Showing 144001 words to 147000 words out of 255051 words

Chapter 49 - KARFEN KAFA complete

nunamin zai zo gidanmu ina ƙin ba shi dama don na riga na san waye shi. Ban

ɓ

oyemaki komai dangane da alaƙarmu ba. Yanzu kam an zo ga

ɓ

ar da zan bar ma'aikatar Revenue, ba zan iya ci gaba da zamansa ba. Ya kamata a

ce dama tun a baya na yanke wannan hukuncin. Amma yanzun ma lokaci bai ƙuremin ba."

Kai Hajiya ta jinjina.

"Ina bayanki, ya dace yanzu kuma ki bar masa ma'aikatar duk da ba tasa bace ta gwamnati ce, kinga kenan ba shi da wata ƙafar da zai yi amf

ani da ita wajen cin zarafinki ko yi miki bita da kulli. Ni ai tunda ki ka ce ya san waccan matar hankalina bai kwanta ba."

Nan da nan Hussein ya fado ranta, ta dubi Hajiya. Ta ji tana son zayyanemata komai.

"Hajiya kin tuna baƙinmu na Adamawa?

"

"Ta ya zan mance su, mutane masu karamci haka Ramlatu? Meyafaru?"

Hajiya ta tambaya cike da ƙaguwa. A zatonta, abinda ƴan uwan Ramlat din ke zargi ne zai tabbata, wato soyayya tsakanin Alhassan da ita. Abinda ba za ta yarda ba kenan ko don mutu

nci da girmamawar da Kausar ke mata.

"Kinsan kuwa suna da alaƙa da Hussein da nake ba ki labari mijin Hajiya Zeenatu?"

Ido waje Hajiya ke dubanta.

"Alaƙa wace iri?"

Tiryan-tiryan ta ba ta labarin duk abinda ta sani. Sai ga Hajiya na sa

lati har da hawayen tausayi.

"Kai duniya! Mata me muka dauketa ne? Matattarar da za'a dauwama ko me? Zunuban kanmu ka

ɗ

ai bai isa ba sai mun zalunci wasunmu? Kaico da wannan rayuwa. Allah Ya sakawa wannan yaro, Allah Ya karya ƙadarin wannan mata."

Hawayen Ramlat suka ci gaba da ambaliya, sam ba ta fa

ɗ

a wa Hajiya abinda ya faru tsakaninsu a yau ba, hankalinta ya yi kansa sosai, tana son ta ji muryarsa ko don tabbatar da lafiyarsa.

"Amma wannan fa ba karamin aiki ba ne na wasa, addu'a ce sosa

i zamu dukufa ga yi masa. Zuwa anjima zan kira Kawunki Malam Yakubu. Na tabbatar shima zai taimaka. Ba a banza matarnan ta bar shi ba."

Zantukan Hajiya masu dadin sauraro suka katsemata tunani. Wani sanyin dadi ta ji, har ta mance kaso mai yawa na dam

uwarta, ta yi murmushi gami da godiya. Daga wannan ta mike ta bar mata dakin zuwanata.

Nan ta iske yaran sun yi baja-baja saman gadonta ana game a waya. Dubansu ta yi gami da murmushi, haka kawai ta ji har ta soma kewarsu. Maimakon ta korasu kamar ya

nda ta saba, kawai sai ta zauna ta biyemusu tare da alƙalanci.

Sai da wani tunani ya fa

ɗ

omata sannan ta kar

ɓ

i wayarta ta basu umarnin zuwa falo. Agogo ta duba, ƙarfe shida da rabi na dare, so ta ke ta kirashi amma ba ta kaunar abinda zai je ya dawo do

n haka ta za

ɓ

i aikamasa saƙo.

***

LAMIƊO CRESCENT...

Yana zaune kamar kurma yana sauraron Hajiya Zeenatu da ke bu

ɗ

ewa John wuta akan ya yi girkin da mijinta ya kasa ci. Ɗora laifi kacokan ta yi akansa, shi dai ƙara russunar da kai ya yi yana

ambaton "Sorry Ma." Hussein da abin ya ishe shi, miƙewa tsaye ya yi gami da daukar wayarsa.

