Showing 153001 words to 156000 words out of 255051 words
hakan ce kuwa, yana tsaye ya sha wata narkakkiyar shadda da
aka yi mishi aiki a jiki. Ƙaton tumbinsa shi za ka soma haskowa kafin ma ka kai ga ganin komai.
"Mtsw." Ta ja guntun tsaki tana jin kamar ta juya, dolenta ta daure ta ƙarasa. Ganinta ke da wuya, ya ƙara daidaita tsayuwarsa yana mai ƙuramata idanu ga
wani haƙoransa da suka bayyana shi a dole murmushin ƙauna ya ke.
"Ranki ya da
ɗ
e Ramlatu."
"Ina wuni."
Ta gaidashi ciki-ciki.
"Lafiya kalau Hajjaju. Wato sai kika ganni kwatsam. Wallahi kasa hakurin na soma kiranki nayi saboda jina nak
e kamar na shi
ɗ
e jiya tsabar tunaninki da ya.."
"Ina mai neman alfarmar ka tafi kai tsaye ga abinda ya kawoka, komai nawa nakan ba lokaci muhimmanci. Da ace dai ka sanar da ni zuwannaka tun wuri zan fi samun sukunin tsakurar maka mintoci ka
ɗ
an daga lo
kutan da nake sa shi. Yanzu dai akwai abinda nake yi ka katsemin hanzari. Amma bari na ƙara fa
ɗ
amaka haƙiƙanin abinda ke zuciyata dangane da kai. Inaga hakan zai taimaka wajen ganin ba mu shiga haƙƙin juna ba."
Chairman Dikko wanda ya zubamata idanu k
amar ya ha
ɗ
iyeta tsabar so, ya jinjina kai gami da gyara tsayuwa.
"Na ji abinda kika ce, ko daga yanda kika tarbeni nasan me kike nufi, kar ki manta kin fa
ɗ
amin ai tun kafin na tako nan. Amma Hajiya Ramlatu, duk wasu bayananki ba zai sa ni Dikko na ha
ƙ
ura da ke ba, ina sonki, wani irin so da rabona da shi tun a kan Mairo uwargidata. Don haka zan jure dukkan ƙiyayya, na rantsemaki da Allah kika shigo gidana ba za ki ƙara marmarin fita ba saboda da
ɗ
in da zan jiyar da ke. Ga kuma madarar ƙauna."
Ya ƙ
arashe da wata shaƙiyiyar dariya. Ta bishi da kallon tsana, ta sauke idanunta kirjinta na ƙara zafi. Kasa cewa komai ta yi har ya kammala sumbatunsa, karshe ta dubeshi.
"Dare ya fara, na kuma gaji da tsayuwar."
Ya sauke ajiyar zuciya gami da duba
n agogo.
"Wallahi ban san lokaci ya ja har haka ba, amma nidai don Allah ki ƙara dubawa tunda dai su Kawu sun riga da sun ba ni ke. Kinga kuwa babu abinda zai hana aurenmu, ki sanyawa ranki salama ki yi tunanin alherikan da ke jiranki a gidana."
Ta ƙara
ɗ
aure fuska, ba ta bari sun yi doguwar sallama ba ta juya ta nufi ciki. Ba jimawa da shigarta sai ga Baba Mai gadi da ledoji har uku shaƙe da kaya, da sauri ta kar
ɓ
a da zummar maida mishi, babu shi babu motarsa.
"Ai ina ce miki ya wuce, ba ki
ji ba."
Fa
ɗ
in Baba Maigadi, cike da takaici ta dubeshi.
"Don Allah Baba kar ka kara amsar saƙon wannan mutumin."
Baba ya
ɗ
an yi shiru, ita kanta Ramlat din sai ta ga rashin kyautatawa tunda dai Baba Maigadi ba ruwansa da alaƙarsu. Juyawa ta
yi ta koma ciki.
"Wai ke wannan kumburin da kike yi, ba fa wanda ya matsa akan sai kim aureshi."
Hajiya ta furta tana dubanta. Ramlat da tuni idanunta sun cicciko da kwalla ta amsa.
