Showing 21001 words to 24000 words out of 255051 words
/>
tum ne mai zuciyar nema da kuma son kyautata iyalinsa da daidai karfinsa. Yana aiki a ma'aikatar ilimi ta gwamnati. Mahaifiyar Aliyu ita ce matarsa ta biyu. Yana sonta da kuma tausayamata ganin ita kadai ce ya auro daga nesa.
Abulle ce ta dage Ju
stice ya mayar da Aliyu makarantar yaransa, wannan abu ba ƙaramin bakin jini ya janyo wa Aliyu wurin iyalan Justice ba idan ka cire Muhibbat da ke jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don dadi.
A hankali bayan sun tasa, ta tattara ta koma gidan Abull
e da zama itama kawai don ta dinga sanya Aliyu a idanunta. Ranar farko da ta soma ganinsa a makaranta yana shaye shaye da abokansa, ranar ta gigita. Za ta gudu ya kamata ya fallamata mari dama da hagu akan yanda ta gani ta binne a nan kar ta sake ta fadawa
wani ko wata a gida. Wannan ta sa ta kama bakin dole. Abin mamaki soyayyar da take mishi bata ragu ba sai ma tausayi da yake ba ta. Kewarta da yayyunta suka yi har ma da iyayenta ta sa Justice da kansa ya zo ya lalla
ɓ
a Abulle dakyar ya tafi da ita. Abulle
ta rantse kaf a jikokinta Aliyu da Muhibbat ne ƴan gaban goshinta.
Aliyu na aji na biyu a jami'a kowa ya fahimci mummunan
ɗ
abi'ar da ya fa
ɗ
a na shaye-shaye, karatun ma ba ya bar maida hankali, kullum yana daki yana bacci. Taro kuwa na family an yi aka
n Aliyu ya fi a kirga, Innarsa kan shiga daki ta yi kuka son ranta. Shi kadai namiji da Allah Ya bata sai kannensa mata uku, sai dai ya zamemata wani tambari wanda ake faƙewa da shi a ci mutuncinta. Mahaifinsa kuwa ya ce sam ba zai yarda ba sai dai yaronsa
ya koma gabansa. Wannan ne silar komawarsa gidansu.
Duk wannan bai sa Muhibbat ta fasa so da tausayin Aliyu ba, takan rufe kanta a daki ta ci kuka ta kuma bishi da kyakkyawar addu'a akan Allah Ya shiryeshi.
Rayuwa ta yiwa Aliyu zafi yakan ji k
amar ya yi hauka duk ranar da Babansa ya kulleshi a
ɗ
aka ya hanashi fita ko nan da can. Makaranta dama ba labarinta don tun ranar da aka rabashi da gidan Abulle ya zuciya ya ce ya fasa karatun gaba daya. Ranar da ya
ɓ
alle ya fice daga gidan, bai koma ba sa
i da ya yi mankas. A ranar Innarsa ta yanke jiki ta fadi. Tun daga wannan rana ba ta ƙara lafiya ba. Ciwon Innarsa ya sanyaya jikinsa kadan, duk da a ganinsa matar sam ba ta damu da shi ba hakan bai mantar da shi matsayinta wurinsa ba.
Bayan farfadow
arta ya daukar mata alkawarin ya dainawa, ba ta ce mishi uffan ba har ya fice. A hankali kuma ya dinga
ɓ
oye munanan halayyarsa, ya maida turare abin fesawarsa, ba ya taba yarda ya zauna na awanni da yan uwansa gudun kar a ga sauyawar le
ɓɓ
ansa adalilin shan
taba. Sai dai ya zama masifaffen karfi da yaji, ya daina ragawa duk wata mace da za ta gasawa Innarsa magana. Akwai ranar da ya kusan yiwa Amaryar babansa duka duk don ta zagi Inna a fakaice. Wannan ya fusata Baban ya ce ya bar mishi gidansa. Zuciya irin
ta Aliyu ya sanyashi ha
ɗ
a komai nasa ya koma gidan Abulle. Ba abinda ya boyemata har da karin gishiri, nan kuwa ta tara meeting ta gargadi kowa akan takurawa Aliyu da ake.
