Showing 189001 words to 192000 words out of 304903 words

Chapter 64 - FULANI COMPLETE

gida gaba daya wunin ranar be tafi kasuwa ba, ko ya iso ya samu Inna ba lafiya, har wani yayansa ya dauko mai allura yayi mata guda biyu.

A gefen tabarma da take kwance ya zauna yana mata sannu, shi kanshi ji yake k

amar lafiyar bata ishe shi ba. Be wuce minti ashirin zuwa ashirin da biyar da zama ba, wata matashiyar budurwa ta shigo gidan tana sallama, makociyar Inna ce dake gyara gida ta amsa mata.

“Hauwa ce?”

“Inna Ramla ina wuni?”

“Lafiya kalau”

Budurw

ar da ba zata wuce sa'ar Fadime ba ta juya gurin Bappa tana mika masa gaisuwa da yaren fulatanci, bayan ya amsa ta fada masa ana masa sallama a waje.

“Bappa wani ne a waje yace a sallamo ka, yace ace Wasim na maka sallama”

Ta fada da yaren fulatanci.

“Wasim?”

Bappa ya maimaita jin sunan wani iri da be tana ji ba, sai kuma ya yunkura cike da gajiya ta mike tsaye yana hamdalla ya nufi kofar gida.

_________

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun y

i mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi ma

lam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuw

ar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kas

ar nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

44

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 080361

26660*

Da tunani kala kala Iya ta isa masarautar, domin ta san ita Fadime zata fara fallasawa kamin ta fadi kowa, tabbas indan ta fadi abun da Zainab ta fada mata kowa zai gane kuma za a yarda da Fadime, sai da ta kusa isa gate din Ammy sannan ta tuna

gargadin da Ammy tai mata cewar kar ta sake shigar mata falo, idan wani abun take so ta fada a sanar da ita. To idan ma ta shiga me zata yi? Ai dai ba zata iya cewa Shattima ya bata Fadime ba, idan ma ta bukaci hakan wani tonon asirinta ne domin Fadime ih

u zata saka ta fara mata ihu tana kiranta da Mayya, anya ma zata iya shiga ciki ta hada ido da Shattima? Idan tace masa Fadime ta zo dauka ai wani karin abun tonon asirinta ne. Zaune tai gindin gate din tai tagumi hantar cikinta sai kadawa take, tana ta tu

ke tana tauna abun duniya ya mata yawa.

“In da na san haka yarinyar nan take, Wallahi kame kurwarta zan yi na matse ta kwanta ciwo sai na ga bakin maganar”

Taja tsaki.

“Dai dai nai kunyar duniya kara ta kiyama gaskiya ba zan yi kunga biyu ba”

T

a mike tsaye ta nufi hanyar bangaren Ammy, da tsoro ta doshi gurin tana kawar dai kai, sai dai jin yadda kowa yake mika mata gaisuwa kamar yadda suka saba yasa ta ji sanyi, ko da yake ko ta fada ai be isa ace har sauran mutanen gidan sun ji ba, sai idan ta

yi kauri. Ta isa bakin kofar ta kwankwasa tana ayyana yadda zata fadawa Ammy cewar daga wani gurin ta fito ta biyo ta nan ta gaishe ta, ba dole sai ta nemi tafiya da Fadime ba ko kurwarta ta samu sa'ar kamawa ta san ya wadatar da ita.

Ta dade tana kwank

wasar kofar kamin ta samu a bude mata, daya daga cikin manyan hadiman gidan nan, a take ta washewa Hadimar hakora.

“Ramatu ana nan”

“Ina nan Iya ya gidan?”

“Lafiya kalau, Allah yasa Ammy na ciki, ita dai Hajiya na gaisota tana nan ita”

“Eh Ammy

tana nan amman ta shiga dakinta kuma tace kar a dame ta”

“Oh bachi take ina jin, to Babban Mutum fa?”

“Aa Shattima baya nan”

“Baya nan? Kin tabbata kuwa”

“Ba shi nan ai ba zan kiki karya ba Iya”

“Haka ne, kuma ba ku yi bakuwa ba ko? Wata ya

rinya haka fara yar makauniya”

“An yi ta baki gaskiya masu shigowa gaisuwa, amman babu makauniya, duk ba ba lallai na san komai domin ba kullum nake zama ba”

“Aa ita fa da yamma nan ne ko awa daya ina jin ba ayi ba”

“Gaskiya makauniya bata shigo b

a, yawancin yan matan da suke zuwa wasu duk kawayen Nana ne”

“Haka ne, to a gaishe da Hajiya ni zan koma”

“Inshallah zata ji”

Iya ta juya ba dan ta yarda ba, wata kila ma Shattima ko Ammy ne suka ce mata yarinyar bata nan, waya sani ko tana can ta

na zuba musu surutun nata. Iya ta ji kamar ya daka tsalle ta ganta a gaban Fadime, tsabar bakinciki bata san lokacin data fara kudar hakora ba tana tsatsagarsu.

