Showing 105001 words to 108000 words out of 255051 words
lumshe idanu. Yana bukatar tunani, sai dai tunanin ya jima da gushewa. Duk kokarinsa, duk irin yaƙin da yake da zuciya da kwakwalwarsa, sun kasa ba shi ha
ɗ
in kai. Kamar yana a
ka saba ne ya afku, matsanancin ciwon kai wanda ya sanyashi hakurin dole ya miƙe ya haye sama.
***
Tun ƙarfe takwas na dare farfajiyar ƙawataccen Event Centre din na Marhaba, ya cika ya batse da yan mata da samari matasa sai tsirarun iyaye. Kwalli
ya iri-iri kawai ka ke gani. Wasu tuni suka shige dakin taron yayinda wasu suka tsaya ƙyam jiran saukar Amarya da Ango. Tana daga can gefe tsaye cikin wani arnen baƙin lace, ta
ɗ
ora silver head. Ummi kadai ce ta biyota wurin taron, zaman
ɗ
ankwalinta take g
yaramata tana fa
ɗ
an muddin ta ƙara cirewa sai dai ta nemi mai
ɗ
auramata don ita ba baiwa ba ce.
"Ni kuma bawa ne, na yarda na amince idan har ƙarƙashinki zan yi aiki zan yi din koda ba biya."
Tun soma maganar ta juya tana kallonsa. Ya ha
ɗ
e cikin
wata gogaggiyar shaddarsa ruwan ƙasa, murmushi kawai ya ke yana dubanta babu ko kyaftawa.
"Uncle Hilal!" Fa
ɗ
in Ummi kafin ta fisge jikinta daga na uwar ta yi gaba a guje ta rungumeshi. Ya durkusa yana mai
ɗ
ago fuskarta yana dariya, dariyar ba ta kom
ai ba ce sai na ganin yanda Ramlat ta ha
ɗ
e fuska don Ummi ta tafi ta bar ta da
ɗ
ankwali a hannu wanda ya warware gaba daya sai jerin ƙananun kalbar da aka yi mata ke yawo a iska.
"Kin ƙara yiwa Mami laifi. Kinga."
Ya yi mata nuni da Ramlat, gan
in haka Ramlat ta kauda kai bayan ta watsawa Ummin harara, ta rufe motarta ta jefa muƙulli jaka ta nufosu. Ganin hakan yarinyar ta tsorata ta yi bayan Hilal da sauri gami da fadin.
"Mami please ki yi hakuri, sunan Hajiya fa ne da ni."
Kusan da ha
kan ta saba cin galabarta, Ummi akwai wayo da saurin ba da hakuri bisa laifi. Kusan dariya ta basu daga ita har Hilal din. Ya mike tsaye bayan ya yakice Ummi dakyar a jikinsa.
"Ba za'a yi mata afuwa ba?"
Ta
ɗ
an harareshi tana murmushi, ya lumshe
idanu ya budesu a kanta, sai kuma sannan ta farga da kato
ɓ
arar da ta yi, ko meye na yi mishi murmushin? Da saurinta ta kauda kai ta soma tafiya da nufin barin wurin. Riƙon da ya yiwa
ɗ
ankwalin Ummin ne yasa ta kallonsa, kasancewar ya tarkata dukkan nutsuw
arsa a kanta yasa kai tsaye idanunsu suka sarƙe cikin juna, ta yi saurin janye nata idanun.
"Ana kallonmu fa."
Ta furta a ƙagauce, zuciyarta har zafi ta soma. Takaici da haushin kanta ne ke mamayeta. Wani sashi na zuciyarta ihu yake mata, yana
mata tunin bai kyautu ace har ta mance baya ba. Bai kyautu ta saurari kowane namiji ba, ko ba komai ta yiwa kanta alƙawarin gudanar da rayuwarta babu aure, ta raini yaranta har su zamo abin alfaharinta duniya da lahira.
"Lah, Yaya Hilal?" Kusan a ki
dime ta kai duba ga mai maganar, Salma ce tare da Halima. Zuwan su Halimar kenan ta ha hannunta don ta yi mata hotuna.
