Showing 264001 words to 267000 words out of 304903 words
mawuyacin hali. Fashewa tai da kuka tana kallon Iya.
“Komai ta lalace ina sonta, dan Allah karku kasheta, ita kadai ta rage min a yanzu, komai halin da ta shiga ina son ganinta bana son na rasa na rasa komai a
yanzu”
Masauki yai mata a faffadan kirjinsa, wanda hakan ya bata damar tausayawa kanta ta fashe da sabon kuka tana jin kamar ta hade zuciya ta mutu ta hutu. Shi kuma ya lumshe ido yana sauraren kukanta dake shiga har cikin ransa yana jin kukanta kamar
Fadime da ya baro tana nata kukan!
***
A lokacin da Ammy ta dawo gida da tunani kala kala da kuma mamakin da bakinciki a lokaci daya na abun da ya faru da Iya, sai ta tararda Masarautar da wani sabon labari na rashin lafiyar Jurry da kuma Hajiya
Babba. Tufafin jikinta kawai ta canja ta shiga bangaren Mai Martaba ta sanar masa halin da ake ciki, sannan ta fito ta nufi asibitin. Ko da ta isa ta samu Kausar da Karima a dakin Hajiya Babba kuma tana kwana sakamakon allurar bachin da akai mata, saboda
yawan maganganun da take na abubuwan da ta aikata, Ammy bata san komai ba akan ciwon kuma wani be labarta mata abubuwan da Hajiya Babba take ta fadaa gadon asibitin ba, sai dai a ta yi mamakin ganin babu family ko daga daga bangaren Hajiya Babba haka ma da
ga bangaren Mai Martaba sai yayanta kawai, su ma suna ta soke kai kamar ba son kallonta.
“Jekadiya tace Juwairiyya ma ba Lafiya, ita a ina aka kaita?”
“Kanta ne yake ciwo, ban san inda aka kaita ba”
Kausar ta amsa cike da damuwa, Ammy dai bata sa
ke cewa komai ba sai kallon Hajiya Talatu take da baki ya juye gefe daya.
“Anya babu hawan jini na ga shi ke saka haka?”
Kamin su amsa mata Hajiya Babba ta fara motsawa ta juyo saitin Ammy dake zaune akan kujera, ta dade tana murza idon sannan ta bu
de ta sauke su akan Ammy dake ta mata sannu, Kausar da Karima kam hankalinsu ya mugun tashin, da sauri Karima ya nufi kofa tana fadin.
“Bari na kira likita”
Cikin hanzari ta fice zuwa kiran likitan, so take ya sake mata allurra tai bachi har sai Amm
y ta fita.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, magani
n sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turar
en sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani z
aku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
60
*Khadeeja Candy*
Litta
fin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Ammy ta dawo gida cike da tunani kala kala, domin babu abun da Hajiya Babba bata labarta mata ba na abun da ta
aika, a lokacin ne Ammy ta kara gasgata abun da Fadime ta fada, Shattima kadai ta labarwa abun da ya faru, sai Jekadiya ba ta sanarwa kowa ba saboda bata son ta sanarwa Baba Waziri a yanzu da yake cikin alhinin mutuwar yarsa. Sai dai ta kwana da tunanin ab
un a ranta tunanin sai ya zame mata kala biyu, ga na Iya ga na Hajiya Babba, sai ta ji tausayin Mai Martaba ya kara kamata da kuma yaranta da ake son ganin bayansu saboda abun duniya da za a mutu a bari. Haka ta kwana bangaren Mai Martaba da tunani kala ka
la a ranta,sai da ta gama azkar dinta sannan ta dawo bangarenta domin hada masa abun karyawa, ko da ta shigo sai ta samu Shattima zaune a dakinta yana latsa wayarsa, ganinta yasa ya dago yana mika mata gaisuwa. Sai ta amsa da murmushi tana kara jin son dan
ta a ranta, lallai ta yarda idan ba kai cuta ba Allah ba zai bari a cutar da kai ba, idan an samu nasara to kadan ne wanda zata zo da jarabawa.
“Tun da sassafe haka ko nan ka kwana?”
“Aa yanzu na iso”
“Lafiya Kalau”
Ya amsa yana murmushi, sai t
a zauna tana kallonsa.
“Shattima ka dage da addu'a, na san kana yi amman ka kara”
“Inshallah, mi ya faru?”
“Komai ai ya faru, lamarin na Iya kadai abun mamaki wanda na san ba dan addu'a ba da a yau ba mu kai haka ba, kuma bayan lamarin Hajiya Bab
ba abun mamaki ne matuka”
“Me ya faru da ita?”
