Showing 6001 words to 9000 words out of 304903 words
kuma rike da lemun tsami yana matsawa a karamin kofin, farar singilat ce jikinsa sai farin tawul din da ke daure a ƙugunsa, fafaren kafafuwansa kuma sanye da takalminsa na bedroom.
Sai da ya gama matsa lemun sannan ya saka tea spoon ya garwaye lemun t
samin da tsamiyar suka hade jikinsu, a take ya daga kansa sama ya hanye, a gurin ya dire kofin ya mike tsaye ya nufi bathroom, he spent more than thirty minutes a bathroom din yana jika kansa da ruwa sannan ya fito rike da wani karamin tawul yana goge kyak
kawan jikinsa, gaban madubi ya tsaya yana goge gashin kansa. Fari ne kyakkyawan gaske, irin kyau nan mai daukar hankali, bafulatani gaba da baya amman idan ba sani kai ba sai ka rantse da Allah baasbine ne ko shuwa, ko'ina na jikinsa yana amsa sunansa na n
amiji kamar yadda muryarsa da siffar zatinsa take haska surarsa. Wani farin mai, mai sanyi ya dauka ya shafa a hannunsa ya murza sannan ya shafa shi a jikinsa, kana ya ware hannayensa yai mika, wacce ta sanarwa dukan jikinsa.
Wayarsa da ke kan gado ce
tai ringing, sai da ya kwance tawul din jikinsa sannan ya nufi wayar ya dauka.
“Nana”
“Na'am Labib ba Lafiya yana ta ihu”
“Waya taba shi?”
Ya tambaya sanin cewar daman can ba lafiya ta isheshi ba.
“Babu ina ma dakin, sai kawai na ji yayi ky
alowa ya fashe da kuka, jikinsa ma duk yayi zafi”
“Ku kira Doc”
“Ammy ta kira shi”
“Gani nan zuwa”
Ya fada yana sauke wayar daga kunnensa, kiran Nana na sauka na Muhseen ya shigo wayarsa, da murmushi Omar yai picking call din.
“Shattima kan
a gurin Ammy? Ko kana Kaduna”
“Ka shigo gari ne?”
“Yeah ina Yola yanzu haka”
“Wow gani zan je fada yanzu”
“Okay mu hadu a can”
Daga haka ya sauke wayar yana murmushi he can't remember when last ya ga Muhseen mutanen Abuja.
Daukar tawul di
n yai yaaje shi a muhallinsa sannan ya bude wardrobe ya dauko farin jean and blue t-shirt ya saka, a gagauce ya shirya ya saka agogon hannunsa ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin.
“Baba Adamu.... A tashi mota yanzu nn zamu j
e fada Labib ba lafiya”
Tun kan ya sauko ya fara kwalawa Baba Adamu kira, abunka da mai jira jikin na rawa Baba Adamu ya nufi motar yai mata key sannan ya fito ya budewa Shattima. Tun kan su shiga motar mai gadi ya bude gate Shattima na shiga Baba Adamu
ya fisgi motar kamar ba Dattijo ba.
“Ahaaa haka nake so, a dinga taka mota kamar mu kadai ne a garin nan”
Omar ya fada yana jindadim yadda Baba Adamu ke gudu da motar kamar dominsu kawai akai titi.
________________________
Did i ever write s
omething about witch? (Mayu)
Do you remember other family Mama Fulani da suke Yola? The story is about them now
🤗
*FULANI -it's not free, if you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
I just
published "Free Page -2" of my story "FULANI". https://www.wattpad.com/1104521181?utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_source=android&utm_content=share_published
*
🐄🐄
FULANI
🐄🐄
*
By Khadeeja Candy
*Free Page -2*
Police din da suke gadin
Masarautar ne suka bude masu gate, suna dagowa Shattima hannun duk kuwa da kasancewar ba su da tabbacin yana ganinsu domin bakin gilashin motar ba zai basu damar ganin ya karbi gausuwarta su ba ko akasin haka
“Fada za mu biya ranka ya dade?”
“A a sa
i na fara duba Labib”
Kai tsaye Baba Adamu ya nitsa da motar cikin harabar Masarautar kamin ya dauki wani bangare da zai sadashi da bangaren Momy.
Kamin su karasa wayar Shattima ta sake ringing cirota yai daga aljihunsa yana dubawa Hajiya Karama ce ru
buce a gaban wayar, sai da tai ringing kamar ba zai daga ba sai kuma yai picking.
“Shattima, Labib ba lafiya”
“I know na shigo cikin Masarautar ai”
Mikewa tai tsaye daga saman kujerar da take zaune ta fito daga dakinta ta zagayo ta fito backyard t
a tsaya tana hango motarsa.
“Okay”
Ta sauke wayar da already ya kashe kiran tun da ya bata amsa.