"Ramlat?" Fadin ita Halimar. Lokaci guda Hilal da Ramlat suka dubi juna kafin ta kauda kai da sauri ta sakarmasa
ɗ
ankwalin Ummin ta
yi gaba wurin Halima. Murya na rawa ta ce.
"Ha..lima., yaushe ku ka zo?"
Halima wacce a farko bakin cikin hadadden gayen da ta gani tare da Ramlat ke tafarfasa zuciyarta, ta ji wani sanyi jin da ta yi Salma ta ambaceshi da Hilal, wato shi ne da
i wanda Ramlat ta gujewa aurensa.
'Marar rabo.' Ta fadi a ƙasan ranta, a fili kuwa murmushi ta yi tana wani ƙwarkwasa a sonta ta burge Hilal.
"Bamu jima da zuwa ba, ashe kina nan kina tsinkar fure. Ki ce shiyasa ki ka ƙi sauraron Oga. Kina da z
azzafa a hannu."
Kalaman Halima wanda da biyu ta yi, ya kara baƙantawa Salma rai, ta karasa ga Hilal a zafafe. Ita kuwa Ramlat kallon ba ki kyautamin ba ta watsawa Halima ta yi gaba, Ummi ta rarumi dankwalin ta bi uwarta a guje tana kiran ta
ɗ
auramata
.
Salma kuwa ta dubi Hilal cike da bakin ciki.
"Yaya kar dai ka cemin ka dawo a karo na biyu zawarcin Ramlat? Duk abinda ta aikata gareka ka mance?"
Daure fuska ya yi yana kallon yarinyar da duka-duka ba ta dade da daina yoyon majina ba,
a cewarsa.
"Ke, yaushe muka soma ƴar haka da ke? Sa'anki ne ni?"
Ta ƙara tur
ɓ
une fuska, zarginta dai ya tabbata. Tasan idan ta kara magana to zai iya yi mata duk abinda ya so, wannan ne dalilinta na juyawa fuu ta ja hannun Halima su bar wurin a f
usace. Ta kuma rantse babu mai dakatar da ita daga fa
ɗ
awa su Anti Fa'iza da Murja, ko ba komai ta hanyarsu saƙon zai fi saurin isa kunnen iyayen Hilal wa
ɗ
anda suka rantse ko bayan ransu basu yarda da aurensa da Ramlat ba koda hakan akwai yiwuwarsa. Wannan
rantsuwa ce da umarni da suka faru tun Ramlat na gidan Aliyu, tun sadda ta fusata zuƙatan iyayensa.
A
ɓ
angaren Ramlat dakyar ta samu ta maido walwalarta sai dai ko yaya ta waiga ta hangi Halima manne da Salma sai ta ji wata irin fa
ɗ
uwar gaba, a baki
n Naja'atu Azare take jin ashe sun san juna tun suna B.U.K. Jin hakan bai ƙare ta da komai ba sai ƙarin fargaba.
Ana kammala dinner, Ango Hisham ya wuce da Amaryarsa gida don dama sai da aka kai ta sannan aka taho Dinner. Daren ranar baccin Ramlat ra
bi da rabi ne, tunaninta me zai biyo baya don ta tabbatar dole Salma ta sanarwa Halima wani abin da ya danganci rayuwarta ta baya, tana ganin kiran Hilal da text dinsa akan yana so su yi magana koda ta mintuna ne amman ta ƙi
ɗ
agawa, a ƙarshe ma ta kashe wa
yar gaba daya.
"I am sorry Hilal." Ta furta a fili yayinda wasu zafafan hawaye suka zubomata ta
ɗ
aukesu da tafin hannu.
***
Ta shiga ofis dinsu da sallama tana mai duban abokan aikinta.
"Yau dai Hajiya Ramlat kin so makara."
Ta yi
murmushi tana duban Salihu mai wannan furucin, ko kusa ba ta son jaye-jayen wasa hakan yasa ta wucewa bayan ta gaida kowa ta zauna a mazauninta. Matan ta duba da mazan da suka halarci daurin aure ta yi musu godiya da fatan Allah Ya kara dankon zumunci daga
nan ta maida hankali ga wani aiki da Oga Ɗalhatu ya ba ta tun wancan satin.
