Showing 48001 words to 51000 words out of 255051 words
iyayenta ba. Ina jiyemaki makomar rayuwarki Ramlatu."
Kowannensu kuka yake, Hajiya ta mike har hakan ya zaburar da Ramlat don a zatonta duka za ta sha, sai dai ta ga ta shige daki ta bar ta nan zaune.
Ita kuwa Hajiya ba ta ga dalilin dukan b
a, wanda ke jin magana kuma ya ke da gatan a fada ya ji ko a tursasa ya bi, shi ne suke da ikon idan bai ba su daga hannu su daka. Banda Ramlatu, ta nuna musu iyakarsu.
Mijinta ta hango kwance a ƙasa rub da ciki. Hannu ta sanya a kai cike da matukar
gigicewa ta buga salati iyaka ƙarfinta. A zabure Ramlat ta shigo, Hajiya tana jijjiga Abban tana kiran sunansa.
"Kar ka mutu Khalid! Ba ita kadai ka haifa ba! Kar ta kashemana kai!"
A can falo kuwa jin salatin Hajiya ya shigo da mata da ƴan samar
i (baƙin Daura) ƴan biki cikin falon Alhajin. Sai dai ba wanda ke da ikon ƙarasawa dakin Abban sai Zulaihat da ta nufi ciki da sauri. Idanun Rafee'ah ya wacce ta zauna dalilin jin wani mur
ɗ
i da cikinta ke yi ya kai saman takardar da ke kan kujera, ta dauka
tana karantawa, sai ta ji kamar an karawa tsohon cikinnata ƙaimi wurin mur
ɗ
awar. Ta matse takardar da karfi tana rike cikin da salati. Daidai sadda aka fito da Abba, samarin suka tari Hajiya da Zulaihat suka rikeshi aka fita.
"Ku dube ni!"
Cewa
r Rafee'ah da ke murkususu riƙe cikinta
ɗ
an wata bakwai, ga hawaye ca
ɓ
e-ca
ɓ
e saman fuskarta. Ai tuni wasu cikin iyaye aka yi kanta aka taimaka ta mike, ga ciwo a jikinta, ga tunanin Abbansu da kuma wannan tashin hankali da bakin ciki da Ramlat ta jawomusu
a wannan rana.
Motar Abba har ta yi gaba, har lokacin ruwa ake ba ƙaƙƙautawa. Itama Rafee'ah motar kai yara makaranta aka ciro, daya daga cikin baƙin Daura ne, Dauda, direban tasi. Shi ya tuƙasu cike a Bus zuwa asibitin.
Tana gefe tana kuka ka
mar ranta zai fita, ba wanda ya kara kallonta, duk wanda ma ya kalla ya tambayeta meke faruwa ba ta ko kallonsa balle ta amsa. Amrah ce ta nufi inda take ta ja hannunta suka shiga daki ta kulle kofar. Ta dubeta a gigice, idanun sun yi ja. Kasancewar Amrah
farar fata ya sanya hatta da fuskar ta dauki ja na wacce ta ci kuka.
"Me kika aikata?"
Ramlat ga
ɗ
ago ta dubeta cikin sheshsheƙa.
"Me ake zaton zan aikata don Allah Amrah? Me ake zaton zai faru da aure irin nawa? Ya sakeni. Ya sakeni saki .
.."
Bata kai ga ƙarasawa ba Amrah ta fidda hannu ta dauketa da lafiyayyan mari. Marin da ya hargitsata ya kuma sa ta cika da dumbin mamaki. Amrah ƙawa kuma Aminiya ita ta fidda hannu ta mareta? Abinda koda wasa ba ta zata ba, ya zo mata a hagunce. Kaf
in ta farfa
ɗ
o daga tunanin da ta fa
ɗ
a na tuna ƙarfin alaƙarsu da Amrah din. Ta ji kaifafan kalamai na fitowa daga bakinta.
