Showing 279001 words to 282000 words out of 304903 words

Chapter 94 - FULANI COMPLETE

labarta masa

abun da ya faru ya fahimci sun kwashe komai domin alamu ya nuna haka, kuma daman can ya san za a rina tun da ya aika mata da takardar sakinta, domin har yanzu ciwon be barta ba sai an kwantar sai an tayar bata iya komai.

Inna har cikin ranta ta jidadin

labarin da Bappa ya bata cewar ya saki Amo, daman can kullum tunaninta da zulluminta kar wata rana Amo ta dawo da zama a gidan, sai dai bata nunawa Bappa ba sai ta nuna masa bata jidadin hakan da yai ba.

“Haba Malam tana cikin ciwo kuma sai ka kara mat

a wannan? Da ma ka hakura har ta samu lafiya tukuna”

Uffan be ce mata ba ya dauki redio sa yana kamo bbc domin 8:30pm ta yi, bayan ya kama tashar ta aje redio ya dauko tuwon shimkafar da miyar kuka ga uban manshanu Inna ta labta masa abun ka da masu abu

, ya bude ya dauki ruwan da ke cikin kofin ya wanke hannunsa ya fara cin, Inna sai gyara masa fitila take tana jinta kamar wata Amarya. (Na ce Ashe su Inna ba a son kishiya

🤣

).

“Na yi magana da Sani mai jakkai na fada masa ya fara kawo mana yashi”



Mashallahu aiki ya tashi kenan?”

“To me ake jira, tun da komai ya mallaka, Shehu ma ya ce abokansa zai dauko yan birni su yi aiki”

“Allah ya taimaka, ai haka yayi kara da ka siyar da wacan gidan ka dawo nan ka gina mana na zamani”

“Eh komai za a s

aka Inshallahu, na fada Shehu gida mai kyau kuma gina mai kwari na ke so, yace ko gidan Mai Garin ba zai kai nawa ba, yace har da tistis za a saka”

Fadime ta kyalkyale da dariya daga can cikin bukkar da take.

“Bappa tiles ake cewa ba tistis”

Daga

Inna har Bappa dariya sukai domin ba su dauka tana sauraren firar ta su ba.

“Ja'ira, to tilis din har shi za a saka Inshallahu”

“Allah ya nuna mana an gama komai cikin kwanciyar hankali da tsawon rai, shi kuma Allah ya saka masa da alheri”

Fadim

e na jin haka sai ta tuno da zancen dazun cewar Shattima zai yi aure, take ta koma ruwa tana kukanta kadan kadan ta yadda babu wanda zai ji. Inna ba ta fadawa Bappa komai ba har sai da dare ya raba ta tabbatar a lokacin Fadime ta yi bachi sannan ta labarta

masa yadda sukai da Fadime dazun. Bappa yayi murmushi.

“Ai hakan da tai ya taimaka mana, ina tabbatar miki da ace ta san da maganar nan da yanzu an yi garkuwa da mu ance mu kawo kudi, amman a haka sai ya taimaka mana babu wanda ya sani sai dai kwatsan

su ji an yi ma Fulani amre”

“Ai haka yafi, daman magana ta yi yawa akanta sai fadar ake bata da miji, ai Wallahi hakan ya min dadi Allah ya bata miji ba karami ba, dan babba mutum kuma babban mutum mai mutunci”

Bappa yayi murmushi jin dadi yana jin

wata kima na kama shi zai yi sakuta da sarki.

FALMATA POV.

Hannunsa na lakkame da wuyanta tana karanta masa abun da ta rubuta.

“Mamana, Babana Kakana”

Ya saka yatsansa ya ja kumatunta na dama.

“Ina mijina?”

Ta yi dariya sai ta kalleshi

.

“Mantawa na yi”

Yatsan nasa ya saka mata a baki ta fara tsasa kamar sweet.

“Yanzu ki rubuta sunanyen mutanen kuma ki manta da mijinki? Teem Teem?”

Ta yi shiru tana murmushin da har dimple dinta ke lasawa saboda yadda ta samu guri in 3 month

s jikinta ya fara kyau, daman can abinci mai kyau ne babu da kuma kwanciya hankali.

“Zan rubuta fa sai aka kira sallah shi ne na tafi sallah sai ka dawo”

Ya kai bakinsa saitin kunnensa.

“Ban san ki da karya ba”

Ta saka hannayenta ta rufe fuska

rta, sai yai murmushi ya kai hancinss yana shinshinar gashin kanta da ya sha gyara sai kamshi yake.