Ta dukufa wurin aiki, Ofis ya cika irin cikar da ta tsana, wato ƴan wasu ofishin su shigo nasu domin hira, wannan yasa tunda ta sunkuyar da kanta ta wasu rubuce-rubucenta a
computer ba ta
ɗ
ago ba, kamar yanda ta daure fuska kamar ba ta ta
ɓ
a dariya ba musamman ganin har da Oga Ahmad wanda ke kokarin sanyata a hirar tana ƙi. Babban abinda ke ba ta mamaki wasu cikin matan ma da aurensu amma yanda suka zage kamar ba auren a kansu
. Kamar da wasa ta ji Halima ta zage tana bada labarin da nan take ya sanyata gumi duk kuwa da irin sanyin Ac da ke ka
ɗ
awa a
ɗ
akin.
"Toh ai yanzu zamanin ne ya sauya. Soyayyar da ƙarfi da yaji ma kwatarta ake yi Oga. Sai na tuno da labarin wata da ak
a bani, ranar da aka kai ta ta nemi kashe Angon saboda ba ta sonsa, aikuwa ya saketa ta auri za
ɓ
inta amma fa ta ci gidansu. Duka, zagi ba wanda ba ta sha ba. A karshe dai yanzu sun rabu, ta na nan kuma ta dawo tana bin shi saurayinnata na farko kamar jela,
kai ka ce karyar da ta hango ƙashi, nema take ƙarfi da yaji sai ya aureta."
Bu
ɗ
ar bakin Oga Ahmad ya ce.
"Ai wallahi ta yi ka
ɗ
an don ubanta! Wannan ma an yi ƴar iskar gaske. Au sai da ta ga rayuwa za ta dawomin?"
"Ni kuma da ni ne, zan aur
eta ko don na koyamata hankali. Sai na sa ta raina kanta fiye da yanda wancan na farkon ya rainata."
Fadin Salihu kenan har da cire hula hira ta yi dadi.
Abin sai ya koma kamar muhawara, wannan ya kawo nashi, waccan ta kawo. Halima ta saci kallo
n Ramlat yanda nan take ta fice hayyacinta, ta kauda kai tana wani irin murmushi, ji take kamar nan duniya ba ta ta
ɓ
a samun farin ciki da walwala kamar ta ranar ba.
Zaman ofis din ya gagareta, ta tabbatar idan ta ci gaba da zaman to fa ru
ɗ
un da ta sh
iga zai bayyana kowa ya gane. Tsalam ta mike gami da daukar jakarta, hannunta har rawa yake ta zura takalminta da ta cire don kafafun su huta kai tsaye ta nufi hanyar fita.
"Ah, Ramlat ina za ki je kuma? Da sauran lokaci fa a tashi."
Fadin Halim
a kamar ta daka tsallen murna, Ramlat ta juya ta watsamata wani banzan kallo ita kuwa ta murmusa gami da kashemata ido
ɗ
aya. Wannan ya kara ba Ramlat tabbacin da gayya ta yi. Tana sane ta yi mata abinda ta yi din.
"Ba ta ko saurari kiran da wasu ci
kin ofishin ke mata ba, ta bude kofa ta fice. A hanyar baranda suka ci karo da Ogansu Ɗalhatu. Ya dubi agogo, sauran bai fi mintuna talatin ba a tashi.
"Ramlat, tafiya? Lafiya kuwa?"
Ta dubeshi dakyar, ba don ya zamto shugaba ba a gareta, za ta
iya giftashi kawai ta wuce don yanda ta ke jin kanta. Yaƙe ta yi.
"A yimin afuwa Oga don Allah, ban jin dadi dauriya nake."
Cike da tausayawa ya ce.
"Assha, sannu. Allah Ya ba ki lafiya. Ko dai na sanya a kaiki?"
Ta girgiza kai.
"A'a zan iya tafiya ba komai. Nagode."
Zai kara magana tuni ta giftashi ta wuce da sassarfa. Sai dai tun kafin ta karasa ga motarta, hawaye sun wankemata fuska, hannu na rawa dakyar ta iya bude ƙofar motar ta shiga. Kuka sosai ta ci fuskarta cikin may
afi, dakyar ta iya dauriyar share fuska ta yi ribas ta fita.
