Showing 33001 words to 36000 words out of 255051 words
runtse ido, tabbas ta ji wannan kalamin can tsakar kanta kuma kamar a mafarki, koda ta farka a gadon asibiti ta ganta Abulle a gefanta tana sharar hawaye da surutan kada Allah Ya sa ta mutu ba ta ga yaran Aliyu da Muhibbat din ba. Ta kudurta wannan buri na
Abulle ba zai samu ba da yardar Allah, ta hakura da Aliyu koda sonsa zai zama ajalinta. Ta ba shi damar auren wacce duk yake so. Ita kam karatunta da yace ba ya so shi za ta koma yanzun. Bangaren iyaye sun dauka a karon kanta ta ce ba za ta koma makaranta
ba, ita da Aliyun ne ka
ɗ
ai suka san sirrin rashin komawarta. Duk don ya kuntata mata ya ce ba za ta koma ba.
Tana ji yayyunnata suka fita a dakin sakamakon sallamar su Amarya da sauran mutanen gidan.
***
Aliyu na tsaye a farfajiyar asibit
in, shigowarsa kenan. Ko kallonsa ba su yi ba, shi kuwa ya bisu da banzan kallo da harara, yana tafe yana tunanin me ya yi mata? Daki-daki ya tuno dukkan yanda aka yi.
_Yana tanga
ɗ
i ya kife saman kujera bacci ya yi awon gaba da shi bayan ya yi magagin
sa ya gama. Bai farka ba sai da sanyin asuba ya ratso falon. Cikin mamaki ya tashi gami da dafe kansa dake
ɗ
an sarawa. A hankali ya shiga tariyo abinda ya faru daki-daki, shi dai ya san sun siya kayan maye da abokansa. Anan motar abokinnasa suka sha banda
G Baba wanda ke tuƙi yana musu dariyar rashin hakurinsu na ƙarasawa gida. Duk cikinsu shi
ɗ
aya ne ya yi aure banda su da ke kokarin hada takardun Degree. Bai manta sadda suka kawo shi gida ba suka yi gaba, bai kuma yi kasa a gwuiwa ba wajen budurin da suka
yi da Muhibbat. Da hanzari ya mike ya nufi hanyar
ɗ
akinta, ba ta nan, ban
ɗ
aki ma haka. Ya fito da niyyar nufar nashi dakin ya hango mutum kwance a hanyar wurin dinning table. Jiki na rawa ya karasa, ba karamin kaduwa ya yi na ganin jini ba. Kai tsaye ya k
ira family doctor din su Muhibbat din da ma jama'ar gidan. Ba
ɓ
ata lokaci ya mishi bayanin halin da take ciki, sanin tana da ciki ya sanya shi bada umarnin kawo ta asibiti. A gigice ya fita da zummar kwankwasawa makwafcinsa, ya ci sa'a ya fito don zuwa Mas
allaci. Lurwan ya dubeshi._
_"Lafiya kuwa Aliyu? Meyafaru?"_
_"Muhibbat ba lafiya, taimaka ka kaimu asibiti nan kusa ne don Allah."_
_Ba tare da
ɓ
ata lokaci ba suka je asibitin aka kar
ɓ
eta suka wuce masallacin asibitin suka yi sallah, likit
a ya tabbatar da fitar cikinta._
"Sai kuma shikenan a dinga yi min kallon mai laifi? Mtsw"
Ya ƙarashe da tsaki don shi dai yasan da ace a hayyacinsa ne ba zai yi wannan gangancin ba. To tunda ta faru ta ƙare kuma shikenan. A ranar aka sallameta b
ayan an tabbatar babu wata matsala, Mama ta tattara diyarta suka koma gida. Ita kanta ta ji dadi da ta ji Muhibbat na batun a raba aurensu da Aliyun. Ranar da take jira kenan.
***
Da sallama ta shiga gidan, ta yiwa Hajiya sannu da zuwa, ko arziki
n kallo ba ta samu ba. Cikin sauri ta fice dakinsu, sai dai tana shiga ta ji an rufe kofar, da hanzari ta waiga. Hajiya ce tsaye da wayarta a hannu, ta ƙaraso tana dubanta.
