Showing 15001 words to 18000 words out of 255051 words
"Wow, gaskiya Madam kin iya za
ɓ
e." Fadin ma'aikaciyar wurin.
"Allah Yasa ya burgeta." Ramla ta fadi da murmushin da ya fi kama da yaƙe don har yanzu kirjinta bai bar bugu ba tsabar kamannin da ta gani ƙarara na wannan mutumin da mijin Hajiya
.
Shi kuwa Alhassan banda murmushi ba abinda yake dokawa, iyakar burgewa takalmin ya mishi har cewa ya ke.
"Idan Tee ba ta so takalminnan ba to ba bulala za ta sha." Suka yi mishi dariya.
"In Sha Allah za ta so."
Daga fadin haka ta mik
e yana mata godiya, ta koma ga kayan maza hannunta rike da rigar da ta daukarwa Ummu. Sai da a kammala ta nufi wurin biya. Duk yanda ta nuna ba ta so hakan bai sa Alhassan fasa biyamata ku
ɗ
in kayayyakinta ba. A karshe godiya kawai ta yi, kusan tare suka fi
to kowa ya nufi motarsa suna kara yiwa juna godiya. Kallonsa take har ya bude mota zai shiga, hatta da tafiyarsu
ɗ
aya ce, a yanzu ta yarda su
ɗ
in ƴan biyu ne babu ko tantama. Har za ta tayar da mota ta ji maganarsa a gefenta.
"Mami, yi hakuri ki sany
amin number dinki, I promise you ina komawa garinmu zan kira na ba ki albishir takalmi ya burge
ɗ
iyarki. Kuma itama ina son ta miki godiya ko?"
Ta yi jim kamar ta ce a'a, ya kuwa narkar da fuska. Sai ta yi murmushi ta kar
ɓ
i wayar ta shigar da lambarta
. Ya kar
ɓ
a ya yi godiya suka yi sallama.
A hanya tunanin biyun masu kama kawai take yi wanda bambancin su fara'a da akasinsa. Banda wannan kamar ta yi yawa. Haka har ta isa gida tana zancen zuci.
https://my.w.tt/ub8deMQ0g9
🕯
️
*ƘARFEN
Ƙ
AFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem
06)
***
Tun fakawarsa a gaban ƙaton ƙyauren na gidan Muhammad Modibbo ya ji
ɓ
acin rai ya lulllu
ɓ
e dukkan wata walwalarsa. Ya kalli gidan, abubuwa da dama suka shiga dawowa
kwanyar Alhassan Aminu.
_"Tunda ubanku ya bijirewa umarninmu ya auri bare ai ko sata aka ce kun yi zan yarda. Har abada zuri'armu ba za ta kar
ɓ
i Uwarku ba balle ku da ku ke yaranta."_
Ya runtse idanu tuna kalaman babban wan mahaifinnasu da ya
yi. Ba don Dada ba ba zai ta
ɓ
a shiga gidan ba. Sai dai matsayi da girmanta ya zarta hakan.
"Sai yau ku ka tuna da ni?" Dattijon mai shekaru sittin da
ɗ
oriya ke wannan kalaman cikin harshen fulatanci sadda ya dubi Alhassan dake zaune a gabansa ya sunn
e kai. Murmushin yaƙe ya yi.
"Ba haka bane, ayyuka ne suka yi min yawa. Ayi hakuri."
Ya maida da harshen fillanci don Modibbo Hausar ba kasafai take fita ba.
"Ka koma, duk radda ka yi ritaya wurin aiki sai ka dawo a ci gaba da zumuntar." Da
ga haka Modibbo ya mike ya shiga
ɗ
akinsa. Idanun Alhassan suka ka
ɗ
a, dama yasan a rina! Bai ma tsammaci zai yarda su gaisa
ɗ
in ba. Ya mike gami da zaro hankicif a share goshinsa. Duba ya kai ga ƙaton enlargement din na yaran Mamman Gidado dake manne a falo
n, yaransa goma sha biyar cif har mahaifinsu wanda ke bi ma Modibbon. Ajiyar zuciya ya saki ya fice daga falon da sauri. Sashin matan gidan ya wuce, su biyu ne kuma duk daga zuri'a guda sai dai
ɗ
aya
ɗ
iyar wa,
ɗ
aya kuma
ɗ
iyar ƙani.