"Ni Hajiya abinda ke tayarmin da hankali, bai wuce yanda
Kawu ya yi saurin aminta da shi ba. Fisabilillah babu bincike babu komai? Ni nasan waye Chairman, ba abinda suka sani a kansa."
"Ke wa ya fa
ɗ
amaki ana dogon bincike akan mai muƙami ko dukiya? Hum, Ramlatu a zamaninnan ba'a wannan. Bar ganin Yayyuna ne
, amma na fi ki sanin halinsu. Ke dai ki dage da addu'a, muddin kuma kina son ki shafe maganarsa toh wallahi ki watsar da komai ki fiddo mijin aure. Shi ne kwanciyar hankalinki da namu baki
ɗ
aya. Ai kin dai ji abinda Uwani ta fa
ɗ
amaki. Yanzu da ace kin tsa
ida hankali wurin
ɗ
an uwan mijinnata ai da yanzun sai dai wata maganar ba wannan ba."
Ramlat kirjinta ya yi nauyi, ta share hawayen da ya soma sauka saman fuskarta. Miƙewa ta yi ba ta ko yi marmarin ganin abinda ke cikin ledojin ba ta fa
ɗ
a
ɗ
akinta. Ge
fen gado ta zauna gami da zabga tagumi. Tana cikin tsaka mai wuya, ita ta sani. Wanda ta ke masifar so kuma ta ke jin za ta iya aura bai san ma tana yi ba. Runtse idanunta ta yi tana mai sa hannu ta dafe kanta.
"Ya Allah!" Ta furta a fili, fuskar H
ussein kawai ta ke gani cikin ƙwayar idanunta. Ta bu
ɗ
e idanun, tuni sun ka
ɗ
a sun yi jazur. A hankali ta kai duba ga hotonsu na Family, Abbanta ta ƙurawa idanu. Take dukkan wani fa
ɗ
i-tashi da aka yi akan zancen aurenta da Aliyu ya fa
ɗ
omata. Murmushi ta yi d
a ya fi kuka ciwo, soyayyar Abbanta ya mamaye zuciyarta, yanzun komai ya zama tarihi. Abba ya bar ta da kewa ta har abada, hakanan Aliyu.
Ta tsinci kanta a sabuwar rayuwar da ba ta san abinda zai haifarmata a gaba ba.
***
ADAMAWA
Misa
lin ƙarfe biyu da mintuna na ranar Talata, Rasheed ne zaune yana faman ha
ɗ
a gumi ga idanunsa da suka ka
ɗ
a suka yi ja tsabar tashin hankali. Labarin
ɓ
atan amininnasa ya matuƙar girgiza shi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
Ya furta a fili,
Dada dai hawaye ta ke yi hakanan Hafsat da ke raƙu
ɓ
e a gefe ta dora hannu saman cinyar Dada. Rasheed ya dubi AlHassan cikin harshen turanci.
"Ban ji dadin wannan labarin ba sam! Sai dai ina ji a jikina duk inda Hussein ya ke yana raye, bai mutu ba. Sa
nnan meyasa ba ku yi cigiyarsa ta gidajen rediyo da talabijin ba? Na dauka wannan ce hanya mai sauki da za ku yi saurin ganoshi."
AlHassan ya jinjina kai.
"A farko duka mun yi wannan amma a karshe sai muka watsar mu ka fawwalawa Ubangiji. Ni kai
na ban yarda cewa Hussein ya mutu ba. Amma ya zamu yi? Babu inda ba mu nemeshi ba, sai dai ba wani labari."
Rasheed ya runtse idanu cike da
ɓ
acin rai, ransa na suya.
"Kuma babu wani abokin gaba da ya ke da shi? Wanda ku ke zargi?"
"Babu."
Rasheed ya yi shiru, so ya ke ya tuna ko akwai abinda ya manta game da Hussein. Duk iyakar kokarinsa ya kasa, a ƙarshe dai AlHassan ya shiga roƙonsa akan ko labari ya ji na abinda ya danganci Hussein don Allah ya sanarmusu. Bai bar gidan ba sai da ya
ci abinci, nan ma kawai cusawa yake, ba zai ce cimarsu ta bambanta ba don shi kam ruwa biyu ne, mahaifiyarsa ƴar jahar Katsina ce. Jimami da alhinin
ɓ
atan Amininnasa ne ke sukarsa. Da wannan ya musu sallama ya bar gidan.
