Showing 39001 words to 42000 words out of 255051 words
babu wanda ya san damuwarsa, tun yana kokarin dannewa har ta soma fitowa fili. Kullum kamar ana ƙaramasa sonta, har yau bai yarda ba ta sonsa ba. Asiri ko tsafi ba abu ne da ya yi amannar su na tasiri ba a k
oyaushe, sai dai haka kawai yake zargin sauyawarta da cewa asiri ne. Yana sonta, ba ya jin kuma zai iya rabuwa da ita. Zai jure dukkan kunci da tsananin da zai fuskanta daga gareta.
Yasan muddin ya tunkaro gidansu a haka, babu
ɓ
ata lokaci Mahaifiyars
a za ta gano damuwar dake kwance saman fuskarsa, don haka ya yanke shawarar zuwa ga Yayarsa wacce ko ba komai za ta sanyashi dariya, mace mai raha da kirki. Idan kuwa aka
ɓ
atamata rai, mutum sai ya toshe kunnensa daga habaici da bakaken maganarta.
Gy
a
ɗ
i-gya
ɗ
i, anan gidan Anti Fareeda yake. Yayarsa ta farko a wurin iyayensu. Daga ita sai Murja kafin kuma shi.
Da yaranta ya soma cin karo, hangame baki ya yi ganin ƴaƴan Murja, Hanan da Ammar suma a gidan. Wannan ya ba shi tabbacin itama Murja na gidan.
Duk yanda ya so kaucewa kar su gane damuwarsa hakan ya faskara, akwai shakuwa tsakaninsu, kamar yanda kuma suka saba magancewa juna su yi su binne ba tare da kowa ya ji ko ya gani ba. Basu da dadi su duka idan an ta
ɓ
osu. Don haka ya za
ɓ
i ya
ɓ
oye abi
nda ke tsakaninsa da Ramlat.
"Yanzu kai Hilal ka kyauta? Kasan ina kasuwanci shi ne ka tsallakeni ka damƙa ragamar lefe ga Bilki? Abinda ka yimin a wurinka shi ne daidai?"
Murja wacce ba ta fiye barin magana a cikinta ba ta kasa hakuri sai da ta
fesar duk kuwa da idon da Fareeda ke mata akan ta yi shiru. Ya
ɗ
ago ya dubeta.
"Nayi zaton duk daya muke. Amma ki yi hakuri wallahi ban kawo komai ba, na yi amfani da cewa Billy tana tare da su, za ta fimu sanin ra'ayin Ramlat. Na tuba kaina bisa wu
ya don Allah."
Harararsa kawai Murja ke yi, Fareeda ta cafe zancen tana murmushi.
"Ai sai ki yi hakuri, ya fiki gaskiya. Bilkisu da mu duk abu daya ne. Wannan ba karya, kuskuren da kike ganin ya yi miki Allah Ya ba ki hakuri Yaya Babba."
Suk
a yi dariya, anan ne yake musu batun service dinsa tunda result ya fito.
"Ai kai auren gata za'a yi maka, ga gida ga mata ga kuma kudi shaƙe a account dinka. Banda kai, wa Baba zai yiwa haka?"
Fadin Murja cike da zolaya, suka yi dariya gaba daya
.
"Shi fa kadai ne namiji, ke kuwa mene ba zai gani ba? Allah dai Yasa ka kammala service cike da sa'a kaima ka tsaya da kafafunka."
Murmushi ya yi, zamansa da yayyunnasa ya mishi amfani kwarai, ko ba komai kaso tamanin cikin damuwar da ya ƙunso
sun ragu.
"Naga Amaryartaka ma ta sauya,
ɗ
an kiran da take mu gaisa ta bari. Idan na kira wayarta kuma a kashe. Naji Umma ma ta ce ta jima rabon da su yi waya."
Maganar Murja kenan karo na biyu wanda ya katse tunaninsa. Nan da nan ya basar.
"Af na manta ma, yanzu haka daga asibiti nake an kwantar da Abba ba lafiya amma da sauki. Ita kuwa Ramlat jarrabawa ce ta sa Hajiya kar
ɓ
ar wayarta."
