Showing 78001 words to 81000 words out of 255051 words

Chapter 27 - KARFEN KAFA complete

like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad http

s://my.w.tt/HMV9ZSdNmab

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

22)

"Ba zan yi shiru ba saboda wannan wulaƙanci ne! Ka wulaƙantani da abinda ke cikina. Haba Aliyu! Sai ka ce ba kai ka min cikin

ba? Wai dama soyayyar da kake yimin a baki ne? Wane zaƙin kalamanka ne ban ji ba akan

ɗ

anmu na fari kafin na shigo gidanka? Wannan shi ne tukuicin son?"

Ta ƙarashe kamar za ta fashe da kuka, idanun sun ka

ɗ

a tsabar baƙin ciki da

ɓ

acin rai.

"Mtsw

. Soyayyar ta ci uwarta! Soyayya ta wuce wanda na nunamaki a shimfi

ɗ

a? Inace yanzu tukuicin son ne a cikinki? Da ace bana haihuwa ni bansan ma irin gorin da za ki yimin ba. Ramla abinda zan iya siya kenan, banda arzikin da ya fi hakan, idan kuma sata kike

so na yi ni Aliyu ba

ɓ

arawo bane, na zan fara a kanki ba. Ko yau kasuwa ta tashi ai

ɗ

an koli ya ci riba. Har mamakin ma yanda kike kokarin sauyamin tunani nake wallahi, bani da tabbas ko kin soma bin malaman tsubbu. Ina mamakin yanda wataran nake bin ra'ay

inki na aikata abinda ban yi niyya ba. Dadin abin Babana Malami ne, zan bazama neman tsari."

"Yau kuma shirka kake zargina da aikatawa? Kodayake ba ka da laifi, ko me ka aikata laifina ne da na nace akan aurenka. Dama kyakkyawar damina daga bazara aka

n gane ta! Aliyu wannan bakin cikin ya isheni, na gaji da shaƙarsa. Aliyu kai da abinda ya shafeka bana sonsu, ka sauwakemin na koma na yiwa iyayena biyayya ko zan ga haske a rayuwata. Na jima ina nadamar aurenka, yau kam na gaji. Na hakura da kai ko kai k

adai ne

ɗ

a namiji a duniya."

Wata dariya ya yi mai ban haushi da ya sanya hawayen da Ramlat ke dannewa su

ɓ

ucewa ya zubo. Ya shafi fuskarta ta buge hannun ta ja baya tana sheshsheƙa.

"Baby, wallahi kinji rantsuwar

ɗ

an musulmi ba wanda ya isa ya ra

bani da ke. Aurena da ke mutu ka raba. Kar ki ji ina batun wai bana sonki, ba zan iya rabuwa da ke ba har abada. Kiyi hakuri dai mu ci gaba da lalla

ɓ

awa a haka. Maman Baby kuma Baby."

Daga haka ya soma tafiya zai bar

ɗ

akin, ta yi wani irin zabura ta b

i bayansa ta rike rigarsa ƙam ta baya idanunta har rufewa suke yi.

"Sake ni Aliyu. Domin Allah ka sakeni!"

Ta zame ta durkusa a ƙasa mararta na tsunkulinta. Ya dubeta ya ja tsaki.

"Wai Baby kin san tsinuwar Allah da Mala'ikun da kike jawowa

kanki bisa wannan furucin? Baby na fadamaki ba zan sakeki ba. Ban aureki don na sakeki ba har abada."

Ta ci gaba da kuka sosai, ya fisgi rigarsa ya yi gaba ya kyaleta anan. Sai da ta yi mai isarta kafin ta mike jikinta duk ya yi mata nauyi ta zauna ge

fen gado tana faman tunani.

Kayan ta kara kallo ta kauda kai. Ba ta da ko sisi a hannunta balle ta fitar ta siya abinda ya dace, idan kuma ta bar kayan da Aliyu ya kawo ita ce da jin kunya a asibiti. Don haka ta mike ta tafasa ruwan zafi ta kawo ta j

iƙasu.