"Zauna magana zamu yi." Ba musu ta zauna a ƙasa ta sadda kai.
"Banda Hi
lal, akwai wani da kike kulawa ne?"
Ta kalli uwar sai kuma ta sadda kai. Jin ba za ta yi magana ba yasa Hajiyar kara magana.
"Na tambayeki ba don ban riga da na sani ba, a'a, ina so ne da bakinki inji kin fada. Idan akwai ya sunansa? Kuma tun yau
she ku ke tare?"
Ta runtse ido tana mai jin ko'ina a jikinta na amsar kuwwar Aliyu, gwara kam a yi ta ta ƙare.
"Sunansa Aliyu."I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/RjJi0Rs2J9
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! A madadina da ƴan rof. Ina kara mika sakon gaisuwata ga Husna Yarbaiwa bisa rasuwar mijinta. Allah Ya mishi Rahma, Yasa aljanna
makomarsa. Allah Ya raya yaransu.
😭😭👏🏿
11)
Wani murmushi na bakin ciki da takaici Hajiya ta yi.
"Shi dai wanda ke karamaki ƙaimi wurin ganin kin bijiremana? Kin sa
ɓ
a umarninmu? Kin ci amanar mutumin da ya yi dakon jiranki? Kina cikin h
ayyacinki kuwa?"
Daga kalaman Hajiya ta fahimci cewa r bincike ta mata a wayar. Ta
ɗ
an tur
ɓ
une fuska yayinda idanunta suka cicciko da kwalla.
"Wallahi Hajiya ina son shi. Kuma shi nake son au..."
Buge bakin da Hajiyar ta mata ne ya dakatar d
a ita lokaci guda hawaye suka shiga kwaranyomata.
"Kin isa?! Har kin isa kin kai ki bude baki a gabana ki ce wanin Hilal kike so?! Innalillahi wa inna ilaihir ra'ajiun! Na shiga uku ni Rabi'atu! Ashe zan ga wannan rana? Ke Ramlatu, ba ki isa ba! Nace
ba ki isa ba don uwarki! Babu wanda zai hana aurennan! Wato kin raina mu? Kin raina mahaifinki! Uban wa ya ce ki ce kina son Hilal ki kuma amince da aurensa?!"
Hajiya ta ci gaba da fada, yi take tana ƙarawa ita kuwa Ramlat sai kuka, duk abinda Hajiya
r ke fadi ji take ba abinda zai sa ta fasa son Aliyu. Tashin hankalinta kawai
ɓ
acin ran Hajiyar, banda haka ba wani abu.
Hajiya ta gama fa
ɗ
an sai kuma ta hau nasiha da nunamata kuskuren yin nema cikin nema da kuma hanyar da ta dauko wanda ba zai
ɓ
il
le ba. Ita kam shiru kawai ta yi ba don tana aminta ba. Ba don kuma za ta sauya ra'ayi ba, asalima ji take kamar ana bude zuciyarta ana ƙaramata soyayyar Aliyunta.
"Kiyi hakuri Hajiya."
Ta fadi tana riko zaninta ganin ta mike a fusace za ta fice
kuma babu niyyar za ta ba ta wayar. Kallonta Hajiyar ta yi, ita ta haifi Ramlat don haka ta san kafiya da taurin kai irinnata zai yi wuya lokaci daya ta saduda. Wannan ka
ɗ
ai ya tashi hankalinta ganin cewa dagaske yanzun ba ta son Hilal, kuma dole ta auresh
i.
"Hakuri daya ki cire yaron daga ranki. Don waya zan ba ki amman sai kin kammala jarrabawa. Ba abinda zai sa a fasa aurenki da Hilal, don haka ki bar ma mafarkin hakan."
