Showing 288001 words to 291000 words out of 304903 words
bakin abun, su nan garin haka suke aure ni Wallahi garin mu ba haka ake ba”
Ta wani turo baki gaba tana jun cikin ya kame mata ta ko'ina, daker bachi yai gaba da ita, la'asar na yi aka tashe tai sallah sannan ak
a bata na yamma, wannan karon da hawayenta da komai ta sha tana ta tsirewa Hajiya Mairo albarta a ranta. Ranta be washe ba sai ta aka fara gabatar da events, ta fara ganin fata da rawar jiki kamar za a cinyenta. Ranar da akai bukar kai wasu yan'uwan Bappa
da Inna suka u
Iso, the following day akai sa lalle na al'adar mutanen Yola sannan akai Walima, aka daura aure on Saturday. A babban masallacin jumma na Katsina aka daura auren Shattima da Fadime, akan sadaki 800k.
Fadar irin farinciki da Bappa yake a
wannan lokaci ba zai yiyu ba, baki bude sai gaisawa yake da mutane yana sanye cikin Blue Shadda mai dan karen tsada sai wani haske take, a babbar Hotel aka yi liyafar cin abinci, sai abun da ranka yake so kake ci, kusan duk wanda yake jigo a masarautar ya
hallarci daurin auren ban da Jarma, da aka nema aka rasa tun lokacin da asirin su Hajiya Babba ya tonu, sai ya tattara komai nasa da iyalansa ya bar garin. Misalin 4 jirgin da sukai booking ya tashi zuwa Yola, karka ku so ganin Fuskar Shattima, murmushins
a ya kasa boyuwa, zuciyarsa kal kamar be taba shiga wata damuwa ko bacin rai ba.
A daren ranar da aka daura auren Ammy tai bikinta tare da kawayenta, sai kuma Amarya da aka jira mai walima ta zo tun daga sokoto birnin Shehu tana gabatar da karatunta, b
abu wanda zai yi ma Fadime kallo daya ya dauke ido, saboda kyau da tai, maroon lace ne jikinta da farar alkibba sun haskata sosai ta yi kyau kamar ba ita ba, ba laifi ta kama kanta sosai domin tun da aka fara bikin Hajiya Mairo da wata yar'uwar Mai Martaba
suka saka ta gaba suna koya mata tafiya da kuma yadda zata rika amsawa mutane idan sun gaisheta, sannan suka gargade ta ba kowa za tai wa murmushi ba, ba kowa zata sakarwa fuska ba. Hakan yasa bata wani sake ba har sai da ta hango Inna ta shigo gurin tare
da tagwarta, kana ganin tufafin da suka saka kasan hadimar ta Ammy ce, Ammy da kanta ya mike ta tarbi Inna dake sanye da atamfa yar ubansu da Hijab ta zaunar da ita kusa da ita, sai Inna ta ji wani girma da kwarjini ya kamata, tana kallon yarta a guri na
musamman da aka kawata ita kuma gata a kusa da matar sarki.
Sai kusan 11pm aka yi addu'ar rufewa bayan mutane da yawa sun gabatar da jawabai ciki har da Ammy, a gaban teburin kowa rika aje takeaway mai cikin da kayan dadi da kuma abubuwan tsinuwa ir
in su agogon hannu wasu tsarka kowa da abun da yake samu a ciki sai dai duk abun da aka saka a cikin sarka ko agogo worth 50k.
On that day Fadime ta kwana a gidan Sarauta kuma ta wuni da mahaifiyarta tana ta mata nasiha kala kala, da yamma aka shiga da
ita bangaren Mai Martaba yai mata maraba da shigowa cikin familynshi sannan ya dora mata da nashi nasihan, karku so ganin yadda wayoyi suke daukar Fadime da camera, daman tun da aka fara events din ake daukarta a video da hotuna, sai haskawa take ga ta ta
sha jan lallen kamar dan ita kawai akai shi. Ita kanta a yanzu ta san ta taka wani matsayi a rayuwa, matsayin zama surukar sarki da kuma matsayin zama matar aure, wadannan abubuwa guda biyu sun zo mata a lokaci daya. Kwance tai a cinyar Inna tana ta haway
e sai a lokacin ta fara missing din abubuwa da ta saba da su, ba ma kamar Inna da kawayenta da kuma Bappa, domin mafi yawan nasihar da Inna take mata na ta yi uwa mijinta biyayya ne, a cewarta su yanzu sun sauke nauyi hakkinta da kulawarta yana karkashin m
ijinta ne, daga karshe Inna ta rufe mata da bankwana tana hawayen ita ma.
