Showing 267001 words to 270000 words out of 304903 words
da ta rubuta babu wanda be gane ba, gurin dariya sai yai murmushi, labarinta ne tun daga kan mafarkin da take har zuwa haduwarta da Wasim da abubuwan da suka faru har zuwa kadeta da Shattima yai
da neman aurenta da Ra'ees yai komai sai da ta rubuta kadan ya rage littafi ya cika, samun kansa yai da dariya sosai a gurin da yake karanta karyar da yi ma su Bappa da kuma gurin da Wasim yake mata dabon maciji.
“Wow...”
Ya furta yana jinsa cikin ni
shadi marar misaltuwa, har ga Allah yana son Fadime ta dayan bangaren kuma yana jin dadin rabuwar da Wasim yai da ita. Ya wuni a asibiti har biyar na yamma sannan ya nufi gidansa, a nan ma sai ya rika tuna irin abubuwan da suka yi ta faruwa a lokacin da ya
kawo ta gidan.
“Ko miyasa ta zama shiru yanzu”
Ya tambayi kansa yana daura tawul.
‘Maybe saboda ta rabu da Wasim’
Wani bangare na zuciyarsa ya ba shi amsa, sai ya kai hannunsa ya tura kofa bandakinsa ya shiga ya tsaya gaban madubi yana kallo
n kansa.
“Yes no one can take my place, ke dai kin jin kewa yarinya amman ba rabuwar kauna ba, ai ke ba ki san so ba, yanzu dai za ki sani”
Ya fada with smiling yana kallon kyakkyawar kirar mazantakan da Allah yai masa. Ya shafa kansa yana murmushi
tunawa da lokacin da take cewa ina ruwanta da ko shi waye, and the time da ta rike masa kafa akan ba zai tafi ya barta a gidan Zainab ba, da kuma lokacin da take fada masa Jekadiya ta zaunar da ita a kasa.
“I like her”
Ya furta yana cire tawul din y
a aje muhallinsa, sannan ya sakarwa kansa shawa ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali. Bayan ya gama ya fito daure da tawul din ya shiga kicin cup ya dauko ya matsa lemun tsami a ciki ya saka kanwa ya zuba ruwa kadan a ciki ya sha.
Be bar gidan b
a sai da akai magariba, a masallacin da ke unguwar yai sallah magariba sannan ya karasa masarautar yai isha'i a can, daman tun shigowarsa dakin Ammy ya lura Fadime bata ciki sai ya sulale ya nufi dakin Nana, duk da ba shi da tabbacin tana ciki, tura kofar
dakin yai ya shiga, sai ya samu Fadime kwance a kasa gefen gadon Nana, tana ganinshi sai tai saurin tashi tana share hawaye. Karaso yai kusa da ita ta duka gabanta.
“Miyasa kika kwanta kasa”
“Gadon na Gimbiya ne ai, be kamata na hau ba”
Ta fada t
ana murza ido, kallon gadon yai sai kuma ya kalleta.
“No ke ma ai sarauniya ce karki sake zama kasa”
Ya zauna a gabanta yana kallon yadda bakinta ke motsawa.
“Kin ci abinci?”
Ta daga masa kai alamar eh.
“Me kika ci?”
“Shimkafa da kaza”
“Eyyy kaza dai?”
Shiru tai bata ce komai ba.
“Ni dai zaka saka a kai ni gida gobe?”
“Why gobe? Kin gaji da ni ne?”
“Ina son na ga Bappana da Inna...”
Ta fada idonta na cika da kwalla, sai yai murmushi.
“Duk wannan saboda Wasim ne ko?
”
Kamar yace bude baki yi kuka, sai kawai ta fashe da kuka. Ido ya sakar mata hakan nan kawai ya ji cewar ba zai iya rarrashinta ba, tun tana kuka a hankali har ta fara yi da karfi.
“Ba zaka ce na yi hakuri ba, ba za ka ce na yi shiru ba?”
Ya kal
leta yana kallon yadda kuka yana mata kyau.
“Kin min kyau da kike kukan nan”
Ta saka hannu ta dafe kirjinsa domin har ga Allah tana jin zafi a zuciyarta irin zafin da ba zata msaltashi a siffa ba balle har ta fadi yadda kirjinta yake mata. Mikewa ya
i tsaye ya isa guri tissue dake dakin Nana ya dauko box din gaba daya ya zo gabanta ya zauna ya cire tissue din ya kama kanta ya rike ya goge mata fuska ya gyara mata hancinta kamar wata yar yarinya.