Daga nan ta sanya kai ta fice. Kukan Ramlat abu biyu ne, kwace wayarta da
kuma batun auren Hilal da Hajiyar ke jaddadamata duk kuwa da cewa ta san ba ta sonsa. Anan ta gane shirun ba zai mata amfani ba, kawaici da kauda kai ba zasu ƙareta da komai ba face tsananin bakin ciki da kuma nadama. Za ta cutar da kanta kamar yanda Aliyu
ya fa
ɗ
i muddin ba za ta fito fili ta nuna ta sauya ra'ayi ba.
Ranar baccinta ya kasance rabi da rabi, duk juyi Aliyu take tunani, sanin da ta yi baccinsa ragagge ne idan bai ji muryarta ba. Sai kusan Asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita.
***
Ranakun da suka biyo bayan su za ta ce ba mai dadi bane sam a wurinta don kuwa Hajiya ta sanyamata takunkumi akan waya. Ba tare da sanin cewa tun a satin da hakan ta faru ta hadu da Aliyu a gidan su Amrah ya kuma cika alƙawarin kawomata karamar waya
yanda za su dinga magana a
ɓ
oye ba tare da ta bari a gida an san tana da wayar ba. Nutsuwa da maida hankali ga jarrabawarsu ta Waec da ta yi har suka kammala ya sanya Hajiya ganin kamar ta fara mancewa da babin Aliyun.
Don ta Hilal suna hira a wayar
Hajiyar bai kuma damu da jin cewa an kwace wayarta ba. Haka kawai hankalinsa ya kwanta da hakan. Ganin lokacin suna cikin shirin jarrabawar Neco ya sanyashi dauke kafa daga gidansu sai dai ta wayar, shi
ɗ
in ma ba koyaushe ba dalilin yana dan jin nauyin Haj
iyar.
***
A gefen Aliyu har sannan Muhibbat ba ta dawo ba don kuwa sosai ta tayar da bore akan ta gama zama da Aliyun. Iyayenta ba wanda bai ba ta goyon baya ba, Abulle ce ta yi tsalle ta dire akan babu mai raba auren. Sai da Muhibbat ta yi wata
biyu cif a gida sannan Abulle ta taka har bangaren Justice da zummar maidata. Ta kuwa ce sai dai takardarta.
"Ke Hibbatu, kar fa kiga ina lalla
ɓ
aki don ina sonki, ba ki isa ki kashe sunnar ma'aiki ba. Aure abin wasa ne? Ko kin manta yanda kike kwana k
ina kuka akan son Zakina?"
Hawaye ta share tana kallon Abulle.
"Bana sonsa, yanzu bana kaunarsa, ba zan koma gidansa ba. Ki yi hakuri nidai kawai ya ban takardata."
Nan fa Abulle ta sanya kuka wai Maryama ta zuge
ɗ
iyarta. A karshe ta tara me
eting don ganawa da kowa. Anan ma Muhibbat ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ce ita kam ba za ta koma ba. Da yake Allah bai ƙaddara nisan zama tsakani ba, duk son Abulle da auren hakanan ta hakura aka rabasu. Kowa ya budi baki shaidar Muhibbat yake da hakuri, k
unya da kawaici. A ganin iyayen tunda har ta iya karya bille ta furta kalmar saki, akwai dalili babba wanda kuma aka bar shi a sirrinsu tunda ba ta ce uffan ba.
Sakin ya fiye mata duk da irin son da zuciyarta ke yiwa Aliyu, so wanda ta girma da shi kum
a ta raineshi. Sai dai an zo ga
ɓ
ar da ta hakura, ba kuma za ta iya ci gaba da tafiyar ba. A bangaren Aliyu sai da jikinsa ya yi sanyi amman kuma bai wani damu ba ko ba komai zai auri za
ɓ
insa kuma abar sonsa.
***
Jarrabawar NECO kadai ya ragewa su
Ramlat wanda tuni aka soma. Ta rame koyaushe ba ta da aiki sai kuka da tunani. Hankalinta ya gaza kwanciya, matsowar auren da irin shirin da ake yi ya fi komai
ɗ
agamata hankali. Zuwa lokacin Hajiya ta gama fahimtar har sannan ba son Hilal take ba, ba kuma
ta
ɓ
oyewa Anti Zulaihat da Rafee'ah ba. Aikuwa ranar da suka zo gidan suka tararmata.