"Please ya isa haka, na fadamaki yunwar ce kawai ba na ji, ba wai girkin ba ne."

Yana kaiwa nan ya nufi matattakala. Ta bishi da kallo kafin ta maido dub

anta ga John, harara ta watsamasa gami da ba shi umarnin tafiya. Hankalinta ya koma ga tunanin abinda ta shirya yi. Wato shan maganin da Gora ya ba ta wanda ya tabbatar da zarar Hussein ya kusanceta za ta samu ciki. Samun cikinta ne zai mantar da Hussein t

unanin kowa da komai face tattalin da zai koma ba ta.

Wannan ta sa da sauri ta jawo kofin ruwa ta daga riga ta ciro ƙullin maganin ta zuba gami da gaurayawa ta kafa baki, ba ta

ɗ

ago ba sai da ta shanye tas tana wani murmushi.

Shi kuwa Husse

in, zube wayoyin saman gado ya yi ya shiga rage kayan jikinsa, wanda ya ke da niyyar shiga, ƙarar shigowar saƙo ya

ɗ

auki hankalinsa. Duban wayar ya yi, kamar kada ya bu

ɗ

e sai kuma ya tuna da saƙon da za'a aikomasa na abinda ya shafi aikinsa. Madadin hakan

ya ci karo da sunan da hannunsa ya rubuta saman lambar da ya

ɗ

auketa da wani irin muhimmancin da bai san dalili ba.

_*Heart*_

Ya furta tamkar baya so kafin ya kai ga bu

ɗ

ewa.

*_"Dukkanmu ajizai ne, mukan yi kuskure da saninmu ko kuma akas

insa. Bana fatan na yi abinda zai jefaka cikin

ɓ

acin rai da damuwa. Shakka babu, Ramlat mai laifi ce, na yarda na shiga personal life dinka, na zaƙe da yawa. Ka yi hakuri, ka yi hakuri. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba. Ka ji?"*_

Murmushi ya yi, ya kar

a karantawa ya fi sau uku, ya so ya gogeshi daga wayar amma ya ji ba zai iyaba. Wani nauyi hakan ya yi mishi don haka sai ya fasa, ya sanyawa wayar muƙulli ya jefa saman gado. Har ya shiga ban

ɗ

aki bai bar murmushi ba.

Fitowarsa ba jimawa ya sanya kay

an bacci, shigowar Hajiya Zeenatu ne ya sa shi dubanta. Saura ka

ɗ

an wata dariya ta kufcemasa. Rigar bacci ce a jikinta shara-shara kuma marar tsawo don duka tsawon iyakarsa gwuiwa. Ƙaton tumbinta da ruguza-ruguzan mamanta wadanda suka zube sun kwanta luf

sun bayyana cikin rigar. Damtsenta kuwa a cike sosai sai dai ba ka misalta shi da na karfafan maza ba. Akwai bambanci.

Duba sosai ya ke mata, riga dai gatanan mai

ɗ

an karen kyau da daukar ido. Lumshe idanunsa ya yi yayinda wani tunani ya bijiromasa.

'Za ta yi kyau sosai.' Ya furta ƙasa ransa, ankara da kuskuren kalaminsa ne yasa shi jan istigfari. Sai kuma lokacin ya tuna da bai yi sallar Isha'i ba ya ke shirin kwanciya. Abin yana damunsa, ya rasa me ke shagaltar da shi daga bautar UbangijinSa

, ma'ana gabatar da sallah akan lokaci. Abin yana mishi ciwo, sai dai mafi yawan lokaci ji yake kamar wanda aka mantar. Sau tari ma wani bacci ke zuwa ya rufe idanunsa da zarar an soma kiraye-kirayen sallah.

Ganin ya mike yasa Hajiya Zeenatu tunkaros

hi, hannayenta biyu ta sanya saman kugunsa.

Ya yi mata murmushi mai kama da yaƙe. Duk yanda ya so nunamata tsana ko wani abun, sai ya ji ya kasa.

"My Zeenat, kin yi kyau sosai."

Wani sanyin dadi ya mamayeta, ta sumbaci le

ɓɓ

ansa.

"Nago

de Sweetheart."

Ganin tana kokarin wuce gona da iri yasa shi janye jiki.

