Showing 198001 words to 201000 words out of 255051 words
ba yana nan daram a ransa sai ma ƙaruwa da ya yi. Kowa ya yi Allah wadai da Hajiya Zeenatu, har da masu kuka.
Ranar dai har dare bai samu kansa ba sai dakyar. Hajiya Zeenatu ta kira
sai hakuri ya ba ta ya nunamata ana ta tambayarta da son ganinta.
"Ko na biyo hanya gobe na zo?"
Ya yi murmushin mugunta jin irin wannan wauta daga matar da ta kusa dosar shekara hamsin.
"Aa Hajjaju, ki yi zamanki, idan zan ƙara zuwa sai m
u dawo tare. Dawowar dindindin."
Wannan amsar ya ba ta sai ta
ɗ
an yi turus, a karshe dai ya yi mata dabara ta sake kafin su yi sallama.
Ƴ
an Maiduguri labari ya riskesu su ma sai murna. Hussein ya san zama bai gan shi ba, zaga dangi ya zamar masa
dole.
***
BAYAN SATI BIYU..
KANO
Ta fito daga motarta a farfajiyar asibitin Baba Dakta. Amrah aka yiwa aiki sakamakon fa
ɗ
uwar da ta yi a bandaki da ya jazamata naƙudar dole, cikinta bai jima da shiga wata na takwas ba, an ciromata Bab
y Boy. Yaron sai ka rantse ya shiga watansa tara cif sannan ya fito duniya. Ta zagaya
ɗ
ayan gefen ta
ɗ
auki kwandon abincin da ta kawomusu Da ka ganta za ka fahimci tana cike da farin ciki. Tun da ta ji labarin auren da Chairman zai yi na huce haushi take j
in ta kamar an mata albishir da gidan aljanna. Yanzun ta kara tabbatarwa babu abinda zai ƙara ha
ɗ
a ta da shi. Ta sha adonta cikin laffaya dark brown mai adon milk flowers a ƙarshensa. Fuskarta babu wani heavy make up, hoda kawai ta shafa sai man le
ɓ
e mai d
anƙo. Ga duk wanda ya ganta sai ya ƙara kalla, Allah Ya ba Ramlat ƙira mai kyau, sai ka rantse ba ta ta
ɓ
a haihuwar ko ƙwai ba ballantana
ɗ
an mutum. Da wannan takun ta ƙarasa cikin asibitin zuwa dakin da aka kwantar da Amrah. Ta murda kofar da sallama ta sh
iga.
Umman Amrah na zaune gefe tana kur
ɓ
ar ruwan shayi, ta karasa suka gaisa. Amrah na bacci. Ajiye kwandon ta yi ta ƙarasa ga gadon Babyn, murmushi kawai ta ke yi tana ƙaremishi kallo, duka-duka yau kwanansa hudu a duniya.
"Ki ciro shi mana Ramlat,
ke da
ɗ
anki."
Ta juyo tana dariya kadan.
"Um um, gwara ya yi baccinsa Umma. Ni gani ya yi yana juyewa zuwa kamannin Zaituna."
Umma ta yi murmushi.
"Gashinan dai, sai sauya kamanni ya ke."
Ta jinjina kai.
"Naga kin warware s
osai yanzu, ko don kin ji labarin auren Chairman ne?"
Umman ta karashe da dariya, itama dayake abinda ke ranta kenan sai ta sa dariyar.
"Umma bari kawai, sosai fa na ji dadin rabuwa da alaƙaƙai."
Dariya sosai ta ba Umma.
"Kai Ramlatu
ba ki da dama, wato alaƙaƙai? Ko ya suka ƙare da Kawunnaki?"
Ta
ɗ
an ta
ɓ
e baki. Chairman a farko cewa ya yi dole Kawu Bello ya biyashi kudaden da ya kashemusu, daga karshe dai ya yafemasa ya ce komai ya wuce.
"Yanzu ki ka zo?"
Muryar Amrah ta
katse su. Suka dube ta.
"Yanzu na zo, sannu ya jiki"
Amrah ta amsa tana kokarin mikewa zaune, cikin sauri Ramlat ta karasa ta taimaka mata. Ita ta yi mata rakiya bandaki ta yi fitsari da kuma brush sannan suka dawo. Umma kuwa ta gyara shimfidar
ta kwantar da ita.