"Wallahi ba ki da hali! Ba ki da hali! Na tsaneki! Haka kika za
ɓ
arwa kanki? Haka kike da son kanki? To ki sani, tun kafin wani y
a wulakantaki! Ke kika soma wulakanta kanki! Tun kafin wani ya ci zarafinki! Ke kika soma nuna ke din ba kowa bace ba ki da daraja da mutunci ko ƙanƙani! Ki yi kuka da kanki Ramla! Ki kuka da kanki bisa duk abinda zai biyo baya! Sai dai ki saka a ranki! Al
lah Madaukakin Sarki Shi ne Ya ce mu bi iyayenmu! Sun mana komai, sun kyautata mana. Ke kuma kin za
ɓ
i ki sa
ɓ
amusu saboda wani banzan Aliyu! Saboda wani shashasha da bai san ciwonki ba! Wallahi Aliyu ba ya sonki! Kema kuma ba sonsa kike ba! Hauka kike! Ni A
mrah Abdullahi ki sani, a yau a wannan rana kuma, babu ni babu ke! Ba zan iya ƙawance da mai hali irinnaki ba. Ban yi sa'ar ƙawa ta gari ba mai daukar shawara. Yau idan Abba ya mutu saboda banzan son rai irinnaki, ki sani kina cikin masifa. Bani babu ke! N
a tsaneki."
Tana kaiwa nan ta bude kofar ta fice daga dakin a guje tana kuka. Ramlat ta zube a wurin tana kuka sosai har da sheshsheka. Sosai maganganun Amrah sun shigeta, kuka take kamar ranta zai fita. Mutuwar Abba da ta ambata shi ya fi komai tsaya
wa a ranta don haka ta mike a gigice ta fito. Matan da ke falo suna jimami suka dubeta.
"Ke Ramla ina za ki?! Ke!"
Fadin Yakumbo yar uwar Abba. Masu kwari suka bi bayanta dakyar ta yarda ta zauna ta jira su dawo gidan. Idan Abba ya mutu ba za ta
yafewa kanta ba! Da gaskiyar Amrah, tana da son kanta da yawa.
***
Da gaggawa aka shigar da Abba ciki, itama Rafee'ah an miƙata Labour room don an tabbatar haihuwa ce ta tahomata kuma bakwaini.
Hajiya na zaune tana kuka har lokacin ba ta cewa k
owa komai ba, Hajja ta zauna gefenta. Cikin fada take magana.
"Wai menene ke faruwa Rabi? Bamu kai mu ji bane? Haba! Tun a mota nake tambaya an min shiru!"
Baba Hajara diyar Hajja ta biyu ta ca
ɓ
e.
"Nima dai Hajja abinda ban gane ba kenan. S
ai kuka ta ƙi magana. Ga Rafee'ah ma na naƙuda. Ki fadi meke faruwa ko hankulanmu zai kwanta."
Zulaihat ta ƙaraso wurin rike da takardar sakin Ramlat da Rafee'ah ta damƙamata kafin a shige da ita daki. Ta dubesu tana kuka.
"Sakin Ramlat fa aka yi
. Ita ta sanya Hilal ya saketa. Wannan ne dalilin faduwar Abba, da kuma naƙudar Rafee'ah."
"Wace Ramlatun aka saka?" Cewar Hajja, tambayar dake zuƙatan maza da matan gurin kenan saboda rudewa ma sun kasa gasƙata batun Zulaihat.
To mene abin
ɓ
oyon? A
binda komai ya riga ya bayyana, zubewar girma da bada kunyar da ake tsoro ya afku. Irin ABINDA AKE GUDU (Batool Mamman) ya riga ya faru. Don haka sai ta musu filla-filla yanda zasu gane. Sai ga mata na kuka da salati.
"Ni dama na san ba inda dolen na
n zai kaimu. Kamar na sani Rabi'atu na ce ki fadawa Khalid a fasa. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Wannan wane irin zamani muke ciki? Lokacin da aka mana auren bamu san mazajen ba ma, mu ce me?"
Hajja ke wannan batun tana kuka.
"Amm, don All
ah Mama ku yi hakuri. Kun yi yawa a asibitin nan, ga marar lafiyarmu ba ya son hayaniya. Don Allah ku ragu, ko kuma ku yi shiru. Kuna damun sauran marasa lafiya su ma."
Likita ke wannan jawabi a tausashe. Ya dubi Zulaihat don fuskarta kadaiya shaida s
ai ta Hajiyar.