“Tashi ki hau gado ki kwanta”
Ta make kafada alam
ar ba zata hau ba, sai ta kwanta a kasa. Mikewa yai tsaye ya dauko filo ya daga kanta dora mata kanta akan filon sannan ya janyo bedsheet din dake kan gadon ya lullube ta, haka nan kuma sai ya ji duk ya damu da rashin sakewarta kukan da tai sai ya dawo a r
ansa ya tsaya. Kwantowa yai kadan ya saita bakinsa saitin kunnenta ya soma karanta mata zuciyar kur'ane wato Yasin, cikin kira'a mai dadin saurararo da kwantar da hankali, lamo tai tana ta sauraren yadda zakin muryarsa ke ratsa kunnenta yana isarwa zuciuay
rta da sassan jikinta, can kuma ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. Be kai karshen ayar ba bachi mai dadi yai gaba da ita.
ZAINAB POV.
Sai da ta ci kukan ta koshi sannan ta fito ta baro dakin zuwa dakinta, sai kuma ta rasa abun da za tai
a dakin kamar wanda ta manta komai haka ta zama sai safa da marwa take a dakin tana tunanin abun da za ta yi. Sake fashewa tai da kuka, tana jin cewar mutuwa zata yi idan ta bar garin Yola, ta ya zata iya rayuwa garin da bata san kowa a can ba, kuma bata
saba ba, gashi ba su yarda da komai na zamani ba balle cigaba? How? Ji tai ita kan ba zata iya bin Wasim ba hakan yasa ta juya da sauri ta fice daga dakin zuwa dakin Iya da zimmar yi masa magana sai ta tararda dakin babu kowa a ciki sai ko matsan kayan Iya
. Juyowa tai ta fito ta koma dakinta ya shiga bathroom ta hada ma kanta ruwan wanka ta watsa a jikinta ta fito kamar wata marar lafiya, wardrobe dinta ta nufa ta dauko wani yadi marar nauyi ta saka bata shafa komai a jikinta ko turaren da take so a yau sai
ta ji bata bukatarsa abubuwa da yawa sun taru sun mata tsaye a rai, idan ta fara tunaninsu sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta. Tana cikin dakin ta ji sallamar Mai gadinta, ba karamin faduwa gabanta yai ba, domin a yanzu tsoron komai take ciki har da s
autin mutane. Haka nan dai ta unkura ta tashi ta fita cikin rashin kuzari, sai ta same shi tsaye jikin kofa yana matsar kwalla.
“Hajiya yanzu aka kirani daga kauye wai Mahaifiyata ta rasu”
Ya fada mata karyar da ya ke ta tsarawa tun dazun, bayan mah
aifiyarsa ta dade da rasuwa, kawai ya zabi yai haka ne domin ya tsorota da jin cewar mayu ne kuma ya zai iya tafiya ya bar hakkinsa ba. Zainab ta yi murmushin bakinciki domin ta san karya yake yayi hakan ne kawai saboda ya tsiratar da rayuwarsa.
“Ina z
uwa”
Ta fada sannan ta juya ta koma ciki, albashinsa na watan gaba daya ta dauko ta ba mika masa.
“Kana da gaskiya, dole ne zaka tsorata kuma ban ga laifinka ba na gode”
Ta fada masa haka a yayinda yake karbar kudin, shi kam godiya kawai yai ya f
ice daga falon, sai ta juya ta koma ciki ta dauko babbar jakarta ta dauki wasu tufafin ta zuba a ciki da kuma wadansu abubuwan da zata iya bukata, sannan ta dauko wata karamar jakar ta zuba tarkacenta ta fito rike da makullin gidan a hannunta, sauran tufaf
insa duk a ciki ta bar su sai da ita gurin motarta ta saka jakar sannan ta dawonta rufe ko'ina na gidan, sai kuma tai baya baya tana kallon gidan hawaye na sauko mata.
“Allah duk yadda ka tsara a gareni haka zai kasance, Allah ka min mafita ka yaye min
damuwata ka shiga cikin lamarina”
Ta saka hannunta ta share hwayenta sannan ta juya ta nufi gate ta bude ma kanta ta dawonta shiga motarta ta fita da ita sannan ta sake dawowa ta rufe gate din ta saka masa key, har ta juya sai kuma ta juyo ta kai hannu
ta taba gate din, sannan ta koma cikin motarta ta ja motar bata tsaya ko'ina ba sai gidansu kawarta Amina, duk da wani shiri suke irin sosai ba but ta san Amina mace ce mai amana kuma mai sanin ya kamata. Amina ta yi mamakin ganinta a irin wannan lokacin
da ake ta kira kiren sallah magariba. Bayan sun gaisa Zainab ta kama hannunta ta danka mata keys din motarta da na gidanta, Amina ta kalli keys din da mamaki sannan ta kalleta.
