Showing 27001 words to 30000 words out of 304903 words
rai driver ya fice da
ga dakin fuskarsa kamar zai fashe da kuka.
“Me kike son ki ci? I will cook for you”
Ammy ta tambaye ta cike da kulawa, sai Nana ta kawardar fuska ita aka dole har yanzu fushi take da Ammy.
“Bana son komai”
Ammy ta hade abu da karfi sannan ta m
ike tsaye ta nufi kofar fita sai kuma ta juyo ta kalleta fuskarta da mamaki.
“Amman ya akao kika fito ba lokacin tashi daga school ba? Ya akai suka bar ki kika fito? Yanzu fa karfe 11:40am how?”
Shattima ya kalleta.
“Ammy za mu yi wannan maganar
daga baya yanzu dai ta samu lafiya”
Ammy bata sake cewa komai ba ta juya ta fice. Sai a lokacin ne Waziri yai magana.
“An kori direban ko? To kin samu abunda kike so idan ma ke kika tsara haka saboda a kore shi burinki ya cika, amman bari na fada m
iki daga yau school bus ce zata rika kai ki makaranta tana dauko ki, ba ki wayar ki”
Ya mika mata hannunsa sai tai saurin kallon Shattima tana son saka kuka, kai ya gyada mata alamar ta ba shi din, sannan ta kai hannu ta bude school bag dinta ta dauko w
ayar ta mika masa tana hawaye. Shattima ya zauna kusa da ita kenan Waziri ya ce.
“Daga yau kar wanda ya sake daukar kudi ya bata ko ya siya mata waya, daga kai har Zainab shi ma Sirleem zan masa magana”
Da mamaki Zainab ta kalleshi sai dai babu dama
r tambayarsa dalilin hakan dan ta fi kowa sanin waye Waziri.
“Zainab je ki kira Baaba ta zo ta bincike dakin nan duk inda kudi suke ta fito min da su, kuma ta kwashe kayan kallon nan da system din nan bana son ganinsu a nan”
Ta amsa masa ta to, sai
da ta kalli Shattima sannan ta fice zuciyarta cike da tambayoyi. Waziri ya kalli Nana.
“Da kin ji sauki ke za ki fara gyara dakinki da kanki, ba za a sake miki ba, ko tufafin da ke saka miki a wardrobe daga yau ke zaki saka idan sun yi datti ki wanke d
a kanki”
Ta kankame Shattima tana fashewa da kuka.
“Wayyo Yaya mutuwa zan yi”
“Kin dade baki mutu ba”
Waziri ya daka mata tsawa yana matsowa kamar zai doke ta, da sauri Shattima ya mike tsaye ya tare ta.
“Ayi hakuri Baba zan mata magana”
Shi kan shi Shattima sai da Waziri ya watsa masa harara sannan ya fice daga dakin, wanda hakan yayi daidai da shigowar Baaba, a take ta hau aikinta sai da ta bincike dakin tsab ta fiddo kudi ba kanana ba har da dollars din da Nana take daukowa dakin Mai
Martaba ta fito falo ta kawowa Waziri sannan ta kira Sarkin Dogarai ya cire tv da decoder da system din dake dakin. Nana na ji na gani aka kwashe kayan aka bar mata daki wayan daga gadonta sai wardrobe da dan karamin dinning dinta na karatu domin har hotun
an artists da saka sai da Waziri ya saka aka cire su a lokacin da ya sake dawowa dakin dan ganin idan an yi yadda ya ce.
“Yaya Wallahi Baba Waziri da Ammy basa so na”
“Shiiiiiiiiii kar na sake jin wannan kwanta ki yi bachi idan kin tashi zan kira Doc
Deen ya duba ki Okay”
Ya daga masa kai sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin. Tai saman gadon ta fara kuka na gasken gaske tana jin kewar mhaifinta domin ta tabbatar da yana raye babu wanda ya isa ya mata haka har shi Baba Wazirin da kansa. Can kuma
ta fara murmushi mai sauti tunawa da yadda AA ya rude a lokacin da suka fadi din, sai a lokacin ta soma dariyar abunda ya faru tsakaninsu tun haduwar farko har zuwa yau.
FALMATA POV.
Cikin rashin jindadin ta isa gida tana jin ina ma ace tan
a da wata dama da zata hana kanta aiki a gidan da ta huta, domin abunda Zainab tai mata a yau be mata dadi ba ga Iya data saka ta gaba ga wahalar tafiya kasa kullum kuma ta dawo.