Rabin tuƙin yinsa take yi ba'a nutse ba. Abinda ta ke gudu ya faru, a hankali abinda ta shuka ya soma fitar da tsirrai, tana tsoron ya fidda ƴaƴan da zasu nuuna har nata ƴaƴan su samu rab
onsu. Tun ba'a je ko'ina ba, komai ya soma bayyana. A yanzun da tsoro ya shigeta, tana ji a ranta za ta iya barin aikinta idan har hakan zai tseratar da mutuncinta da na yaranta a idon duniya. Za ta killace kanta a gida.
'Kin manta cewa watan watarana
dama sai rana makamancin wannan ya zo? A gidan a tunaninki kin tsira?'
Ta hau gyada kai kamar ƙadangaruwa kamar mai ganin zuciyarta a fili.
"Zan tsira, yarana ba zai shafesu ba tunda ba su da laifi! Ni mai laifin a yimin kowane irin zagi zan ju
re!"
Tana maganar a fusace ita daya a mota, ba ta yi aune ba ta kai dab da dab da wata mota, duk kokarin ganin ta ci burki hakan ya faskara har sai da ta daki bayan motarsa. Masu salati na yi hakanan masu fadin kai! Kai! Suma suna nasu.
Luguden
da zuciyarta ke yi ya ƙaru,
ɓ
acin ranta ya ninka na farko. Ta kasa koda motsi, ta kasa fitowa balle ta je ta ba mai shi hakuri ta nemi gafararsa.
'Da ka san damuwar da ke cikin zuciyata, da ka yimin uzuri kamar irin wanda na ta
ɓ
a samu a wajen wani...
'
Ta kasa ƙarasa zancen zucinta ganin wacce ta fito daga mazaunin kusa da direba. Shakka babu fuskar ba ranar ne farkon ganinta da ita ba. Fuskar da ta zo har ofishinsu.
"Isa da taƙama za ki nunamana?! Kin yiwa motata illa kin zauna kin hakimc
e ko gezau? Ke ƴar gidan uba wace ce?!"
Sanin da ta yi ita din mai laifi ce yasa ta fitowa daga nata motar, har lokacin akwai hawaye a fuskarta. Wannan hargagin na Hajiya Zeenatu bai dameta ba kamar yanda sanyo ubanta ciki ya yi mata zafi, ko ba koma
i shirunta ya jazamata.
"Kiyi hakuri don Allah." Ta fadi tana ha
ɗ
iyar yawu, damuwar da ke ranta ma ya isheta. Kowa ya yi mata caa akan ba ta kyauta ba yayinda Hajiya Zeenatu ta dage akan lallai sai ta raina kanta, sai ta biya
ɓ
arnar da ta yi mata.
Ramlat kallonta kawai ta ke sakaka, ita ta ma rasa me za ta ce da ita. Hakuri kawai ta ke bata don ba ta jin yin fa
ɗ
an musamman a yanzun da ta ke jin tsanar kanta har cikin ranta.
Basu yi aune ba sai jin ƙarar murfin mota suka yi, hankalinsu y
a kai gun. Kowa kallonsa yake har ya ƙaraso yayinda Ramlat ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, ba ta ta
ɓ
a zaton wani abu zai ƙara sa ta ganshi ba. Yanzun kan ta yi amannar ba zai kyaleta ba sai ta biya
ɓ
arnar da ta yi musu, ko ba komai yanzun zai ce da gayya ta
ke mishi ta'adi.
Shi kuwa koda ya ƙaraso kallonta ya yi na ƴan sakanni, kallon sani ya yi mata, kallon na ganeki. Ta kauda kai shima ya kawar, kallon da ya kai Hajiya wuya, ta daga hannu da nufin marin Ramlat, caraf ya riƙe hannun. Jama'a aka saki ba
ki don diramar ma tafiya yanda ya kamata, an baza baki da hanci, go slow kam sun ha
ɗ
a, masu zagi na yi, masu tsayuwa kallo suna nasu aikin.
Hajiya ta dubeshi a fusace.