"Bari nayi sallah."

"Sallah, wace sallar?"

Yanda ta fadi a mamakince shima sai ta jefashi cikin mamakin kalamanta. Ya zubamata idanunsa mai adon fari ƙal da baƙin

kwayar idanu si

ɗ

ik.

"Me kike nufi? Wace Sallah muke yi matsayinmu na musulmai?"

Gaban Hajiya Zeenatu ya bada dam!

_*"Kiyi duk yanda za ki yi, ki dinga shagaltar da shi daga ibada, zamu turamasa arnen aljan wanda zai tayaki yaƙi. Ina kara gar

gadinki! Kar ki kusa ki bari ya dinga sallah akan lokutanta!!!"*_

Wannan yana daga cikin farkon abinda Gora ya fadi mata sadda suka soma zuwa wurinsa a karon farko game da lamuran Hussein.

Ganin ta tsaya tana kallonsa yasa shi giftawa ya fice zu

wa ban

ɗ

aki. Ta bi ƙofar da kallo.

'Ke me zai dameki? Ba yanzu za ki yi aikin da za ki samu ciki ba? Idan kika samu komai zai zo karshe!'

Wani

ɓ

angare na zuciyarta ya tunatar da ita. Ta sauke ajiyar zuciya tana wani irin murmushi kafin ta zauna ge

fen gadon. Tana kallonsa ya yi sallah a tsanake, ya yi addu'a kafin ya na

ɗ

e dardumar ya mike.

Mintuna talatin da suka biyo baya, komai ya kammalu kamar yanda ta ke so, murmushi kawai take kamar koyaushe cike da gamsuwa idan ka

ɗ

auke Hussein wanda ran

sa sam ba dadi. Kusan hakan ce ta saba faruwa da su, zai iya cewa wahalar da shi kawai ta ke yi a kowace tafiya don ba wani gamsuwa yake ba. Ganin ta soma jan munshari yasa shi miƙewa ya fa

ɗ

a ban

ɗ

aki. Can ya fito ya sauya kaya, yunwar

ɗ

azun ce ta dawo mish

i. Matsawa ya yi ya tasheta. Cikin magagin bacci ta dubeshi.

"Lafiya?"

"Muje ki

ɗ

an

ɗ

umaman abinci, nasan yanzu John ya sanya a fridge."

Yamutse fuska ta yi.

"Wallahi na gaji, ko nan da can ba zan iya motsawa ba. Ka je kawai ka tashes

hi ya yi maka."

Daga haka ta juya ta cigaba da bacci, girgiza kai ya yi gami da gyaramata abun rufa. Wayoyinsa ya dauka ya fita daga dakin cike da damuwa. Kamar akwai abinda ya rasa, kamar yana da wata damuwa amma ya kasa gane kan zaren.

Maimako

n ya kira John da ya wuce Boysquarters, sai ya

ɓ

ige da dafa ruwan shayi, ya za

ɓ

i shan tea da bread kawai. Sai da ya kammala ya dawo falon, wayarsa ya fiddo ya kunna Data. Kwanaki biyu kenan rabonsa da hawa online, wannan tasa saƙonni suka shiga fa

ɗ

owa, da

na mutanen da ya sani da baƙin lamba kamar koyaushe. Ya kuma riga da yasan baƙin lambobin bai wuce na mata, idan da sabo ya ci ace ya saba.

Saƙonta ya

ɗ

auki hankalinsa, ya kuma yi mamakin ganinta online, ya kara duban lokaci. Ƙarfe goma daidai na d

are. Murmushi ya yi ganin amsar da ta ba shi a wancan lokacin, maimakon mayar da martaninsa sai ya

ɓ

ige da wata tsokanar.

"Ba ki yi bacci ba? Da wa kike hira toh?"

Yana aika hakan sai ya maida kai ya ci gaba da shan shayinsa. Tausayinta ya ji ya

mamaye zuciyarsa, shakka babu sam bai kyauta ba.