“Na meye?”
“Na motata ne da na gidana, na yarda ke shiyasa na baki ajiya
r wannan, kuma dan Allah a rika kula min da gidana”
“Miya faru?”
“Ba komai kawai zan bar garin nan ne, na wani lokaci ke kadai na yarda da ke a duk kawayena”
Amina ta mike tsaye tana kallon yadda hawaye ke saukowa a idon Zainab.
“Dan Allah ki
fada min idan wata matsala ce”
“Zan kira ki a waya anjima, na baki mana, idan kuma kika ga na dauki lokaci ban dawo ba ki siyar da komai ki min sadaka”
“Wannan wace irin magana ce Lafiya kike Zainab?”
“Lafiya kalau na ke Amina”
Ta fashe da kuka
, tare da saurin mikewa tsaye domin bata son mijinta ya dawo ya tararda ita a gidan.
“Amman zan fada wa Mai gidana, idan be aminta ba zan hannata fada miki a waya sai ki fadi wanda a hannatawa abun”
“Ba matsala na gode”
“Allah yai miki mafita y
a yaye miki ko miye a ranki”
“Amin sai wata rana”
Zainab ta fada cikin kuka sannan ta juya ta fice da sauri, daman ta cire akwatinta a wajen motar sai ta karasa ta ja shi zuwa gate Amina ta fito ta tsaya bakin kofar falonta tana kallon Zainab hawaye
na sauko mata. A Hotel Zainab ta kwana tun a dare ta siye ticket din zuwa Katsina, washe gari ta shirya ta nufi airport cikin shiga ta doguwar rigar atamfa da mask sai dan karamin mayafi da kwatinta sai yar karamar jakar hannunta.
Karfe goma daidai jir
ginsu ya daga zuwa Katsina, sai a lokacin ne ta ji wani irin kewa da tausayin kanta ya kara kamata.
<<<<<<<<
Da 9pm zan turo wani Inshallah, jiya ban samu na yi ba saboda ba nepa.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na
Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bah
aushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nas
u na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'in
a a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
61
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza
Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kamar wacan lafiyar da su kai da Fadime, haka ta sauka garin Katsina kai tsaye ta nufi tashar ta samu motar da zata kaita garin bayan ta yi jinga da direban, shi kuma ya fada mata ya san g
arin amman zai kaita bakin kofar garin ne kawai ya dawo, tace masa ta aminta. Sai ta shiga motar ita kadai, suka dauka zuwa garin. Tana cikin motar shiru sai kallon hanya take, a duk lokacin da tai yunkurin kuka sai ta kasa, sai dai abun ya shiga zuciyarta
ya zauna sosai ta yadda ko numfashi tai da karfi sai ta ji kirjinta yayi ciwo.
Kamar yadda ya fada nesa da kofar garin ya sauke ta daman tun a tasha ta biya shi kudinshi sai ta bude motar ta fita ta fara takawa da kafa tana tuna zuwansu na baya da Fadim
e, a lokacin da ta zo a boye kuma cikin rashin sani, tsabanin yanzu da ita kanta ta kawo kanta domin ta san zata gina rayuwarta a nan ne, garin da babu network babu tv babu mota balle wani abu na cigaban zamani. Tun kan ta karasa bakin kofar garin ta hango
Wasim tsaye yana jiran isowarta hakan na nufin ya san da zuwanta kenan ko kuma an sanar masa. Sai da ta kai daf da shi sannan ta tsaya ita da shi suna facing din juna, ta kasa ce masa komai shi ma haka sai karantar damuwarta yake zuciyarsa na cika da taus
ayinta. Can kuma sai ya sakar mata murmushi ya kai hannu ya karbi akwatinta ta juya ya fara tafiya sai ta daga kai tana kallon kofar garin kamin ta juya ta kalli hanyar da ta biyo tana tunawa da Yola. Sai kuma ta juyo ta ni bayan Wasim har suka isa gurin d
a farin dokinsa yake ya taimaka mata ta hau ya dora akwatinta a sama, shi kuma ya rike linzamin dokin a hannu dayan hannunsa yana tafiya a kasa, kallon garin take da mutanen cikinsa kamar yadda su ma suke kallonta ganin tufafin jikinta dabam kuma ta hau do
kin Wasim da kansa yana jan dokin. Tafiya su kai mai dan nisa sannan suka isa masarautar su Wasim, a nan ma shi ya taimaka mata ta sauko sannan yai gaba ta bi bayansa tana tafe tana kallon mutanen dake cikin masarautar da su ma kallonta suke suna saurin ka
war da ido saboda Wasim. Banbanci wacan tafiyar da wannan wacan ta yi ta ne a cikin tsoro da zullum tsabanin wannan da bata jin komai ko da ace tana zuwa kasheta za su yi ta riga ta goge komai a zuciyarta. Wata matar ce mai kama da hadiman masarautar tai s
aurin zuwa ta karbi jakar da Wasim yake roko ta Zainab, shi kuma ya nufi cikin masarautar sai ta biyo bayansa suka shiga har ciki. Abun da ba ta yi zato ba ta samu daga sarki wato tarba da murmushi ya kuma ware mata hannayensa alamar ta karaso gareshi. Sai
ta tsaya can bakin kofar fadar idonta ya cika da hawaye.