Ranar dai ya tayarmusu da alhi
nin Hussein, wunin ranar sun yi shi sukuku ba da
ɗ
i idan ka cire Taheer da bai san me ake ba.
Burinsa kawai ya shaƙu da Hafsat kuma ta kaunaceshi, sai dai abin ya faskara.
***
KANO
Wata wawuyar dariya Hajiya Zeenat ke yi tana ƙara rungum
e wayarta a kunne, ƙafafunta kamar za su rabu da cinyarta tsabar girgizasu da take. Kallo
ɗ
aya za ka yiwa yanayinta ka fahimci ko ma wane kalar labari ake ba ta ba ƙaramin da
ɗ
i ya yi mata ba.
"Kai Dikko! A ganka nan a bar ka inda kake! Da ace za ka s
an da
ɗ
in da wannan labari ya min za ka sha mamaki. Kai ma kwallon shege ne!"
Can kuma ta ƙara nutsuwa ta ce.
"Kana ji na? Kar ka sake ka yi wasa! Kar ka
ɗ
aga ƙafa, wani ganin ba ta sonka ko ta tsaneka wannan duk a banza ce muddin ta fa
ɗ
o hannunka
. Ka dai ƙara ƙaimi wajen sakarwa makwa
ɗ
aitan iyayennata aljihu, na tabbatar maka ƙarfin dukiya ya fi komai tasiri a duniyarnan. Don ubanta dole ma ta sarara ta aureka. Ni kuma na maka alƙawarin wata kyauta mai tsoka muddin ka mallaketa matsayin matarka."
Jin haka daga can
ɗ
aya
ɓ
angaren, Chairman ya shiga zuba godiya da kirari, wannan ya ƙara fasa kan Hajiya Zeenatu, har wani lumshe ido take tana murmushi, koda ta ji motsin saukowar mutum daga bene ta yi sallama ta ajiye kan wayar. Duban mijinta ta shi
ga yi tana murmushi sosai, ranta na wani irin sanyi kamar ƙanƙara. Shi kuwa bai san ma tana yi ba, kacokan hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa na Hisham game da kasuwanci na ha
ɗ
in gwuiwa da suke son yi.
Har ya sauko ya ƙaraso bai kammala ba, gan
in irin kallon da ga ke jifansa da shi yasa shi fadin.
"I will call you back." Daga nan ya katse wayar.
"Lafiya?"
Abinda ya ce kenan. Ta yi farr da ido, ya kauda kai.
"Ba komai, kawai dai kyau ka yimin Yalla
ɓ
aina."
Ɗ
an murmushi y
a yi bai ce uffan ba.
"Amm, dama ina son zuwa asibiti."
Ya dubeta.
"Meke faruwa?"
Cike da ƴar damuwa ta ce.
"Kwanakinnan komai na ci sai na ji kamar zan yi amai, ga yawan kasala."
Kirjinsa ya bada dam! Haka kawai zaton da ya
yi sai bai mishi wani dadi sosai ba. Ya daure ya gyada kai da murmushin da ya fi kama da yaƙe.
"Ya kamata ki je, ba'a wasa da lafiya."
Ta ƙara rausaya ƙwayar idanunta.
"An gama Baby, da safe za shirya na je. Fatana Allah Yasa mu ji alheri.
"
Ta ƙarashe tana shafa cikinta, ya yi murmushi kawai ya maida hankali kan wayarsa. Hotom Fatima ya bu
ɗ
e yana kallo, gani yake idan har Hajiya Zeenatu za ta haifamasa irinta, toh yana marhaba. Kaunar yarinyar ya ke ji sosai. Abu daya ya tuno da ya ji
ba dadi, wato dai rabon da ya ga Ramlat ma a online tun ranar da ta turo mishi hoto.
"Wannan kuma wacece?"
Tambayar Hajiya Zeenatu da ya yi saurin maidoshi tunaninsa. Ya sauka daga whatsapp din ya rufe wayarsa, cikin fa
ɗ
uwar gaba ya ƙirkiro ƙar
ya ya shirgamata.
"Ƴar sister din Hisham ce. Ta miki kyau ko?"