"Kar ma ki fara wannan iskancin! Wallahi kika bari ya je kunnen Abba sai kin gane shayi ruwa ne. Ke ba abin kunya bane ba ma ace kin yaudari Hilal? Ya yi rayuwa
a ƙasar waje, ya ga wacce ta fi ki komai da komai bai sa ya ji zai sauya sheƙa ba, sai ke da amana ta miki ƙaranci ko?"
Ta turo baki gami da tsuke gira, kalaman Rafee'ah ba karamin zafi da suka suke yiwa zuciyarta ba. Kai tsaye ta ba ta amsa babu shak
kar komai.
"Ai ba ni na sanyawa zuciyata son Aliyu ba, Allah ne Ya ha
ɗ
amu. Kuma da yardarSa, shi zan aura. Hilal ni na kawoshi na ce ina so yanzu kuma nace bana so bana ra'ayinsa, yanda ba'a yiwa wani cikinku dole ba nima..."
Marin da Anti Zulaih
at ta watsamata ya sanya ta yin shiru da dafe kuncinta. Ta mance rabon da fuskarta ta ji mari, jin zafin zuciya da na marin na neman ha
ɗ
emata ya sa a haukace tana kuka ta ci gaba da magana murya a sama.
"Eh! Eh! Ba zan daina son Aliyu ba! Zan iya kash
e kaina muddin ku ka aurar da ni ga Hilal! Bana sonsa! Bana sonsa ko za'a yimin dole?"
Tana gama magana ta fice a guje daga dakin Hajiyar zuwa
ɗ
akinta ta rufe kofar gami da sanya muƙulli ta zube kasa tana kuka. Sa'arta guda Hajiyar na sashin Abba.
Zulaihat da Rafee'ah suka shiga kallon kallo tsakaninsu da tsananin mamaki da kuma sanyin jiki.
"Cab
ɗ
i! Akwai aiki!" Fadin Rafee'ah bayan ta farfa
ɗ
o daga suman zaunen da ta yi. Ita kuwa Zulaihat salati ta yi ta shiga safa da marwa a tsakar
ɗ
akin ka
fin ta tsaya ta dubi Rafee'ah mai fama da karamin ciki.
"Wallahi aikin asiri ne. Maza-maza Hajiya ta zo a san abin yi."
"Kamar kin shiga zuciyata wallahi. Ko waye shi kin san bai barta a banza. "
"Meke faruwa? Hayaniyar me ku ke yi?"
Kusan a razane suka juya, Abba ne a gaba sai Hajiya a gefensa. Shakka babu muryar Ramlat ce ta fiddosu.
"Bakomai Abba." Fadin Zulaihat cikin son kwantar da hankalin Uban nasu. Itama Hajiya shiru ta yi sanin abinda ke gudana, ranta na
ɓ
aci don har w
ani huci take fitarwa, tuni ta gane hayaniyar Ramlat ce, kuma ba akan komai ba sai akan Aliyu. Tana jin Abba na fada akan kar su ƙara.
"Ku mata ne, bai dace a dinga jin muryarku a
ɗ
age haka ba, bana so kar a kara."
Suka amsa da toh kafin ya fice
Hajiya ta dubesu kamar ta yi magana sai ta fasa ta bi bayansa.
Ita kuwa Ramlat sai da ta ci kuka mai isarta kafin ta fito, kusan hakan ya zamemata jiki, duk sadda abu ya
ɓ
ata ranta, ta fi kaunar ta kulle
ɗ
aki ta yi kuka har ta huce a karon kanta ka
fin ta fito. A falon ta iskesu gaba daya har Abba, a gefe ga Yaya Munir shima ya zo. Kusan ma a kanta suke tattaunawa, ta
ɗ
an ja burki ganin ba su ganta ba ta dan koma baya. Batun
furnitures ake yi sai kayan kicin da za'a damƙa ragamarsu a hannun Zulaihat.