Tunani sosai ke daukarta ranta na suya, tana kokarin yin takatsantsan adalilin kulawar da aka ce ta yi saboda muddin ba ta yi wasa ba za ta kamu da hawan jini. Mararta na kara mur

ɗ

amata. Ta yi kokarin tashi ta wanke kayan sai dai ta kasa.

Abu kamar wasa tun yana yi yana lafawa har ya soma yin tsanani. Aka yi Magriba, Isha'i ta zo ta gifta, ba labarin Aliyu, cikin kuma bai bar ciwo ba.

Juyi kawai take tana salati, cikin taimako na Ubangiji wayarta ta dauki suwwa. Ta kai hannu ta daga ba

ta tsaya duba sunana ba ta sanya a kunne.

"Assalamu alaikum."

Daga jin muryar Abbanta zuciyarta ta karye, shi kuwa ya kira ne ya yi batun bude account na banki da ya ce ta yi, ta soma kuka ba ta ko iya amsa sallamar ba.

"Ya Salam, Ramlatu?

Lafiya kuwa?"

"Abba cikina, ciwo yake min."

"Ina shi Aliyun?"

"Ya fita."

Ta amsa murya na rawa.

"Kwantar da hankalinki, yanzu zan turo Rabi."

Bai tsaya sauraron komai ba ya katse kiran. Ta yi jifa da wayar.

Awa daya na

ta rufa ba ta ji ana kwankwasa kofar gidan. Kuka kawai ta sanyawa ji take kamar ba za ta iya takawa ta je ta bude ba.

Hajiya ce ta kara kiranta a waya.

"Lalla

ɓ

a ki zo ki bude Ramlatu, daure don Allah "

Ta amsa dakyar sannan ta mike, dakyar

ta iya ganin inda ta ajiye mukullin, tana tafe idan ya mur

ɗ

o sai ta tsaya cak tana salati, koda ta je kofar kasa zura mukullin ta yi ballantana ta bude.

"Ranki ya dade zuro mukullin ta ƙasa kawai, sai na bude."

Ta ji muryar direban Hajiya. Daky

ar ta iya daga hannun ta tura mukullin, ya bude Hajiya ta shigo hankalinta a tashe ga Indo mai aikinsu a bayanta. Suka kamata zuwa cikin mota.

"Kayan haihuwa fa?" Hajiya ta tambaya. Nuni kawai ta yi da cikin gidan, tana so ta kai karar Aliyun ba dama.

Abinda take gudu ne zai afku. Hajiya ta koma ciki, a saman gadon ta hango ledar kaya da taimakon hasken nepa da suka kawo wuta. Ɗagawa ta yi ba ta ko tsaya dubawa ba ta fito.

A mota suna tafe ta tambayeta.

"Su ne kayan haihuwar?" Kai kawai ta g

yada tana kuka.

"Eh su ne Hajiya. Wash Allahna."

Suka shiga jeramata sannu, Hajiya ta kira Abba a waya ranta a

ɓ

ace amma ta danne.

"Alhaji na ce a kirashi a fadamasa mun yi asibiti da ita, naƙuda ce."

Abba ya amsa da toh.

Tana so

n sanarmasa cewa basu wani siya kayan haihuwa ba amma ta yi shiru. Sai da suka karasa asibitin da Ramlatun ke awo kamar yanda ta fadamusu sunan, aka kar

ɓ

eta aka shige Labour room da ita. Nurse ta nemi a bada kayan haihuwa ta miƙamata.

Koda ta bude ta

dubesu, kafin ta yi magana Hajiya ta amsa.

"Yi hakuri yanzu za'a kawo sauran, rudewa ne."

Ta

ɓ

e baki kawai Nurse din ta yi tana murza ido don bacci ma ya soma daukarta. Hajiya ta dubi Indo.

"Indo ki tsaya ina zuwa.,"

Ta amsa da toh.

Kai tsaye Hajiya gidan Ramlat suka koma, har sannan Aliyu bai shigo ba, kayan Ramlat din ta dauka kala biyu da kuma undies ta sanya a leda ta fita don ba ta kaunar ma ta ha

ɗ

u da surukinnata.

