Showing 240001 words to 243000 words out of 304903 words
ganin ita ce yasa ya bude mata ta shiga, ko sannu da zuwa da yake mata bata amsa ba tsabar hankalinta baya jikinta. Sai da ta shigo cikin falon ta zauna sannan ta samu yar natsuwa
ita ma kadan, gaba daya hankalinta ya tattara ya koma kan Masarautar, sai neman dalilin kama Zainab din take ta rasa tudun dafawa idan ta kulla wannan ta kwance wacan. Mikewa tai tsaye ta isa gurin kofar falon ta rufe da makulli sannan ta dawo ta bude dak
inta ta shiga ta maida kofar ta rufe. Hijabinta ne farkon abun da ya fara cirewa sannan ta aje jakarta ta nufi gurin da take aje tukunyarta ta bude ta dauko tukunyar tai magana a cikin sai kuma ta maida tukunyar ta aje, ta nufi karkashin gadonta ya janyo k
wayar nan da take ajiyar kurwa a ciki, ta bude ta dauko kurwar Maijidda ta warware zaren jiki taka bakin mayafin dake saman gadonta ta lullube kurwar da shi. Tana cirewa sai ga kurciya a hannunta fuska a hade ta kama wuyan kurciyar ta murde iya kar karfint
a har sai da jini ya fito ta tabbatar da ta kashe ta sannan ta saka a wani karamin kwanon, ta dauko dayar kurwar ta warware ta saka bakin zanen ta lullubeta, tana budewa sai wani tsohon zakara marar lafiya ya fara motsawa.
“Yanzu idan masarautar ta girg
iza sai mu ga waye kuma za a dorawa laifi? Sai na ga yadda za ki yi ke da yayanki”
Iya ta fada tana zaro manyan idanuwanta masu mugun ja da mummunar fuskarta da bata da kyau gani.
WASIM POV.
Ya mike tsaye yana kallon Kakansa.
“Har t
sawon wane lokaci za ka dauka kamin ya bar yarinyar can ta samu lafiya?”
“A kullum fata na ke mata na samun lafiya, ku dai zan tambaya sai yaushe za ku kyaleta ta samu lafiya?”
“Sai ranar da k yardar ka bi umarnin mahaifinka, kuma ina mai tabbatar ma
ka tana daf da rasa idonta gaba daya, domin mutumen da aka hannatawa ita daf yake da taba idonta, kuma ka san makomar hakan matukar ya taba idon ba za su taba dawowa ba, hakan kuma ba zaka mu bar ka ka aureta ba, domin ba zaka taba auren wanda ba jininmu b
a”
Wasim ya koma ya zauna hankalinsa a tashe, domin ya san dukan abun da Kakansa ya fada masa abubuwan da ya riga ya gani ne.
“Kana wahalar da ita ne kawai, domin tuni ta taba hannun wacan dan Sarautar da yake haukan nemanta kuma ta ji sanyi”
Was
im ya dafe kansa da mugun karfi kamar zai cire kan daga jikinsa, zuciyarsa ta shiga bugawa da karfi, daman abun da yake gudu kenan shiya saka shi kasa taba hannunta tun a wacan lokacin, tsoronsa daya kar ya taba bata ji sanyi ba. Ya daga kansa ya kalli kak
ansa hawaye masu zafi na sauko masa.
“Kaka ka sani ina son ta”
“Kana sonta kake bari tana cutuwa? Ka nisanta da iyayenta? Ka kaita inda aka gusar da hankalinta? Kuma ka saka take kokarin rasa idonta? Wanda kake so za kai masa fatan samun farinciki ko
kuwa farincikinsa na nufin bakincikinka ne”
Ya lumshe ido yana jin wani irin kalar yanayi da be taba jin irinsa ba, yana tuna kalaman Zainab.
“Wani lokacin dole ne mu sadaukar da farincikin mu saboda wadanda mu ke so su samu farinciki...”
Kansa y
a daga sama sai ga hawaye sun sauko masa ta gefen idon, wani irin zafi da radadi yake ji idan yai yunkurin tunanin rabuwa da Fadime.
“Rabuwa da Fadime ba shi yake nufin na auri Liya ba, kuma ba zan taba barinta ta samu farinciki ba”
“Kana da damar au
ren wanda kake so matukar jininmu ce, amman wacan yarinyar idan za ka kashe maza dubu ka zata yi mu'amala da su, ba za ta taba aurenka ba”
Hannunsa ya daga sama ya daki tsakiyar kansa da dukan karfinsa ya rufe ido yana girgiza kai. Mikewa yai tsaye yana
wani irin huci kirjinsa har wani sama yake kamar sai yi tsalle.