Duk suka sanya salati cike da jimami kafin su yi fatan Allah Ya ba shi lafiya. Ya jima sosai suna tat
taunawa game da biki tare da ƴan uwansa kafin ya fice.
***
Washegari da karfe hudu na yamma aka sallami Abba ya dawo gida, hakan bai hana wasu cikin abokan kasuwancinsa zuwa
dubiya ba. Hajja ma ba'a bar ta a baya ba, ta dinga fadan meyasa ba'a sanar
mata da wuri ba. Dakyar aka lalla
ɓ
ata.
"Jiya fa aka kai shi Hajja. Kiyi hakuri don Allah." Cewar Yaya Munir da ya gaji da mitarta.
Ya mike tsaye, ya dubi Bilkisu da ta zo dubiya, sai raba ido take cike da burin sanin meke faruwa har haka, sai da
i babu wanda ta ga alamar zai fadamata.
"Mu wuce."
Maganar Yaya Munir ya katse mata tunani, ta mike ta kara yiwa su Hajiya sallama sannan ta bi bayansa suka tafi. Ta saka a ranta sai ta san meke faruwa a gidan.
Bayan da kowa ya watse ne Haj
iya ke labartawa Hajja halin da ake ciki, Hajja ta hau salati ta sa aka kira mata Ramlat.
"Yanzu ke Ramlatu wa zai
ɓ
ata ran iyayensa saboda son zuciya? Anya kina da hankali? Yaron da koyaushe yabonsa muke, yana zuwa har gida ya gaishemu? Inace kwanaki
har Daura kika cemin ya je an gaisa?"
Ta maida akalar zancen ga Hajiya dake ji kamar ta mur
ɗ
e wuyan Ramlat din kowa ya huta.
"Hakane ya je."
"Ahaf, irin wannan yaron kike so mu watsawa ƙasa a ido? To ba ki isa ba! Don ƙaniyarki a farko wan
i ya ce ki kawomana shi ki ce kina so?"
Maimakon ta samu goyon baya irin wadanda kakanni ke yiwa jikokinsu, sai ta ga sa
ɓ
anin hakan. A barta ma ta ji da abinda ke damunta, a barta ta ji da rashin ji da ganin Aliyu. Gobe ne take da jarrabawa wanda daga
shi takarda biyu ta yi musu saura su kammala duka, ko ta halin ƙaƙa a goben sai ta yi yanda za ta yi ta ha
ɗ
u da shi.
Rankwashin da ta ji a ka yasa ta farfadowar ba shiri.
"Don ƙaniyarki shine ina magana kika yimin shiru?"
Ta
ɗ
ago rinannun idan
unta da suka fa
ɗ
a ta dubeta hakan ya yi daidai da zubar ruwan hawayenta, to me za ta ce? A yanzun wa ya ke ta ita a gidan? Wa ke damuwa da ci ko shanta? Hakanan Indo za ta kawo abinci ta maida ba ta ko kalla ba, da ta gaji da horar yunwar don kanta ta yiwa
kanta fada take ci duk kuwa da cewa ba wani dandanonsa a bakinta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ke Ramlatu, ashe zan ga rana irin haka? Wane zamani muke ciki ne da yara kana musu magana amma hankalinsu na can wani wuri? Ina rabaki, ina rabak
i da namiji! Matukar kika bari ki ka shiga hannunsa sai kin manta hanyar garinku."
Hajja dai har ta yi ta ƙare ba abinda Ramlat ta ce sai kuka, Hajiya don takaici ma tashi ta yi ta koma wurin mijinta wanda ya samu bacci. Sai a sannan Ramlat ta mike ta
na share hawaye rai a
ɓ
ace.
"Ni dai don Allah ki kyaleni Hajja, wannan fa rayuwar aurena ce, idan kuwa kun matsa na auri Hilal, za ku tarar da gawata a gidansa."
Daga haka ta sa kai ta bar falon inda Hajja ta yi sokoko tana bin ta da ido don ita
lamarin ma tsoro ya ba ta. A haka Hajiya ta risketa, ganin ba Ramlat a wurin yasa ta sanin inda zancen ya dosa, ba ta kai ga zama ba Hajja ta dubeta.