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta labarta masa abun da ya faru da kuma irin kalaman da Hajiya Babba take ta fada mata a lokacin da ta je ganinta.
“Hajiya Babba ba ta ba ni mamaki ba kamar Jurry
, mahaifinta? Kuma ni ma dan'uwanta ne, wace irin zuciya ne wannan?”
Ta fada cikin tsananin mamaki marar misaltuwa. Ammy da idonta ya cika da kwalla ta ce.
“Shiyasa ake son addu'a kana rokon Allah ya baka zuri'a ta gari mai tausayinka da kaunarka ku
ma wanda zata amfani al'ummar musulmi kuma Annabi yai alfahari da ita”
“Allah sarki Mai Martaba bayan duk dawainiyar da yai da ita tana jin ta kai matsayin da take ganin ya kamata a kawar da shi? Ai ko ba amana bata kama su yanzu ba, ba za su taba samun
salama a cikin rayuwarsu ba, ko da ko abun da suke da buri ya kasance”
Cewar Shattima yana jinjina lamarin da yake jinsa kamar ba gaske ba. At the same time ya ji wani irin kaunar Fadime ta kara shiga ransa, domin dukan abubuwan da ta fada sun tabba ha
kan na nufi ba karya tai ba, kuma ta taimaki rayuwarsu, a lokacin da yan'uwa na jini da kuma irin su Iya suke so ganin bayansu. Samun kansa yai da murmushi duk da irin hali yake ciki na mamaki da alajabin abun da Ammy ta fada masa.
“Smiling...?”
Amm
y ta tambaya tana kallonsa da dan mamaki, sai yai sauri kallonta domin be san yana murmushin a fili a tunaninsa iya cikin zuciyarsa ne yake.
“Ah Amman Mai Martaba ya san da wannan magana?”
“Bana son tada masa da hankali, ya zai ji ace matarka da Yark
a suna kokarin ganin bayanka? Ga kuma Iya a gefe?”
“Yeah amman dole ne zai sani, and the most important thing is komai ya bayyana a yanzu, and Inshallah zan sake sakawa a yi masa saukar kur'ane duk da an sha yi masa a baya, amman hakan ba zai haka mu ka
ra ba, Ammy kuma ki kara tunatar da shi addu'a ya rike ta sosai”
“Shattima kenan, ni zan baka wannan shaidar da baya addu'a wata kila ta yanzu an manta da labarinsa, kuma duk da hakan zan saka a rubuta masa bismillah guda dubu ya sha, domin ita ma tsari
ce sosai daga komai”
“Allah ya kara tsarewa, ni fa daman ina tunanin Sirleem ba son Nana yake ba kamar hadinta ne...”
Shattima na kai Aya Nana na turo kofar dakin ta shigo.
“Ammy ina kwana, Ya Shattima Good morning”
“Morning dear”
Shattima
ya amsa mata Ammy kuma ta sakar mata murmushi.
“Ammy har yanzu shiru”
Nana ta fada tana zaunawa kusa da ita, sai Ammy ta kai hannu tana shafa kanta murmushi kwance a fuskarta ko bata fada ba ta san abun da take nufi.
“Already na yi magana da wan
da zai masa komai, so idan ya gama zai neme ni ni kuma zan masa magana, ai ni na ce zan yi ko?”
“To maganar gidan fa?”
“Hankalinmu ne ba a kwance ba, kwana biyun nan kin sani, bana son na yi ma Mai Martaba magana shi kuma yai ma Waziri da maganar a y
anzu, ki bari nan da sati daya idan komai ya daidaita sai mu ga abun da Allah zai yi”
“Okay Ammy wace makarantar kike ce a sama mishi?”
“Ban sani ba tukunan, ya fada min dai engineering yake son yi, kuma na fadawa Prof a sama masa makaranta mai kyau
mai tsada”
Wata kalar dariyar jindadi Nana tai.
“Thank Youuu Ammy...”
“Ki karbi account dinsa a saka masa 1million ya siye tufafin tafiya”
Shattima ya fada, sai Nana ta ware ido da karfi ta dawo kusa da shi ta rumgume shi tana murna.
“Than
k Youuu so much Yaya wow....”
Sai kuma ta dawo gurin Ammy.
“Ammy ara phone din pls”
Bata ko tsaya jiran umarni ba ta dauki wayar ta fice da sauri tana murna. Bayan fitar Ammy ma ta kintse ta nufi kicin domin ita da kanta take shiryawa Mai Martaba
abun da zai ci. Kamar fitarta Shattima ke jira ya aikawa Ra'ees da kira. Sai da tai ringing tana daf da tsinkewa sannan yai picking da muryar da ke nuna yanzu ya tashi daga bachi.