Ɗ
akin Uwargida Hajja Fa
tuma ya soma shiga. Kadahan-kadahan ta amsa mishi, wurin yaranta ne ya samu tarba sosai, bai yi mamaki ba don dama basu da matsala tsakaninsu su cousins.
A
ɗ
akin Hajja Amarya kadai ya samu shimfidar fuska, dama can ita ke mutunta su da
ɗ
an uwansa da
mahaifiyarsu.
Anan ya shantake har girki ya kwasa suna dariya karshe ya mata sallama ta bada turarukan wuta a kaiwa Dada sai na matarsa.
Yara yasa suka shiga da kayan lemuka da ya yo tsaraba, bai ko kara shiga ba ya ja motarsa. Washegari kuwa samma
ko ya yi ya bar garin Kano.
***
*ADAMAWA*
Tana tsaye jikin madubin
ɗ
akinta tana kokarin gyara zaman
ɗ
aurin
ɗ
ankwalinta. Doguwar riga kalar ruwan madara ta sanya wanda aka yiwa aikin paint work. Sauri-sauri take don tasan mijinnata na dab
da shigowa gidan dalilin waya da suka yi ya sanarmata ya shigo gari. Sai dai saurinta ya kusan haifar da nawa sakamakon hon dinsa da ta ji a bakin gate. Ba ta san sadda ta turo baki ba don ita kam a duniya ba abu mai wuya wurinta irin
ɗ
aura ƙaramin
ɗ
ankwal
i. Ta yi jifa da shi gefe ta koma wardrobe ta dauko karamin mayafin da ya dace da kayan ta fita. A falon suka ci karo, ya sakarmata murmushi gami da ajiye ledar saman kujera ya bu
ɗ
emata dukkan hannuwansa, aikuwa da sassarfa ta ƙarasa ta shige, ya maida han
nuwan ruf.
"Sannu da zuwa Abu Fatima." Ta fadi tana mai
ɗ
agowa daga jikinsa. Ya ja karan hancinta.
"Kema sannunki. Kin yi kyau sosai."
Ta yi godiya, daga nan suka fa
ɗ
a
ɗ
aki, ta taimaka ya yi wanka ya rama sallolinsa kafin su fito falon. M
iƙar da ƙafafunsa ya yi saman kujera ha
ɗ
i da kiran wash.
Ta
ɗ
aga ƙafafuwan ta zauna sannan ta
ɗ
ora saman cinyarta. Cike da tausasawa ta dubeshi.
"Sannu Abu Fatima, ka kwaso gajiya."
Ya lumshe ido da murmushi.
"Bari kawai Ummina, na sh
a tafiya ba ka
ɗ
an ba amman Alhamdulillah tunda na cimma nasarar abinda ya kaini. Zuba abincin."
Ya fadi yana mai miƙewa zaune bayan ya sauke ƙafafunsa. Yana cin abinci yana mata hirar diramarsa da Fatima. Banda dariya ba abinda ta yi.
"Ci gaba d
a biyewa yarinyarnan dai, watarana sai ta ba ka kunya. Hum, naga kokarin ma Matar da ta biyewa shirmenku."
Harara ya watsamata.
"Shikenan, kin ja wa kanki na fasa ba ki taki tsarabar."
Ta kama kunne tana murmushi.
"Na tuba. A yimin afuw
a."
Ya yi murmushi kawai. *Kausar* kenan, matarsa kuma ƴar uwarsa. Sun gina rayuwa ta fahimta, so da kuma kaunar juna. Ɗiyarsu guda a duniya Fatima, tun daga kanta Allah bai ƙara ba su haihuwa ba.
Sai washegari ya je gidan Dada, bayan sun gai
sa ya isar da sakon gaisuwar Modibbo da jama'ar gidansa gareta, ta ji ba
don ta yarda ba. Ya ba ta tsarabar da Hajja Amarya ta ba shi. Murmushi ta yi.
"Wannan kam na yarda." Shima murmushin ya yi bai ce uffan ba.
"Daddy takalmina." Fadin Fat
ima tana kara mannewa jikinsa gami da turo baki. Ya na dariya ya janyo leda, ya bude kwalin ya soma kokarin sanyamata a ƙafa.