Ramlat ba ta wani jima ba ta yi musu sallama ta fice zuwa wurin aikinta. Tana tafe tana tunani, idan har Hussein zai iya mance ta ko a whatsapp bai neme ta ba, ita kuwa meyasa ba za ta dangana ta hakura da shi ba? Ta gama saddaƙar
wa babu ita a ransa, ba ya ta tata. Don haka tana ji har zuciyarta ta hakura da soyayyarsa. Da gaskiyar Auta A'isha da ta ta
ɓ
a ce mata gani take kamar Hussein ya fi ƙarfinta, yanzun kuwa ta yarda kuma ta gasƙata. A hankali ta sa bayan hannu ta share kwalla
r da ta cika idanunta. Muddin zai fa
ɗ
omata a rai to fa sai ta ji kwalla.
Wayarta ta
ɗ
auki ƙara, ta kai duba. Baban Hanif, kamar yanda ta sanya sunansa, wani ne da ba su yi ko sati da ha
ɗ
uwa ba, ta kai yara shopping, a farko ya dauka tana da aure don haka
ya hakura, sai dai haduwarsu ta biyu a kofar gidan Hisham kasancewar shi gidansa a Badawa Layout yake, ya ganta. Ya san Hisham don haka bai ƙasa a gwuiwa ba ya faka motarsa ya sauko suka gaisa da Hisham, ta gaidashi ta shige cikin motarta. A bakin Hisham
ya ke jin cewar ba ta da aure, anan ya nunawa Hisham yana so. Hisham ya yi shiru a sannan, a karshe ya nunamasa ba ruwansa ya nemi soyayyarta. Da kansa ya yiwa Ramlat magana ta fito daga motarta, ta tsaya ta dan saurareshi. Ita kuwa ganin tunda har Hisham
bai hana ta kulashi ba, kuma aminin Hussein ne, to tana da tabbacin babu alamar Hussein na sonta. Wannan yasa ta dangana ta hakura ta ba Baban Hanif dama.
Sauke ajiyar zuciya ta yi ganinhar wayar ta katse ba ta
ɗ
aga ba. Ya ƙara kira ta
ɗ
aga. Bayan a
msa sallama ta ba shi uzurin tuƙi dole ya hakura.
***
"Shi kika tsayar kenan matsayin miji?"
Tambayar Baba Dakta ya sa gabanta ya fa
ɗ
i, kanta a ƙasa yayinda yake zaune saman darduma idanunsa sanye da gilashi yana duba wani littafi na addini. Ta
ha
ɗ
iyi miyau, ta hakura yanzun za ta auri Baban Hanif. Ko ba komai ta yaba da hankali da nutsuwarsa. Hatta da Hajiya wannan karon da ma yan uwanta kansu, hankalin ya kwanta da shi.
"Eh Baba."
"Ramlat, kamar yanda ki ka amince da aurensa, bana s
on jin wata magana ta
ɓ
ullo daga baya."
A hankali hawayenta ya zubo, ba wanda ya fadomata a rai sai Aliyu da kuma yanda aka yi gumurzu a lokacin bikinsu. Abbanta ta tuna wanda a yanzun ta ke kallon Baba Dakta kamar shi. Basu da hadi sai zumunci tun s
hekara da shekaru da ya kasance Baba Dakta har yana da karfin ikon yanke hukunci a kan iyalin Abbansu, kuma ta zauna.
"Na ba ki nan da kwanaki uku, ki yi tunani dakyau, idan har kin amince ki zo ki sanar da ni. Zan ba shi damar ya turo magabatansa.
Allah Ya za
ɓ
amaki abinda ya fi alheri."
Ta kasa amsawa a fili sai a zuci, jiki a sanyaye ta mike ta mishi sai da safe ta kama hanyar gida. Kiran kenan daman, koda ta isa gida ba ta
ɓ
oyewa Hajiya komai ba. Hajiya ta yi murmushi.