Sai dai me? A farfajiyar gidan suka yi kici

ɓ

us ya shigo y

ana busa karan sigarinsa. Yana ganinta ya

ɗ

an russuna ya gaidata ba tare da ya jefar da sigarin ba, ya dai cire a bakinsa ya riƙe a hannu.

Hajiya ta ji kunya da takaici sun rufeta, sai da ta ji inama wata can cikin dangi ta kira ta tsaya a lamarin Ra

mlatun ba ita ba. Duk cewar da ake yana shaye-shaye ba ta zaci rashin kunyarsa akai ya kai wannan gejin ba.

"Yauwa lafiya kalau. An fadamaka tana asibiti ko?"

"Eh yanzu zan taho."

"Allah Ya taimaka."

Abinda ta ce kenan ta yi gaba. Ya b

i bayanta da harara cike da

ɓ

acin rai, wato Ramlat har ta san ta kira gida ta ce tana naƙuda amma ta ƙi sanarmishi? Don ba shi da kudi ya talauce shi ne za ta mishi tonon silili a duniya.

"Idan naje asibitin Allah Ya tsinen." Abinda ya furta kenan bay

an ficewar Hajiyar gami da jan tsaki da nufar ciki. Wanka kawai ya yi ya sauya kaya gami da nufar club.

Hajiya ba ta nufi asibiti ba sai da ta soma biyawa wani Nassarawa ta yi amfani da kudin da Abba ya bata ta rike ko za'a buƙaci wani abu ta siya d

uk abinda ya kamata na jariri bisa umarnin Abban wanda daga baya ta ga dacewar ta fadamasa. Ya jinjina lamarin ba ka

ɗ

an ba.

***

"Alhamdulillah." Abinda Hajiya da Indo suke fadi kenan sadda suka tsinkayi muryar jariri na tsala kuka. Nurse ta fito d

a fara'arta kamar

ɗ

azun ba ita ke yatsina ba.

"Hajjaju ga fa kishiyartaki ta fito duniya."

Murmushi Hajiya ta yi ba ta amsa ba sai Indo ce ta amsa da Barka Barka.

***

Abba ya yi farin ciki sosai da jin batun haihuwar Ramlat, idar da

sallar nafilarsa kenan yana mai roƙamata sauƙi da rangwamen naƙuda a wurin Allah. Ya yiwa kaf yan uwanta har Munir text ya sanarmusu da haihuwarta. Babu wanda bai kira ya tayashi murna ba, Munir bar wa cikinsa komai ya yi ya kira Abban ga mishi murna da t

ayashi farin ciki.

Abba ji yake kamar ba'a ta

ɓ

a haifamasa jika ba.

"Allah Ka shiga lamarin Ramlatu, Ka yafemata kura-kuranta. Allah Ka dubeta da dukkan rahmarKa. Ka rayamata abinda ta haifa."

Ya furta a fili yana kara jinjina lamarin Aliyu

da aka ce bai taka ƙafa ya je asibitin ba.

***

Ta bude idanunta tar bayan ta fito daga wanka inda ta kimtsa jikinta da taimakon Indo. Dinki ciki da waje aka yi mata, azaba kam ta sha ta godewa Allah. Idanu ta ƙurawa jaririyar tana kallo, so da kaun

arta na ratsa dukkan sassan jikinta. Ta kauda kai ganin Hajiya na kallonta, murmushi kawai Hajiya ta yi ta cigaba da murje dukkan dau

ɗ

ar jikin yarinyar. Yanzun ne ta siyo bahon wanka har da gado mai net na jarirai.

Aliyu bai zo ba, kuma bai kira ba,

wannan ya fi komai ta

ɓ

a zuciyar Ramlat. Ta fakaici idanunsu ta zubda hawaye. Wuraren karfe biyu Hajiya ta yi niyyar tafiya gida, Abba ya ce ta zauna ta kwana babu damuwa. Idan ma wani abu ne ita Indo ta dawo gidan saboda A'isha. Ta yi zamanta tana jinjina

irin kaunar da Abba ke yiwa Ramlatun, ko Uwani (Zulaihat) mai sunan Hajja uwar riƙonsa ba ya yi mata hakan.

***

"Wai ke mijinki ba zai zo ba? Ki kirashi ki ce an sallameki."