“Zan rabu da ita, amman sai na taba mutanen da suka taba ta, sai sun shiga kunci fiye da ita”
“Wannan kuma aikin duna ne, zan zan nemo shi... Na ka aikin ka tafi gurin shugaba ka fada m
asa ka yarda da dokinsa, ni kuma zan bude idanunta”
Kakansa ya fada da yarensu, sai Wasim ya kalli inda Fadime ta ke yawan zauna a lokacin da ta zauna dakin kakansa. Matse hannayensa yai yana jin rabuwa da ita kamar fitar rai ne daga jikinsa, kai ya gir
giza ya koma ya zauna.
“Ba zan iya ba, wata kila ka fada min haka ne saboda ku cin ma burinku a kaina”
Kakan yayi murmushi.
“Lallai kana sonta sosai tun da har ka iya karyata ni, amman bari mu gani daga nan zuwa jibi idanuwanta za su bude ne ko ku
wa za su tabbata har a bada a rufe? Amman ka sani daga lokacin ni da kai babu abun da zamu iya yi domin dawowa da idanuwanta....”
HAJIYA BABBA POV.
“Amin wa'alaikissalam”
Ta amsa sallamar da Hajiya Zariya tai mata a yayinda ta kara kunnen
a wayarta.
“Hajiya ina yini ya gida ya Mai Martaba da jikin”
“Alhamdulillahi”
Ta amsa cike da kasaita kamar ba yar'uwarta ba.
“Hajiya na ce ko Sirleem yayi aure ne ba a fada mana ba”
“Wane Sirleem kuma?”
“Sirleem dai na ki, na wuce ne ji
ya ta gaban gidansa da yake nan kusa da mu na ga mutane na fitowa na tambaya aka ce min walima ake wai Amarya aka kawo, shi ne abun ya ba ni mamaki na ce to ko anyi bikin ne ba a sanar mana ba”
Hajiya Babba ta aje farantin dankalin jos dake hannunta.
“Aa ai ke ma kin san ba zai yiyu ba, Sirleem yai aure ba ki sani ba, ko da ba a fada miki ba ai duk garin nan sai ya dauka, shi kadai ya rage min fa namiji, kuma aurensa da yar sarautar ai dole ne ma duniya ta sani”
“Ni kaina na yi mamaki, tun jiya abu
n ya tsaya min a rai ina ta son na kira dai ban samu dama ba, mutanen ma da na ga suna fitowa daga gidan ba wasu na azo a gani ba ne, ko dai haya ya bada gidan ne?”
“No gidansa da ke kusa da unguwarku ai yafi ko wane gida nasa kyau da tsaruwa, ba zai ba
da hayarsa ba, kuma bana jin zai arawa wani, Amman kin shiga cikin gidan kuwa?”
“Aa wannan dabarar bata zo min ba, ban yi wannan tunanin ba”
Shiru Hajiya Babba tai tana nazari.
“Zan bincike shi idan ya shigo”
“To Hajiya sai an jima a gaishe da
su Kausar”
“Za su ji”
Hajiya ta sauke wayar cikin tsananin mamaki, anya ma kuwa gidan ne? Ta tambayi kanta sai dai bata jin Hajiyar Zariya za tai kuren fahimta domin ta san gidan ba ita kadai ba ma yawancin mutanen unguwar sun shaida gidan saboda tsa
ruwarsa gashi farin gida mai bakin gate sai daukar hankali, sai dai ba kowa ya san cewa na Sirleem ba ne sai daidaikun mutane yan'uwa da kuma wadanda suke kusa da shi sosai.
Tunawa da tai da zancen da yai mata shekaranjiya na cewar zai kwana a can sabod
a baya jin dadi da kuma jiya da yace mata yana son komawa can so that ya samu damar maida hankali kan harkokinsa yasa gabanta mugun faduwa. Har ta dauko wayarta ta kira shi sai kuma wata zuciyar ta hana ta, da sauri ta mike tsaye ta nufi inda mayafanta suk
e ta dauko farin gyale ta saka ta nufo gurin da aka jekara takalminta ta saka ta dauki jakarta tare da wayarta ta fito falo.
“Juwairiyya”
“Jurry bata nan”
Karima ta amsa.
“Ke tashi ki kai ni gidan Sirleem da ke 300 houses yanzu nan”
“Okay,
amman Hajiya lafiya?"
“Ita na ke son na tabbatar”
Ganin yadda hankalin mahaifiyarta yake a tashe yasa tai saurin dauko mayafinta ta fito rike da makullin motarta, har suka saukon ta shiga motar mamakin abun da ya faru take, ko dai minene ta san abu n
e da yake son sirri shiyasa ta zabi ta kaita a maimakon direbobinsu da suke gidan.
