Showing 45001 words to 48000 words out of 255051 words
Sai dai mahaifinsa mutum ne mai magana
ɗ
aya, yanda ya dage akan ba wanda ya isa ya hanashi aurawa Hilal abinda yake so, hakan ya kashe
bakin kowa sai ƙananun magana da ba'a rasawa wurin mata.
"Ina wuni Anti Bilki."
Ta gaisheta ciki-ciki don yanzu ba wani mutunci suke ba.
"Lafiya kalau Laila ta Majnun."
Sanin cewa magana ta ya
ɓ
amata ne yasa ba ta ce komai ba.
"N
i na rasa abinda Hilal ya gani ya maƙale maki alhalin yanzu ba kya ta ta shi. Wallahi mata hudu ya so zai iya aura a lokaci guda. Amma da yardar Allah ko ya aureki sai mun mishi aure."
Cewar Anti Bilki tana mai kwantar da Yasmin a saman tana jijjigat
a don ta yi bacci. Ramlat dake shirin tayar da sallah ta dubeta rai a
ɓ
ace.
"To ko hakan za'a yi? Ki tambayeshi wanda ya nacewa wani tsakanin ni da shi. Nace bana so, bana yi, wai dole ne?"
Ta ja tsaki ta fice daga dakin zuwa can bayan gidan wuri
n ciyayi ta zauna tana aikin kuka.
Ita kuwa Bilkisu ranar wuni ma ba ta yi ba a gidan yanda ta yi niyya, ta goye diyarta ta fice ba da sanin mijin ba.
Duk borin da ta je ta tayar a gidan su Hilal game da kalaman Ramlat din, iyakar su matan kawai
ta tsaya don su Jidda har da kukan takaici da tausayin yayansu. Ji suke kamar a fasa gaba daya sai dai ba su da ta cewa tunda iyaye maza sun tsawatar.
***
Duk wani hidima da za'a yi Abba ya ce ayi kafin a daure aure, don a cewarsa ana daura auren
to fa dakinta za'a miƙa ta.
Shagulgulan koda sun yi armashi, basu yiwa Ramlat ba. Baƙin komai take gani. Dinnerparty Hilal yace ya fasa ganin irin shirin da ƴan uwansa ke yi na gasawa Ramlat magana a ranar.
"Shirun Ramlat na nufin abubuwa d
a dama."
Fadin Hajiya bayan daurin aure, a sadda Zulaihat ta bi ta sashin Abba don amsar laffayar da Ramlat din za ta sanya.
"Nima nayi mamakin yanda ta kwantar da kai ake bikin lafiya ba kamar yanda na zata ba. Amma ko ma mene ita ta sani. Mijin
ta ne yanzu, idan ma ta wulakantashi ita za ta kai kanta wuta."
Cewar Zulaihat cikin halin ko in kula.
"Uwani kenan, ku dai dinga zagayawa kuna yi mata fa
ɗ
a. Ta dauki duniya da zafi, ta sauke."
Ba ta son ma zancen, don haka ta sungumi karam
in akwatin da aka zuba kayan da duk Ramlat din za ta yi amfani da shi a ranar farko bayan kai ta gidan kafin a kawomata sauran akwatin, ta fice daga falon.
Hajiya sai ta tsinci kanta da kasa fita wurin yan uwanta, ta zauna ta yi shiru cikin tunanin m
eke tafiya a zuciyar yarinyarnata.
"Allah Yasa dagaske kike Ramlatu."
Ta furta cikin faduwar gaba kafin ta yunkura ta mike ta fita.
***
Dogon hijabi ta sanya a saman leshin da ke jikinta. Ga kunshi da kitso an mata. Kwalliyar fuskar ta
kara fiddo kyawunta sosai.
"Ina zuwa?" Cewar wata Hannatu ƴar Gwaggonsu Sa'adu ta Daura.
Murmushi ta
ɗ
an yi.
"Yanzu zan dawo."
"Ki sauri don Allah, yanzu za'a zo nemanki tunda an yi magriba."
Ta ja guntun tsaki ta fice. Allah Ya
taimaketa har ta fice ba ta hadu da su Zulaihat ba.
"Malam Hassan. Malam Hassan."
Ya fito daga dakin gugar. (Daki karami a gidan inda Malam Hassan ke musu gugan kaya)
"Na'am."
Ta
ɗ
an waiga sai kuma ta yi shiru sanadin wasu da suka zo
wucewa. Ta kauda fuska har suka fita. Cikin sauri ta dubeshi.
"Ya ake ciki?"
Cikin rashin gaskiya ya kalli jama'a kafin ya ba ta amsa.
"Bayan gidan na ajiye, na tabbatarmaki ba wanda zai kawo komai don kusa da inji ne."
Ta yi murmushi.