Sai dai babu yadda ta iya idan tace zata bar aikin ta san sakamakonta a guri
n Umma wacce tai ruwa da tsaki ta sama mata aikin saboda ta rika bata albashin. Kamin ta isa gidan sai da ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta su kai yar fira har ma ta kunan wakar Sirleem M2 a wayar Khadija ta kalli video wakar sannan ta wuce gida. Tana
isa bata ko tsaya hutawa ba, ta dauki bokitin diban ruwa ta nufi bohol daman diban ruwa ne abu na farko da take idan ta dawo daga aikin, sannan tai surfe.
Haka ta cika komai na gidan sannan ta zuba surfe ta surfe iya wanda zata iya ta wanke ta bawa dab
bobi kasarin, ita kuma ta debi ruwa tai wanka ta shirya cikin uniform dinta na islamiya wanda ya gama kodewa har ya fara yagewa a wani gurin ma. Ta dauki jakarta ta makaranta ta nufo dakin Iya.
“Umma makaranta zan je”
Iya ta hankada fillonta ta dauk
o naira talatin ta jefo mata.
“Kwadon da mu kai be ishemu ba, ga talatin nan ki siye awara ko dankali”
“To na gode”
Ta saka hannu biyu ta dauka sannan ta juyo ta fito daga dakinta idonta cike da kwalla. Idan zalinci da danne mata hakki ko kuma sa
kata aikin wahala ba yau Tumba ta saba ba, amman ta kasa sabawa a kullum idan akai mata sai ta yi kuka, cikin damuwa taje makarantar sai dai a yadda suke cikin ajin da dalibai ana wasa da dariya yasa ta waye kamar ba ita ba.
Kwalama ta siya da kudin a
lokacin da suka tashi daga makarantar, bata ci abincin kirki ba sai da dare da aka sauke tuwo. A yau ma sai da wani ya sallamo mata wani dabam ba na jiya ba, shi ma ya mata siyaya kuma ya bata kudi after ya kunna mata wakar Sirleem M2 ta kalla a wayarsa. Y
au kam kamin ta kwanta iya ta bata rubutun ta sha, hakan yasa da safe ba ta bata ba. Sai a kullum Falmata bata fashin bismillah idan zata sha addu'ar safe da yamma kuma ta zame mata jikin duk da karancin shekarunta.
Cikin tsoro da tunanin abunda akai m
ata a jiya ta shiga masarautar ga kuma tunanin haduwa da Iya. Sai dai har ta isa bakin kofar falon Ammy bata hadu da ita ba sai dai hakan be saka ta fidda ran haduwa da ita a dakin yaran ba ko a falon. Sai da ta karanta addu'ar neman tsari sannan ta danna
door bell din, ba dadewa Nana ta bude mata kofar sai ta tsaya kallonta.
“Me aka yi?”
Har kasa Falmata ta sirina ta gaishe ta sannan ta ce.
“Zan gyara dakin yan uku ne”
“To shigo”
Nana ta matsa daga jikin kofar tana dingishi ta koma a set d
in kujerun farko da suke falon ta zauna ta cigaba da cin plantain chips. Da sauri Falmata ta shiga dakin ga mamakin yau kam sai ta samu Luma a kan gadon jarirai ta mike tsaye tana ta ihu sai zabura take kamar ana tsikararta. Da sauri Falmata ta karasa inda
take tana kallonta.
“Laaaaaaaaaaa”
Ta fada tana kallonta cike da burgewa sai dai ganin yadda take zabura kamar mai tsoro yasa ta karanta ayatul kursiyu ta tofa mata a kai sannan tai bismilla ta kai hannu ta dauke ta tana mata wasa. Tana juyowa ta yi
arba da Shattima tsaye bakin kofar yana kallonta fuska a hade. A rude ta aje yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri tana girgiza masa kai alamar ita ba ta yi komai ba.
“Wallahi Wallahi.... Wallahi ganin nai tana kuka tana zabura shiyasa nai mata addu'a
kuma na dauke ta, Dan Allah kai hakuri na shiga uku”
Ta fashe da kuka ta duka har kasa tana rokonsa kamar ance mata dukanta zai yi. Be ce mata komai ba ya karaso cikin dakin ya dauki yarsa wacce ke faman kuka tun da Falmata ta maida ita cikin gadon, be
ce mata komai ba ya fice. Ita kuma bata fasa kuka tana nadamar abunda tai ba har ta yi aikin ta gama ta fito, ba karamin dadi ta ji ganin babu kowa a falon ta fice da sauri har lokacin hawaye take.
Sai da ta fito daga habarar Ammy sannan ta ji kamar a
na binta a baya, da sauri ta juya suna yin arba da Iya gabanta ya buga da karfi.
“Shattima ya ce a fada miki karki sake dawowa daga yau”
Kasa cewa komai Falmata tai Iya kuma ta juya ta koma ciki tana rumgume da hannayenta a baya. Babu wacce ta fado
mata a rai sai Tumba, ta san idan ta fada mata abunda tai aka kore ta zata kara mata da nata ne.