Suna isa unguwar Hajiya ta saka tai bakin nesa da gidan sannan suka fito suka taka da kafa har gaban gidan, Karima ta kwankwasa gate din sai mai gadin ya leko. Karima za ta
i magana Hajiya ta tari numfashinta
“Amarya na nan?”
“Eh suna nan Hajiya Bismillah ku”
Ya bude musu gate din, suka shiga ciki hango motar Sirleem da Hajiya tai ya fi komai kayar mata da gaba, Rima kam tana gefenta da mamakin jin abun da Hajiya ta
fada, suka nufi hanyar shiga falon zuciyar Hajiya sai bugawa take kamar zata fasa kirjinta ta fito, sai da ta fara tura kofar ta ji ta a rufe bata ko tsaya duba inda door bell din yake ba ta kwankwasa. Jin shiru ba a bude ba yasa ta sake kwankwasawa. Sirle
em ne ya bude kofar yana sanye da jallabiya milk color.
“Hajiya....”
Ya fada kamar wanda ya rude. Tura kofar falon tai ta wuce ciki falon, sai tai arba da abun da bata yi zato ba, wato Falmata tana sanye da doguwar rigar atamfa hannunta rike da dankw
ali, daga bakin Hajiya har hancinta da idonta kallon Falmata yake with shock, can kuma ta juyo ta kalli Sirleem baki sake ta nuna shi da yatsa, sai kuma ta kasa magana, ta sake juyowa ta kalli Falmata ta daka mata tsawa idonta na cika da kwalla.
“Me kik
e yi a nan?”
Falmata ta kasa cewa komai jikinta sai rawa yake, Sirleem yayi saurin nufar inda take yana kallon Hajiya.
“Sirleemmmmmm.....”
Hajiya ta kira sunansa daker sannan ta ce
“Dadiro kuke yi?”
“No Hajiya Subhanallahi, she's my wife”
Wife wife wife wife wife wife wife wife wife.... Haka kalmar tai ta maimaita kanta a kunnen Hajiya, nuna shi tai ta nuna Falmata sai kuma ta nuna kanta kamin ta fadi kasa zaune saman tile din. Sirleem na ganin haka yai saurin kama hannun Falmata suka fic
e daga falon cikin sauri, motarsa ya nufa da ita Rima ta bi su da kallon mamaki ido bude. Sai da ya taba motar ya ji a rufe, sai ya rasa yadda zai yi baya son komawa ciki saboda zuciyarsa na raya masa Hajiya zata iya cewa sai ya sak Falmata a take. Hannunt
a ya kama be ko kula da dankwalinta dake hannunta ba suka fice daga gidan gaba daya, Falmata kuka kawai take jikinta na rawa kamar mazari. Suna fita su kai sa'a da Napep, cikin sauri Sirleem ya tare Napep din dake tare da wata mata suka shiga, yana fada ma
sa inda zai kaisu.
Sai da suka bar unguwar sannan Falmata ta lulluba dankwalin da ke kanta, mai Napep kam sai mamakin wanda ya dauko yake a zahiri dai fuskar Sirleem yake gani fitaccen mawaki sai dai ba shi da tabbacin shi din ne ko waninsa. A gaban gi
dan Momy ya sauke su Sirleem ya fito yana fadin.
“Jira ni ina fitowa”
Ya buga gate din gidan mai gadin na budewa yaja hannun Falmata suka shiga ciki, yana isa bakin kofar falon Momy ya buga kofar da mugun karfi, hakan yasa Momy tai saurin budewa hank
ali tashe. Ganin Sirleem da Falmata ya bata mugun mamaki.
“Sirleem”
“Momy dan Allah ki boye min yarinyar”
“Lafiya?”
“Dan Allah ki boye min ita yanzu yanzu, zan dawo ki saka a daki ki kulle dan Allah kowa ya zo karki fito da ita”
Momy ta nuna
Falmata da mamaki.
“Wannan ba Falmata ba ce?”
“Ita ce Momy please ki boye min ita”
Ya fada cikin tashin hankali, saurin kama hannun Falmata tai ta shiga da ita ciki shi kuma ya juya ya koma, upstairs Momy ta nufa da Falmata da ke kuka ta bude dak
in Ameer ta saka ta ciki ta rufe ta makulli ta sauko kasa da mamaki kala kala.