"Yaron ya san abi
nda ya ke yi da alama, kuma ko ba komai
ɗ
an babban gida ne tunda Kakansa ma abokin Kakanki ne, wato Mahaifina. Zuri'ar Imam Shu'aibu Lawwali bani da shakku a kansu da yardar Allah. Kuma ke a dadinki ma tunda ba gida daya zai ha
ɗ
aku ba da matarsa."
Ram
lat ta yi shiru jikinta a sanyaye kawai tana sauraron Hajiya. Ta daure ta yi murmushin da bai kai zuci ba. Tana ji a ranta ko mutuwa za ta yi, wannan karon ba za ta ba iyayenta kunya ba. An yi ta kuma an ƙare.
A wannan yanayin Munir ya shigo gidan a
fusace, suka dube shi. Oyoyon da su Affan ke mishi bai amsa ba. Bayan zamansa Hajiya ta dubeshi bayan amsa gaisuwarsa.
"Lafiya kake kuwa?"
Ya yi kwafa.
"Hajiya, wallahi Bilkisu ta haukace. Ba ta da hankali. Akan zama a gaban mota ta kama Hun
ainah da duka."
"Da cikin?!" Fadin Hajiya da Ramlat har suna hada baki.
"Na gaji! Wallahi na gaji da wannan rigimar ta Bilkisu. Haka kwanaki ta kawo wannan ƴar iskar ƙanwarta Salma, yan iskan samarinta na zuwa tafiya da ita night club ni kuwa na
kora ta gidansu ba zan iya ba."
"Kai ba wannan ba, ka ce ta daki yarinya, yanzu ya ake ciki?"
Munir da har lokacin bai huce ba yana aikin karka
ɗ
a mukullin hannunsa, ya dubi Hajiya.
"Ba ta yi mata rauni ba, ni ne dai na raunata Bilkisun, kum
a na kora ta gidansu na sake ta."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kana da hankali kuwa? Yanzu kai ba za ka iya hakurin zama da mace ba? Haba Muniru! Ai idan rai ya
ɓ
aci, hankali ke dawo da shi."
Ya saki baki don mamaki, duk irin cin kashin
da Bilkisu ke yi amma ana kiran meyasa ya sake ta? Hajiya sosai ta yi fa
ɗ
a ta ce ta ba shi nan da gobe ya maida aurensa da Bilkisu kafin ransa ya
ɓ
aci. Ganin bai samu goyon baya ba haka ya tattara ya fice sai gidan Baba Dakta. Nan ma dai duk kanwar ja ce,
sai dai
ɗ
an saukin da ya samu jin cewar Baba Daktan zai kira Kawu Jamilu su je gidan tare a washegari.
***
Kwanaki ukun da Baba Dakta ya ba Ramlat na cika, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ƙara kiranta don jin ta bakinta. Kai tsaye cikin fawwalawa Ubangi
ji lamarinta ta ba shi damar yi mata za
ɓ
i a wannan karon.
"Idan har shi ka za
ɓ
armin Baba, na amince zan zauna da shi kuma ba zan ba ku kunya ba."
Baba Dakta sosai ya ji dadin batunta, ya sa mata albarka karshe ya ce duk abinda ya yanke daga baya
za ta ji. Da wannan suka ajiye maganar.
"Kar ki yi gaggawar amincewa da Baban Hanif." Amrah ta furta bayan Ramlat fitar Umma daga dakin kasancewar ta dawo gida an sallame su. Ramlat da ta ƙurawa Zayyan idanu, yaron Amrah, ta yi murmushi.
"B
a zan yi ba in sha Allah. Watakila shi ne alherina, na dai bar wa Allah za
ɓ
i, duk abinda Baba ya yanke kaina shi ne daidai. Idan ya amince da aurena da Baban Hanif shikenan."
"Ba ki tunanin Hussein kan iya dawowa watarana?"
Ta hadiyi miyau a koka
rinta na danne damuwarta.
"Koda ya dawo mene ne ha
ɗ
ina da shi? An fa
ɗ
amaki kalmar so ta ta
ɓ
a shiga tsakaninmu?"
Amrah ta sauke ajiyar zuciya, ta sani da gaskiyar Ramlat. Hussein bai furta yana sonta ba, kuma ko a waya ba ya nemanta.
"Amma s
ai naga kamar yana sonki."
Ta girgiza kai.