Hajiya ce ta gaji da jiran gafara Sa ba ta ga ƙaho ba ta karya bill

e ta yi magana. Ramlat abin ya jima yana ci mata tuwo a kwarya, daidai da Abulle da wasu a dangin Aliyun sun zo ganin jaririyarta amma banda uban gayyar. Idan ta kira har ta gama ringing ba zai

ɗ

aga ba, a karshe ma saƙo ya turomata ta waya cewar wallahi ƙa

farsa ba za ta taka asibiti ba tunda ba shi ya kai ta ba. Wadanda suka kai ta su zamemata gatan su biya duk abinda aka kashe. Idan ma ta ga dama daga asibitin ta wuce gidannasu ba shi da kudin ciyar da ita da abinda ta haifa. Talaka ne Aliyu. Wannan shi ne

saƙonsa.

Ta ƙara kallon Hajiyarta, tasan abin ya yi mata ciwo ne kuma ta gaji ne ta yi magana. Zulaihat da Rafee'ah suna gefe suna cin abinci ba wanda ya ce uffan.

"Hajiya ya ce ba zai zo ba."

"Ba zai zo ba kamar ya? Me yake nufi da ha

kan?"

Ta sunkuyar da kai tana fidda hawaye don ita wulakancin Aliyu har mamaki yake bata, kamar wanda aka shiga tsakaninsu.

"Uhum, Allah Ya kyauta."

Fadin Zulaihat kenan, Rafee'ah ta amsa da amin. Yau ne zuwanta na farko asibitin ita kam,

hakan ma don Hajiyar ta kira ta mata tas a waya ne.

"Kenan suna ma bai shirya ya yi maki komai ba?"

Ba ta ko iya amsawa Zulaihat tambayarta ba, bakin ciki da kunya sun rufeta.

"Wannan abun ya yi yawa, wannan wane irin jahilci ne ke daw

ainiya da shi?"

Hajiya ke wannan sababin, har ta yi ta gama ba wanda ya amsa a yarannata don su kam gani suke ai dama wanda bai ji bari ba zai ji hoho.

***

Da yammaci bayan an yi sallama, Ramlat ta yi mamakin yanda Hajiya ba ta kara ce mata u

ffan akan Aliyu ba. Ba ta kuma san yanda aka yi aka biya kudin asibitin ba, ta san dai ba Aliyun ba ne. Ta tattara suka wuce gidansu da ita. Hakan ya fi komai yi mata dadi, idan ta juya ta dubi jaririyarta a hannun Rafee'ah, sai ta ji wani sanyin dadi ya r

ufeta. Ta lura ko ba komai yan uwanta na son yaranta kawai ita din da Aliyun ne basa kauna. Duk kauce kaucen Rafee'ah ta yi ta kyale ta hakura ta karbi yarinyar.

Har suka je gida ba wanda ya tayar da zancen Aliyun.

Daki guda aka bata da

ɗ

iyar

ta. Hajiya da kanta ta dauki jaririyar ta kai wa Abba.

"Masha Allah." Ya furta yana murmushi.

"Kamar Ramlatu tana karama." Ya fadi gami da duban Hajiya. Murmushi ta yi maganar Aliyu na cinta sai dai ta bar wa cikinta tunda Abban ya ce a rabu d

a shi a zubamasa na mujiya.

"Wane suna suka za

ɓ

amata?" Fadin Abban yana kallon Hajiya ganin bai fi saura kwanaki biyu ya rage sunan ba.

"Ina ya

ɗ

aga wayarta balle ya fa

ɗ

a? Sai dai a tambayota."

Abba ya murmusa, Hajiya dai ko yaya abu ya

ɓ

ata ranta sai ta san yanda ta fitar ko yaya ne.

"Tambayota."

Ya fadi kai tsaye.

***

Ramlat ta dubi Hajiyarta. Ita kuwa wa take da shi sama da Hajiyar yanzu? Iyayenta sun mata komai duk da irin tokar da ta ba

ɗ

amusu a idanu.

"Kin

kuramin ido, ko shima sunan sai kin tambayeshi?"

Hajiya ta furta a zafafe.