"Nagode." Daga nan ta daga zani ta fiddo kudi masu yawa kulle a leda ta mikamasa.
"Abinda kake zargi ba shi zai faru ba kamar yanda na rantsemaka. Barazana ce kawai."
Ya yi murmushi ya gyada kai. Shi ko mene ba damuwarsa ba ce tunda ya ji d
umus. Hankali kwance ta koma ciki, suka yi kici
ɓ
us da Zulaihat.
"Ina kika je?"
Ta yi murmushi.
"Shikenan kuma ba damar na yawata a cikin gidanmu?"
"Nan da awa kadan za ki bar gidan zuwa gidanki kema."
Fadin wata abokiyar wasansu A
sabe. Aka yi dariya, ita kuwa ta shige don kaucewa kaifafan idanun Zulaihat din dake kanta, kallon rashin yarda tsantsa take mata.
***
Aka kammala shirin kai ta gidan miji, Abba ya ce aje zai je har gidan washegari ya yi nashi fadan. Hajiya kuwa ta
ce wanda yayyunta da gwaggonni suka yi ya wadatar.
"Saura ku yafemata."
Cewar Dije abokiyar zaman Hajja. Daga Abba har Hajiya suka ce sun yafemata duniya da lahira.
Tana kuka aka tafi da ita gidan Hilal. Gidan da ta ke mishi kallon wuta.
Aka watse aka bar ta, jikin Amrah a sanyaye, ta kara juyowa ta dubeta da lullu
ɓ
in har lokacin. Dawowa baya ta yi tana hawaye ta lalubo hannunta ta rike.
"Na sanki Ramlat, ba ki fiye cire abu a ranki da wuri ba. Na sanki kamar yunwar cikina. Kiji
tsoron Allah. Ki ji tsoron Allah."
A hankali ta ji Ramlat ta zare hannunta daga nata.
"Amrah muje, suna jiranmu."
Fadin Maryam da ta leƙo. Amrah ta mike tana kallon Ramlat, kafin kuma a sanyaye ta juya ta fita bisa gargadin Abba da ya ce b
a ya son abar mutum ko daya da zummar wani siyan baki.
Kamar jira ta ke sahu ya dauke, kamar jira ta ke ta bar jin motsin kowa a gidan. Ta bude lullu
ɓ
in laffaya gaba daya ta fito. Babu kowa kamar yanda ta zata, ba ta damu da dukiyar da aka zuba a gid
an ba, bai isheta kallo ba hakan yasa a gaggauce ta fita. Komai da sauri take yi tana kara waigen kofa har ta zagaya bayan gidan. Nan ta iske baƙar ledar da ta tabbatar shi ne saƙonta. Ta dauka ta jijjiga sannan ta murmusa. Ledar ta cire ta dauki sakon zuw
a ciki. Ta adana a karkashin gadon ta zauna.
"Komai zai zo karshe a yau, daga yanzun ba wanda zai kara tadamin hankali akan Hilal. Babu shi!"
Ta furta a fili, ƙarar bude gate da ta ji ne ya sanya ta warware
ɗ
ankwali da yin wurgi da ribbons din
ta a gefe. Idanunta kuwa dama kallo
ɗ
aya za ka yi mata ka gane irin kukan da ta ci.
"Yau ko ni! Ko kai Hilal!"
Ta ƙara fadi.I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/iRW2CA35T9
🕯
️
*ƘARF
EN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
14)
Kallo
ɗ
aya za ka yi mishi ka hango annashuwa a zuciyarsa. A jikinsa yake ji komai ya zo karshe, a jikinsa yake jin ya samu soyayyar Ramlat da yardar Allah. Sai da
i bai san meyasa kirjinsa ya hau bugu bayan daka motarsa da fitowarsa ba. Ya
ɗ
an yi shiru yana kallon kofar gidan, bai jima da rabuwa da babban amininsa Ma'aruf ba. Sosai ya ba shi shawarwarin da suka dace game da zamansa da Ramlat. Ya dauka dari bisa dari
.
Ya kalli sama, walkiya ake yi sosai ga hadari. A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi kari cikin gidan.
Ya rufe kofar falon sannan ya ƙaraso ciki da sallama, falon ya tsaya ƙarewa kallo. Ɗakin Amarya kam ya yi kyau iyakar kyau, abu daya ida
n ya tuno yakan dakushe farin cikinsa sai dai kuma karfin gwuiwar da ya samu daga Amininnasa shi ya rinjayi komai har ya sa shi nufar hanyar
ɗ
akinta da sallama. Bai son gayyar abokai da sunan rakiyar Ango.
Ya cika da mamakin rashin ganinta zaune a sa
man gadon kamar yanda ya zama al'adar aure.
"Ramlat." Ya kira da tattausan murya yana karasa shigowa dakin.