"Tunaninki kenan, yanzu dai a bar zancen ba shi da wani amfani."
"Ai shikenan. Allah Ya yi maki za
ɓ
i na alheri."
Daga haka Amrah ba ta kara tada zancen ba.
***
BAYAN KWANAKI UKU...
BAZATA.....
Tana kwance a saman doguwar kujera tana karatun wani littafin hausa mai suna KE ALHERI CE a wattpad, dariyar Nene ta ke yi sosai har
ɗ
ankwalinta na zamewa. Tana sanye cikin riga da siket ƴan kanti da ya yi mata kyau. Ummi da su Ansar sun
a farfajiyar gidan su na wasa, sai ji ta yi su na ihun oyoyo Uncle. Ta yi ƙasaƙe tana sauraro can kuma ta yi murmushi don jikinta ya ba ta idam ba Hisham ba toh Hilal. Mikewa zaune ta yi ta gyara zaman
ɗ
an kwalin kanta, ta mike gaba daya da zummar
ɗ
auko ma
yafi, sai dai sallamar wanda ta ji ya katse dukkan yunƙurinta.
"Wane ne ya zo ne nake jin...Au, Husseini?"
Hajiya dake fitowa daga daki bayan idar da sallah ta ke tambayar, ganin wanda ke tsaye bakin ƙofar suna kallon kallo da Ramlat yasa ta kat
ae tambayar. Ramlat da sauri ta fada daki don
ɗ
auko hijabi, shi kuaa ajiyar zuciya ya sauke ya ƙaraso ya durkusa yana gaida Hajiya da bakinta ya ƙi rufuwa. Gaba daya ya sauya sai ka ce wanda ya fita ƙasar waje, ya ƙara kyau da ƙiba abinsa.
"Dama za k
a dawo
ɗ
annan? Ni na
ɗ
auka kuma sai dai mu bi bayanka da kayanka. Nan abokinnaka shima ya zo ya gama jajensa."
Dariya ta ba shi.
"Ayi hakuri Hajiya, na yi laifi ko a waya ban sanar maku batun zuwana ba."
"Ba komai ai."
Nan kuma aka sh
iga hirar yaushe gamo, Hajiya ta aiki Ummi kiran Maminta don kawo ruwa. Ta fito cikin dakin ba ta ko kalli inda yake ba ta shige kicin. Hussein yana nazarinta a hankali. Har ta kawo ruwa ta ajiye da murya ƙasa-ƙasa ya ce.
"Kin fi koyaushe kyau."
Ta
ɗ
an dubeshi, ya watsamata lumsassun idanunsa yana murmushi. Ta kauda kai kirjinta na bugu da sauri-sauri. Zubamishi ta shiga yi a kofi hannu na rawa. Koda ta miƙa maimakon ya kar
ɓ
a sai ya
ɓ
ige da tambayar Hajiya.
"Na yi zaton zan tarar an yi bikin
Ramlat."
Ta dube shi ranta na zafi, wato dai yana kara tabbatar mata babu ita a shafin rayuwarsa. Ta mike ta nufi daki sadda Hajiya ta soma ba shi labarin yanda ta kaya da Chairman.
Bai katse ta ba har ta kammala.
"Allah Ya kyauta." Shi ne
kadai abinda ya furta. Daga bisani ya sanyo wata hirar daban inda a karshe ya kira Dada a waya video call ya ha
ɗ
a su suka gaisa, Dada godiya ta shiga yi sosai da sanyawa Ramlat albarka. A karshe ta nemi gaisawa da Ramlatun, Ummi ta kar
ɓ
i wayar ta shige da
kin a guje ta kai wa Ramlat da ke kwance saman gado.
"Mami, ga Dada."
Tana shirin magana sai ganin fuskar Dada ta yi saurin mikewa zaune ta maudo fara'arta. Suka gaisa har ta ba Hafsat ma suka gaisa. Godiya kam ta sha shi, tuni Ummi ta fice daga
dakin. Daga bisani suka yi sallama ta katse kiran, dama a wayar Hafsat ne. Hankalinta ya kai ga hotonsa dake saman screen din, ya rungume throw pillow guda a kirjinsa yana kwantar da kai yana murmushi. Sai take ganin kamar ita ya ke yiwa murmushin hakan y
asa ta yi saurin jan guntun tsaki gami da hararar wayar kadan kafin ta cillar da zummar sai Ummi ta shigo ta maida mishi.