Sai dai ya zame mata dole ta fadi gaskiya dole ne ta fada mata gaskiya. A kullum idan zata je gida tana ganin tafiyar tana mata nisa amman ban da yau da tak
e cikin tashin hankali sai ta ga kamar an ragewa hanyar tsawo.
*
🐄🐄
FULANI
🐄🐄
*
By Khadeeja Candy
*7*
Dogon wando ne da da yellow t-shirt a jikinta, kanta ba dankwali gashin kanta na dunkule guri daya da ribbon, se kai tana ganinsa ka
san ya kwana biyu ba a taba shi ba. Tana tafe tana dingishi har ta shigo cikin falon, Rima na kallonta ta dauke kai ta cigaba da damna wayarta, hakan yasa Nana ta ja mata tsaki kamar ba yayarta ba. Ta kalli Juwairiya wacce ke tambayarta abunda ya same ta.
“Anty Jurry ima Hajiya?”
“Tana dakinta, Nana me ya same ki?”
“Hadari na yi”
“Garin ya?”
Nana ba ta ce mata komai ba ta nufi hanyar dakin Hajiya, bata ko yi knocked ba ta tura kofar dakin ta shiga tana kiran Hajiya wacce take ganin har ta fi
mata Ammy. Hajiya da ke makale da waya a kunne tana ganinta ta sauke wayar da sauri tana fadin.
“Subhanallahi Daughter me ya same ki?”
“Hadari na yi”
Nana ta fada kamar zata fashe da kuka, da sauri Hajiya ta mika mata hannu alamar ta karaso fusk
arta na nuna tsantsan damuwa. Nana ta karasa kusa da ita ta zauna bakin gadon sai Hajiya ta kwantar da ita jikinta.
“Garin ya hakan ya faru daughter?”
Irin karyar da tai ma su Ammy ita tai ma Hajiya.
“Amman an kore shi ko?”
“Yes Ya Shattima ya
kore shi”
“Da ba a sallame shi ba, da sai na saka an hukunta shi sannan na masa korar wulakanci”
Hajiya ta fada cikin bacin rai, wanda hakan ba karamin dadin yai ma Nana ba. Babu abunda ta rage bata fada mata ba akan abunda Baba Waziri yai mata jiya
har da hawayenta. Hajiya ta shafa kanta tana murmushi
“Haba daughter kar hakan ya dame ki, ba dai ina raye ba babu wanda ya isa ya taba ki, nan da kwana biyu zan maida miki duk wani abu da Waziri ya cire a dakinki, ni kaina ya min magana wai ni da Sir
leem mu daina ba ki kudi ko siya miki wani abu, amman kin san ba zan yi haka ba ko? Domin ni ina kaunarki sosai”
Nana ta rumgume ta.
“Na gode Hajiya, za ki rika ba ni kudi?”
“Sosai ma, duk lokacin da kike bukatar kudi ki zo ki min magana, amman f
ada min me kika masa?”
“Ni ban masa komai ba, ban san miyasa yai min haka ba daman can shi baya so na ai”
“Mu ai muna sonki, bari na kira Sirleem ya zo ya kai ki wata asibitin a duba ki”
“A a Ya Shattima ya Kora Doc Deen ya duba ni jiya”
Ta mik
e tsaye jin maganar asibiti, domin zuwa asibiti da allura sune manyan makiyanta a duniya. Hajiya ta mike tsaye ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko kudin da za su kai 20k ta juyo ta dawo kusa da Nana ta mika mata kudin.
“Karbi wannan ki siye wani ab
u”
Da sauri Nana ta saka hannu ta karba tana murmushi.
“Na gode”
Murmushi Hajiya tai mata a respond ita kuma ta saka kudin cikin aljihun wandonta ta juya tana dingishin ta fita daga dakin, Hajiya ta bita da kallo tana murmushi. Hakan da Hajiya ta
i mata ba karamin dadi yai mata ba, daman can ta san babu mai sonta sai Hajiya domin ta fi kowa sakar mata kudi ita da Hajiya Karama. Sai da ta fito daga bangaren Hajiya gaba daya sannan ta fiddo kudin ta karga 20k ne cif ta maida a inda ta saka dazun sann
an ta nufi hanyar da zata sadata da bangarensu.
“Imagine Muhseen ya tafi be min sallama ba”
Cewar Zainab tana mamakin tafiyarsa ba tare da saninta ba.
“Yana busy daman Mama Fulani kawai ya kawo, any problem?”
Shattima ya fada ba tare da ya
kalleta ba.
“No kawai na ji tafiyar ta sa a ba za ta ne, ita ma Mama Fulani ban ganta ba ai ko tare suka tafi?”