"Wai ni Rabi'atu, kina yiwa yarannan addu'ar neman tsari kuwa?"
Wani murmushi Hajiyar ta yi.
"Hajja kenan, idan dai lamarin wannan yarinyar ne toh ki kwantar da hankalinki. Ta yi nisan da ba ta jin kira, ba kuma ta jin maganar kowannenmu. Don haka mun zubamata ido, idan an yi auren ma je mu yi mata sutura a miƙata gidanta na gaskiya. Kinga ai sa
i ta girbi abinda ta shuka sannan."
Hajja ta san halin diyarta idan ranta ya
ɓ
aci don haka sai ita ba ta ja zancen ba, banda Allah Ya kyauta ba abinda ta ce.
***
Cikin sauri-sauri ta shirya cikin uniform ta fito, Hajiya na falon ta gaidata. Ko
kallo ba ta samu ba balle kuma ta amsa.
"Na tafi."
Nan ma ba amsa, idanun Ramlat suka cicciko da kwalla, ta mike ta kama hanyar fita.
"Idan bamu isa da ke ba, idan ciwon da kika jazawa mahaifinki bai isheki darasi ba. Ki je ki hadu da Aliyu a
yau, sai dai ki sani idan magana ta shiga tsakaninku ban yafemaki ba."
Ji ta yi kamar an zaremata dukkan lakar dake jikinta, an kashe duk wata ga
ɓ
a na jikinta. A hankali ta juyo ta dubi Hajiyar. Itama Hajiyar kallonta ta yi.
"Kin raina karfin al
aƙar da ke tsakanin uwa da abinda ta haifa ko? Ko kina dauka shekarun da muka yi a duniya mun yi su ne a wofi? Ki gyara lamuran rayuwarki, lokaci bai ƙuremaki ba Ramlat, kar duniya da abinda ke cikinta su ru
ɗ
eki, kar ki wannan kuskuren."
Ta tsinci kan
ta da furta toh kafin ta juya ta soma tafiya tana bitar maganganun Hajiyar, masu sauki a baka sai dai kuma nauyinsu wane dutsen dala. Hawaye take har dakyar take ganin gabanta, a karshe ta share, ta kuma daukarwa rai da gangar jikinta alƙawarin za ta kiyay
e haduwarta da shi, za ta daure.
Amrah ta tareta sadda suka fito daga jarrabawa. Ɗago kai ta yi tana kallonta. Tausayin Ramlat ya sanya hawayen da take riƙewa tun ganinta da ita a safiyar ranar, ya soma tsiyaya.
"Haba Ramsy, ki tausayawa kanki ki
tausayawa rayuwarki da tamu don Allah. Kin sauya kin koma wata daban da bamu sani ba. Kin illata walwala da farin cikinmu da kuma naki, akan me? Allah da Ya halicci soyayya bai halicci hakuri da dangana ba? Ko kuwa kin fi karfin ki rungumi ƙaddara kamar k
owane bawa? Ballantana ina da tabbacin muddin kika zauna da mutum irin Hilal ba za ki ta
ɓ
a dana sani ba."
Wani murmushi mai ciwo Ramlat ta yi gami da
ɗ
an kauda kai kafin ta kara dubanta.
"Ita soyayyar ba ƙaddara ba ce? Ko kin manta cewa bawa bai
isa ya
ɗ
orawa kansa abinda Allah bai
ɗ
ora mishi ba? Hakuri ana yinsa idan bakin alƙalami ya riga ya bushe, sai dai nawa
alkalamin har yanzu a jiƙe yake. Na dauka idan duk duniya za'a ha
ɗ
a kai a ƙi goyon bayana, banda ke Amrah. Sai ki ka shayar da ni mamaki
, ki ka kara fahimtar da ni nisan alaƙarmu, kin bada tazara ba ka
ɗ
an ba. To ki sani, yanzu na soma son Aliyu, kuma in sha Allah zan zama mallakinsa ko ba jima ko ba da
ɗ
e."