Misalin 8pm aka shiga da amarya gidanta gaba da baya manyan motoci ne na alfarma, daidai kofar shiga falon aka faka motar Amarya aka shimfida mata wani jan carpet wanda zata taka
ta shiga ciki, Gwaggonta da wata Gwaggon Shattima ne suka riko hannunta suka fito da ita motar hadimai na zuba kirari, masu guda suka karade gidan da guda, daga bisani aka soma busar sarakuna.
“Ki ce bismillahi”
Gwaggon Shattima ta fada tana sanye
da black lifaya tana rike da hannun Fadime, Jekadiya kuma na daga baya tana fesa mata turare. Daker Fadime tai bismillah saboda kukan da take domin a yanzu ta yarda rayuwarta ta canja kuma ta yarda ya rabu da su Inna da Bappa zata koma rayuwa da Shattima d
a yan'uwansa, ga wani jazabar aure da take jin tana sauko mata, a katon falon na biyu aka daunar da ita baka jin komai sai guda da kamshin turare ta ko'ina, daga waje kuma masu busa suna ta aikinsu.
ZAINAB POV.
Bata gamsu Iya ta mutu ba har sai da W
asim ya kaita gurin kabarinta ta saka hannunta ta taba kasar gurin sai ga ta tana hawaye da murmushi a lokacin daya, ko za a kasheta a yanzu ba zata iya fadar yadda take ji ba, ba ta san yadda zata misalta ba.
“Finally...”
Ta furta tana mikewa tsaye
sannan ta sannan ta juyo ta kalli Wasim da ke tsaye bayanta, takawa ta fara yi har ta isa inda yake tsaye yana kallonta cike da tausayi.
“Ban taba mafarki ko tunanin wata rayuwa za ta zo min a haka ba”
“Haka ne abubuwa da yawa ba mu saka su a tsari
n rayuwarmu ba kuma su kasance mana”
“Yeah haka Allah ya tsara, yana tsarawa bawa abun da yake so ba abun da bawa yake so ba”
Ta karasa tana danne kukanta, ya fara takawa tare da ita suna tafiya. Tana tafiya hawaye na wanke mata fuska, a ranar mutuwa
ne kawai Zainab ba tai ba akan kuka, duk yadda take jin rashin kyautar Iya da yadda take jin kamar zata iya tafiya ta barta mutuwarta ya kawar mata da komai, sai ta ji kamar ace bata mutu ba, no matter how bad she is ta ji tana bukatarta a kusa da ita. Da
kukan tai bachi da shi ta farka da asuba ma haka tai ta kuka sannan tai alwala bayan ta gama sallah asuba sai ta daga hannunta da zimmar yi ma mahaifiyarta addu'a sai kuma ta fashe da kuka, idan ta yi mata addu'ar za a amsa mata ko kuma aa?
Within a mon
th Zainab ta koma abar tausayi bata iya cin komai sai yayan itatace da ruwa, jikinta ya koma very weak bata da wani kuzari, duk yadda Wasim yake son ta sake sai ta kasa bata komai sai yawan kallon mutane ko saurare abu mai wahala ta bude baki tai magana, a
bubuwa da yawa sun taru sun yi mata yawa, gashi a nan bata chat balle ta rage wasu abubuwan.
After some months...!!!
** ** **
As usual suna zaune akan wani dutse yana ta mata fira amman kwata kwata hankalinta ba ya gurin, ko saur
arensa bata yi.
“Wasim... Idan na bar garin nan zaka rika kawo min ziyara ne?”
Kallonta yai jin yadda ta dauko wani zance na dabam, ba akan firar da suke ba.
“Zan biki dai mu tafi tare, ta ya zan kyale ki rayu inda baki da kowa kuma ke kadai?”
“Bana ka aikata wani laifi da zai saka yan'uwanka su ga laifinka, kai kana jindadin zama a garin nan, kuma kowa na ka yana nan be kamata ka bi son ranka ba ka aikata kuskure, bana fatar wani ya sake aikata wani kurkuren saboda ni”
“Idan har babu ke a
garin nan, ai garin ba zai min dadi ba, ban ga amfanin zamana a nan ba matukar ba ki tare da ni”
Ta kalleshi
“Saboda me?”
Sai shi ma ya kalleta ido cikin ido
“Saboda ina son ki...”