"Komai na Ramlatu ina so ya zama na musamman, kamun kan yarinyar ya fi komai burgeni, ba ta biyewa samarin zamanin nan ba, ba kuma ta tarasu ba barkatai. Hakan ya fi komai kyau, kuma shi ya fi dacewa da dukkan wata
ɗ
iya mace da ta san ciwon kanta. All
ah Ya yi mata albarka da ku gaba daya."
Idan ka cire Yaya Munir da ya amsa fuska a sake, su Hajiya kam sun amsa cike da tausayin Abban wanda bai da masaniyar abinda
ɗ
iyarsa ke shukawa.
"Ni kaina Ramlat ta burgeni ta kuma shayar da ni mamaki Abba
. Allah Yasa ayi komai lafiya a gama. Ya basu zaman lafiya."
Aka amsa addu'ar Munir da Amin. Ta juya a hankali ta koma dakin, wani sabon kukan ta shiga yi. Ji take inama za ta iya ture dukkan komai ta mika zuciyarta ga Hilal, inama za ta iya wannan
kawaicin ta auri Hilal ko don wannan kyakkyawar shaidar Abba da Munir gareta ya bibiyi rayuwarta. Sai dai kuma daga sadda dare ya raba, duniya ta dauki shiru sai kukan karnuka, kunnuwanta suka shiga sauraron kalaman Aliyu masu tsumata da ƙaramata dukkanin
kwarin gwuiwa, daga sannan ta sanya ƙafa ta shure tunanin kalaman mahaifinnata da Yaya Munir. Ta ƙara rudewa susucewa akan Aliyu. Ta kuma kudurce da kara daukar mishi alkawarin yanda ya rabu da Muhibbat dominta, haka za ta rabu da Hilal ta aureshi.
Ta shagala iyakar shagala wurin fayyace mishi abinda ya wakana a yau da kuma irin tijarar da ta yi duk a kanss, ba zato ta ji an yaye bargon rufarta gaba daya. A gigice ta mike duk a zatonta A'isha ce, sai dai ganin Hajiya tsaye a kanta ya sanya cikinta
ɗ
urar ruwa. Kafin Hajiya ta ce komai sai da ta
ɗ
aga wayar ta ha
ɗ
a da jikin bango ai kuwa ya fadi anan ya tarwatse,Ramlat jiki na rawa ta bude baki da zummar magana ta dauketa da mari hagu da dama.
"Waya?! Wayar dare?!! Har wuyanki ya kai wannan kaurin?
Ramlatu wace irin jaraba ce wai! Wane irin jahilin so kike yiwa Aliyu? Anya ba asiri ya yi miki ba? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
"Waye shi? Meke faruwa?"
Ba Ramlat ba, hatta da Hajiyar sai da ta ji hantar cikinta ta ka
ɗ
a. Abba ne ke tam
bayar tsaye bakin ƙofa sanye da doguwar jallabiya, basu san adadin lokacin da yake a tsayen ba, sai dai ya ji komai. Ba wani abu da bai shiga kunnensa ba. Jikinsa har rawa, kallo
ɗ
aya za ka ga tsananin
ɓ
acin rai da mamaki shimfi
ɗ
e saman fuskarsa, yake ya ƙ
araso cikin dakin.
Ya ji sunan Aliyu a bakin Hajiya sai dai ya fi kaunar ya gasƙata don tsoro yake ya zamana kunnuwansa ne suka sami matsala. Ya dubi Hajiya ya kuma kai duba ga Ramlat kafin ya dubi wayar dake a tarwatse a ƙasa.
"Dare ya yi, ko mene
a bari zuwa safe." Abinda ya iya kokarin furtawa kenan kafin ya fice. Hajiya ta kwashi wayar da ta tarwatse ta dubi diyarta. Ramlat ta ka
ɗ
u da ganin hawaye a fuskar Mahaifiyarta, har ta fice ta ja kofar ba ta iya cewa uffan ba. Ta hada kai da gwuiwa ta sh
iga kuka, kuka iyakar ƙarfinta. Ba za su gane ba, ba kuma zasu fahimta ba, son Aliyu kawai take. So marar algus. Wannan daren ta rasa inda za ta sanya kanta,