"Tooh." Ya kara ambata ganin farin laffaya da
ɗ
ankwalinta yashe saman gadon, hanyar ban
ɗ
aki ya kalla, kai tsaye ya shiga bayan ya aj
iye babbar riga da hula saman gadon. Nan ma wayam, sai tashin kamshin turaren wutan da aka sanya da kyallin fararen tiles da ya kashemishi ido.
"Gani nan!"
Sautin muryarta a sama, wannan ne ya sa shi juyowa da sauri yana kallonta baki sake. Ya
kai duba ga jarkar da ke hannunta na hagu da kuma ashanar da ta rike a dayan hannun. Tana tsaye a tsakiyar dakin, kallo
ɗ
aya za ka yiwa idanun ka san ta ci kuka ba ka
ɗ
an ba. Tana tsayen amma jan majina take yi, ga wasu hawayen da ke ƙara sauka saman fuska
rta.
"Ramlat? Me ya haka?"
Ya furta cikin nuna dakiya sai dai zuciyarsa tamkar ta fasa kirjin ta fito tsabar tashin hankali. Duban tsana take mishi.
"Ka fini sanin mene haka Hilal tunda ka nace akan lallai sai ka zauna da ni! Nace bana sonka
! Na fasa aurenka! Amma ka tursasa lallai sai da aka auramaka ni! Dole ne? A farko wa ya yimin dole? Ba ni na kawoka gidanmu na nuna ina sonka ba? To na fasa! Na fasa! Bana sonka amma ka nunan kai maye ne! Kafin ka cinyeni ni zan soma kashe ka! Dama ni ray
uwata ta kare tunda har aka daura aurena da mutumin da na fi tsana! Muddin ba ka sake ni ba wallahi ina maka rantsuwa da Maƙagin dare da rana, yanzu ba anjima ba, zan watsa fetur dinnan kuma na
kyafta ashana mu mutu gaba daya! Kar ka yi tunanin guduwa domi
n na rufe ko'ina a gidannan! Na rufe
ɗ
akunan!"
Tunda ta soma maganar ya ƙuramata ido, mamaki da baƙin ciki suka cika zuciyarsa. Bai ta
ɓ
a kaiwa ƙoluluwa a
ɓ
acin rai bisa yanda take mishi ba irin yau. Bai kuma ta
ɓ
a zaton za ta aikata makamancin hakan ba
.
"Ramlat? Yau soyayya ce ta koma ƙiyayya? Dama ƙiyayyar ta yi zafin haka? Kin manta Hilal? Kin man..."
Bai kai ga ƙarasawa ba ya ga ta
ɓ
alle murfin jarkar ta hau watsa kalanzir a tsakar dakin har da bangwaye, ba ta ko damu da yanda ya ke jiƙa ri
ga da hannunta ba. Cak ta ji ya riƙe hannuwan wanda ya yi sanadin faduwar jarkar a ƙasa. Idanunsa sun ka
ɗ
a saboda tsananin tashin hankali da
ɓ
acin rai. Ganin yanda take kici-kicin kwatar kanta ya sanyashi watsi da hannun har hakan ya yi sanadin fa
ɗ
uwarta a
ƙasa, har lokacin ba ta bar kuka ba, ganin ta na kokarin kyafta ashanar ya sa ƙafa ya buge hannun, ashanar ta fa
ɗ
i a ƙasa. Durkusawa ya yi saitinta.
"Ba sai kin kai ga kashemu ba! Ki je ki auri wanda kike so, ni Hilal na sake ki. Sai dai ki sani, ida
n har da hakkina, Allah zai min sakayya. Shakka babu kin yimin butulci, kin tarwatsa dukkan farin cikina. Kaicon wannan ranar." Daga haka ya mike yana kallon yanda take dariya tana share hawayen fuskarta. Ya juya saboda kallonta ma kuma
ɓ
ata ransa yake. Sh
akka babu mai hakuri bai iya fushi ba.
"Ina za ka? Ai da saura!"
Bai yi niyyar tsayuwa ba sai dai dole ya tsaya din jin ya mur
ɗ
a kofar amman ko gezau. Jakar hannunta ta nufa ta fiddo karamin littafi (Memo) da aka raba na bikinsu, a take ta yage
bangon ta yar a ƙasa, ya bi bangon da kallo, hotonsu ne, bai mance ko ranar da za'a yi hotunan sai da ta gasamishi maganganu masu zafi, sai dai hakanan ya danne ya shanye. Kallonta kawai yake yana ƙara mamakin yanda so ya koma ƙi. Ramlat da a baya zai iy
a bugun kirji ya ce ta fi sonsa kan yanda yake sonta. Yau ita ce ta juyamasa baya lokaci guda. Bai dauka abin zai biyo har cikin aurensu ba. Ba kyawunta ne ko diri ya ru
ɗ
eshi ba, kaunarta yake da zuciya
ɗ
aya. Da ace
ɗ
ayan biyun da ya lissafa ne, ba zai rab
u da ita ba tare da ya gogamata tabon da har ta mutu ba za ta mance ba. Bai kuma mance yanda Ummansa ta
ɓ
atamasa rai ba duk akan ya nace sai ya aureta.