Saurin mikewa tai tsaye tana maida numfashi tare da hade ya
wu da karfi, zuciyarta ta shiga bugawa tana rabawa sassan jikinta jini. Daman da dade da fahimtar hakan a kalamansa da yanayin yadda yake mu'amalantarta sai dai bata tsammaci haka daga bakinsa ba a yanzu, kuma a irin wannan lokacin. Shi ma mikewa yai tsaye
yana kallonta.
“Kin ji abun wani iri ko? Ni ma haka na ji a lokacin da abun ya fara kamani...”
Ta yi shiru bata ce komai ba, shi maWaziri shirun yai can kuma yana kallon yadda hawaye ke sauko mata.
“Cancanta ba ko? Ko kuma na yi sauri ne? Ko ki
na duba alakar addininki da nawa ne?”
Hannu ta kai ta share hawayen ta da ta tafiya ba tare da kalleshi ba.
“Zan shiga ciki na huta”
Da kallo ya bita har ya daina hangota sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya saka hannayensa biyu ya shafa kansa zuwa f
uskarta, he can't lie to himself shi kansa ya san yana son Zainab kuma yana tausayinta fiye da yadda yake tausayin kansa, but still yana jin son Fadime har yanzu a ransa, maybe sooner or later zata fice mishi daga rayuwa da tunaninsa but for now idan ya tu
na yana jin wani iri.
FALMATA POV.
Tana jingine jikin gadon shi kuma ya dora kansa saman karamin cikin nata yana sauraren hausar da take karanta masa.
“Ko wane jaririya ko jaririya su kan yi kuka a lokacin haihuwarsu da kuma kurciyarsu, sai dai
kuka bayan girma kowa yana da dalilin yinsa
Da ace na wa kukan na mutuwa ne, da nafi kowa farinciki, ashe ba sai rai ya bar gangar jiki ake mutuwa ba, na tabbatar da mutuwa kala biyu ce, kaico ni Aminatu!
A yanzu kan na gasgata cewar na dade da mutuwa g
angar jikin ce kawai a aje, kuma na yarda mace bata da gata, gurin yan'uwa da al'ummarta...”
Ta rufe babin tana juya bayan littafin tare da karanta sunansa tare da sunan marubuciyar.
“BAKAR WASIKA Na Khadeeja Candy, gaskiya daga ganin littafin nan za
i yi abun tausayi”
Dan dagowa yai kadan ta kai hannunsa ya taba bakinta.
“Ko?”
Sai tai murmushi ta kalli agogo.
“Ka ce 9:30 zaka tafi gashi har 10 ya wuce fa”
Lumshe ido yai ya saka dayan hannunsa yana shafa wani bangare na cikinta
“Ban
gaji da ganawa da dana ba ne shiyasa, let him meet his dad”
Ya karasa tare da kissing din cikin nata na 5 months.
“Kai ne oga kuma kai kake karya dokar kamfani”
“Zan fada musu madam ce ta hana ni fitowa tana ta ba ni.... ”
Be karasa ba ta bug
e masa baki domin ta san abun da zai fada, ba kunyarta yake ba dirty talk any how yake mata, shi da fada ita da jin kunya. Sai ya tashi yana dariya tare da gyara suit dinsa.
“Me zan dawo miki da shi?”
“Bana son komai”
“Really....”
Ya kanne mat
a ido zai fara barin zance ta dauki fillo ta jefa masa, sai ya fice dakin da gudu yana kyalkyalar dariya, ita ma dariyar tai ta sauko da kafafuwanta kasa.
“I love you babyn Baby”
Ya fada da murya da zata iya jinsa, murmushi tai ta mike tsaye ta isa
gurin window tana kallonsa yana daga mata hannu har ya shiga motar yana jefo mata kiss, ita kuma ta karba ta manna a kumatunta duka biyu.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu
ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke
kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son
komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna a
ika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
66
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via
08036126660*
Bayan kowa ya fice masu nasiha sun yi daga bangaren Amarya kuma Nana da wata cousin dinta sukai kasancewar Fadime bata da kawaye a gurin.
Shattima ya kai hannunsa ya daga mayafin amayarsa dake ta kuka, domin ta gane da gaske rabuwa za
tai da kowa ta koma sabuwar rayuwa, hakan yasa duk wata murna da farinciki da take na aure sai ya kau. Ido ya kura mata yana ta kallon kyakkyawar fuskarsa da ta sha makeup hawaye sai sauko mata yake. A yau ta fi masa kyau fiye da kullum domin har wani ann
uri da haiba take tsabar kyau da tai.
“Subhanallahi ahsanal halikin”
Ya furta yana kallon yadda Allah ya jera mata kyau gwanin kyau da burgewa, kuka take amman dan karamin bakinta motsi yake kana gani kasan magana take da kanta can cikin rai. Matsaw
a ya kara yi daf da ita ta yaye mayafin gaba daya ya rumgumeta.