"Kina iya biyoni ofis."
Ta amsa da toh tana share hawaye ta bishi a baya. Can kuwa Nos ta fito ta na fadan ba wanda ya tsaya wurin Rafee'ah gashinan ta haihu kuma ana bukatar kayan amfani.
"Me ta haifa?" Har suna hada baki wu
rin tambaya.
"An samu namiji. Itama kuma da sauki jikinnata."
Suka sauke ajiyar zuciya, nan aka yiwa mijin Rafee'ah waya akan ya zo kuma ya taho da kaya da gaggawa, ta haihu. Abinda ya jefashi cikin ru
ɗ
u da mamaki kenan, an haifar masa bakwaini.
***
Likita ya yi fa
ɗ
a kwarai akan yanda aka bari jinin Abba ya hau sosai, ya kuma ce anan zai riƙe shi har sai ya warware. Zulaihat kuka kawai take. Ya kammala rubutun ya miƙa mata takarda.
Har ta mike ta dawo.
"Dr don Allah ko za ka kira
min Munir a waya."
Likitansu ne, hakan yasa suka saba sosai da mutan gidan. Ya fiddo wayarsa ya dannawa Munir kira.
Shi kuwa Munir dama tun sadda ya dinga kiran wayar Abban ya ji ba'a dauka, ya fito ya taho bai ko damu da ruwa ba. Kwanciyar hank
alinsa daya, uayi tozali da Abban.
Ya na hanyar nufar gidan ne, kiran Dr Sunusi ya shigo. Da mamaki ya
ɗ
aga, maimakon ya ji muryar Dr Sunusi sai ya ji ta Zulaihat. Ba shiri ya gangara gefen titi kirjinsa na bugu ya
ɗ
aga.
"Hello Baban Yasmin,
Zulaihat ce."
"Meke faruwa Zulaihat? Ina Abba? Ya kirani ya yimin wasu zantuka marasa dadin sauraro."
Cikin kuka ta soma zayyane mishi dukkan abinda ke faruwa bayan fitar Dr daga dakin. Salati kawai ya ke, jiki na rawa ya katseta.
"Ganinan z
uwa Zulaihat, don Allah a ragu a asibitin. Ki ban Dr, kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba yanzu."
Ta amsa da to ta leka ta mikawa Dr Sunusi sannan ta yi gaba. Shi kuwa Munir ya jaddada wa Dr Sunusi cewa kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba daga nan suk
a yi sallama ya sauya location zuwa asibitin.
***
_*Bayan Cudewar Awanni*_
Safiya ce, garin ya yi sanyi kuma ya yi luf-luf kamar a lokacin wani hadarin ne zai hadu ruwa ya ƙara sauka kamar yanda aka kwana ana yinsa.
Kamar wacce laka ya f
ashewa a ciki, haka ta shiga taka barandar asibitin. Idan yaro zai yi mata kallo
ɗ
aya, nan take zai ayyana a ransa cewa mahaukaciya ce. Ga duk mai hankali kuwa zai ga tsantsar tashin hankali da damuwa cike fal shimfide a saman fuskarta.
"Mutuwa akai
mata da alama."
Ta tsinci muryar wasu mata a gefe, ba ta kallesu ba balle ta tofa. Ba kowa ta ke ganewa ba,ba kuma kowa take gani ba. Abbanta kawai take son sanyawa a idanu. Da shi ta kwana kuma ta tashi.
Hijabin jikinta duk ya cukurku
ɗ
e ya yi jirwa
ye na ruwan hawayen da ta dinga gogewa da shi. Silifas ne a kafarta na baƙin gidansu, ba ta san inda nata yake ba. Ta dai tuna da shi Hajja ta yi amfani wurin dukanta. Fuskarta yatsun Amrah ne kwance a samansu wadanda har yanzu basu baje ba. Tana fashin s
allah, wannan yasa ba ta kalli gabas ba balle fuskar ta ci darajar wanki. Ta dai tsarkake inda ya zamemata dole saboda kyankyami irin nata, ko ba komai kula da lafiyar jikinta ne. Ta shanye komai a awannin da suka biyo baya. Zagi, tsinuwa da ma duka, duk t
a dauka daga dukkan wadanda acewarta sun kai su yi mata su. Ta ji ta dau komai idan har za'a bar ta ta ji da abinda ke cin ranta.
