sama”
“Yayi kyau Allah ya tsare hanya, kamin ku tafi Jekadiya zata b
a ki tsabarki”
“Na gode ranki ya dade Allah ya saka da alheri”
“Godiya take, godiya take Ammy Allah kara miki lafiya”
Jekadiya ta fada da dariya sannan ta sake rikon hannun Fadime suka fito daga dakin. Dakin Nana ta sake maida ita, dakin da take k
omai a ciki wanka abinci canja tufafi duk a dakin take, Nana ta bata kusan kala biyar duka sabon kaya da zata rika canjawa idan ta yi wanka.
A dakin ta wuni, abincin ta na dare ma a dakin aka kawo mata, sai dai bata wani ci da yawa ba, kadan ta ci ta bar
sauran, ta tashi da kanta ta shiga bandaki ba tare da ta yi addu'a ba, daman can addu'a bata dame ta ba, tana tura kofar bandakin ta shiga sai ta ji wani irin iska da yanayi kamar ba a bandaki ba, juyowa tai ta zimmar fitowa sai ta ji ta taka abu kamar ti
ti juyowa ta sake yi ta taka gaba sai ta sake jin abun, ta kara yin baya sai ta sake jin abun. Can kuma ta ji wani irin kara ya cika mata kunne gashi bata ganin komai sai duhu, tsaye tai a gurin kamar an dasata. tana ta sauraren karar da bata san ko na min
ene ba, sai dai tana jin sautin kamar ya mata yawa a kunne, can ta soma jin sautin bugun wani abu kamin ta fara jin sautin muryar mace.
“Lalalala...lafiya ...kika tsaya a tsakiyar titi?”
“Titi”
Fadime ta maimaita tana juyo ta inda take jin sautin
muryar matar, kamin matar ta sake magana mijinta ya karaso ya jata ya maida bayansa da dayan hannunsa yayinda dayan yake rike da jariri.
“A ina nake?”
Ta tambaya tana jin kamar ta taba jin abun da ake kira da titi. Matar ta kalli mijinta mijin ma ya
kalleta.
“Bana ganin komai sai duhu dan Allah a ina nake?”
Fadime ta sake tambaya, sai matar ta waiga tana karewa unguwar dake cike da haske a ko'ina kamar ba dare ba.
“Daga ina kika zo nan? Waya kawo ki nan?”
“Ni ma ban sani ba, ban sani ba”
Ta fada hawaye na sauko mata.
“Ya sunanki?”
“Ban sani ba, ya sunana to?”
Ta dafe kai.
“Miyasa na ake jin kaina kamar ba komai ciki? Miyasa bana ganin komai sai duhu a ina nake?”
Ta fashe da kuka ta durshe a gurin. Matar ta kalli mijinta c
ike da tausayi.
“We need to help her”
Wani kallo yai mata na mamaki, kana ganinsa kasan irin miskilan mazan nan ne da magana ke musu wahala.
“Aliyu bana son na ga mutum a cikin damuwa ban taimaka masa ba, na san yadda ake ji, ni ma babu irin wahal
ar da ban sha ba kamin rayuwa ta kawo ni a nan, har bara na yi, ko ka manta? Babu irin wahalar da ban yi ba babu irin wulakancin da ban gani ba, bana son na ga wani a cikin damuwa na kasa taimaka masa”
Dauke kai Aliyu yai ko kadan baya son tunawa da hal
in da matarsa ta shiga a baya, domin har yanzu yana ganin shi ne silar komai saboda dashen kodar mahaifiyarta da akai ma matarsa uwargidansa, his late wife Rahma.
“Fine idan kuma ba mutum ba ce ba? Ataa think please”
Ya fada kamar ana matso maganar d
aga bakinsa.
“Daga gani mutum ce, aljana ta yi wuri ta fito mana haka, ko isha'i fa ba a gama ba wani gurin, idan mu ka tafi muka bar ta nan zata sha wahala kamin ta samu taimako, ka san unguwar nan fa kowa na cikin gidansa, kamin ka ga wulgawar mota ma
aiki ne, ko ma dai wacece mu da zuciya daya zamu yi mata taimako, Allah ba zai bata ikon cutar da mu ba”
Kallonta kawai yake yana gyara takwaransa dake kafadarsa. Sai ta saka hannayenta biyu ta rike kunnenta.
“Please Hamma na....”
Uffan be ce mat
a ba, daman can kowa ya san Aliyu ya san magana ma wahala take masa, juyawa yai ya koma gurin motar ya bude mata back seat alamar ya aminta kenan.
“Yauwa dan wajen Mama Fulani i love you”
Cewar Ataa tana dariya, shi kuma sai yai murmushi ya zagaya s
ide dinsa. Ataa ta leki fuskar Fadime.
“Ta so mu je”
Fadime ta dago tana kallon Ataa kamar tana ganinta.
“Su waye ku?”
“Ni sunana Aisha amman ana kirana Ataa, mijina kuma sunansa Aliyu, cutar ki zamu yi ba taimakonki zamu yi”
Yunkurawa tai t
a mike tsaye sai Ataa ta kama hannunta suka nufi gurin motar, sai da tai addu'a sannan ta saka ta a motar ta rufe, ta bude front seat ta shiga ta zauna.
“Ka wo Haidar din”
“Kyale shi bachi yake”
Ya fara tuki da hannu daya yana fadin.
“Za mu far
a zuwa police station”
“Why? Ni fa ka san na tsani police, saboda Doc Asim mutanen nan suka rufe ni a cell kwana na biyu a ciki, bayan kuma ni ke da gaskiya, sanadin haka na rasa Lukman the one and only brother da nake da shi”
“Miyasa kike ta kokarin
sai kin tuna min da abubuwan da suka faru a baya ne Ataa? Kin san zafin da nake ji? Yanzu ai komai ya wuce ya kamata ki manta”
Ta furta cikin muryar da ke nuna ransa ya bace, kallonta ta kwantar da kanta jikinsa.
“Im sorry”
He kiss her front head
sannan ya cigaba da tukin. Lokaci zuwa lokaci take juyawa ta kalli Fadime da ke bayan motar duk da bata ganinta sosai saboda duhun motar sai dai ta gane kuka take saboda yadda take ja majina.
Fadime dai sai hawaye take tana ta sauraren tafiyar motar da t
ake jin kamar ta taba