"Duk wanda ba zai bi shi da Addu'a ba kar ya zageshi ya kara bin duniya. Kai k
uma Abdussalamu ba ka isa ka rabashi da gidan ubansa ba. Ko yau yaro ya ga dama zai je. Don kunga an samu ya soma gyaruwa shikenan kuma sai ku kara sanyashi ya bi duniya? Ke kuma Amarya ki ci gaba, idan dai za ki ci gaba da gasawa Amina magana, yaron nan b
a zai fasa kir
ɓ
arki ba. Shashasha."
Nan yaran suka shiga ba ta hakuri gami da nunamata kuskuren Aliyu cikin sanyi. Aliyu ya ba Amarya hakuri aka ce ya ci gaba da zama anan gidan Abulle. Bayan watsewar surukan da jikoki, Abulle ta nemi shawarar ta yand
a za'a inganta rayuwar
yaron tunda ya ƙi boko. Nan take Justice ya kawo shawarar a dorashi kan kasuwanci. Ba musu kowa ya yi na'am. Justice da kansa ya dauki nauyin budewa Aliyu shago da komai. Nan kuwa Abulle ta yi ta sanyamasa albarka daga nan aka tattau
na batun auren yanmatan da suka isa aure a zuri'ar da zarar sun kammala Sakandire don a sannan suna ajin karshe. Budar bakin Abulle ta ce.
"Banda Muhibbat, na yi mata miji."
Kalamanta sai da yasa kirjin Justice bugawa, tsoransa kar ya zamana abin
da yake gudu ne zai afku. Duk yanda suka so jin waye mijin Muhibbat ta ƙi basu fuska. Asalima goronta ta hau tauna ta ce su mike su bata wuri ta sallame su. Jiki ba kwari dai Justice ya tafi.
Ita kuwa Abulle tun wani dare da ta kama Muhibbat na kallo
n hoton Aliyu tana kuka ta ci alwashin sai ta auramata shi. Ba ta bari ta ganta ba ta juya ta ci gaba da baccinta cike da farin ciki da tausayin yarinyar.
Cikin lu
ɗ
ufin Allah zaman kasuwa ya kar
ɓ
i Aliyu, dakyar yake ajiye wasu kudaden don shi da za'a
bar shi ya yi facaka zai fi son hakan. Bai fasa shaye-shayensa ba sai dai ya fi yi da dare wanda daga ya sha ya
ɗ
an yi tam
ɓ
elansa zai
ɓ
ige da bacci. Taba kuwa ko a kasuwa zuƙarta yake don zuwa lokacin bai dauketa abar tashin hankali ba. A wannan lokacin n
e kuma Inna ta tashi lafiya kalau, daga baccin rana ta gamu da ajalinta, ta rasu. Mutuwarta ta girgiza jama'ar gidan musamman kishiyoyinta wadanda suka cika da dana sanin zaman gaba da hassadar da suka yi da ita. Batun mijinta kuwa ba'a magana, Abdussalam
ya shiga tashin hankali marar misaltawa. A gefen Aliyu da yaran Innar mata suma ba'a magana.
"Ka ji tsoron Allah." Shi ne abinda Innar ta fi yawan fadamasa a kalamanta masu tsawo, sai a sannan ya san yana son mahaifiyarsa halinta na banzatar da lamur
ansa kawai ya tsana. Yan uwanta daga Gombe duk sun zo. Mutuwar Inna ya karawa Abulle da Muhibbat tausayi da son Aliyu.
Suna kammala Sakandire magabata suka yiwa Muhibbat caa akan ta fiddo da miji, ita kuwa ta kasa za
ɓ
en ko
ɗ
aya saboda Aliyu.
Ak
a yi sa'a koda Abulle ta tari Aliyu da zancen Muhibbat don jin ta bakinsa sai ta ga ya hau murmushi, nan take ya nuna ya amince don dama ya jima da sanin yarinyar na sonsa. A cewarsa
ko ba komai zai ƙara martaba a idon duniya kasancewar mahaifinta wani ne
kuma
ɗ
an uwan mahaifinsa.