“Wallahi sai na nunawa yarinyar nan iyakar ta, ai daman na fada duk wanda ya shigo gonata na

ke kawarwa, ba a taba min abun da tai min ba, babu wanda ya san sirrina sai da ta zo, babu wanda ya damu da rayuwata sai da aka ka kawo min fitina, gashi har Zainab tana kokarin ballo min wani balli, lallai wannan makauniyar sai ta san ta taba maye...”

Ta yi kwafa tana jin wani irin bakinciki a ranta. Ji tai ba zata iya tafiya ba tare da ta tabbarta Fadime tana cikin gidan ba, juyawa tai ta koma ciki sai da wannan karon ta gurin dawakai ta nufa, domin tana da tabbacin a can ne kadai zata yi abun da take

so ta gama ba tare da an ganta, domin ta saba shiga gurin. Sai da ta gaisa da mai kula da dawakan sannan ta shiga ciki tana fadin.

“Wai dokin Babban mutum zan duba, na san yayi kewata kwana biyu”

Shiga tai can kurya har ta wuce dokin Shattima ta kara

sa can ciki sannan ya duke kasa gurin dawakan, ta fara karanta wasu abubuwan tana tsutsar halshe, jikinta na tsama sai kafafuwanta suka fara nadewa guri daya suna yin shatin jikin kadangare irin ogan nan (Kiski a hausar ta Sokoto da Gusau) idanuwanta suka

fara rikidewa ko'ina a jikinta ya dauki dumi tana ta fisga a hankali, sai da kafafuwanta suka fara zama siffar kiskin sannan jikinta ya soma dauka idanuwanta suka fara rikidewa suna kara ja daman can jajaye ne irin na mayu, har ta fara kankancewa sai kuma

ta koma daidai.

“Oh Oh”

Ta furta tana aje numfashi da karfi kamar wanda tai gudun fanfalaki. Tana ganin hakan ta san ba zata iya rikada a yanzu ba, domin rabon da ta rikida ta zama wani abu tun kamin cikin Zainab, idan har tana son ta koma tana rikid

a kamar da sai ta sha garin maganinsu da suke amfani da shi suna sha duk shekara wasu kuma duk sati wasu duk wata wasu kuma kullum ne, ya danganta da kalar maitar da ka dauka da kuma irin karfinta, domin wata maitar tafi wata karfi, akwai wadanda basa gash

i idan sun kama kurwa a take suke cinyeta danya ba tare da sun soya ba, irin su ne suka fi kowa hadari a cikin mayu domin su kap daya suke yi wa mutum, bayan su sai masu saidawa su ma idan sun siyar basa karbowa sai wani ikon Allah, akwai kuma masu siyarwa

basa ci, wasu kuma su ci kuma su siyar, irin su ne suka fi arziki a cikin mayu.

Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta ta fito a gurin ba dan ranta ya so ba, sai dan ta san idan har ta sake yunkurin zata wahalar da kanta ne kawai, idan har tana son tai saur

in riki dole ne sai ta sha maganin wanda zai suma jikinta ta taimakawa aljanin maitar da take yawo da shi. Mai kula da dawakan na mata magana bata ko kula shi ba tsabar haushi da takaici ta wuce shi kamar ana turata ta nufi gate.

WASIM POV.

Bap

pa ya mika wakawa Wasim hannu suka gaisa, sannan Wasim ya cire hular kansa ya kalli Bappa.

“Sunana Wasim, na san baka san ni ba, duk da bani da tabbacin ko Fadime ta taba labarta maka wani abu akaina”

“Aa bata taba fada min komai ba, lafiya dai”

W

asim ya gyara tsayuwarsa tare ta saka hannayensa duka biyu aljihun wandonsa na jean.

“Na dade da sanin yarka sai dai bata tana sani na sai daga baya, ina yawan ganinta idan taje kiwo ko diban ruwa, amman ban taba mata magana ko nuna na santa sai daga b

aya, cikin kankanen lokaci muka shaku da ita, ni ne mutumen da ta bukaci na yi mata dabon maciji na yi mata ta dawo gida da maciji a tulu an yi haka?”

