Showing 156001 words to 159000 words out of 255051 words
/>
ɗ
an
ɗ
ano na gishiri ya sauka a le
ɓɓ
anta ta cije le
ɓɓ
an. Kitt! Ta katse kiran, ba ta tsaya anan ba sai kawai ta kashe w
ayar gaba daya ta jefa gefen gado. Kwanciya ta yi ta runtse idanu, me ya rinjayeta har haka? Hussein fa? Kamanninsa suka yi dirar mikiya cikin idanunta, tunaninta ya
ɗ
auketa ya cillar tun daga ranar da ta soma ganinsa har zuwa yanzu da suke tare.
"Ka
fi ƙarfina Hussein, Allah Yayemin wannan jarrabawar."
Ta furta a fili, ta yi addu'a ta kunna Mp3 Suratul Baƙara na tashi a hankali tana bi. Tun tana tunani har bacci ya yi awon gaba da ita.
***
"Baƙo?"
Ta furta a mamakince tana mai tsur
awa Baba Maigadi idanu, tana kyautata zaton kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Daga ita sai hijab saman rigar baccinta wanda ta dora zani a samansa.
"Nima kaina nayi mamaki Ranki ya da
ɗ
e, sai dai kuma kallo
ɗ
aya na yi mishi uzuri."
Daga haka ya j
uya bai ƙara dogon jawabi ko ƙarin bayani ba. Ta bi bayansa baki galala sannan ta
ɗ
ago idanunta ta dubi agogo dakyau. Bakwai da rabi da safe.
'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'
Ta furta a zuciya, Hajiya ba ta kai ga tashi ba. Itama baccin ta kas
a, ta rasa ya za ta yi da ranta, babu jimawa da fitowarta falo ta ji kwankwasar Baba Maigadi, ya kuma isar da saƙo ya bar ta tsaye da mamaki da fargaba. Ta dai daure ta yi shahada ta zura silifas ta fito. Fuskarta fayau sai dai albarkacin ruwan alwala da t
a yi yasa ya yi kyan gani.
Ido da ido suka dubi juna, daga shi sai riga da wando na sport. Ya zura hannu cikin aljihun wando, idanun sun yi luhu-luhu hakanan sun kanƙance, gashinnan a birkice kamar yanda fuskarsa ta nuna. Ta kasa kauda idanunta kamar
yanda shima ya kasa kauda nasa, kirjinta lugude yake kamar ana surfa gero. Ya tako har gabanta ya tsaya.
"Me na miki? Ki fadamin laifina, kiyi hakuri."
Ta lumshe ido ta bude don mamaki, sai a sannan ta samu damar magana.
"Me ka yimin Huss
ein? Ba abinda ka yimin ni."
Ya girgiza kai, ta kalleshi sau daya ta kauda idanunta da sauri.
"Kin kashe waya ba ki yimin magana ba, don nace ki turon hoto? Wasa nake maki. Ki yi hakuri, na shiga rayuwarki da yawa."
Ta girgiza kai, kamar ya
nda idanunsa ya ka
ɗ
a, haka nata ya cicciko da kwalla.
"Ni wallahi ba abinda ka yimin, kuma maganar da nayi wasa ce kawai nayi ba wai da wata niyya ba. Shi ne dama ka doko sammako? Ka yi hakuri."
Ya yi shiru bai daina kallonta ba. Ganin shirun ya
yi yawa ta kara kallonsa.
Hussein tambayar kansa yake abinda ya ru
ɗ
ashi, ya hargitsa tunaninsa. Mene abin
ɗ
aga hankali don Ramlat ta kashemasa waya? Me ya birkita kwanyarsa har bacci ya kauracewa idanunsa kamar yanda ya kasa bambance daidai ko akasi
nsa? Hajiya Zeenat baccinta take shar
ɓ
a ya fito, meyasa tunanin ta farka ta nemi ba'asi bai fa
ɗ
omasa a rai ba sai yanzun da ganin Ramlat ya haifarmasa da sukuni da kwanciyar hankali? Sai dai kuma akwai wani duhu da ya kasa nemo haske a cikinsa, watakila sa
i nan gaba! Ya ayyana a ransa.
"Shikenan, zan tafi. Ki gaida su Mama."