“Karki sake bari a taba kiki kai, bana son mace da kitso, gashi yana kara min sonki”

“Kai ma karka sake yin aski”

Ya fada tana jin kamar ta kai ha

nnu ta taba shi kuma tana jin kunyarsa har yanzu, shi din ne baya jin kunyar yi mata komai ko kuma yin komai a gabanta.

“Sirleem”

Dayan hannunsa ya saka ya buge mata baki a hankali ta yadda ba zata ji ciwo ba.

“Ban ce ki daina kirana haka ba?”

Dariya tai tana jin kunyar kiransa da sunan da ya rada ma kansa a kanta.

“To Baby...”

Ya amsa daker yana kai wannan karon halshensa ya kai gurin wuyanta yana mata zirya da shi.

“Hmmm”

“Dan Allah Baby, yaushe zan tafi gida?”

“Ba yanzu ba

Babyn baby, sai kin shekara”

Ta dan bata rai, domin har ga Allah tana son fitar amman ya hanata kullum sai yace mata sai ta shekara.

“Dan Allah fa”

Ta fada a shagwabe kamar ba ita ba, sai ya dago yana kallonta fuskarta da kadan ya rage hancinta ya

taba nasa.

“Idan kin je gida me zaki yi? You know i hate wannan matar dai ko?”

“Ai ba ita zan je gani ba, Babana”

Bakinsa ya saka ya tsose cinin hancinta tass sannan ya dauke bakinsa yana maida numfashi.

“Da dare zan kai ki ganshi, ni kaina

ina son na kyautata masa amman wannan matar ke bata min rai, ta fa wahalar min dake, and ji yadda tai ma dan'uwanki”

Falmata ta kalleshi da sauri domin ta san bata taba labarta masa cewar Ameer dan'uwanta ba ne, kuma bata ce masa Tumba ta yi masa asiri

ba.

“Wa ne dan'uwana?”

Hannunsa ya saka cikin rigarta yana shafa cikinta.

“Ameer mana, Momy ta fada min komai, kuma the way da take ba ni labarin kana ji kasan asiri akai masa, ta ya mutum zai gudu ya bar uwarsa kuma ya kasa nemanta, i wonder ya

zai ji idan ya sani”

Falmata ta yi shiru tana tunani.

“Allah sai ya mana shari'a da matar nan, ta cutar da mu sosai”

“Har kike son ki je ganinta”

“Ba saboda ita zan je ba saboda Baba, komai yai min ai shi Babana ne”

Ya kwaikwayi muryarta ha

r da wani juya kai kamar mace.

“To masu Baba zamu je anjima mu gaisheshi, daga nan sai Tumbin ta gan ni ko ya za ta yi?”

Ta yi dariya.

“Zata ce ya akai ka zama yaro, kuma Sirleem, mawaki”

Ya shafa kansa tare da cire hannunsa a jikinta ya mike

tsaye.

“Da ne ai wannan, yanzu kuma mu da waka sai dai kallo, Hajiya ta hana kuma na hanu”

Ya nufi upstairs ta bishi da kallo.

“Ba cewa kai makarantar zaka je ba?”

“Wasa na ke miki, wane irin karatu yanzu ina cin amarci? Ki dai iya wanda nake

koya miki idan kin haihu sai na saka ki wacan din”

Ta mike tsaye.

“Haihuwa kuma”

Sai ya juyo yana kallonta.

“Yes... Ko ba ki san kina da ciki ba?”

“Ba ni da ciki Wallahi”

“Ki daina rantsuwa ni na san abun da na yi, yan mata fresh irinki

suna saurin daukar ciki idan sun hadu da mazaje irin Jaruman nan na gaske, kuma na san abun da na ke yi kullum Hajiyata”

“Ni ban gane ba”

Yayi dariya tare da juyawa ya cigaba da hawa stairs din.

“Anjima zan ganar dake Babyn Baby”

Da kallo ta

bishi har ya haye sama sannan ta kai hannu ta taba cikinta.

As he said sai da dare suka shirya daga shi har ita cikin tufafi mai tsada shi yana sanye da shadda sky blue ita kuma lace ja sai mayafinta sky blue, ba karamin kyau tai ba ko ranar da aka kawot

a gidansa ba tai kyau kamar na yau ba, tufafin jikinta kadai sun isar da kyaut balle kuma kwaliyar da ta sha kamar wanda zata tafi gurin biki. Yana zaune falo yana waya ta soma saukowa da talkamin yan kwakwasa sai amsa amo suke na daukar hankali, dagowa ya

i yana kallonta sai gashi ya mike tsaye yana kokarin yanke wayar da yake.