Nan da nan annashuwar saman fuskar Hajiya Zeenatu ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi.
"Sosai yarinyar ta yi kyau. Zamu haifi fiye da hakan ma."
Ya gya
ɗ
a kai kawai
.
***
"Wai wa ya fa
ɗ
amaki ina sonsa? Ni wallahi ban ta
ɓ
a sauraronsa ba."
Ramlat ke fa
ɗ
i a gundure, gaba
ɗ
aya zancen Chairman ya isheta. Ta kuma lura mitar Rafee'ah ba mai ƙarewa ba ce.
"Ai shikenan, idan dai kina son a tabbatar da haka
n sai ki daure ki fiddo miji. Ko kuma shawara, ki samu Baba Dakta kawai ki fa
ɗ
amasa."
Cewar Rafee'ah.
Ramlat ta yi shiru, da sun san damuwar da take ciki na son maso wani da basu takuramata da zancen Chairman ba.
"An fa
ɗ
amaki Baba Dakta
n shima zai saurareta ne idan ba wani ta kawo ta ce shi za ta aura ba? Malama ki yiwa kanki fa
ɗ
a tun wuri wallahi idan ba haka ba za'a ji kunya. Baban Twins yana da labarin Chairman Dikko, ba abinda ban sani ba na tarihinsa."
Wannan karon ma shiru ta
yi, Ramlat ta yi dana sanin dawowarta gidan da wuri, da ace ta san da zuwansu ba abinda zai kawo ta. Ta dawo ta iske Hisham ya gaji da zolayar ya aikomata motarta. Yinin ranar da tunanin Hussein ta cinyeshi, don dakyar ta dinga fuskantar aikin da ke gaban
ta, yanzun kuma ta zo ta iske yayyunnata, sun sanyata tsakiya kowanne da kalar nashi zancen.
Tsam! Ta mike tsaye ta kwashi tarkacenta na ofis da zummar wucewa.
"Au, mu za ki yiwa rashin ta ido? Don ana fa
ɗ
amaki gaskiya?"
Ta kasa ba Anti Z
ulaihat amsa, cike da damuwa ta dubeta kawai.
"Wuce abinki, ke kika sani. Rayuwarki ce."
Ta furta a zafafe, Ramlat ta ciji lebbanta tsabar takaici, karshe ta yi gaba zuwa daki tana ji Hajiya na fadin su bita a sannu.
Ruwan ma kasa watsa
wa ta yi don haka ta bi lafiyar gado ta kwanta, a hankali ta shiga fitar sa hawayen baƙin ciki. Kewarsa ta ke ji kamar ta yi me, ga wani irin sonsa da ke nuƙurƙusarta, kwana biyu ba su yi magana ba, bai ganta online ba kuma bai nemeta ta waya ba. Wannan ya
sa ta ƙara tabbatarwa ita ka
ɗ
ai ke haukan sonsa. Ta kai minti goma sha biyar a haka ba ta iya ko motsawa ba, tausayin kanta take ji, da ace su Ummi na gidan, ko ya ya zasu
ɗ
ebemata kewa, kiran sallar Magriba ce ta tasheta. Ta fa
ɗ
a ban
ɗ
aki ta kama ruwa ta y
i alwala.
Sai da ta idar da sallah kafin ta ninke Hijab ta fice zuwa falon. Wannan karon ta yi ƙoƙarin saita zuciyarta ta ƙaƙalo walwala, suka ci gaba da hira da ƴan uwanta kamar wani abu bai faru ba. Tattaunawa ce game da bikin da ya taso a Daura,
wanda zasu tafi dukkansu don karshen sati ne. Su ma basu ƙara tayar da batun Chairman ba.
Sai bayan sun bar gidan, Hajiya ta shige daki don watsa ruwa, itama ta fa
ɗ
a nata
ɗ
akin da niyyar hakan.
Ganin hasken shigowar saƙo bai sa ta yi wani raw
ar ƙafa ba, hakan ya faru ba adadi a yini biyunnan, sai dai daga ta duba, saƙon Muhibbat ne ta ke gani, wani lokacin Hilal, wani lokaci kuwa saƙon kamfanin layukanta. Tunanin hakan yasa ta ƙin daukar wayar har sai da ta fito daga wanka ta gama shafe-shafen
ta ta shirya cikin riga da wando na bacci. Ta dora rigarta na sallah ta shimfida darduma. Sai da ya idar da sallar Isha'i ta yi duk abinda ya dace sannan ta ƙara samun nutsuwa.