***

A

ɓ

angaren Ramlat, tana kwance ne tana kallon Status, duk duniyarta ba dadi. Ga lamarin Chairman ga kuma Hussein da ya yi fushi da ita. Tana shirin sauka ganin uban hamman da ta ke dokawa, sai ta

nemi baccin ta fasa ganin saƙon da ya shigo. Da wani irin

ɗ

oki ta bu

ɗ

e ta karanta. Murmushi sosai take yi ha

ɗ

e da dariya ciki-ciki. Ko ba komai hankalinta ya kwanta.

"Kai nake jira, hakuri nake so na ƙara ba ka."

Abinda ta aikamasa kenan.

***

Yana kammala shan shayin, ya dauki wayar, ganin abinda ta ce yasa shi jin wani daam, lumshe idanu ya yi kafin ya bu

ɗ

esu. Sai kawai ya za

ɓ

i kiranta. Kai tsaye ya dokamata kira, sai da ya kusan katsewa sannan ta

ɗ

aga.

***

"Kira war haka? Ina M

adam dinka? Ka rufan asiri."

Abinda ta ce kenan bayan

ɗ

aga wayar.

"Ni kenan na tonawa kaina asiri ko? So kike yi a gane damuwar da ke kwance saman fuskata na jefaki a damuwa?"

Maganarsa sai ta yi mata nauyi, ta rasa amsar bayarwa, can ta dau

re.

"A'a, ni ce mai laifi, ni na zaƙe da yawa. Ka.."

"Kika ƙara bani hakuri ina miki rantsuwa da Allah za ki ganni a gidanku yanzu."

Yanda ya yi maganar daga ji ka san ba wai fa

ɗ

a ya yi ne kawai ba. Kirjinta ya soma bugu da ƙarfi, ta ji kant

a na neman tarwatsewa. Ta kasa gane a maudu'in da za ta jefa kalamansa. Ta rasa abinda ya ha

ɗ

a kalmar hakuri da batun ziyartarta a wannan lokaci don haka sai ta kasa cewa uffan. Shiru ya biyo baya na ƴan sakanni sai numfashin junansu da kowanne ke jin fit

arsa.

"Ɗazun na ce kinsan me? Ba ki bari na ƙarasa ba, yanzun ki bani damar na ƙarasa maganata."

Ta kasa ce mishi uffan. Har ya kara magana.

"Na baka." Ta furta a hankali.

"Ke ce mace ta farko bayan Zeenat, da lambarta ya shiga cikin

wayata har nayi saving. Ke ce mace ta farko da ƙafata ya taka har gidansu, ke ce mace ta farko da na zauna muka yi hira da ita har na tsawon mintoci ba tare da naji hirar ta ishe ni ba. Kawai dai idan so ki sani, kina da babban matsayi a rayuwata da ba zan

ce gashinan ba. I want you to keep staying in my life, ina jinki kamar wata ƴar uwata mai bani ƙwarin gwuiwa. Kamar dai kina ban ƙarfin ci gaba da rayuwa, na daina tunanin inama Allah Ya dauki raina, na bar tunanin bani da kowa a duniya. Please Ramlat, ka

r ki gujeni ko me zai faru, ko me zan miki. Kiyi hakuri, nayi maki laifi a

ɗ

azun da ni kaina ba haka na so ba. I just can't do otherwise idan aka zo irin wannan lamarin. Ban kuma san dalili ba."

Wani sabon yanayi ke shigarta game da HUSSEIN, wani abu

take ji na yawo tun daga tsakar kanta har yatsun ƙafafu. Zuciyarta gaba daya ta cika da tausayinsa. Ganin kamar tana neman wuce gona da iri yasa ta saurin magana.

"In sha Allah hakan ba za ta faru ba. Allah ne Ya ha

ɗ

a mu, ban isa na kawo karshen zumun

tarmu ba. Ina rokon Allah Ya yayemaka dukkan damuwarka. Sai dai don Allah ina roƙonka akan ka dage da kai kukanka gareSa. Kamar yanda ka bani shawara a

ɗ

azun, kaima yanzu ina so ka yi amfani da hakan."

Murmushi ya yi mai sauti yana ƙara gyara mazaunin

wayar, ƙafafunsa a saman kujera.

"Kina shiga haƙƙin Madam

ɗ

ita fa."

Harara ta bugamishi kamar yana kallonta, wani abu ta ji kamar ya soke ta a ƙahon zuci mai kama da KISHI.