“Ra'ees”
“Na'am barka da asuba”
“Gida na ke son a nemo min within
Katsina and Kaita gida mai kyau”
“Kai zaka zauna?”
“No kyauta zan yi”
Raees yayi hamma sannan ya karasa tashi zaune.
“Okay amman wanda zaka bawa kyauta babba mutum ne ko karami”
Shattima ya san dalilin tambayarsa da yake saboda ya san irin
gidan da zai samo masa ne.
“A samo mai kyau dai karka damu da ko nawa yake, ina sonsa cikin kwana biyun nan pls”
“Okay”
Ya amsa sannan ya kashe wayar, Shattima ya jingina da kujerar da yake zaune yana murmushi tunawa da lokacin da ya taba kade Fa
dime.
***
Karfe goma da yan mintuna direba da ya dauko Mama Fulani da Shattima da Aliyu da kuma Fadime ya faka harabar masarautar. A nan kallo ya koma sama gurin Fadime, girman masarautar da kyauta har tsoro ya bata ba dan ta san masarauta ba ce ita
kan sai tai zaton unguwa ce mai zaman kanta ko wani babban kamfani. Yawan hadiman da suke ta harkokin gabansu ma kadai abun kallo ne, tafe take idonta na kalle kalle duk da kasancewar bata cikin farinciki da walwala saboda Wasim. Ita kadai aka bari baya t
uni Aliyu da Muhseen sun wuce gaba sai Mama Fulani da ke binsu, sai da ta shiga bangaren Ammy ta gane bata ga komai a waje ba, domin tsaruwar falon da yadda aka kawata shi ya wuce misali, ko'ina kallo take tana bawa ido hakkinsu, sai a yanzu ta yarda wata
sarautar ta fi wata lallai wani dan sarki ya fi gaban wani sarki, kamar wata kurma haka ta shiga cikin dakin Ammy sai kalle kalle take, idonta na sauka akan Ammy sai ta ji wani irin kwarjininta ya cika mata ido, gurin haske da gashin gira iri daya ne da na
Shattima, sai dai Shattima ya fi ta kyau nesa ba kusa ba, zaunawa tai a kasa tana ta kallon tsadadden lace din dake jikin Ammy da ke gaisawa da Mama Fulani, jin an taba kofar dakin yasa ta juyo sai tai arba da Shattima da ya shigo sanye da farar shadda ma
i wani irin haske da daukar ido, bakar hular kansa ta saka fuskarsa har wani annuri take, ga dogon hancinsa ya kara fitowa kamar an ja shi, farar fatarsa ma sai shining take kamar wani balarabe, murmushin da ya yafawa fuskarsa sai ya kara fito da saka siff
ar zatinsa da kwarjinin da ya cika idon Fadime har ta mike tsaye tana kallonsa, gaba daya ya canja mata kamar ba shi ba, wata kila ba dan tana da tabbacin fuskarsa a wayar da tai da shi ba sai ta rantse da Allah ba shi ba ne.
“Zauna...”
Ya fada yana
nuna mata gurin zaman a dai dai lokacin da kamshin turarensa ya kai mata hari a hanci. Zaunawa tai ba tare da ta dauke idonta daga gareshi ba shi kuma ya wuce inda take yana yi ma Mama Fulani sannu da zuwa.
“Mama barka da sauka”
Sai da ya gama gais
awa da ita sannan ya kalli Fadime ya sakar mata murmushi.
“Tashi ki zauna akan kujera mana”
Bata motsa ba balle tai alamar tashin sai kallonsa take tana jin zuciyarta na bugawa da mugun karfi.
“Wacan akwai rigima tun jiya kuka take ban san abun
da akai mata ba, na yi tambayarta har na gaji, yau kuma da ta tashi ba ta yi ma kowa magana ba”
Mama Fulani ta fada, sai Ammy ta kalleta
“Ko bata da lafiya ne?”
“Lafiyarta kalau”
Shattima ya amsa yana kallon da tai masa mugun kyau kasancewar a
cikin bakar abaya, irin kyau nan na fulanin asali masu haiba da daukar hankalin namiji.
“Ina Muhseen?”
Ya tambaya ba tare da ya dauke idonsa daga barin kallon Fadime ba, kamar yadda ita ma ta kasa dauke nata idon, sai sakwanni suke turawa junansu.