Daga nan ya juya ya shige motarsa, iska da sanyin safiyar na busata, ba ta fasa kallonsa ba har ya shiga motar. Gilashin ya sauke yana kallonta, sakanni biyu zuwa uku kafin t
a farga, ta juya da sauri ta fa
ɗ
a gida. Ya ja motar kamar wanda kwai ya fashewa a ciki.
Allah Ya taimaka Hajiya ba ta falo, da sauri ta shige dakinta ta rufe, a bakin ƙofar ta zame ta cure wuri guda, kuka ko dariya za ta yi? Ba ta sani ba, ba ta da t
abbacin abinda kwakwalwarta ke kokarin hasasowa sai dai ta jera Hussein a sahun mutanen da suka san ƙima da darajar *ƊAN ADAM*. Ta sauke ajiyar numfashi tare da neman tsari daga Ubangijinta akan sharrin zuciya da saƙe-saƙenta.
***
"Daga ina kake?"
Ta yi tambayar ba tare da ta bari ya ƙarasa fitowa daga cikin motar ba, ya kalleta kallon tsaf. Gabansa na fa
ɗ
uwa sai dai akwai wani ƙwarin gwuiwa da yake ji na iya kallon cikin idanun Hajiyar da
ɗ
an ƙaramin kuzari.
"Bai kamata ki fito haka ba."
Ya fadi a sanyaye ganin daga ita sai doguwar rigar bacci, damtsen hannun duk a waje ga tumbi da ya
ɗ
aga rigar. Hajiya Zeenat idanunta a ka
ɗ
e, ji take kamar ta shaƙe wuyan Hussein saboda wani irin kishi da ya mamayeta. Tasan ƙarya ne a kowane yanayi mace
ta ga Hussein ba ta ƙyasa ba, ta kuma sani ba zai ta
ɓ
a zuwa wajen kowace mace ba musamman da safiyar fari. Amma tana son tabbatar da inda ya je don ta samarwa zuciyarta hujjar da za ta nutsu sosai.
Gaba ya yi zuwa cikin gidan, ta mara mishi baya. Yan
a niyyar taka matattakala ta riƙe hannunsa. Ya runtse ido da sauke ajiyar zuciya alamar gajiya, bai bari ta ƙara tambaya ba ya tari numfashinta.
"Wasu takardu na kaiwa Hisham. Shikenan?"
Ta bishi da kallo tana mai sakin hannun, ya haye sama. Ƙary
a abu ne mafi muni cikin munanan
ɗ
abi'u, ya shiga istigfari a ƙasan zuciyarsa. A
ɓ
angaren Hajiya Zeenat, tasan waye Hussein, ƙarya ba ta daga cikin shirginsa, don haka sai ta gasƙata amma ta soma jin tsanar Hisham a ƙoƙon ranta. Yana neman shigemata hanci
da ƙudundune. Ta yi ƙwafa kawai ta bishi saman.
Kwanciya ya yi ya rufe har kansa da bargo saboda bai shirya amsa wasu tambayoyin daga Hajiya Zeenat ba bayan wancan. Murmushi ya tsinci kansa da yi, murmushi sosai, Ramlat da firgicin dake kwance samam
fuskarta shi ya ƙayatar da shi a yanzun.
***
"Jimin ja'irar yarinya! To ba kya sonsa wa kika kawomana za ki aura? Ko an fa
ɗ
amaki akwai wani cikin iyayennaki da za ki je wa da wannan magana su
ɗ
auka?"
Dada ke wadannan kalaman sadda Ramlat ta kai
mata ziyara da kuma roƙonta akan a janye batun Chairman. Jin abinda ta ce Ramlat ta
ɓ
ata fuska.
"Da ace kinsan waye shi da ke za ki zama farkon wacce za ta ce aa."
Ta zayyanemata kaf labarin Chairman, tun Dada na fa
ɗ
in toh meye a ciki? Har ta y
i shiru tana gya
ɗ
a kai. Ramlat na kaiwa aya ta dubeta.
"Toh yanzu ya dace ace kun bayar da jininku ga wannan mutumin? A ma
ɗ
auke duk wannan, bana sonsa. Ba shi da kyawawan
ɗ
abi'un da zan kaunaceshi dominsa. Bana son na maimaita gidan jiya, abin nufi,
ina gudun na sa
ɓ
a umarninku a karo na biyu naga ba daidai ba."