"A sanyamata Rabi'atu."

Hajiya ta

ɗ

an yi shiru sai kuma ta fita. Kamar ta ce ba ta son jinin Aliyu da sunanta sai kuma ta share.

Tana fadawa Abba ta yi daki ta

kyaleshi yana dariya. Kai tsaye ya yiwa yarinyar hu

ɗ

uba.

***

Ranar suna komai da aka yi Abban ne karfinsa. Daga gidan Aliyun an kawo kayan barka, kamar yanda Abban ya ce, ba su nuna komai ba suka karba duk kuwa ba kayan a zo a gani bane.

Y

arinya ta ci sunan Hajiya su na kiranta da Ummi. Hajiya tun tana kawaicin har ta saki ranta dalilin kaunar yarinyar da Allah Ya doramata. Balle kuma Abba wanda koyaushe tana hannunsa idan yana gida.

Wannan gatan kadai ya

ɗ

an rage damuwar Aliyu a ra

n Ramlat, ta dai yi rama ta kuma yi duhu. Amrah na zuwa lokaci zuwa lokaci musamman daga makaranta, tana koyawa Ramlat abinda aka yi a ajin. Yaya Munir bai leƙo gidan ba koda wasa sanin da ya yi Ramlat din tana nan. Bilkisu kam zuwanta biyu gulma na kawot

a, duk irin habaici da za ta yi ko bakar magana, Ramlat ba ta kallonta balle ta amsa. A nan ma ta ke jin batun auren da Hilal zai yi, kai tsaye ta ce Allah Ya sanya alheri ta share batun wanda ba haka Bilkisun ta so ba.

***

Aliyu ba waya kuma

bai zo ba har suka cika kwanaki arba'in cif a duniya. Kamar daga sama kuma suna cikin kwanaki sittin a gidan Hajiya, sai ga Aliyun.

"A kyaleshi, ban yarda a nunamasa wani abin ba. Wanda ya yi nagari, kansa. Ba yanda kika iya ke kuma, sai hakuri."

Abban ya fadi bayan ya je ya yi magana da Aliyu, hakuri kamar koyaushe shi Aliyun ya bada ya kuma ce ba zai kara irin kuskuren ba kamar dai alkawarin da yake yi a baya idan magana ta zo kunnen magabata. Tuban muzuru kenan tunda ba ya fasawa.

"Toh

Abba." Cewar Ramlatu idanunta cike taf da kwalla. Ta mike tana gyara zaman mayafinta, bisa umarnin Abban ta je su gaisa da Aliyun kafin a sanya ranar komawarta.

***

Yana falon saukar baƙi ya yiwa jaririyar ƙuri da idanu, sallamarta ya sa shi

ɗ

agow

a ya kalleta. Gaba dayansu sun yi kewar juna. Ta kauda idanunta tana jin tsanar kanta da irin son da take yiwa wannan halitta.

Bayan ta gaidashi ya matso jikinta sosai.

"Baby dubi yanda rashinki ya ramar da ni. Baby ina miki Laifuka, wallahi k

i sani, bansan ya zan yi na yaƙi wannan fushi da zuciyartawa. Kin fi kowa sanin ina sonki, ina son abinda kika haifarmin. Takaici da bakin cikina, kiran da kika yi waya a gidanku a kaiki asibiti amma kika kasa kirana. Haba Baby, kinsan ba ki kyauta ba."

Ta kalleshi da niyyar gasamishi bakar magana, sai dai hawayen da ta gani a fuskarsa ya kashemata jiki. Ya kwantar da kansa a kafa

ɗ

arta. Ta runtse idanu, wutar so da kaunar Aliyu na kara dagula lissafinta, yana don cin galaba a kanta kamar koyaushe. Ta

ɗ

an ja jiki za ta matsa, ganin haka ya

ɗ

ago yana kallonta.

"Baby, wayo kika yimin. Ummi kamar ki ta dauka sak. Amma ta fi ki dimple mai kyau."

Ya ƙarashe yana sanya yatsansa dai dai inda ke lotsawa a kumatunta. Itama ta kurawa yarinyar ido, kaun

arta na ratsata. Suka kasa kauda idanu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login