Daga haka ta gifta ta wuce itama tana nata sharar hawayen. Amrah ta bi ta da ka
llo cike da kara jin tsanar Aliyu har cikin ranta, babu irin haka da ta ta
ɓ
a faruwa garesu sai a kansa.
"Da yardar Allah ba za ki ta
ɓ
a auran Aliyu ba Ramlat, wannan Aliyun ba alheri ne ga rayuwarki ba."
Ta furta a fili.
***
Ga Ram
lar kuwa, tana fita ta yi turus, ta kasa koda motsi don gani take kamar mafarki, Aliyu a makarantarsu?
'Kema kinsan zai iya faruwa, mutumin da ba ya ji kuma ba ya ganinki?'
Fadin wani sashi na zuciyarta tana mai ci gaba da kallon Aliyun dake tsa
ye ƙasan wata itaciya a kofar makarantarsu. Shima ita ya zubawa idanun, kamar yanda ta rame shima haka ya rame. Ta shiga kalle-kalle, sai da tabbatar babu alamar an taho daukarta kafin ta soma yunkurin tsallakawa. A gaggauce ta isa wurinsa ta tsaya suna ka
llon juna, abubuwa biyu suka fa
ɗ
omata a rai lokaci guda. Na farko dokar makarantar da ta hana tsayuwar ta
ɗ
i, muddin aka lura da hakan to fa za'a
ɗ
au mataki. Na biyu zantukan Hajiyarta da suka fi komai tsayawa a ranta. Sai ta soma ja baya, ga samu ga rashi.
Ya yi nasarar riko gefen hijabinta, a dole ta tsaya ta kuma juyo sadda ya saki.
"Ba zan iya hakura da ke ba, ke din nake so Baby. Zan iya jure komai saboda na aureki. Rashinki kwanakinnan yana wahalar da zuciya da gangar jikina. Me zan yiwa Abba ya
so ni? Kamar yanzu ba kya tausayina kema, kar ki manta na sadaukar da komai saboda ke. A dalilinki na rabu da Muhibbat,
bana kula kowace mace. Kar ki sakamin da auren wani ba ni ba, ba zan jure ba."
Duk zantukan tana jinsu har ƙwaƙwalwa, ji take inama
za ta iya cewa wani abu, sai dai ba za ta sa
ɓ
awa Hajiya ba. Dabara ta fa
ɗ
omata, a gaggauce hannu na rawa ta sauko da jakarta a baya sannan ta durkusa ta ciro takarda da biro. Shima bai yi ƙasa a gwuiwa ba wurin durkuson, maimakon abinda ta maida hankali w
urin yi (wato rubutu), sai ya maida hankali wurin kallo da karantar yanda ta rame idanunta suka zurmuƙa ciki. Siririn karan hancinta ya ƙara fitowa, ji ya yi inama yana da damar da zai iya daukemata hawayen da suke bin karan hancin zuwa baka. Ta kammala ru
butun ta miƙa mishi takardar, ya karba yana dubanta har suka mike a tare. Dakyar ta iya juyawa da sauri yana kiranta ba ta ko waigo ba. Tasan a hakan ma ta sa
ɓ
a umarnin Hajiyarta, dole kuma ta nemi gafara. Ta taki sa'a har za ta koma cikin makaranta wata t
a kirata wai an zo daukarta. Ta juyo da azama za ta nufi mota, Amrah ta hango tsaye a wurin Aliyu tana mishi magana shi kuwa yanzu ya bada baya maimakon a farko da yake kallon gaba. Hankalinta ya tashi, sai sannan ta kula da wanda ma ya zo daukarnata, Abba
nta ne. Ba damar ta je garesu, ganin kaifafan idanun Abban a kanta ya sa dole ta bude motar ta shiga.
Ita kuwa Amrah sosai ta ja wa Aliyu kunne akan ya rabu da kawarta.
"Ka raba ta da iyayenta, ka raba ta da mutumin da zuciyarta ta soma so a dun
iya. Me kake nema haka? Ance ba za'a ba ka ita ba, meyasa ba za ka hakura ba? Ka daina bibiyarta, ba don na zo na zama katanga tsakanin fuskarka da na mahaifinta ba, da yau ban san halin da ganinka zai jefashi ba."