"Ai ba ni na kiraka ba, sai da safe."

Tana ji yana dariya sa

dda ta datse kiran. Ita kuwa kwanciya ta yi ta shiga duniyar tunani. Murmushi sosai ta ke yi, wani sabon yanayi take ji game da Hussein wanda a yanzu ta kasa ƙaryatawa. Tunaninta ya tsaya cak! A gefe guda kuma tausayin kanta ya mamayeta. Wato dai ta gama f

ahimtar ta fa

ɗ

a SON MASO WANI.

Miƙewa ta yi ta fa

ɗ

a ban

ɗ

aki ta dauro alwala, nafila ta shiga yi kafin ta yiwa Hussein addu'a ta musamman.

***

Washegari ta tashi ranta fari ƙal, kaso mai yawa na damuwarta ya yaye. Ta yarda ta kuma aminta, ta ra

sa dabara ko wani makami da za ta kare kanta na cewar ta fa

ɗ

a tarkon SO.

Tana kai yara makaranta ta wuce kai tsaye Head of service inda ta kai takardar neman transfer da ta rubuta. Kusan sun yi waya da Zulaihat da Rafee'ah, duk sun goyi bayanta don a ce

warsu mutunci ya fi komai.

Kai tsaye ofishinsa ta nufa ganin da ta yi ya iso. Kwankwasawa ta yi gami da sallama, jin muryarta da gaggawa ya bata umarnin shigowa. Ta shiga fuska a ha

ɗ

e. Kallonta yake har da

ɗ

an miƙewa duk ya rikice. Ya san da cewa ya m

ata laifi amma ba yanda ya iya, gani ya yi idan ya biyemata to fa za ta kai shi ta baro ne. Ba tare da ta damu ta gaidashi ba ta fiddo ƙaramar envelope waanda ta sanya dukkan ku

ɗ

a

ɗ

en da ya bata.

"Idan har wannan ce damar da ka samu na zuwa tambayar au

rena a gidan iyayena, to ka sani daga yau na rusata. Kuma kar ka manta, ni ba yarinya ba ce ballantana ka yi tunanin za'a tursasani ko a yimin dole akan aurenka."

Ta zazzage kudin saman tebur.

"Ka ƙirga ka gani, idan da su kake taƙama har ka yim

in wannan aika-aikar, ko sisi ban ta

ɓ

a a cikinsu ba. Ina fatan daga yau komai zai wuce. Kar kuma ka kara tunanin cewa zuwa wurin Kawu Bello zai ba ka dukkan wata dama a kaina."

Daga haka ta juya da zummar tafiya ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunan

ta. Ta juyo tana dubansa fuska a daure. Gaba daya ya sauya fuska.

"Haba Ramlat, saboda na bi hanyar da addini ya tsara na neman iznin aurenki gurin magabata shi ne za ki watsan ƙasa a ido? Wannan wace irin kiyayya kike nunamin? Ina da kudi, ina da gi

daje da dukkan matsayin da na cancanci ki so ni dominsu, amma ke wannan duk bai sa kin saduda ba. Idan don matana ne, wallahi wallahi ba zan ha

ɗ

aki gida

ɗ

aya da su ba. Kin ji rantsuwar

ɗ

an musulmi. Ya kike nema ki yimin wannan kwalelan?"

Ta dubeshi du

ba na raini, ita dariya ma ya soma bata.

"Ni kudi bai isa ya siyeni ba, hakanan ba ku

ɗ

i ake nema a zamantakewar aure ba. Yarda, biyayya, kauna, so, mutunci, daraja da ƙima dama sauransu, su ake neman a aure. Babu ko daya da ka samu a idona. Ina kara n

eman alfarma akan ka rabu da ni ka fita daga rayuwata. Ba zan iya aurenka ba."

"Idan kudi na siyan soyayya! Wallahi Ramlatu sai kin aureni koda ba kya so! Mu zuba ni da ke!!"

Ya fadi a tsawance, kalaman sun fa

ɗ

armata da gaba, ta dake ta yi murmus

hi.

"Allah Zai tsayamin."

Daga haka ta sa kai ta fice dama ba da niyyar zama ta zo ba. Maimakon ta yi gida sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login