A gaban wata katuwar kofa wacce ta sha ado kamar ba za a mutu ba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito da sauri ya budewa Shattima. Cikin wata irin is
a da kasaita Shattima ya sako da kafafuwansa waje ya fito daga cikin motar yana wata irin tafiya ta takama kamar wanda baya son taka kasa, a zahirin takamarce da isa da kuma kasaita a tare da shi kamar yadda idon kowa na cikin Masarautar ke gani, sai dai a
badini sam babu hakan a tare da shi ko da rana daya be tana jin ya fi wani ba dan yana dan sarauta, be taba jin wani ba sa'ansa ba ne dan yana da dukiya da ilmi, ba zaka taba fahimtar hakan ba har sai idan ka zauna da shi ka fahimce shi sosai da sosai.
Fadawan da ke gadin kofar ne suka bude masa da sauri suna risinawa tare da zuba gaisuwa, dayan kuma nata aikin isar da kirari, ko kallonsu be yi ba balle ya amsa musu gaba daya hankalinsa yana gun dansa kiran da Zainab tai masa bayan na Nana yasa hankali
nsa ya kara tashi.
Cikin tafiyarsa ta kasaita ya natsa kafarsa cikin wani babban guri.
Wani irin katon falo ne mai dauke da Turkish furnitures tun daga kan kujeru har carpet da center table, da kuma side table dake kowace kusurwa ta kujerun, ga katon H
oton mai Matarba, sai kuma hoton Ammy sai na Hajiya daga gefe na mai Martaba a tsakiya sai hotunna wasu muhimman mutane na Masarautar dake tsaye a falo, idan ka cire farin fentin da ya kawata falon komai na cikinsa ja ne gwanin sha'awa, falon ya sha ado sa
i dai ba ado irin na komai a zuba ba, a a adon yan zamani wanda za a kawata falon da abu kadan amman masu kyau da tsada ta yadda duk wanda ya shiga ciki sai ya manta a wace duniyar yake, idan kana a cikin falon za kayi zaton akwai hadari a waje ne ko kuma
yamma ta yi ko ma kai zaton farkon budewar safiya ne sakamaon hasken da aka kawata falon da shi kadan ne, mai daukar hankali, sanyin ac ta ko'ina, ga wasu manyan kyandira irin na zamani masu aiki da wutar lantarki suna bada haske a falon gwanin burgewa, ta
dayan bangaren kuma wani irin kamshi ne ke tashi a cikin falon kashin da ba zaka iya tantance wane irin kalar turarene ba.
Wata babbar kofa ya nufa mai kyau da kyalle kamar an am mata ado da zinari, ya kai farin hannunsa ya tura kofar ya shiga, sai ya
tsinci kansa a wani matsakaicin corridor mai kama da karamin falo an cika ko'ina da na gurin da manyan fulawoyin na kasko da jan carpet.
Mikewa yai straight zuwa katon stairs din da ke gabansa, gabansa kawai yake kallo har ya haye sama, kofar farko ya far
a turawa tun kan ta karasa budewa ya jiyo kukan dansa, hakan yasa shi hanzarin cira kafa ya shiga cikin falon mai kama da da wata karamar fadar turawa, a wannan falon kam komai na cikinsa blue ne idan ka cire farin fentin mai kawata ko'ina na gidan, ta ban
gare daya kuma wani gini ne akai a cikin gurin mai kamar swimming pool sai dai wannan anyi shi da dan yi tsayi, an masa kwalliya da kwaryar da kuma rudayi sai dawusu a samansu yana furzo ruwa gwanin sha'awa, a iya cikin gilashin ruwan ke tsawa ko kadan bas
a digowa kasa balle har su sauka.
Falo ne mai dauke da set din kujeru uku kujerun farko kanana ne an jerasu kamar kujerun dinning wato a zagaye, sai dan karamin tebur a tsakiya da kuma wani karamin carpet blue, na biyun su kuma manyan turkish ne masu d
aukar hankali, sai wasu daga can karshen falon su ma blue kamar dai sauran an zagaye gefen da su, su ma kuma suna da karamin carpet da center table.
A gaban falon kuma wani katon kirsten tv stand ne fari mai gloss fronts da haske blue, left and right na
tv stand din matsakaicin show glass ne mai haske a ciki blue color an masa kwaliya da turaruka na alfarma masu kyau da tsada gwanin burgewa.
Ga wani katon plasma da aka kawata tv stand da shi kamar matanen ciki za su fito waje.
A dayan gefen kuma wani
karamin madubi ne na aka manna mai dauke da gurin wanke hannu, yamma da falon kuma matattarar cin abinci ce mai zamam kanta wacce aka ware mata kofarta dabam kusa da wani katon freezer mai kofa biyu, a dinning area din ma akwai madaidaicin plasma wanda za
i bawa duk wanda yake zaune a dinning din damar kallo.