Bakin kofar dakin Falmata ta zauna ta fashe da wani irin kuka marar misaltuwa, sai ta ji kamar bata taba fuskantar tashin hankali irin wannan ba, kuka take sosai tun tana yi b
a sauti har sautinta ya fara fitowa, kuka tai bana wasa ba har sai da idanuwanta suka fara kumbura, hawayen suka daina zubo mata. Mikewa tai tsaye tana goge idonta da dankwalinta, kamar ance mata juyo ki kalli gefe, tana juyowa sai tai arba da wani tsohon
hoton mahaifiyarta, an fadadashi har ya kusan tsawonta, an ajeshi a tsaye yana fuskantarsa, mutuwar tsaye tai tana kallon hoton with shock.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu
ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke k
adai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son k
omawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna ai
ka kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
55
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Sai da ya koma cikin gidan sannan ya shiga cikin gidan da tunanin Hajiya Babba tana nan har lokacin amman be tararda ita a falon da aka bari a bude, dakinsa ya shiga ya dauko kudi ya sallami mai Napep din sannan ya sake kowa ya dauko makullinsa motarsa ya
fito ya shiga motar, sai da yai mata key sannan ya fara tunanin da wani ido zai kalli Hajiya? Me zai fada mata? Taya zai fara mata bayani? Anya ma zata fahimce shi? What if ta cilasta masa sakin Falmata? Haka ya bar motar kunne ya rasa abun yi tafiya ko za
ma, can dai ya ja motar ya fice daga gidan yana tukin kamar wanda baya son tafiyar.
Tsakanin gidansa da masarautar tafiya ce mai dan nisa amman sai dai a yau sai ya ji tafiyar ta masa sauri sosai, a maimakon yai fakin a inda ya saba sai yai fakin daga b
akin gate din kamar wani bako ya fito yana tafiya gumi na keto masa kamar wanda yai sata, sai a yanzu yake jin cewar ya aikata wa Hajiya Babba laifi, sai dai ya san ida ya fada mata ba zata amince ba, a ganinsa shi mijin mace hudu ne zai iya auren Nana da
wata ma.
Kamar wani marar gaskiya haka ya shigo cikin katon falon na Hajiya, idanuwansa duk sun wani fito kamar wanda aka ciro daga rame, ganin babu kowa falon yasa ya nufi dakin Hajiya Babba, yana turawa sai ya samu Karima da Kausar a zaune saman kujer
a sun kurawa Hajiya Babba ido. Ita kuma tana zaune saman gadonta har lokacin tana yafe da mayafinta da jakar da ta fita da ita duk suna hannunta har talkamin ba ta cire ba, Wardrobe dinta kawai take kallo, ko kyabta idon ma sai an dade take yi. Sirleem ya
karasa kusa da ita ya duka a kasa, Kausar da Rima kan kallon mamaki kawai suke masa, Rima ba dan ta ji da kunnenta ba kuma ta gani da idonta ba da ba zata yarda ba ko waye zai fada mata haka karyatawa za ta yi.
“Hajiya....”
Sirleem ya kirata sai ta j
uyo a hankali ta kalleshi. Shi kuma ya sunkuyar da kai ya rasa abun da zai fada mata.
“Yaya ba a yanzu ya kamata ace ka gane ka aikata kuskure ba, tun kamin ka aikata ya kamata ace ka gane kuskure ne kake kokarin aikatawa, fisabilillahi me zaka yi da ya
rinya kamar wacan? Kuma ka san Hajiya ta zaba maka Nana a matsayin matar aure? Ko da baka son Nana be kamata kai aure a boye ba, mahaifiyarka tana raye mu ma kanenka muma nan danginka kowa yana nan...”
Karima ta fada cike da jin zafin abun da dan'uwanta
ya aikata. Sirleem dai be ce komai ba kuma be dago kansa ba, gaba daya ya rasa abun da zai yi. Murmushi Hajiya Babba tai irin murmushin da kana ganinsa ka san ba na farinciki ba ne, wasa wasa ya kwashe kusan 3 hours a dakin, tun yana jin nauyi da kunyar
yi mata magana har ya kai yana rokon tai magana.
“Hajiya ki ce wani abu mana, ki furta wani abun, na san ban yi daidai ba ki fada min ki ce Sirleem baka kyau ba”
Ya fada idonsa cike da hawaye domin har ga Allah ya san ya saka mahaifiyarsa a damuwa. H
aka ya gaji da rokomta ya gaji da magiya ya mike tsaye ya fice tana ta innalillahi.
Cikin motarsa ya koma ya zauna ya dafe kansa ya rasa abun da zai yi, ya rasa inda zai saka ransa ya ji, ya rasa abun da zai yi ya samu sassauci. Kunna motar yai ya juya k
anta ya fice daga gidan gaba daya.
Sai da ya fita sannan Hajiya Babba ta tashi ta fito daga dakinta ta zauna a falo, ta maida hankalinta gurin tv tana kallo, ba dan babu