Tashi
ɗ
aya kowa ya ce bai yarda da auren ba, Justice dai ya yi alkunya ya yi shiru, daidai da mahaifin Aliyu bai amince a ba Aliyu auren Muhibbat ba. Ita kuwa Abulle ta rantse ko bayan ranta aka ƙi aurawa Aliyu Muhibbat ba t
a yafewa yaranta ba. Kuma bakinta sai ya bi su, wannan ya tashi hankulansu, a dole suka amince.
Justice ya yi mamakin murnar da Muhibbat ta nuna. A gefe guda Mamarta Saudatu na cika da batsewa.
"Dama kina sonsa?" Ta riga Justice jefamata tambaya
, ta kara sunkuyar da kai tana murmushi kafin ta mike a guje ta nufi daki. Saudatu ta dubi Justice dake hamdala da alama abin ya mishi dadi.
"Kana nufin ka amince da auren yaron da ya fitini kowa a dangi da
ɗ
iyarka kamila?"
Yayi murmushi.
"
Allah Ke shiryawa, kuma Ya shirya Aliyu sai dai a ci gaba da yi mishi addu'a. Farin cikin Muhibbat ya fiyemin komai, fargabana kar ya kasance ba ta sonsa. Tunda har tana sonsa shikenan, Allah Ya tabbatar da alheri. Ba zan ƙi bin umarnin Mahaifiyata ba."
"Tab
ɗ
ijam!"
Abinda Mama ta furta kenan. Rigima sosai ta tayar akan lallai sai dai a fasa auren, karshe Justice ya zuciya ya fita harkarta, har yaji ta yi da ta gaji ta dawo
ɗ
akinta. Abulle ta rantse ba don darajar ta haifomata sanyin idaniyarta Mu
hibbat da sauran jikoki ba da sai ta saka an saketa. A dole ta dangana aka yi auren Aliyu da Muhibbat wanda alokacin ya yi nisa da son Ramlat.
Muhibbat ta sauke ajiyar zuciya, ta kara maimaita sunan Ramlat da mijinta yake yawan kiranta da shi a shim
fi
ɗ
a. Hannu ta sanya ta dauke hawayenta. Kauna da son Aliyu abu ne da ta fara tun ba ta mallaki hankalin kanta ba. Ba kuma ta jin za ta daina. Addu'a za ta dage da yi har Allah Ya fidda Ramlat daga ran mijinta. Ba ta santa ba ko a hoto, ta dai
santa a baki
n mijinta. Takan yi mamakin yanda Ramla ke aminta su yi waya da mijin aure har cikin dare. Ta rasa gane SON ZUCIYA ne ko kuwa a'a?
Fatanta Allah Ya karkato hankalinsa gareta su ci gaba da rayuwa kamar yanda suka fara a farko.
***
*DAWOWA
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
08)
_*Dawowa Labari*_
A kofar gidan Amrah
ɗ
an sahu ya ajiye Ramlat. Ta biyashi tana mai kama hannun Affan wanda duk ya
ɓ
ata kayansa da cakulet suka far
a knocking. Aka bude, harararta Amrah ta yi.
"Sai yanzu ko? Yinin kenan?"
Ramlat na dariya ta juya.
"Shikenan, bari mu juya daga nan." Da sauri ta kama hannunta ta maidota baya suna dariya.
"Ni ban ce ba, yi hakuri."
Suka shiga ciki s
uka zauna, nan take sanarmata sai da ta biya gidan Muhibbat.
"Allah Sarki Muhibbat, matarnan akwai kirki wallahi. Ba ruwanta, kinsan babu ranar da ba za ta turomin gaisuwar juma'a ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Ai wannan daban take cikin muta
ne ma. Allah dai Ya bamu ikon yin zumuncin mu ma."
Amrah ta amsa da Amin. Ramlat ta shiga waige-waige.
"Ke ina ƴata wai? Tun da kika ce min kun dawo ita nake son ganin yanda ta girma."
"Tana wurin Mama na kai mata yaye. Abinda ya ban mamaki ko c
iwon nono ban yi ba."
Ramlat ta dara.