“Tabbas la shakka an yi haka”

Bappa ya fada yana kara kallon Wasim da kyau a take ya nemi gajiyar d

a yake ji ya rasa sawun giwa ya take na rakumi.

“Na yi mata, bayan haka ni ne mutumen daya sauya mata murya a ranar da wani zai zo ganinta daga birni sai dai ba tare da ita din ta so haka ba, ka tuna”

Bappa ya daga kai cike da gamsuwa.

“Na san da

wannan”

“Ni ne mutumen daya fada mata akwai wuta maita da take bibiyarta, kuma ni ne mutumen da na kama mayyar na daki cikinta a lokacin tana cikin siffar mage, ban san iya abun da tai ba, amman ba dukan wasa nai mata ba, doka ne wanda ke taba hankali

duk wata halitta mai jini da hanta, wanda n tabbatar har yanzu bata samu lafiya ba”

“An yi haka, hakikanta amri”

“Ban yi zato ba yarka ta zo tare da wata mata ta fada min cewar tana son na shiga da matar garinmu ta dauki hoto, na kaisu ba saboda mata

r ba sai dan saboda Fadime duk da na san garin mu gari ne da basa karbar bako, a lokacin ne muka samu akasi har mahaifina ya ganta, yasa aka kira mu ya bata naman kura yace ta ci, ta ci naman da ke saka duk wanda ba dan garin ba kaiyi a makoshi da baki, a

kokarin mahaifina na horani sai yace be yarda a fitar da yarinyar daga garin ba, wanda na san yayi haka ne saboda ya san zata matsu ni ma kuma zan ji ba dadi na takurar da mahaifina yai mata, sai a nan ma na kasa bin umarninsa saboda ta matsa min da kuka c

ewar tana son na dawo da ita a nan, na fito da ita ba tare da izinin sarkin garinmu ba, mahaifina kenan wanda haka ne ya haddasa mata makanta, shi ma daga mahaifina ne a kokarinsa na sake min horo ni da ita, wanda ko gobe aka ce ta zo garin ko kuma ni na k

aita ba zan kara ba, Kaka ne ya fada min cewar an tura mata makanta kuma kun dauketa zuwa asibiti har a inda zan same ta shi ne ya fada min kasancewarsa matsafi ne, ni na na shiga asibitin na dauke na fitar da ita daga garin da sunan zan kawo ta gurinku sa

i na kaita wani gurin ajiya, a inda na kaita kuma na kafeta irin kafin da ko mutuwa tai ba za a iya dawowa da gawarta har sai idan ni naje na dawo da ita...”

Bappa jin yai kafafuwansa ba za su iya daukarsa, sai ya nemi guri a kusa da kofar gidan ya rage

tsayunsa, wanda hakan yasa Wasim din shi ma da kansa ya rage nasa tsawo. Ban da kallon Wasim babu abun da Bappa yake, a yadda yake ganin kamala da natsuwa a fuskar Wasim da kuma ladani alamansa sam ba zaka ce zai iya yin wani tsafi ba.

“Kenan kai dan

garin can ne da ake kira da Garuk?, amman miyasa ka dauke ta?”

“Saboda za a iya taba idonta a nan, idan baku kaita asibiti wata kila zaku iya gwada yi mata na hausa, wanda ko wane a cikinsu yana da illar da zai iya saka ta rasa ganinta gaba daya, bayan

wannan a nan za ku yi mata fada ba zaku saurareta ba, musamman kai da kake mahaifinta, domin a kullum maganarta Bappa zai karyata ko sai ya kusa asheta, na zabi zuwa na fada muku gaskiya domin na san ba lallai ne Fadime ta fadi gaskiya ba saboda tana tsoro

n ku, kuma saboda na kwantar muku da hankali ku samu natsuwa kuma ku sn cewa yar ku tana nan cikin koshin lafiya, kuma da zarar idonta ya bude zan dawo da ita dawowa ta har abada”

Bappa yayi shiru out of words be san abun da zai sake cewa ba for now. Ab

un da Fadime ta fada masa cewar aljanu ne kenan ba gaskiya ba ne? Ashe duk abun da take fada masa karya take shirya ba, sai a yanzu Bappa ya tabbatar Fadime ta wuce tunaninsa da iya tsara abu kamar ya faru da gaske. Dagowa Bappa yai yana fadin.

“To amma

n da ka....”

Da sauri Bappa ya mike tsaye yana waige waige ganin babu kowa a gurin sai shi kadai.