Murmushi Dada ta yi ba tare da ta furzar ba. Ta jinjina kai.
"Ai shikenan, zan yi magana da shi Bellon, ya dace su yi bincike mai kyau a kansa, idan da hali ma gwara a tattara a ajiy
e zancensa gefe. Sai dai kuma da shara
ɗ
in ki fiddo miji nan kusa. Da ƙananun shekarunki ba zamu zubamaki ido ki yi ta zama haka ba aure ba kuma kina yawon wurin aiki, babu ƙima da mutunci a hakan Ramlatu."
Ramlat ta gya
ɗ
a kai cikin tausayawa kanta.
"Ki tayani addu'a Dada, Allah Ya za
ɓ
amin nagari."
Dada ta amsa da amin. Ta
ɗ
ora da fa
ɗ
in.
"Yaushe angwayen nawa zasu dawo ne?"
Murmushi Ramlat ta yi, tana gyara zaman mayafinta, takanas ta biyo daga wurin aiki don ta roƙi alfarma wurin D
adar.
"Ni kaina ina kewarsu, amma mun yi waya da Muhibbat ta cemin za ta je ta
ɗ
aukosu zuwa gidanta su yi kwana biyu tukunna ta maidosu. "
"Allah Ya nunamana. Za ku je Daurar?"
Dada ta ƙarashe tana
ɓ
allar goronta daidai sadda Ramlat ta dauk
i jakarta.
"In sha Allah zamu je. Inace su Nusaiba ma duka za su je?"
"In sha Allahu. Ai bikin na gida ne."
Fadin Dada, a karshe suka yi sallama ta fice ba ta ko yi sallama da sauran jama'ar ba don tana jin haushinsu ganin mafi yawa na goyon
bayan Chairman. Ita mamakin ma irin kar
ɓ
uwar da Chairman ya yi a gidan ta yi don ko a gidansu bai samu hakan ba.
***
Tsakaninta da Hussein sai gaisuwa, ta rasa dalilin sauyawar alaƙarsu. Wani jzolaya da wasa duk ya daina. Kamar wani kalma na sabo
bai ta
ɓ
a ratsawa tsakaninsu ba. Wannan ya jefata damuwa, ga matsin lamba daga Chairman wanda ba dare ba rana sai ya kira. sai dai har ya kammala ringing ba ta
ɗ
auka, idan ya dameta kuwa ta latse wayar gaba
ɗ
ayanta.
Tafiyarsu Daura ta gabato har Hajiy
a zaa je wannan karon sai Amarya Hunainah wacce ta saki jiki da su sosai ake zumunci ba kamar Bilkisu ba wacce tun hayan auren Munir ta ha
ɗ
e danginsa kaf ta jerasu layin munafukai. Wannan ne ya siyawa Hunainah daraja da ƙima ba ka
ɗ
an ba a idanun su Ramlat.
Gidanta ne dai har sannan Ramlat
ɗ
in ba ta taka ba, ba kuma don wani abin ba.
Ana gobe zasu wuce gaba daya su Rafee'ah har Hunainah mai karamin ciki sun zo cikin gidan kwana, Aisha ma ta na nan ta zo ayi sallama. Hira suke yi cike da nisha
ɗ
i ana da
riya, sallamar Munir ce ta katsesu. Suka amsa ya dubi Ramlat.
"Ke wancan na wajen ne Chairman din naki?"
Nan da nan annashuwar Ramlat ta dauke.
"Zuwa ya yi?"
Ta fadi ranta a
ɓ
ace, tasan ya kira ta ƙi
ɗ
agawa ya yi mata text akan zai zo
su gaisa ta maida masa martanin ba ta buƙatar hakan.
"Nikam dai bari na leƙa naga waye wannan Chairman din."
Rafee'ah ke fa
ɗ
i tana ƙoƙarin miƙewa.
"Shi auren a igiya kika ratayeshi? Ba ki da kai fa Rafee'ah naga alama."
Munir ya fadi g
ami da harararta.
"Go
ɗ
ai-go
ɗ
ai da ke kina abinda ko Auta ba za ta yi ba. To ki je ki ce masa me? Ki leƙa wuta ma ko?"