"Kika sani ko wani cikin ya shiga? Tsarabar Lagos?"
"Allah Yasa. Ai nikam ina so wallahi."
Ba ta yi mamakin kalaman Aminiyarta ba don tun bayan aurenta sai da ta shekara biyar ba ta samu ciki ba sai
yanzun. Mijinta Ɗahiru ya ce ba ita babu planning sai ta yi biyu.
"Allah Ya kawo mai albarka toh. Nidai yanzu yunwa nake ji."
Miƙewa suka yi a tare zuwa kicin Amrah na fadin.
"Mutuminki
ɗ
an wake nayi niyyar yi kuwa, na ha
ɗ
a komai ki dora ruwa
idan ya tafasa ki yi sakin bari na yanka maha
ɗ
in."
"To da ban zo ba fa?"
Amrah ta yi dariya.
"Ai kuma tunda kin zo din magana ta kare. Yi hakuri ki taimaka ban jin dadin jikin."
Haka ta soma sakin
ɗ
an waken tana yi suna hira.
"Ni
kuwa ina Hilal?"
Tambayar Amrah ta tunasar da ita yanda suka yi a kwanakin baya, text ya yi mata akan ta sanyamishi rana da lokaci ya zo
su tattauna abu mai muhimmanci sai dai ba ta yi karambanin ba shi amsa ba, daga ranar kuma bai ƙara nemanta ba.
"Kamar ban kyauta masa ba, amma a wurina hakan ne daidai."
"Me kika yi mishi?" Jin abinda Amrah ta ce yasa ta fahimci zancen zucin ya fito fili, nan ta bata labarin yanda suka yi. Ajiye wuƙar hannunta ta yi ta juyo da mamaki ƙarara saman fuskart
a tana dubanta.
"Meyasa kike yiwa kanki irin wannan gangancin?"
Cikin rashin fahimta ta
ɗ
an dubeta.
"Wane gangancin kuma?"
Haushi da takaici ya kusan kashe Amrah anan tsaye.
"Tambaya kike Ramsy? Ko kin manta na tunamaki waye Hil
al? For all abinda ya faru bai sa ya juyamaki baya ba, bai kuma sa ya bar sonki ba, don me yanzu kin samu damar gyara laifukanki kike kokarin juyamasa baya? Allah Kike son yiwa butulci?"
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ba ta ce komai ba ta juya ta ci
gaba da sakin
ɗ
an wake, sanin hali na idan ta ga dama ba za ta ce uffan ba yasa Amrah itama ta ci gaba da aiki sai dai ta kumbura kiris ya rage ta fashe. Dama sun saba irin haka tun yarinta.
Ita kuwa sai da ta kammala ta wanke hannu ta jira ya dahu t
a kwashe ba ta ko tsaya tambayar inda filas yake ba ta dauko. Sai da za ta zuba ne Amrah ta dakatar da ita.
"Wannan na Daddy ne." Tana nufin mijinta, murmushi Ramlat ta yi don tasan ƙawarta ta shaƙa, ta fice daga kicin rike da plastic din da Amrah ta
yanka kayan cin dan waken. Sai da ta soyamusu manja sannan ta fito itama. A falon suna zaune sannan ne Ramlat ta dubeta a nutse.
"Tsaya don Allah ki saurareni."
Amrah ta dakatar da zuba
ɗ
an waken da take kokarin zubamusu bayan ta
ɗ
ibarwa Affan na
shi ya ja gefe. Harararta ta yi.
"Me kuma za ki cemin bayan kin maidani wata banza don kawai ina nunamaki abinda ya dace."
Hannunta ta riko tana dubanta.
"Kiyi hakuri, wallahi duk ba haka bane. Amrah yanzu ke a tunaninki da wane ido zan kall
i Hilal na ba shi dama a karo na biyu bayan ni ce ummul aba'isin duk wani abu da ya faru a baya? Ko kin manta ba da Hilal kadai zan zauna ba? Akwai matarsa kuma akwai danginsa da babu ranar da zan goge bakin fentin da na yiwa kaina a idanunsu? So kike na b
ar wa ƴaƴan da zan haifa da shi abin gori? Yanzun ma wadannan din da ya na ƙare? Kin fi kowa sanin abinda ya faru, kuma kin fi kowa sanina Amrah. Da ace zan iya auren Hilal, da tuni yanzun wani labarin ake banda wannan. Amma bakin alƙalami ya bushe, zan iy
a yin aure ga kowane mutum a doron ƙasa banda Hilal. To balle ma auren babu shi a gabana yanzu, na gwammace na zauna na kula da yarana. Hakan zai fiyemin komai dadi."