“Karaso gareni Yata...”
Sarkin ya fada da murmushi a fuskarsa, daman can babu wanda ya kai yan garin Garuk son yan'uwansu balle kuma Sarkin da ya san cewar Zainab jininsu ce, hannu ta saka a
share hawayenta sannan ta karasa inda yake ta rumgume shi kamar yadda ya bukata sai duk sauran yan fadar suka duka kasa suna kai mata gaisuwa, ko da ba mutanen kwarai ba ne at least ita dai tana da yan'uwa da za su iya karbarta a lokacin da duniya ta tsane
ta.
“Na gode”
Ta fadawa Wasim tana kallonsa, sai ya sakar mata murmushi da bukarsa da tunanin rabuwa da Fadime yasa ta zurma ta haifar masa da rama sosai. Shugaba da kansa ya nuna mata inda zata zauna a kujerar dake kusa da ta shi, sannan ya gabata
r musu da ita cikin farinciki duk da bata jin abun da yake fada sai dai tana kallon fuskarsa ta san farinciki yake. Bayan sarkin ya gama Wasim ya shiga yi masa magana da yarensu.
“Sai dai ita tana kan addini ne na dabam tsabanin wanda mu kai ba, ina fa
tar ba za a hanata ibadar ta ba”
“In har zata zabi dawowa gida cikin yan'uwa da dangin mahaifiyarta me zai hana ta watsar da komai ta rike na mu”
Wasim ya kalleta.
“Kina da ra'ayin barin addininki ne Zainab?”
“Har a bada, ba zan taba barin mus
ulunci ba, ko da kuwa hakan na nufin mutuwa ta ne”
Ya juya ya kalli Sarki yana mayar masa da amsa da yarensu sannan ya dora da.
“Be kamata a hana kowa yin abun da yake so ba, musamman mutane irina irinta wandanda su ka bar kasar nan su ka bar garin
nan su ka shiga duniya su ga cigaban da duniya ta samu, an cigaba an wuce wannan babin”
“Ba ma ra'ayin addininta”
“Idan har ba ku ra'ayin addininta hakan na nufi ba ku ra'ayinta, ni kuma zan iya daukarta mu bar garin nan, ba zai yiyu a kara mana wani
bakinciki ba ni da ita”
Ya fada da yarensu sannan ya kalli Zainab.
“Ta so muje”
Zainab ta mike tsaye ta bi bayan Wasim. Sai ya shiga da ita can cikin masarautar a inda mata da yaya suke da kuma dakuna gwanin sha'awa, daki daya ya ware mata a mat
sayin nata sannan ya kawo mata uku wadanda zasu rika yi mata hidima. Wannan furucin da Wasim yai ya saka ba su hana Zainab yin sallah ko saka kalar tufafin da take so ba, hakan kuma da take sai ya burge mutanen garin musamman ganin tufafinta na zamani ne g
ashi idan ta saka za su rufe mata jiki har kasa, sai dai su matse ta kasancewar duk tufafinta haka suke mata. Idan ta fito waje tana sallah wani lokacin sai su yi taro suna kallonta, alwalar da take ma kallonta suke suna ganin ta yi wani abu na dabam da ba
su saba gani ba, gashi bata jin yaren mutanen garin idan tana son magana da su sai ta sha wahala sosai, abinci ma bata