Dariya suka sa mata idan ka cire Ramlat da ta yi daki ranta na ƙuna. Kamar ba za ta fita ba, sai kuma ta yanke ta je kawai ta t
unkare shi komai zai faru ya faru. Mayafin rigar jikinta ta yafa. Koda ta fito lokacin Hajiya na zaune.
"Ke dama haka kike zuwa hirar fuska kamar baƙin tukunya?"
Munir ya fa
ɗ
i yana duban Ramlat da ta nufi Hajiya don sanarmata.
"Yaya Munir
nidai da ka roƙarmin alfarmar mutuminnan ya bar zuwa gidannan. Na fa
ɗ
amasa ya kyaleni bana sonsa wallahi."
Ta
ɓ
e baki Munir ya yi.
"Au, wato dai gidan jiya kike neman a maimaita? Ai yanzu babu mai miki dole Ramlat, a baya ma ba'a iya anyi maki ba
sai yanzu? Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, ki samu wadanda suka kar
ɓ
i ku
ɗ
insa."
Yanda gaban Ramlat ya buga da ƙarfi, haka fuskokin Hajiya da su Zulaihat ya nuna razani da mamaki.
"Me kake nufi? Ku
ɗ
in auren Ramlatun su Yaya Bello suka kar
ɓ
a?
"
Munir ya dubi Hajiya yana mai murmushin tambayarta.
"Haba Hajjaju, a kar
ɓ
i ku
ɗ
in auren Ramlatu ba ki sani ba? Kawai dai yana sakarmusu bakin aljihu ana bushasha."
Wani wahalallan ajiyar zuciya Ramlat ta sauke, cike da bakin ciki ta kama ha
nyar ficewq daga falon. Maganar su dinma sai suka bar ta anan adalilin Hunainah dake wurin, ko ba komai suna buƙatar sirri.
***
"Girman kujerarki ce tasa na jure dukkan wata shanya da kika yimin, sai dai koda na bushe ganinki ya maidani ruwa tsundu
m."
Murmushi yake yana ci gaba da dubanta, jinsa yake kamar wani saurayi mai shekaru talatin idan yana gabanta. Ramlat ta dubeshi a
ɗ
aure.
"Ina ha
ɗ
aka da girman Allah da ManzonSa s.a.w ka fita hanyata. Kaga mu ba yara bane da za mu tsaya muna m
agana da maimaici. Ina za ka ji da
ɗ
in zaman aure da wacce ba ta jinka a ranta? Wane kyautatawa ka ke tunanin za ta yi gareka?"
Chairman ya yi wata ƴar dariya.
"Kina tunanin barazanar kisa a daren amarcinmu zai sa na sake ki? Aa Hajjaju, wannan
namiji ne ba muna maza ba. Ba ki da abinda za ki fa
ɗ
armin da gaba har ya yi sanadin rushewar alaƙarmu."
'Innalillahi..' Ta kai har ƙarshensa yayinda jiri ke neman kwasarta. Dakyar ta samu ta daidaita tsayuwarta bayan ta dafe Black Camry din Chairman.
Wani yawu ta ha
ɗ
iya.
"Me kake nufi?" Ta fadi cikin sarƙewar harshe. Chairman ya yi dariya karo na biyu.
"Abun dariya, kunkuru ya yiwa busjiya ƙafa, banda abinki Ramlatu ai maganar duniya ba ta
ɓ
uya, kin
ɗ
auka haka kike zaune ana ganin ina neman
aurenki ba'a kawomin sukarki ba? Ai ba zai yiwu ba. Kedai ayi sha'ani kawai."
Shiru ya biyo baya ga idanunta sun cicciko da kwalla.
"Idan ka gama zancen zan koma ciki."
Chairman ya marairaice.
"Haba Ramlatu, me kike gujewa a auren mutu
m irina mai muƙami da kuma rufin asiri? Kinsan adadin matan da ke neman irina kuwa? Da za ki ga matan da ke bina za ki cika da mamaki. Ramlatu sonki nake dagaske amma kin ƙi fahimta. Da ace na biyewa Kawunnanki da tuni an daura auren, yanzu ma abinda ya ka
woni batun turowa ne suka bn iznin nayi, shi ne na zo mu kara daidaitawa kafin lokacin."