"Wowww! Daddy ya yi kyau sosai."
Dariya ta basu shi da Dada.
"Sai ki zo ki yiwa Mamin Boutique godiya."
Ta
mike tana tsalle ganin yanda takalmin ya yi kyau a kafarta kamar wata balarabiya.
Ƙ
arshe ta rungume wuyan Uban tana magiyar a kiramata Mamin Boutique. Ba musu ya fiddo waya ya danna kira.
***
KANO
Misalin ƙarfe biyar da mintuna ne na y
ammacin ranar, dawowarta kenan daga wurin aiki ta miƙe ƙafa a falon cikin yayyunnata mata wadanda a ƴan kwanakin suke shigowa dalilin bikin A'isha da ya taho gadan-gadan. Rafee'ah ke riƙe da takarda da biro tana lissafin kayayyakin da ya rage a siyo a kasu
wa yayinda Zulaihat ke nunamusu wasu hotunan sabbin warmers ƴan Dubai a waya.
"Kai Maman twins, sun yi kyau sosai wallahi."
Fadin Ramla tana ƙara sanyo kai ta gefe ita da A'isha.
"Kyau ai ba
ɗ
aya ba Ramla. Nidai idan ma ba za'a siya
wa Auta ba ina so zan siya."
Fadin Rafee'ah tana ƙara kallon hotunan cikin santi.
"Kai Sis. Aa nidai ina so wallahi."
Fadin A'isha, ganin Hajiya ta kalleta sai ta ji kunya ta ruga
ɗ
aki. Dariya suka yi gaba
ɗ
ayansu. Daidai sadda ta ji ƙarar wa
yarta, ta koma mazauninta ta
ɗ
auka. Ganin baƙuwar lamba ne ya sanya ta yi mata ƙuri, sai dai tuna ko akan abinda ya shafi wurin aikinta ne ya sanya ta
ɗ
agawa da sallama.
"Waalaikumussalam wa rahmatullah Mamin Boutique."
Ta
ɗ
an yi shiru sanadin a
bu biyu, jin muryar namiji da kuma jin sunan da ya ambata.
"Sunana Alhassan Aminu, wanda ku ka hadu a Afrah Boutique dake kan..."
"Ayya sai yanzu na gane. Fatan kana lafiya?"
Ta katseshi da sauri ganin yanda ƴan uwan suka raba hankalinsu, w
ani a abinda suke wani kuwa a kallonta ana ƴar dariya ƙasa-ƙasa.
Suka ƙara gaisawa sannan ya miƙa wayar ga Fatima.
"Assalamu alaikum Mamin Boutique. Ina kwana."
Yanda yarinyar ta yi sai da ta murmusa don kuwa ta burgeta. Ta amsa mata, na
n yarinyar ta shiga zubamata hirar takalmi ya yi kyau Maminta ba za ta yi mata dariya ba. Ita dai Ramla ta biyemata, karshe Abbannata ya kar
ɓ
i wayar.
"Idan kika biyemata sai ku cinyemin ku
ɗ
in wayar ai."
Suka yi dariya kusan a tare, ya ƙara yi mat
a godiya ta bada saƙon gaisuwa ga mutan gidan daga bisani suka yi sallama.
"Mene?" Ta furta tana mai duban Maman twins da Rafee'ah.
"Kin fimu sani ai, har kin samu wani majnun
ɗ
in ba labari ko?"
Ta saki baki kawai ta kasa magana.
"Bar ta. Ni kai da naga ana shirin kasamin in law."
Hajiya ta dubi Maman twins.
"Wa kenan?"
"Baba Bashir yayan Baban twins mana, wanda matarsa ta rasu. To ai shi ne ya ga Ramlar kwanaki can ya nunan ana so. Maganar kenan da nake son nayi
da ita amma ƴar albarkar ba ta kirani ba, ba ta zo gidannawa ba."
Ramla ta ja guntun tsaki.