“Na san zaki ji babu dadi, amman ba a kuka a irin wannan ranar ta farinciki ranar da mutane da dama suke ta fatan gani ba su samu haka ba, ranar yau rana ce mai muhimmanci a rayuwarmu”
Lamooo tai kamar wata mage tana saurarensa, fanfan kirjinsa ya wadatar da kukanta a take ta ji kukan ya yanke mata, sai dai bata jin wani abu mai kama da farinciki a yanzu kuma bata tare da kishiyarsa. Hannunsa ya kai ya kama hannunsa da ya sha jan lalle y
a rike yan siraran yatsunta yake kallo yana wasa da su a hankali, dayan hannunsa kuma na shafa bayanta.
“Yau kin zama yar gata, matsayinki ya karu, za a fara rubanya miki ladarki daga yau, kina so ai ko?”
Ta daga masa kai a hankali.
“To ki gode Al
lah”
“Alhamdulillah”
Ta furta a shagwabe.
“Iyeee ashe kin iya? Fada min ina kika tsaya a karatunki?”
“Na sauke ai”
“Really?”
“Yes”
“Bayan nan fa”
“Shikenan”
“Ba ki yi wasu littafan ba?”
“Ban yi ba”
“Amman ai a makaranta an
koya miki yadda ake wankan haila ko?”
Ta dan yi shiru kamar ba zata ce komai ba.
“Eh Inna ce ta koya min”
“Janaba fa?”
“Minene kuma Janaba?”
Ya wara ido tare da saka hannunsa ya dago kanta ta fuskance shi.
“Da gaske ba ki sani ba?”
“
Wallahi ban sani ba, abinci ne?”
Murmushi yai mai kyau murmushin da ya bayyana hakoransa, sai ya kai bakinsa saitin nata, a tunanin wani abun zai fada mata sai ta ji bakinsa cikin nata ya kama lips dinta ta tsosa tana ta kokarin kwace kanta ta kasa, har
sai da ya daga fuskarsa daga nata, sai ta sa hannu ta goge bakin ta fara tara yawu tana jin wani kyankyami a zuciyarta. Ba dan tana kunyarsa a yau ba da sai ta fada masa bata son kazanta, amman ta masa uzuri saboda ita amarya ce a yau, kuma ance tai biyay
a an fada mata kar ta daukaka halshenta sama da na shi, kuma idan yana mata fada tai shiru ta saurara sai ya gama sannan ta fada masa manufarta cikin kyakkyawan lafazi. Kokarin mikewa tai tsaye.
“Zan shiga ban daki”
Yana jin haka sai ya rigata mikew
a tsaye ta saka hannayensa ya dauke ta cak sama, abun da da marar jiki sai gai sama sosai kamar ya dauko filo, dariya tai ta saka hannayenta ta zagaye wuyansa.
“Ashe zaka iya daukata”
Murmushi yai ya nufi upstairs da ita, ya tura kofar dakin ya shiga
har cikin bandaki ya sauketa.
“Fitsari zaki yi?”
“Aa bakina zan wanke”
Sarai ya gane saboda ya yi kissing dinta ne zata wanke bakinta.
“Ashe ina da aiki”
Ya furta yana murmushi.
“Aa baka da aiki ai ni zan wanke da kaina”
Kamin yace
komai ta kunna fanfon ta fara kurba ruwan tana kuskurewa, sai da tai hakan sau kusan bakwai yana tsaye yana kallonta sannan ta juyo.
“Ya wanku?”
Ya tambaya yana matsawa kusa da ita, sai ta daga masa kai.
“Eh”
“Mu gani”
Ta wangale masa baki
n sai ya kai hancinsa kamar zai shinshina sai ya sake kama lips dinta ya fara tsotsa ya saka hannunsa ya rike kwankwasonta ta yadda ba zata iya matsawa ba, abun ka da an dade ba a hadu ba sai ya samu damar shanye 15% na kishirwar kiss din a tsaye cikin ban
daki, tun tana iya tsaye ta kafafuwanta har ta kai ta ta fara yin kasa sai saka hannayensa ya dauke ta yai sama da ita, duk yadda zata yi ta ya saki bakinta ta yi yaki saki domin daukar da yai mata sai ta bashi damar matse hannayenta inda karfinta a nan ya
ke, sai ya zura mata halshensa sannan ta sama damar cije sa ba shiri ya zare bakinsa yana runtse