Tausayinta sosai ya kama Amrah, har ba ta san sadda hawaye ya zubomata ba, ita kanta
uwar gayyar sai jin
ɗ
uminsa ta yi saman kuncinta. Ta kuwa shiga yi ba kakkautawa.
"Na cuci rayuwata Amrah, na cutar da mutane da dama wanda har gobe ban bar dana saninsa ba. Amrah har gobe ina tunanin bakin cikina ne sanadin mutuwar Abbana duk kuwa
da irin rabuwa ta salama da amincin da muka yi. Ƴan uwana ba sa fahimtana, har gobe suna min kallon mai laifi a idanunsu. Ya zan yi ne wai?"
Nan fa suka shiga kukan har Affan wanda ganin Mominsa na kuka shima ya shiga yi. Dakyar suka rarrashi kansu sa
kamakon ƙarar da Affan yake da kuka yana rirriƙe Ramlat. Komai da komai ya shiga dawowa kwanyarta, daga lokacin da ta saki jiki suka soma gudanar da soyayya mai karfi tsakaninta da Aliyu, daga lokacin ne komai ya faro asali wanda har gobe ta kasa goge *BAƘ
IN FENTIn* a zuƙatan masoyanta.
***
*BAƘIN FENTI*
_*Komai yana da sila, komai da mafarinsa. Duk abinda bawa bai
ɗ
ora kan turba mai kyau da tsari ba, mafi yawan lokuta ƙarshensa nadama ne! Koda ace a haka kaddarar ta zo masa.*_
"Wai Rams
y me kike ne? Ki fito kina
ɓ
ata lokaci."
Muryar Amrah kenan sa'ilin da ta ke kokarin shigowa dakin. Zuwa yanzu ta kai matakin da ba ta jin za ta
ɓ
oyewa kowa a duniya sonta ga Aliyu. Wannan tasa ko bayan shigowar Amrah ba ta fasa amsa wayar a nutse ba
ba ta ko damu da kallo da murmushin Amrah ba.
"Kai wannan Hilal, shi ba ya jin kudinsa ko? Daga Malaysia mutum ya kira a yi ta wayar fin sa'i biyu? To nidai don Allah ya kyalemin ke ai daya, idan ba haka ba wallahi zamu yi lattin."
Ba ta da niyy
ar ba ta amsa, ta fahimci ba ta gane wanda suke wayar ba, ko ma ta ce ba ta sanshi ba.
Daga dayan gefen Aliyu wanda ke zaune a falon Muhibbat yayinda ita kuwa ke kicin tana shiryamusu abincin rana ya
ɗ
an hade fuska kamar tana kallonsa.
"Baby way
e Hilal? Baby ashe ban Kai darajar da har yanzu za ki iya sanar da mutane ni din kike so ba ba wani banza ba? Watanni goma da soyayyarmu wanda ya fi karfin na wadanda suka kwashe shekaru goma suna yi shine har yanzu ban samu kar
ɓ
uwa ba? Sai anjima."
Y
a katse wayar gaba daya yana fitar da huci. Fitowarta kenan daga kicin, ta ji dukkan abinda yake fadi, sai dai ta yi kamar ba ta ji ba. Ranta na ƙuna kamar koyaushe, ta ha
ɗ
iye kwallar dake barazanar tona abinda ke ranta. Ganin ya
ɗ
an kalleta ya kauda kai
ya ja tsaki ya sanya ta kakalo murmushi ta nufi inda yake zaune a darare.
"Yaya na kammala girkin."
Ya yi mata kallon sakara. Ta sauke kwayar idanunta, a duniya idan da abinda ta tsana