Kwanciya ta yi har sai da ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta. Ta jawo ta duba, lambar da ba ta sani ba. Ta bude.
_*"Wayart
awa itama raba ni da ita kike son yi yanda ki ka yimin iyaka da HEART?"*_
I just published "BABI NA HAMSIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1013598891?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=sh
are_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=1t7u8q%2B2i2CmVekKWI5wFx%2BLsRJJivM5TtUSxqfucEgX0H3IsSDvgfmbOaj%2FRM2R1oO3SAwAvV7%2FIJ95dbqOXcbxCoIbZ9MIciCSdP0fW4VijXfBR0gyHI42Cn5Za4Rc
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*R
ufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
54)
Ranta idan ya yi dubu to ya
ɓ
aci, takaici ya sa ta wurgi da wayar gami da hararar wayarsa da ke ajiye ta ja tsaki. Ta rasa gane me Hussein ya ke nufi da ita, ba ta san wane matsayi ya aj
iye ta ba. Ta cije lebbanta tana karka
ɗ
a ƙafa daidai sadda Ummi ta fa
ɗ
o
ɗ
akin a guje.
"Mami, wai inji Uncle.."
Ba ta bari ta ƙarasa ba ta yi saurin yi mata nuni da wayar.
"Maza dauka ga ta can ki miƙa masa."
Ummi wacce ba shi ya aiko t
a ba, ta girgiza kai sai dai ba ta fasa
ɗ
aukar wayar ba kazalika ta ci gaba da zancenta.
"Wai ki zo zai tafi."
Harara ta watsawa Ummin.
"Ki ce ba ki ganni ba."
Ummi ta bude baki.
"Mami kin fa hana mu.."
"Kika karasa sai na bu
ge bakinki. Naji ba zan zo ba wuce ki ban wuri."
Rai ba dadi Ummin ta fice, Ramlat ta sauke ajiyar zuciya. Kwanciya ta yi sai dai karatun littafin da ta ke yi ma ya fice a ranta. Ba zato ta ji muryar Hajiya.
"Ramlatu yaushe ki ka sauya? Baƙo ya z
o domin ya gaishemu shi ne za ki aikamasa mugun kalamai? Me kike nufi da ba za ki je ba? Wani abun ya ha
ɗ
a ku ban sani ba?"
Jikinta sai ya yi sanyi, Hajiya ta ba ta umarmin fita, a dole ta mike tana ba ta hakuri sannan ta gyara zaman hijabin ta fice r
anta na tururi.
Ba kowa falon sai wata ƙatywar leda a gefe, don haka ta tsaya gami da juyowa da zummar komawa ciki, suka yi kici
ɓ
us da Hajiya. Harararta ta yi.
"Ki je yana waje tare da yara. Tsaraba ya kawomusu. Ki mishi godiya don Dadarsa ta ai
komin fura da nono."
"Toh." Ta amsa a ciki-ciki tamkar ba ta so sannan ta fice, ita dai Hajiya bin bayanta da kallo ta yi da mamakin wannan sauyi a fuska da gangar jikinta.
***
Yana zaune a mazaunin direba ƙafarsa
ɗ
aya a waje, alewa ce a hannun
sa yana kokarin
ɓ
arewa Affan. Ta kauda kai daga kallonsa ganin ya
ɗ
ago nashi kan, kallonta yake da murmushi a saman fuskarsa. Sai kuma ya miƙawa Affan alawar ya dube su.
"Oya ku shiga ciki."
Dama haka suke jira musamman Ummi da ke rike da ƙatuwa
r ledar kayan kwalam da ya damƙa mata su je su sha. Ba ta son hararar da uwar ke watsomata wannan ta sa ita ce farkon sheƙawa a guje sauran ma suka mara mata baya.
Ta rasa dalilinsa na korar yaran don haka ta ja numfashi ta furzar. Cikin dakiya ta du
beshi kirjinta na bugu da sauri-sauri.
"Hajiya ta ce na kara miƙa mata godiya. Allah Ya saka da alheri. Mun gode sosai