Har ta iso dakin da Abba ke kwance tana tunani mai zurfi, ta gane dakin a dalilin hango Mijin Rafee'ah, Isma'il da ta yi
zaune a saman kujera, gefensa Yaya Munir ne su na magana.
Yaya Munir na kallonta tana kallonsa.
_"Ban yarda
ɗ
ayanku ya ta
ɓ
a lafiyarta ba, kar wanda ya tuhumeta akan abinda ta yi, ni da kaina zan auramata wanda take so. Na dauki laifina na y
i mata auren dole kamar yanda ta ce."_
Ya tuna kalaman Abbannasu a jiya ga Hajiya, Zulaihat da kuma shi Yaya Munir din. Sai dai ya yiwa kansa alkawarin babu shi babu Ramlat. Don haka ya kauda kai kamar bai ganta ba. Isma'il ne ya tsayar da ita suka ga
isa yana mata fadan ba ta kyauta ba, tsam Yaya Munir ya mike.
"Muje ga Rafee'ah ko?" Ya katse Isma'il. Hakan yasa shima ya mike suka tafi. Ta bisu da kallo idanun taf da kwalla sannan ta murda kofa ta shiga dakin Abban da sallama.
Babu kowa a c
iki sai Abban dake kwance ya yi shiru idanunsa biyu. Ya juyo ya dubeta, ga mamakinta murmushi ya yi mata. Ta sunkuyar da kai ta ji saukar hawayen da take riƙewa a saman kuncinta. Hannu ya miko.
"Zo nan Ramlatu."
Tana tafiya kamar a iska tsabar
ramar da ta yi ta zauna saman kujerar gefensa ta rike hannun sai kuka.
"Abba don Allah ka yafemin. Abba na tsani kaina, na kasa rankwafar da zuciyata na yi maku biyayya. Abba ka yafemin na tuba. Na shirya zama da Hilal kamar yanda ku ke so. Ku ce ya
maidani. Wallahi zan zauna."
Murmushi Abba ya yi, ya shiga girgiza kai.
"Kin ji nace ba zan ba ki Aliyu ba? Ko wani ne ya ce hakan? Ki yi shiru ki daina kuka, ni na yi laifi da na dage wurin yi miki aure da wanda bakya so. Ki yi hakuri ki yafemi
n kinji? Zan aura maki Aliyu cikin satinnan in sha Allahu. Yau zan koma gida ba zan ƙara kwana a asibitin nan ba. Idan har Khalid na raye, sai kin auri za
ɓ
inki. Ki daina kukan. Na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya yi maki albarka."
Ya ƙarashe da ra
rrashi, ta kasa gane zantukan Abban suka dosa. Ta kasa gane dagaske yake maganar ko kuwa mai harshen damo ne? Don haka ta bi umarninsa ta share hawayen. Ya dinga jan ta da hira har ta yi dariya. Hankalinta ya
ɗ
an kwanta. Amman maganar Abban ta shiga yawo
a kwanyarta cike da rashin gamsuwa. Maimakon ma ta yi murna, sai ta shiga firgici da kuma faduwar gaba.
Daga nan ta karasa dakin Rafee'ah, ba ta shiga ba, ta hango baby mai kyau dai, ta yi murmushi sannan ta koma ga Abban.
***
Kwana biyu da s
allamar Abba, ya sallami dukkan baƙi ƴan Daura, ya basu hakuri akan abinda Ramlatu ta yi. Daga nan ya tara iyalinsa ya tsawatar akan bai yarda ko maganar banza wani ya yiwa Ramlat ba.
Abba da mahaifin Amrah, da ma wasu a ƴan uwa, suka dunguma har
gidan su Hilal. Suka ba iyalinsa hakuri cike da nadamar abinda Ramlatun ta aikata don tuni sun ji abinda ta yi har ya saketa. Bai
ɓ
oye wannan ba. Wannan ya
ɗ
an sassauta ran iyayen Hilal, ko ba komai iyayen Ramlat sun nuna ba hannunsu. Basu nemi sulhun kom
e ba, koda sun nema iyayen Hilal sun yanke wannan alaƙar. Hatta Alhaji Aminu mahaifin Hilal wannan karon ya yi Allah wadai da irin Ramlatu. Toh Abban ma bai da ra'ayin komawarta.