Kai tsaye ta nufi wurin wayar, sunan da ta gani a saƙon ya sa ta jin nau
yi a ƙafafunta, kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, haka ta bu
ɗ
e bayan ta zaune gefen gado.
*Na lura kina da kishi, wato don ban nemi ki turomin hotonki ba ne yasa ki ke shan ƙamshi ko? Oya, a turomin yanzu. Happy?*
Lumshe idanu ta yi tana murm
ushi.
I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ysuMTT3Orcb
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
42)
Dukkan godiya tabbata ga Sarki Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Ubangijin Talikai.
Ina kara amfani da wannan damar wurin godiya gareku gaba daya. Alhamdulillah na kammala exams lafiya sai fatan sa'a in sha Allah. Ina godiya da h
akuri da uzurinku gareni. Allah Yabar zumunci. Ameeen. Sai dai kar ku manta dama ba kullum nake posting ba, ina tsallake kwana daya. Allah Yasa mu ga karshen Ƙarfen Ƙafa lafiya. Ameen.
******
*Ya ya zan yi in misalta soyayya..? Ya ya zan
yi in fasalta soyayyaa..? Ita ce ba'a siye da kudi duk dukiyaa..Ita ce mai gida na mulki shi ne zuciyaaa..Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuyaa..ya zubda hawayen idaniyaaa..!* Umar M Shareef
Hoton
ɗ
an aljan mai murmushi kawai ta tura mishi. Aka yi sa'a ya ha
u online. Ganin ya bu
ɗ
e ta yi saurin kife wayar ta runtse idanu kamar yana gabanta, kirjinta na wani dukan tara-tara. Jin ƙarar shigowar saƙo yasa ta karkata wayar a hankali kamar marar gaskiya ta duba.
*"Please."*
Don ƙara tabbatarwa ta ƙara mu
rza idanu ta duba, roƙonta fa ya yi? Anya? Kuma akan hotonta? Ina Hajiyarsa?
Duk wannan tambaya ce da babu mai amsamata sai shi, har abada kuma ba za ta tambaya ba. Ta jingina kanta jikin gado tare da miƙar da ƙafafunta.
*"Angel
ɗ
ina ya hana ni
aikawa kowa hotona."*
Ta ba shi amsa duk kuwa da cewa ba ta ji dadin amsar ba, sai dai ta lura idan ta biyewa kanta, za ta iya tona asirin zuciyarta har ya gane inda ta dosa.
Ya bu
ɗ
e, kusan mintuna biyar shiru, goma, sha biyar, duk shirun ne, s
hi bai sauka online ba kuma bai ce uffan ba. Ramlat dai har bacci ya soma fisgarta babu amsa daga Hussein. Don haka ta ajiye wayar ta mike ta kakka
ɓ
e shimfidarta ta kwanta. Ta soma addu'oin kwanciya bacci kenan wayarta ta yi ringing. Da sauri ta kai idanun
ta, lambar da ta gani ya hargitsa kwanyarta, miƙewa zaune ta yi b shiri. Sai da ta kusan yankewa kafin ta samu nutsuwar
ɗ
agawa. Le
ɓɓ
an ke rawa, zuciyar na ƙara ƙaimi wurin bugu sai dai lanƙwasa harshen har ta iya ha
ɗ
a kalma kwakkwara ta gagara.
'Haka
so yake?' Ta jefawa zuciyar tambaya. Ta san ba wannan ne farkon soyayyarta ba, wanda ta shimfi
ɗ
a a baya ya girmi wannan. Sai dai wannan shigarsa da tasirinsa mai sauri ne kuma mai sanyaya zuciya da ruhin ma'abocinsa.
"Kin yi shiru."
Ta dawo dag
a duniyar tunanin abinda ya yi mata nisa, TAZARAR DA KE TSAKANINSU kamar tazara ƙasa da sararin samaniya ne. Ɗumi ta ji a kumatunta, wani