“Sun fa riga ni shigowa, na dauka ma nan suka shigo ai, maybe sun wuce gurin Mai Martaba ne, na ji Aliyu na fadin ma zai koma yau”
“Hmm dan wajen Fulani ba a son shiga mutane sai dole”
Ammy ta fada, sai Shattima ya mike tsaye.
“Fateema ya han
ya? Za ki ba ni labarin jirgi dai ko?”
Ta kasa cewa komai kamar ba ita ba sai kallonsa take, daman tun a jiya bakinta ya mutu saboda Wasim, yanzu kuma da ta zo nan ta ga wata sabuwar duniya sai ta raina kanta bakin ya kara mutuwa mututus. Murmushi ya sa
ke sakar ya kanne mata ido daya for the first time, hakan ya saka ta hade yawu da karfi ta cigaba da kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ta kai hannu ta dafa zuciyarta.
Ta inda Mama Fulani take shiga ba nan take fita ba, ta rufe Ammy da fada kan
shirun da tai bayan sanin komai, bata kara sanin Annabi a faku ba sai da Ammy ta labarta mata abun da Hajiya Babba take, kamin a jera musu abun ci da na sha ta dauki wayarsa ta kira Baba Waziri ta sanar masa sun iso kuma tana son ganinsa kamin ta iso gidan
sa, bata kashe wayar ba sai da ta soma lasa masa zumar abun da ya faru, ko awa daya ba kara ba sai ga Baba Waziri a gidan cikin tashin hankali, a nan Mama Fulani ta zazzage masa komai na abun da ya faru kana Ammy ta dora da nata. Ba karamin baci ran Baba W
aziri yai ba kuma be ga laifin kowa ba sai Ammy.
“Amman kin ba ni mamaki Ammy, ni yar'uwa na daukeki ba matar dan'uwa ba, ta ya za a hada kai da matata a cutar da dan'uwana kuma kin sani ki kyale ba ki fada min ba? Ta ya matar dan'uwana za ta so kashes
hi kuma ki zuba ido kina fadin baki da hujja, kin san abun da ake nufi da makiyi kuwa? Ashe baki dauki ran yayanki da kuma Mai Martaba a bakin komai ba kenan”
“Ato ni ma abun da na gani kenan, kasan wannan har zaka boye yanzu hakaabun da take fada min w
ai bata labartawa Mai Martaba abun da Hajiya Babba take ba, ta dai fada masa an kaita asibiti bata da lafiya”
Baba Waziri ya jinjina lamari.
“Ni na yi mamakin irin abun da Hajiya Talatu take yi, na san tana son Maijidda amman ba irin son da zai saka
ta shiga wannan halin ba saboda mutuwarta, shiyasa da aka kaita asibiti likitocin suka ce ba su ga komai ba kwakwalwarta lafiya kalau take, kuma sai sunayenku take ambata”
“Ni ma na yi mamaki sai dai na yi zaton ko saboda mutuwar ne”
Cewar Ammy tana
sauke ajiyar zuciya.
“Dole ne Mai Martaba ya san da wannan maganar, kuma har abada Juwairiyya ba zata taba yin albarka ba har abada”
Baba Waziri ya fada cikin wani irin bakinciki da bacin rai marar misaltuwa.
“Kar a tsine mata abun da ta aikata k
adai ya isheta”
Ammy ta fada sai Mama Fulani tai mata wani kallo.
“Allah ya tsine mata albarka, yarinya tai yi kokarin kashe mahaifinta kuma ki ce kar a tsine mata, Allah ya kwashe mata albarka ita da uwarta”
Ammy ta runtse ido tana girgiza kai k
o kadan bata son abun da ya shafi tsinuwa domin ta san yadda take cin jiki da dukiyar mutum.
***
Sai dare Shattima ya sake saka Fadime a idonsa, fitar da yai dazun daga dakin Ammy gurin gaisuwa yaje be tashi ba azahar daga can kuma ya wuce asibiti zu
wansa na farko tun bayan da akai masa transfer, guri shugaban asibiti ya fara zuwa suka gaisa da shi daman sun san juna yai masa maraba sannan yasa akai masa iso zuwa office dinsa, ko da isa ya samu office dinsa da komai a kintse, takardunsa da komai na sa
da yake can Ra'ees ya turo masa su a nan kuma an jera masa sa komai, kwalayen da ke aje gefe ya rika budewa yana dauko abubuwan da ke ciki tare da dorasu a muhallin da yake so, a kwali na uku yai arba da littafin Fadime, murmushi yai ya zauna a saman kuje
rarsa yana karantawa tana da good handwriting domin duk abun