“Fadil za su sake kiranka”

Ya katse wayar yana kallonta cike da so da kauna, kusan kullum kara kyau take masa.

“Wow Babyn Baby kin duba madubi kuwa? I swear kin yi kyau ov

er”

Ta yi murmushi, kamin ta karasa saukowa ya iso ya daga ta sama yana juyawa.

“I love this girl, look at you ga pretty face, and heart of gold, ga beauty skin, kai Alhamdulillah”

Ta yi dariyar da ta bayyana hakoranta. Sai ya mika mata bakinsa.

“Kiss me kiss me”

Ya duko bakinsa ta saka cikin nasa, sai da ya tsotse bakinta sannan sauketa ya rumgume.

“Sweet lips”

Runtse idonta tai yana jin kunyar abun da tai, duk da kasancewar ya kusan zame mata jiki, domin kullum sai yayi kissing dinta

at any time any how kuma yace shi ma tai masa. Wayarsa ya ciro ya juyo da ita ya soma daukarsu hoto.

“Mu fa komai ba mu yi ba, ko dan pre-wedding pictures din nan da ake ba mu yi ba, ba dan ma gurin bikin kamfanin mu na sanar ke a matsayin matata ba da

har yanzu wasu ba su san na yi aure ba”

“Ai pre-wedding ba shi da kyau a musulunci”

Ta fada sai ya sumbancin kumatunta.

“To ya Sayyada”

Be yarda ta taka ta kafarta zuwa gurin motar ba, daukarta yai har gurin motar ta bude mata ta shiga sannan

ya zagaya dayan side din ya shiga, be yi ma motar key ba har sai da ya saka yatsunsa cikin nata ya rike hannunta sannan ya fara tukin. Kamin su isa gida ya biya ta gurin wani katon shopping mall mai tsada na manyan attajirai yai ma Baba siyayya turare san

nan ya dawo cikin motar ya sake rike hannunsa suka kama hanyar, kamin su isa sai ta rika jinta a wani yanayi na daban, wai ita ce zata je ganin gida daga gidan mijinta kuma tare da mijinta, so all her sad story ya zama story yanzu, take ta ji idonta ya cik

a da kwalla saboda canjin da Allah yai mata bayan dubun hakuri da wahalar da ta sha. A hankali ta kalli Sirleem sai shi ma ya kalleta sai turo mata bakinsa yai.

“Kiss me Kiss me”

Hannu ta kai ta buge bakin a hankali sai yai dariya ya kai hannunta sa

itin bakinsa yai kissing din hannun. Saboda yanayin unguwar yasa yai bakin waje ya dauko glass dinsa ya saka so that yayi badda sau, sannan ya bude motar ya fita ya zagaya bangaren Falmata ya bude mata ta fito, yai saka ma motar lock suka nufi hanyar da za

ta sada su da gidan yana rike da ledar turarun da ya siyowa Baba. A lokacin da suka isa bakin kofar gidan sai ya tsaya daga waje har sai da tai sallama ta fara shiga sannan ya shigo yana sallama da karewa gidan kallo.

Tumba na zaune bakin kofar dakinta r

ike da sandar da take dafawa idan zata tashi ko tai tafiya, sakamakon cirewar da kafarta tai sanadiyar natsarin da tai, ba a maida kafar ba saboda jijiyoyin su tsinke, daurin da akai nata a hannu ma ya kumbura sai ruwa yake mata, satin da daya asibiti ta d

awo gida saboda babu kudin magani, a lokacin da ta dawo gida sai yan bani na iya suka rika duba mata ciwon suna kara janyo mata aiki, bayan ayi daurin aka dade ba a duba ba ko da aka kwance sai aka ga ya fara ruwa daurin ya lalace, haka nan dai da karfin h

ali da taimako aka koma da ita asibitin aka sake mata wani nan ma ba a dace ba, ta sake dawowa gida tana jinya, jikin nan nata duk ya zube ciwon ya janyeta har wani tsufan wahala ya taso mata.

Akwai hasken farin wata ga kuma gulof kasancewar akwai nepa a

mman hakan be wadatar da ita ba sai da ta dauki touch light dinta ta haska Falmata domin tantancewa.

“Falmata ke din ce da gaske?”

Tumba ta tambaya tun kamin Falmata ta karaso inda take.

“Na'am Umma ina wuni”

Ta tabe baki tana jin wani irin ba

kinciki ganinta cikin shiga mai kyau ga jikinta ma ya fara kyau.