“Subhanallahi”

Ya furta cike da tsoro marar misaltuwa.

“Ya bace bat...!”

Da sauri Bappa ya juya ya koma cikin gidan, a gaban makociyar su Inna

ya labartawa Inna komai, a take Inna ta tashi zaune tana jin kamar ta samu lafiya.

“Amman da ya taimaka ya kawo mana ita, in ya so sai mu kiyaye duk abun da ya fada”

“Ni ma abun da na tashi fada masa kenan ina dubawa sai na ga babu mutum”

“Kasan

tsafi ne da su, wata kila yana da layar bata, layar zana”

“Ba mamaki, amman Fulani akwai karfin hali yanzu har ta taka taje garin nan? Anya kuwa Fulani bata da aljanu gaske? Kwata kwata babu tsoro ko fargaba komai a idonta”

Inna ta rausayar da kai.

“Fulani kam Allah dai ya shirya, gaba daya rayuwarta ban san wace iri bace, kuma babu yadda ban yi mata gargadi ba akan kar taje garin nan amman bata ji, to yanzu ya zamu yi kenan?”

“Hakuri zamu yi kawai, kuma gobe idan Allah ya kai mu sai na tafi na

fada musu na na jany karar”

“Bappa Fadime ai ba kara ka kai ba, kai cijiya ka kai musu, dan haka ka kyalesu kawai domin idan ka koma wata kila ma za a ce ka kawo wani abu ne, ka kyale su kawai idan ma sun ji wani abu ai za su kira tun da Shatu tace ka b

ada number wayarka”

Cewar mamansu Ramla. Bappa ya amsa mata cike da gamsuwa.

“Haka ne kuma da zancen ki, amman dai idan kana jin mu bawan Allah ka daure ka kawo mana ita, mu kuma ba zamu nema mata maganin komai ba”

Inna ta daga kai tana kalle kal

le kamar ance mata zata ganshi.

HAJIYA BABBA POV.

Tun rasuwar Talba Hajiya ta koma kamar wata marar lafiya, bata da kuzari walwalar duk ta gushe kullum tana dakin sai idan za ta yi wani abun sannan ta fito waje, zuciyarta ta saka sakin tunanin T

alba, ba mutuwarsa take ji ba kamar rushewa al'amuranta, gashi a da tana tunanin zata fi Ammy gado ko da Mai Martaba ya rasu, saboda Talba yana a matsayin Shattima Juwairiyya da Karima kuma suna matsayin namiji daya sai Kaunar dake matsayin Nana, yanzu kum

a sun za daya tun da Talba ya tafi, Sirleem kuma ba zai gaji Mai Martaba tun da ba dansa ba ne, Tunanin hakan yasa tun farko ta zo a haihu da yara a gidan amman be bata da yawa ba, sai ya bata hudu, namiji hudu mace uku.

Ga burin da take da shi na son Ta

lba ya samu sarauta yanzu ya kau, sai abubuwan suka taru suka mata tsaye a zuciya ko abincin kirki bata iya ci. Tana zaune tana ta tunanin duniya Sirleem ya turo kofar ya shigo yana sallama, sai ta amsa masa da muryarta dake karantar da shi tsantsan damuwa

r da take ciki, kusa da ita ya zauna yana jin babu dadi a yanayin da ya same ta, domin duk dan kwarai ba zai so ganin mahaifiyarsa a cikin damuwa ba.

“Hajiya...”

Juyowa tai ta kalleshi cikin kwanakin nan naman fuskarta ya sauka fiye da da, ma'ana ta

yi rama sosai.

“Sirleem kana lafiya?”

“Lfy kalau ya jikin?”

“Alhamdulillah, magana nake son yi da kai, magana ta karshe ba shawara zan baka ba umarni ne”

Tun kamin ta karanto masa abun da take so gabansa ya fadi.

“Minene Hajiya?”

“Bana so

n wakar nan da kake yi, kaskanci ne a gareka da mu da kowa ma naka, bana son wakar da kake, baka rasa komai ba a duniyar, me zai kasa ka zabi waka?”

“Waka sana'a ce Hajiya”

“Na yarda sana'a ce, amman ba ga dan babban mutum kamar kai ba, mu ya kamata

ace muna kyautatawa mawaka muna musu alheri muna basu dukiya, kai fa idan ana son kiranka kai kayatar a taro ko biki, ina jin zafi kuma kaskanci ne a gareka a matsayinka na a gola a gidan Sarki kuma dan former vice president, abun da ko wane dan babban mut

um yake a yanzu kokarin yaga ya yi kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login