"Don Allah ku bar wannan maganar, shi fa da kuke ganin mun yi waya, takalmi ne na tayashi za
ɓ
ar ƴarsa shi ne dalilin da ya kira suka yimin godiya don tak
almin ya burge ƴar. Maman twins shi kuma Bashir ai kin ba shi lambata, sau
ɗ
aya ya ta
ɓ
a kirana kuma na
ɗ
aga mun gaisa na ba shi hakuri. Mai kuma zan daga kiransa ya kara cemin?"
Daga haka ta kwashi tarkacenta ranta na zafi ta kama hanyar barin falon.
"Ai fa, wannan zafin rai da taurin kan ba zasu ta
ɓ
a bari ki yi gaba ba Ramla. Ki dai bi sannu tunda yanzu ke mai ba wa wasu labari ce. Kinga dai makomarki."
Ba ta san sadda ta juyo gaba dayanta ba tana duban Rafee'ah wacce ta fusata. Ba dai t
a ce komai ba ganin Hajiya na tsawatarwa ta juya ta wuce ciki, sai dai kafin ma ta kai ga shiga dakin tuni ta soma fidda hawaye. Tana ƙarasawa ta rufe gam da muƙulli ta fa
ɗ
a saman gado. Ta yiwa kanta illa, tun ran gini tun ran zane, tana kyautata zaton dal
ilin ne yasa abu kadan ta aikata sai cibi ya zamo mata ƙari. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta ta fa
ɗ
a wanka. Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar jallabiya mai
ɗ
ankwali. Idanunta ya kai ga
ɗ
an akwatin mai kalar golden da ke ajiye saman mirror dinta.
Ƙarasawa ta yi ta bu
ɗ
e, wani envelope ta fiddo ta zauna gefen gado ta bu
ɗ
e. Hotunan ta ciro tana ƙaremishi kallo. Wani lokaci ta tuno wanda har abada ba zai gushe daga kwakwalwarta ba.
***
*MATAR MUTUM*
Tun tafiyar Hilal ta ƙara jin kewa ta
cika zuciyarta. A bangare guda ga tunanin Aliyu da ya zamemata abin yi safe da rana. Wannan ta sanya suna kammala zana jarrabawarsu ta zango na biyu a makaranta, (2nd term), ta tattara Abba ya kaita Yakasai ta yi hutun a can ko ta sami nutsuwa.
T
a ci sa'a kuwa jikokin gidan wadanda suka kasance sa'anninta duk suna nan suma. Aikuwa suna ganinta suka ruƙunƙumeta da murna.
"Oh yarannan shikenan kuma za ku hana bakinmu ya huta da bari-bari kamar wasu ƴan shekara hudu. Ai ko su A'isha sun fi ku h
ankali." Cewar Talatu ƴar kawun Abba wacce ta dawo nan da zama daga Daura.
"Bar su su yi son ransu Talatu idan ba so kike yanzu Hajja ta maidaki Daura ba." Fadin Abba yana dariya. Hajja dake taunar goro tana tayashi.
"A'a to, rabu da su. Wataran
sai labari duk suna gidajen aurensu."
Maganar Hajja ta ba su Ramla kunya, duk suka mike su ka yi
ɗ
aki har suna bangazar juna.
"Magulmata." Fadin Hajja cikin dariya. Abba ya shantake har da cin kwa
ɗ
on zogale kafin daga bisani ya yi musu sallama.
Washegari da misalin karfe uku na yammaci ƴanmatan su biyar, Usaina, Maryam, Jidda, Nafisa sai Ramla. Suka shirya suka fita zuwa gidan babban
ɗ
an Hajja Zulai, Kawu Kabiru don ziyara.
Tun kafin su fita titi Ramla ke mitar ita kam ba wacce za
ta dauka saman cinyarta sai dai su yi abin hawa biyu.
"Kai Mrs Hilal, don
ɓ
arnar ku
ɗ
in mota?" Fadin Jidda tana auna abinda zasu kashe daga Yakasai zuwa Zoo road.
"Aa fa, da gaskiyar ƙawalli, ba zan yarda nima na
ɗ
ora kowaccenku a cinya ba, k
e kuma Jidda idan har za ki iya hawa bayan kujera shikenan."Fa
ɗ
in Usaina.
Ta ƙasashe suna dariya don ita kanta ta fa
ɗ
a ne, a ƙiba kam duk Jidda ta fi su.
"Allah Ya kiyaye." Cewar Jidda.