“Hmmm ashe kina tunawa da ni? Ai mutunci da karamci be ce haka fa Falmata, saboda ba ni na haife ki ba, shiyasa kika ji zuwa ganina asibiti ko? Sai yanzu za ki dauko kafa ki taho dan ba k

i da kunya, wato tun da mun aura miki tsoho mai nera kina can kina kwantawa a gado mai kyau kina yadda kike so sai ki watsar da mu”

Kamin Falmata ta yi magana Sirleem dake tsaye ya ce.

“Yanzu ma Baba muka zo gani, ina fatar yana nan”

Falmata ta k

alleshi da sauri jin abun da ya fada, Tumba kuma ta sake daukar fitilarta ta haske shi.

“Wanene wannan? Kanen mijinki ne ko dansa?”

Falmata ta kalleshi sannan ta kalli Tumba ta ce.

“Mijina ne”

“Wannan...?”

Tumba ta tambaya da karfi har zaw

o na kubuce mata, ta sake haska fuskarsa da sauri tana ganin kamar ta taba ganinsa.

“Ke Falmata kalli fa wannan ki gani, mu da muka aura miki tsoro? Na shiga uku ko aljani ne dai”

Cewar Tumba sai wani maida numfashi take cikinta na murdawa.

“Wall

ahi mijina ne Umma shi ne kuka aura min”

Falmata ta fada, tana kallon Naja da ta shigo gidan da sallama, at first kallon mamaki ta fara yi ma Falmata, sai Sirleem ya cire glass din idonsa so. that Tumba dake haska shi ta tantance ko waye. Naja na kallo

m Sirleem dake tsaye tai baya baya, bata san lokacin da ta daka tsalle ta daki kirji tana fiddo.

“Umma Sirleem Sirleem M2 Wayyo na shiga uku Wallahi Sirleem M2”

Ya fada cikin rikicewa mai kama da hauka ganin celebratie a fili kuma a cikin gidansu, ab

un da ba ta taba tsammani ba.

_________

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zum

a daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin am

are na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin

neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

64

*Khadeej

a Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Tumba ta fito da ido waje tana kallonsa, sai a yanzu da Naja take fadar sunansa ta gane ko waye

duk da ba wani saninsa tai can sosai ba, sai dai tana ganin hotunansa da wakokinsa can sama sama.

“Sirleem dai mawaki”

Tumba ta fada tana nuna shi jikinta na rawa, kamar ta unkura ta tashi sai kuma ta saka tsabar mamaki da kuma rashin kafarta ta had

u.

“Allahu Abkar, to to to ni ban gane wannan abun ba, daman can shi ne yai siffar tsofi ko kuma babansa ne?”

“Shi ne dai”

Falmata ta amsa tana kallon Sirleem. Tumba ta girgiza kai tana kallonsa, domin a iya tunaninta sun aurawa Falmata tsoho ne

kuma inda zata je ta sha wahala ashe gurin jindadi ta kaita ba tare da ta sani ba, daman can waya isa yai ma bawa abun da Allah be masa ba?

“Allahu Akbar Allahu Akbar, wani abu sai Allah, hakika abun da Allah ya rubutawa bawa be isa ya wuce shi ba, Wal

lahi yanzu kam na yarda”

Ta fada cikin kuka, tana kallon Baba da shigowar kenan rike da jakarsa ta zuwa kasuwa, Naja taje ta sauri ta karba saboda halayen kirkirin da ta kirkiro masa ganin ya fara wulakanta mahaifiyarta balle kuma ita, sai ya fisge abar

sa ya karaso yana kallon Falmata.

“Wa na ke gani haka?”

Ya tambaya cike da far'a kamar ba shi ba, abun da Falmata ba tai tsammani ba daga gareshi.

“Ni ce Baba Sannu da zuwa”

Ta fada tare da kai hannu ta karbi jakar sai ya girgiza mata kai ya

duka da kansa ya aje.

“Yanzu kuma Allah ya dauke miki wannan nauyin, dawainiya ta koma gurin mijinki”

Ya fada yana kallon yarsa cikin da farinciki da ya shafe shekaru be yi ba, Sirleem ya duka yana gaishe shi cike da girmawa tare da aje masa ledar t

uraren da ke hannunsa, kana ya kai hannu aljihunsa ya dauko kudo mai kauri ya saka a ciki ledar.

“Lafiya Kalau Wannan fa?”

“Wanda kuka aura min ne Baba”

Baba ya ja baya da sauri yana nuna Sirleem ganin zankadaden saurayi a gabansa bayan kuma shi y

a san tsoho ya aura mata.

“Wannan? Ko dai idona ne ba su gani daidai kamar yaro na ke gani”

“Shi ne Baba”

Baba ya kalli Falmata wanda ta amsa masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login