Kofar da Umar ya shigo ce kawai gini a cikin falon sauran duka glass ne gwanin burgewa.
A dayan bangaren kusa da dinning akwai wata karamar kofar glass, shiga cikinta na sadarda mutum da wani keba
ntaccen guri mai dauke da set din karamin dinning har biyar an rarrabasu an jera ko wane set dabam da wani.
Ta backyard din mutum zai iya hango wanda ke tafe da kuma abunda ke gudana a harabar Masarautar sai dai ba zai bawa mutum damar hango bangaren m
ai Martaba ba, dama da shi kuma wanda ke tsaye a gurin zai iya hangon garden din dake bangaren Momy, shi ma kuma ganin mai shiga ko mai fitowa ne kawai mutum ke da damar yi ba wai komai da komai na cikin ba kasancewar garden din na da manyan itatuwa da kat
on Swimming pool a gafe na dutse.....
Nana na ganinsa ta mike tsaye rike da Labib da tana jijjigashi ta nufi gurinsa. Cike da kulawa da tausayi da kuma kaunar dansa ya sa hannu biyu ya karbe sa.
“What happened?”
“Ba wanda zai fada maka ga abunda
ya faru fa, ina dakin kawai yai kyalowa”
“No karya kike na fada muku a daina barinsu su kadai”
Bata sake unkurin cewa komai ba ta koma ta zauna tana kallonsa.
A kafadarsa ya dorashi yana jijjigashi tare da karanta masa ayatul kursiyu ya tofa masa s
annan ya nufi hanyar dake kusa da dinning da kansa ya bude kofar ya shiga, yana shafa bayan Labib a hankali yana kallon abunda ke gudana a kasa.
Ta kofar farko Hajiya Karama ya fito ta nufo inda yake tsaye.
“Har ka iso, ya jikin na shi?”
“Da sauk
i”
Ya amsa mata domin ya daina kukan da yake.
“Me ke damunshi”
“Ban sani ba”
“Kawo shi”
Ta karbe shi tana jijjigashi cike da kulawa domin ita ma kanta tana kaunar yaran.
“Nana tace kyallowa yai, na fada musu a daina bar min yara su kada
i, if not zan dauke su daga gidan nan”
Ya fada yana juyawa ya kalli wata harabar dabam kana ya aje numfashin da sautin da ke nuna ba da wasa yake ba, biyoshi tai tana girgiza kai.
“Nono Ammy ba zata jidadi ba, am samu mai kula da dakinsu fa, na ce a
barta ta kula da su Iya tace bata yarda da ita ba”
“Wacece?”
Ya juyo yana tambaya.
“Wata ce ba zata wuce 16-17 years ba”
“Miyasa ba ta yarda da ita ba?”
“I don't know ko maybe saboda ta yi kankanta ne”
Kare mata kallo yai ya dauke kai
“Ji dress dinki, na sha fada miki ki daina irin shigar nan”
Ya karasa yana takawa a hankali zuwa gurin karfen dake gabansa. Sai ta kalli jikinta.
“What's wrong with my dress?”
Be amsa ta ba ya juya ya fice daga gurin ya barta rike da Labib din
a kafadarta.
Murmushi tai tana kara kallon kanta, dogon wando ne da wata riga mai guntun hannu wacce ta tsaya iya kwankwasonta, ba laifi kayan sun matse ta sai dai ba irin matsuwa can can sosai ba, a gurinta hakan normal ne ko ba komai tana jindadin yadda
hankalin maza yake tashi idan sun yi arba da irin halittar da Allah yai mata, hakan na mata dadi sosai wai sai dai a gani a hade yawu babu yadda za'ayi da ita.
Bin bayansa tai ta kofar da ya shiga tana cigaba da murmushi, a kujerar da ke kusa da kofar t
a zauna ta sa dayan hannunta tana gyara yar karamar jar hular da ke kanta.
“Yayi shiru?”
Nana ta tambaya tana nufo inda Zainab din take zaune.
“Yeah i think yayi bachi”
Ta taba jikinsa sai ta ji shi da dan zafi za tai magana Zainab ta mike tsa
ye tana kallon Doc Deen wanda ya shigo rike da dan karamin akwatin magani, fuskarsa sanye da farin gilashi.
“Sannu da zuwa Doctor”
“Hajiya Karama”
Ya amsa mata yana murmushi tare da kallon Shattima wanda ke tsaye jikin window ya rumgume hannayensa
ta baya yana kallon harabar gidan.
Har Doc ya zauna Zainab ta mika masa Labib ya fara duba shi Shattima be juyo ba.
“Miya same shi?”