"Ita yar iskar ina ce za ta tsaya tana ƙaremaka kallo?! Dama nasan ai da b
iyu ta bugi motar! Na ganeta! Ba ita ce wannan marar kunyar ba ta Revenue? Za ki san ki ta
ɓ
oni!"
Daga haka ta fisge hannunta ta yi gaba, Ramlat na hawaye ta ke kallonsa. Bakinta ya yi nauyi, dakyar ta motsa.
"Ka yi hakuri. Wallahi ba da gangan
na aikata ba."
"Ba komai." Ya fadi ƙasa-ƙasa, daga nan bai ce uffan ba ya wuce ya shiga mota ya ja suka bar wurin. Itama motarta ta shiga tana ji wasu na fadin.
"Ke kam Allah Ya so ki da rahmarSa. Tab!"
Wasu kuwa cewa suke.
"Ina rahm
ar? Ba ku ji me Hajiyar ke fadi ba? Da alama ta san ma'aikatar yarinyar, za kuwa ta yi mata sanadin barin aiki."
Ita dai Ramlat wacce kanta ke bala'in sarawa, ta ja motarta dakyar ta bar wurin.
Koda ta isa gida, Hajiya ta tambayeta abinda ya far
u ganin yanda ta yi kaca-kaca, idanunta jage-jage da hawaye. Ba ta
ɓ
oyewa Hajiyar komai ba. Ranta ya
ɓ
aci.
"Ai ga irinta nan! Ga irin ABINDA AKE GUDU nan Ramlat! Shekara nawa da wucewar abu, yanzu gashinan yana bibiyarki. Ita kuwa wannan Hajiyar a z
atonki za ta kyaleki ki ƙara taka ma'aikatarku? Uhm, Allah Ya kyauta."
Daga nan Hajiya ta yi shiru tana huci, ta tausayawa Ramlat amma fa haushinta ba ta da matakin dauka, ba ta da abin yi don kuwa Ramlatun ce ta fara
ɓ
atawa kanta suna. Har Ramlat ta
yi
ɗ
aki ba ta ce mata uffan ba.
Ta kudurce a ranta za ta bar aiki, sai dai kuma ta ya za ta dinga wasu cikin hidindimunta har ta taimakawa gida da yaranta?
Ta mirgina saman gadon gami da lumshe ido. Can kuma ta bu
ɗ
e su cikin zurfin tunani. Y
a yi daidai da dawowar yara daga islamiyya, gaba daya suka shigo
ɗ
akinta suna mata sannu da zuwa. Tana murmushi ta mike zaune.
"Kun dawo?"
"Eh, yau Affan bacci ya yi ta yi a aji." Cewar Ansar, Affan kuwa ya yi lamo jikinta, ta shafi kan yaron
tana murmushi.
"Wai haka?"
Ya gyada kai, bai iya ƙarya ba ko don tsoro. Suka cikata da surutu, dakyar ta korasu su wuce chanja kaya.
Aliyu ya fa
ɗ
omata a rai, mutumin da ya bar duniya bayan ya yi kyakkyawar shahada, shi ne ake jefamata b
akar magana ake yayata abinda ta aikata dominsa?
'Ko me ya faru, laifinki ne.' Ta shiga gyada kai tana gaskata sashi na zuciyarta dake tunasar da ita hakan. Shakka babu laifinta ne. Dakyar ta samu ta shafe babin a kwakwalwarta ta mike ta shiga wanka
. Ta san ƙaryarta ta iya barin aiki saboda Hajiya Zeenatu. Addu'a ya fiyemata komai. Shi ne makamin kowane mumini.
***
"Aikin banza! Kaima ai kallonta ka tsaya yi! Akan wane dalili?"
Hajiya Zeenatu ke wannan kalamin, tun dawowarsu gida duk i
nda ya saka ƙafa sai ta bishi da zafafan kalamanta na zargi. Idanunsa suka ka
ɗ
a, zai shiga wanka ta nufi kofar ban
ɗ
akin.
"Wankan me za ka yi? Wato ba ka ga girman laifin da ka aikata ba ko? Shi ne har za ka shiga wanka?! Wallahi ka jawowa yarinyarnan
! Sai nayi