Kamar wacce aka harbawa mashi, haka ta ji wani radadi a kirjinta. Daidai sadda ta ke share hawayen da ya zuba saman kuncinta ta kalleshi.
"Me ka ce? Iznin ka
turo fa suka yi maka?"
" Kwarai kuwa, kuma kinsan dama ce da ba zan ta
ɓ
a bari ta su
ɓ
ucemin ba. Na zo ne don kawai na kwantar da hankalinki, ki ƙara samun nutsuwa da ni don idan har ina numfashi kina yi, babu wanda ya isa ya rabani da ke."
Ranta
ya
ɓ
aci ainun.
"Sai mu gani inda ake dole! Aure ne bana yi, ba zan aureka ba. Ina mai tabbatarmaka ko ka turo babu inda zancen zai
ɗ
ara."
Daga nan ba ta juya ba ta ko waigo ta ji dalilin kiran da ya shiga kwalamata ba.
***
"Lafiya?"
Kusan lokaci guda suka jehomata tambayar ganin yanda ya fa
ɗ
omusu
ɗ
akin. Ta kasa magana sai kallo, karshe ta wuce
ɗ
aki.
Ganin haka Munir ya mike ya fita waje, Chairman ya shige abin hawa har ya fice. Ya dawo ciki ya sanar da su ya tafi.
Gaba daya suka b
ita dakin idan ka
ɗ
auke Hajiya da Munir da suka fa
ɗ
a tattaunawa game da lamarin Ramlatun.
"Ai mafita fa a wajen su Kawu shi ne kawai ta nemo wani ta kai musu. Yanzun bata da abinda zai kwace ta a hannunsu. Su gani suke sun kama dami a akala. Rannan ma
na shiga gidan na tarar Malam (Kawu Rabe) yana ta rubutu, wai mai neman auren Ramlatun yake rubutawa na tsarin jiki. Kinga kuwa ba karamin kamu suka yi mishi ba, fahimtar da su barin aurennan sai da taimakon Allah."
Hajiya ta yi salati. Tana mamakin
ƴ
an uwannata, idan kuma ta tuna wasu abubuwan da suka wanzu a baya na irin rashin jituwarsu a wasu lokutan matsayinsu na ƴan uba, sai ta ga fiye da hakan ma zai iya afkuwa. Ha
ɗ
in kan ma da yanzun ake yi da iyalinta tasan bai je koina ba. Yaransu dai gashin
an sun fi su hankali.
"Biri ya yi kama da mutum, Allah Ya kyauta."
Ta furta a fili ranta na zafi. Munir ya amsa da amin.
***
A bangaren Ramlat kuwa, daga Zulaihat har Rafee'ah zagin Chairman suke su na ƙarawa. Hunainah dai tausayin Raml
at ta ke ji sosai.
"Kema kin so hakan ta faru, ai kinsan babu yanda za'ayi a zubamaki ido. Ruwan ido ne ko me? Don ba za ki ce ba ki da manema ba. Korarsu kike kin ƙi ba kowa fuskar fitowa, daga samarin har masu auren da dattijai. Ai gashinan ana nem
an yi miki bita da ƙulli."
Fadin Rafee'ah dake jin kamar ta shaƙe Ramlat tsabar takaici. Ta furzar da bacin ran ta hanyar dakawa
ɗ
iyarta Daddy tsawa ganin kokawar da suke da kanwarsa Afrah.
"Uhum, kema dai Rafee'ah kya fa
ɗ
a. Ai tunda haka ta za
ɓ
a sai ta zauna a cuceta. Koda dai watakila za ta iya tunda ba yau farau ba."
"Ba yau farau ba? Meyasa abinda ya wuce ba za ku bar tayarwa ba? Meyasa ku ka riƙi abinda na aikata ku ka kasa yimin uzurin kasancewata cikin ajizai kamar ku?"
Ramla
t ta furta da duban Zulaihat. Su kansu ba wai da wata niyyar abin ke tasomusu ba, sai dai a lokuta irin haka idan ta ƙona ransu, takan motsa musu da abinda ya wuce
ɗ
in.
"Anti Hunainah ki zo inji Uncle."
Daddy wanda ya fita ya