“Tana cikin garin gurin yan'uwa”
Ya bata amsar still be kalleta ba sai aikin taba System dinsa yake, ita kuma tana shafa wani mai a fu
skarta jikinta sanye da sleeping dress wando da riga. Suna haka Nana ta shigo falon ta nufo inda suke tun kamin ta zauna Zainab ta ce.
“Ammy na nemanki”
“Me nai?”
Zainab tai murmushi
“Sai kin yi wani abu Ammy zata nemeki? Haba Baby ta shiga da
kinki bata ganki ba na fada mata kin tafi bangaren Hajiya, tace idan kin dawo na turo ki”
Ta juya ba dan ranta ya so ba ta nufi dakin Ammy, a kasan carpet ta samu Ammy zaune rike sanye da hijab hannunta rike da carbi. Ta karasa ta sauna bakin gadon tana
turo baki tana kin kallon mahaifiyarta. Ammy ba ta bi ta kanta ba ta kalleta a natse ta ce
“Ya jikin na ki?”
“Da sauki”
“Na shiga dakinki ban same ki ba, Zainab tace kin je bangaren Hajiya Balki me kika je yi?”
“Naje na fada mata duk abunda Ba
ba Waziri yai min”
“Da kika fada mata sai ta miki maganin me?”
Turo baki tai ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sai da Ammy ta daka mata tsawa.
“Nana....! Ina magana zaki tashi ki fita?”
Ta juyo tana turo baki amman bata dawo ta zauna ba.
“
Daman ai na san ba so na kike ba, gidan nan daga Ya Shattima sai Hajiya Karama sai Hajiya Babba kadai ke so na, sai Mai Martaba....”
Mikewa tsaye Ammy tai ta karasa inda Nana take ta fisgeta iya karfinta ta jefar kasa sai da kanta ya bugi gadon dakin. A
take Nana ta bude baki ta fara ihu daman kukanta na kusa, da gudu Zainab da Shattima suka shigo dakin, Zainab ta nufe ta da sauri ta rika ta.
“Ban mata komai ba ta jefar da ni kasa”
Ta fada cikin kuka tun kan Zainab ta tambayeta.
“Okay tashi mu
je room dinki”
Da taimakon Zainab ta mike tsaye suka fice daga dakin. Shattima ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana karantar yanayinta.
“Ammy ki rika dagawa Nana kafa she is still young, ba isa tai irin wayon da kike so tai ba”
Ammy ta kalleshi.
“Wata yarinya kamar ta tana da hankali da tunani, wata yarinya kamarta ta san ciwon kanta, Nana ban isa na ce kar ki yi ba ta bi umarnina, ban isa na hana ta ba ta hanu, bata san komai ba sai a bata kudi ayi mata kaza, abunta ya fara yawa ace Nana idan t
a ga kudi sai ta saka hannu ta sata?”
“Nonono Nana ba zata taba haka ba In-Sha-Allah, Ammy ki daina mata wannan fatan, tana dauka ne saboda tana ganin a gidansu ne, kuma wannan halin da ta yi wayo zata daina”
Ammy bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuc
iya. Jin muryar Hajiya Babba yasa Shattima mikewa tsaye ya fito falo. Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa mishi da far'arta kamar ko yaushe tana kare masa kallo.
“Hajiya Zainab tana ciki?”
“Eh tana ciki”
Binsa tai da kallo sai da ya isa gurin sys
tem dinsa sannan ta dauke kai ta tura kofar dakin Ammy ta shiga. Daga bakin kofar dakin ta tsaya tana kallon Ammy.
“Hajiya Zainab kin kyauta kenan?”
Ammy ta mata kallon rashin fahimta.
“Me ya faru? Karaso mana kika tsaya daga bakin kofa”
“A a
bar ni a nan da ina da muhimmaci a gareki ai da kanki zaki aika min abunda ya samu Nana, ko ba komai Nana yata ce kuma surukata ina hakkin sani”
Surukata yafi komai yi ma Ammy za fi domin har ga Allah bata son hadin nan na Sirleem da Nana, sai dai babu
yadda ta iya tun da sai da aka tambayi Nana da kanta tace tana son shi sannan akai musu baiko. Murmushi karfin hali Ammy tai tana kokarin maida abun ba komai ba.
“Haba dai, dan
ɗ
an wannan sai ace sai an tashi hankalinki, garin shiritarta ne taje ta ji
ciwo kuma ba wani rauni ne sosai ba, kin dai san halin Nana da raki shi ne kawai”
“Uhmm ko da ace ba ni na haifi mijin da Nana zata aura ba, na ga dai nima uwa ce a cikin gidan nan, ko ciwon kai Nana take ya kamata a fada min, abunda kike yi sam ba yi
ba ne, yau idan