“Ba komai haka kawai yai ihu”
Nana ta amsa shi tana zaunawa kusa da Doc kamar ita ce zata duba yaron, Doc Deen
yayi murmushi yana kallonta.
“Ko na baki ki duba shi?”
Dariya tai mai sauti ta make kafada tana girgiza masa kai. Zainab ta yi murmushi ta nufi gurin da Shattima yake tsaye ta tsaya ta jera tare da shi tana kallon dokin da yake kallo wanda ake yi w
a ado irin na sarakuna.
“Yaushe ka dawo?”
“Jiya....”
Ya amsa mata a takaice duk kuwa da kasancewar yana a cikin yanayin da baya son magana, amman ba zai iya kin amsa ta ba, babu abunda Zainab zata bukata ya kasa mata, bayan girman da tai a kusa d
a shi ta bude ido, kusan ta fi shakuwa da shi fiye da kowa, tana jin maganarsa kamar yadda shi ma yake saurarenta yana girmamata a ciki har da sunan mahaifiyarsa da ta ci, wanda hakan yasa ake mata lakabi da Hajiya Karama, gashi tana da sirri idan ya fada
mata A babu mai ji sai idan shi ya umarce ta data fada, babu abunda za tai ba da saninsa ba, babu abunda take boye masa ita da shi abokai ne kuma shakikai.
“Wannan shi ne karo na biyu da ka sauka wani guri ba Masarautar nan ba, and i don't think hakan
zai mana dadi”
A hankali ya busar da iskar bakinsa ya zuba hannyensa aljihu yana cigaba da kallon dokin ta cikin gilashin falon ya ce.
“Abubuwan gidan nan basa min dadi”
“Yeah amman some time muna bukatar shawararka, ko bukatar wani abu kusan kai
ne Sarki a gidanan tun da Mai Martaba bashi da Lafiya, be kamata ace kana nisa da gida ba, and the way you act Ammy ba zata jidadi ba”
Murmushin gafen baki yai ya kalleta.
“Zan gyara Hajiya Karama”
“Good”
Ta fada with smile on her face, sanna
n ita ma ta saka hannunta aljihu tana wasa da dayar kafarta, shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi
“This time around ina son nai wani abun da zai bawa kowa mamaki as a photographer i want to do something differently like..... ”
Sai kuma ta kasa ka
rasawa ta ware hannayenta kamar mai tunanin abunda zata fada. Kallonta yai kadan ya dauke kai.
“Well i think ki shiga kauye, ki duba wata culture ko yare ki duba wasu addinai na wasu da suke wanda ya sha banban da wanda ake gani sai ki dauka”
Ta war
a idonta tana murmushin jindadi.
“Wow shiyasa bana son kai nisa da ni, a duk lokacin da na nemi shawara sai ka sama min mafita”
Murmushi yai mata kamin ya juyo da sauri jin muryar Muhseen.
“Wow wow wow..... Longest time Dude”
Tsakanin shi da
Muhseen aka rasa wanda ya fi wani sauri, a tsakiyar falon suka hadu suka rumgume junansu ko wanensu fuskarsa dauke da dariya da farincikin arba da dan'uwansa.
Nana ta taso da sauri ta rumgume Muhseen.
“Ya Muhseen oyoyo”
“Hey Little One”
Zainab
ma side hug tai masa tana welcoming dinsa, sai da ya kai wa Doc Yazeed hannu suka gaisa sannan ya zauna kusa da Zainab.
“Hajiya Karama how far?”
“Fine ya Abuja?”
“Kalau”
“Ina Aliyu and Mama Fulani?”
“Yana nan kalau Mama kuma tana kasa tare
da Mai Martaba”
Shattima ya karbi Labib dake bachi a hannun Doc Deen yana fadin.
“Doc me ke sa su yawan zaburar nan ne wai?”
“To Wallahi ba zan iya fada ba, adai rika yi ana hada musu da addu'a especially idan za su kwanta bachi ko idan sun farka
, and a daina barinsu a duhu ko barinsu su kadai”
Yana fadar hakan ya mike tsaye ya rufe akwatinsa yana musu sallama, sai Nana ta mike tsaye ta bi bayansa suka fita falon tare, yana saukowa stairs din ta ce.
“Doc yaushe zaka kai ni gurin wannan siste
r taka wace kace tana kama da ni”
Kallonta kawai yai ya dauke kai yana murmushi be ce mata komai ba har ya sauka ita kuma bata fasa tambayarsa tana masa magiya ba har ya isa gurin motarsa.
“You know what? Sometimes dabi'unku daya da Ya Shattima, sai
ku rika yi ma mutum wulakanci idan kun ga yana son abu”
Sai da ya bude motarsa ya saka akwatin sannan ya juyo ya kalleta daga sama har kasa, green lace ne jikinta kanta ba dankwali ta kulle gashin kanta, babu yan