Washegari kuwa kamar yanda suka nemi iyayen Aliyu, sai gasunan sun zo.
Ba
ɓ
ata lokaci Abba ya karbi sadakin ƴarsa. Nan aka daura auren Aliyu da Ramlat don duk wani bincike an yi ta hanyar Yaya Munir an kuma tabbatar daga Hilal har ita Ramlatun babu idda a kanta.
"Ga sadakin aurenki Ramlatu, na auramaki Aliyu. Ina fatan
wannan zai faranta ranki. Zai sa ki dawo da walwalarki. Ki kuma maido soyayyarmu a zuciyarki?"
Ta
ɗ
ago ta dubi Abba tana hawaye. Abban murmushi yake har hakoransa tana hangowa. Ita ya kamata ta yi irin wannan kalar fara'ar, sai ya kasance ita ce mai
kuka, Abban da mutan gidan na dariya.
Hajiya ma sosai ta sakarmata fuska.
"Ramlatu matar Aliyu. Allah Ya baku zaman lafiya."
Wannan ne kalaman Hajiyar kafin ta fita zuwa asibiti wurin Rafee'ah duba lafiyarta.
Ramlat ta shiga daki
ta zauna, ta yiwa kudin da Abba ya damƙamata kuri da idanu, abin mamaki su dinma jiƙasu ta soma da hawayenta. Ranar da ya kyautu ta yi rawa da juyi, ranar da ya kyautu ta fi kowa farin ciki. Abin mamaki kuma ya sanyata, kukan ta shiga yi kuwa iyakar ƙarfin
ta, koda za'a shaƙeta ba za ta ce ga dalili ba.
Ba ta da masaniyar cewa Mafarin kenan!!!
***
https://my.w.tt/iRW2CA35T9
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
15)
Kallo
ɗ
aya za ka yi mishi ka hango farin ciki tsantsa da walwala marar misaltuwa a saman fuskarsa. Sigari ya sanya a bakinsa yana zuƙa lokaci daya yana fesarwa. Ihu da kurantawa shi kawai ke tashi daga bakin maza da matan wurin.
"Cau ca
u Aliyu Angon Ramlat!"
Fadin G Baba. Hakan sai ya kara tunzura Aliyu har sai da ya zuƙe kara biyu cikin ƙanƙanin lokaci kafin ya kwantar da kai yana kallonsu ƙasa-ƙasa yana doka murmushi. Ko ba komai yau burinsa ya cika. Ko ba komai ya mallaki abinda
ya jima yana dakonsa. Ya na a jingine da kujera cikin club
ɗ
in, yana kallon yanda ake rawa da rausaya mata da maza. Duk ana yi don tayashi farin cikin samun cikar burinsa. Hannu ya zura a aljihu ya ciro bandir din dubu daya ya bude ya watsamusu. Aka hau k
wasa ana ihu da kara korantashi. Abin na mishi dadi. Wayarsa dake saman tebur ya duba, kira ke shigowa ba kuma na kowa ba sai na Granny. Ya mike tsaye ya yi musu bankwana ya
fice. Yau bai sha abin maye ba don ya fi son a yi komai cikin hayyacinsa ya gani.
Bai daga kiran ba har sai da ya bude sabuwar karamar motarsa Honda wanda Abulle ta sanya aka siyamishi ya shiga. Ya soma tuki a nutse kafin ya dauki waya ya kira Granny.
"Ina ka shiga wai? Ka zo mu tattauna game da lefen."
Ya yi murmushi g
ami da kara lumshe lumsassun idanunsa.
"Ina hanya Kakus, gani nan tafe."
Ya kashe kiran bayan ta mishi addu'ar zuwa lafiya. Ya kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Karfe tara da mintoci na dare. Buga sitayari ya yi gami da sakin
ƴ
ar ƙara da furta.
"Yes!!" Cike da nishadi ya kara gudun motar gami da ware ki
ɗ
a. Har ya isa gidan