Sai a sannan ya fahimci dalilin zuwa
n yarinyar da kuma dawowarta
ɓ
arin da dole zai juyo. Manufarta ta burgeshi sai dai kalamanta sun ba shi dariya hakan yasa shi murmusawa.
"Ban ta
ɓ
a ganin Amrah ba sai yau, duk kuwa da cewa kafata ta taka kofar gidansu ya fi a kirga a dalilin Baby. To b
a zan yi mamakin kalamanki ba, amma ina so ki sani. Daga ni har Ramlat, Allah ne Ya ha
ɗ
a soyayyarmu. Ina mai ba ki hakuri sai dai ki yiwa yar uwarki uzuri, shi so ba ruwansa da komai, ki mata uzurin halin da take ciki yanzu. Ba yin kanmu bane. Addu'arki it
a ce abin bukatarta da ni dinma a yanzu, abu daya kawai nake so ki rike a ranki. Wannan dai banzan Aliyun, idan Allah Ya ƙaddara shi ne mijin Ramlat, babu mahalukin da ya isa ya tsayar. Na bar ki lafiya."
Ya wuce ta bishi da kallo, takaici biyu. Wato
dai ba zai saduda ba, a gefe kuma ta tuna sadda ta ambaceshi da banza. Amman ai ba ta furta a gabansa ba, hakan na nufin Ramlat na ba shi labarin duk wani abu da aka ce game da shi. Wani wawan tsaki ta ja tana mai jin kamar ta samu Ramlat din ta yi mata du
kan kawo wuƙa.
***
_*Ba zan iya ce maka uffan ba bisa alkawarin da na dauka sanadin Hajiya ta, ina kaunarka Sweet Aliy, har gobe kai ne za
ɓ
ina. Ka sa a ranka babu mai yimin dole, babu shi. Ko an yi ba zan zauna ba. Zan fito kawai domin na aureka. Na
maka wannan alƙawarin. Abba bai da lafiya, an kai shi asibiti yana da hawan jini, a yanzu dole za mu
ɗ
an yi hakuri mu rage ha
ɗ
uwa. Don Allah ka dinga cin abinci. I love You._*
Ya ninke takardar ya zura a aljihu, son wannan yarinya ba zai kashe shi ba.
Kai tsaye gida ya nufa wurin Abulle.
"Kai Zakina, kana kuwa cin abinci? Wannan uban ƙashin wuya? Kodai so kake a maido maka da matarka yanzun nan na kira Babanta na tursasashi?"
Ya ja guntun tsaki gami da shafar suma. Kwantar da kai ya yi jikin
kujera ya lumshe ido. Nan da nan Abulle ta sa aka kawo mishi abinci.
"Maza ci wannan daga gidan Babanka Alƙali ne, irin wanda kake so."
Abincin gidan Justice kusan ya fi kowanne dadi wannan ta sanha jikokin ke rububi idan an aikowa Abulle. Ita k
uwa
ɗ
an gaban goshinnata take ajiyewa.
A dole ta sanyashi a gaba ya dinga ci kamar mai tauna magani. Karshe ma ya ture kwanon.
"Ni fa aure zan yi."
Nan da nan Abulle ta washe haƙora.
"Kai Alhamdulillah, ko kai fa. Wa ka samu?"
Ya
runtse ido.
"Wacce nake so iyayenta ba sa sona. Sun mata miji, kuma itama nan duniya ni take so."
Nan da nan ta daure fuska.
"Kar dai wacce Babanka Abdussalam ya ce iyayenta sun aiko nemanka akan ka fita hanyarta?"
Ya dubeta sosai, sai
kuma ya daure fuska.
"Na meye za'a dinga yawo da zancen kuma? Wannan kuma ya zama terere. "
Abulle ta yi mishi daƙuwa.
"Nace karbi nan, don an fadamin shi ne terere? Kai yanzu ba abin kunya bane ma a ji wai kana son yarinya an turo a yi maka
kashedi don ka rabu da ita? To ahir dinka! Ka rabu da ita tun wuri kafin ka jawomin ƙananun magana cikin gidannan."
Ya ta
ɓ
e baki, shi kam ba wanda