Aikuwa dai sai rabawa suka yi, kusan a tare suka sa
mu abin hawa, Ramla da Usaina su biyu kacal a adaidaita sai Jidda, Maryam da Nafisa wuri guda.
Sai da suka kusa Zoo road ya samu fasinja. Sallama ya yi ya shigo, kusan da sauri ta dubeshi. Shi ne, shima yana zama ya kai duba gareta. Duk da yanda ta
yi saurin kauda kwayar idanunta gefen Usaina wannan bai hanashi ganeta ba. Ta ƙara matsawa jikin Usainar ganin yanda jikinsu ke
ɗ
an gogar juna. Murmushi ya yi ya matsa ta yanda ya san za ta fi sakewa.
Bai ce uffan ba banda murmushin da yake faman dok
awa, abin mamakin shima Zoo road ya nufa. A hankali ta kai duba gareshi ta cikin karamin gilashin
ɗ
an sahu. Kwayar idanunsu ya sarƙe da juna ta yi azamar janyewa. Ba ta ƙara gangancin kallonsa ba, mutumin da take kwana da tashi da tunaninsa. Kirjinta bai b
ar bugu ba, ba ta fahimtar zantukan da Usaina ke yi.
"Sauka mana." Ta ji muryar Usaina karo na biyu, sai sannan ta dawo nutsuwarta ta dubi gefenta, tsaye ta hangoshi a waje yana sallamar mai adaidaita. Ta kauda ido ta fito, Usaina na bayanta.
"Ɗauka har da nasu." Ya furta ga
ɗ
an sahun.
Nan suka ce a'a, ya rantse shi zai biya, Ramla na shirin jan musu ta ji Usaina ta
ɗ
an bugi kafa
ɗ
arta alamar ta yi shiru. Godiya suka yi mishi, hango su Jidda sun tsaya ya sanya Usaina nufarsu.
"Ra
mlat."
Ta tsaya cak gami da juyowa ta dubeshi, ba ta yi mamakin jin ya ambaci sunanta ba don Usaina ta kira sunan ya fi a ƙirga cikin adaidaita. Ya
ɗ
an matso ka
ɗ
an.
"Karo na biyu Allah Ya yi ha
ɗ
uwarmu. Tun sadda na sanyaki a idanuna har yau bani
da sauran sukuni. Wallahi ina sonki!"
Ya furta fuskarsa na nuna alamar gajiyawa da kuma gaskiyar abinda ke ransa.
Ta matse yatsun hannunta jin yanda kirjinta ke bugu, ta
ɗ
an kuramasa idanunta da suka cicciko da kwalla. Shima kallonnata yake d
a nashi mayun idanun wadanda tuni sun dulmiya cikin tafkin kauna da shauki.
"Ayya ka yi hakuri Malam, wallahi an sakamata rana. Nan da shekaru uku ba ka
ɗ
an bikinta."
Kalaman Usaina ya maidota hayyacinta, ta tsinci bakinta da maimaita abinda aka
ankarar da ita.
"Eh, an sanyamin rana. Ka yi hakuri."
Ya yi murmushin yaƙe. Ya dubi Usaina.
"Kaicon wanda zai yi wasa da damarsa. Akwai kuskure a jan lokaci har haka. Watakila kuma rabon Aliyu ce. Ina muku fatan alheri."
Ya dubi Ra
mla da fuskarsa wacce ta yi narai-narai.
"Matar mutum Ramla, matar mutum.."
Daga haka ya juya ya bar wurin. Ramla ta tsaya kamar wata mutum-mutumi. Kafa
ɗ
arta aka jijjiga.
"Ke dillah can! Mene hakan? Waye shi? Ko kin manta da sanya ranar
da ke kanki? Ke Usaina waye shi?"
Duk Nafisa ke wannan kalamin daidai sadda suka ƙaraso, zantukan ƙarshe sun sauka saman kunnuwansu.
Tuni ta soma tafiya kanta a ƙasa, tana ji Usaina na basu labarin abinda ya faru suna jan tsaki da kiran kwalel
ansa. Can kuma ta ji suna ko
ɗ
a iya
ɗ
aukar wanka da kuma kyan da Allah Ya mishi daidai gwargwado. Ta shiga tariyowa.