"Tunanin me kake? Kar
ɓ
a ka rubutamin a rubuce."
Dadda
ɗ
ar muryarta da a yanzun ta zama kamar ta
zakanya a kunnensa ta katse shi. Ya kar
ɓ
a yana kallon kwayar idanunta, ta yi amfani da wannan damar ta harareshi ta tsuke baki gami da kauda kai. Ya maida kai ga takardar yana kammalawa ta kar
ɓ
a. Bakinsa na rawa ya ce.
"Ban mukullin."
Ba ta ko kalle
shi ba ta ciro mukulli cikin riga ta miƙamasa. Ya karba da sauri ya bude kofar ya fice zuwa falo.
A gaggauce ta mike ta zura hijabinta dogo na sallah da aka daukomata. Ta dauki jakarta ta fito. Yana zaune a falo ya dafe da hannuwansa biyu yana fidd
a hawaye kirjinsa na suya. Ba ta ko kalleshi ba ta fita, burinta ya cika.
"Duk abinda ya faru, ka so faruwarsa!" Ta furta a fili kuma a hankali sa'ilin da take share hawayen fuskarta.
Tana tafe tana sharar hawaye, ga wata irin iska da ake yi da
walkiya. Allah Ya taimaketa ta samu abin hawa kai tsaye gidansu ta nufa. Ta yarda idan ma kasheta za'a yi, su kashe. Ko mene su yi mata. Amman ita kam ba za ta iya zama gidan Hilal ba da sunan mijinta kuma a waje tana cin amanar mijin aurenta na sunnah ba.
Ba za ta iya wannan munafuncin ba don ta san karshen abinda soyayyar Aliyu da auren Hilal zai jawomata kenan.
***
Abba ya dubi Hajiya da murmushi a saman fuskarsa.
"Yau ina cike da farin ciki. Na kashe matsalar Ramlatu, fatana yanzu Allah Ya
sa ta zauna lafiya da mijinta."
Hajiya dake kakka
ɓ
e shimfi
ɗ
a ta yi murmushin yaƙe. Har lokacin hankalinta bai kwanta ba. Sam ba ta da wata nutsuwa.
"Amin."
Ba tare da ta kalli Abban ba, ta ci gaba da aikinta. Ya sa hannu ya riko hannunta, h
akan ya dakatar da ita ta dubeshi. Tsoro, fargaba su ya hango cikin kwayar idanunta.
"Ya aka yi? Ashe ba za ki fawwalawa Allah komai ba? Ki bar tunanin wani abu akasin alheri."
Ta gyada kai kawai tana jin saukar ruwan hawaye. Hayaniyar da suka j
iyo na mutanen gidan ya sanya su kallon juna cike da rashin fahimta.
"Meyafaru?" Fadin Abban hankali a dan tashe, Hajiya kuwa kirjinta ne ta shiga bugu fiye da baya. Da hanzari suka fito suka nufi babban falon gidan na Hajiya.
Tana tsaye jikinta
sharkaf sakamakon ruwan da ya yi mata duka cikin adaidaita sahu, kuka take yi yayinda taron dangin uwa da uba suke neman ba'asi hankali tashe. Hajiya ji ta yi jiri na shirin kayar da ita hakan yasa ta samu ta zauna saman kujera tana salati.
"Ya isa
haka!" Tsawar da Abba ya daka cike da karfin hali don jikinsa ma rawa yake yi, shi ya katse su duka.
Kai tsaye ya karasa ga Ramlat ya kama hannunta suka shiga bangarensa. Irin su Zulaihat da Amrah da suka san komai dangane da auren, kuka kawai suke y
i sanin cewa koma mene Ramlat ta shuka wata tsiyar ne.
***
"Daina kuka Ramlatu, ya isa, ya isa. Ki fadamin meke faruwa?"
A hankali ta ciro takardar a jakarta, babu inda ba ya rawa a jikinta ta mikawa Abban.
"Don sonka da Annabin rahma s.
a.w, Abba ka yafemin. Ba zan iya zama da Hilal ba."
Ta furta tana sheshsheka sosai. Abban ya fita shiga tashin hankali,ya fita shiga ru
ɗ
u. Hannunsa rawa yake, kirjinsa zafi yake. Yana ji inama mutuwa ta taddashi tun kafin ya haifi
ɗ
iya kamar Ramlat?
Daidai lokacin da Hajiya ta turo kofar ta shigo.
"Wace irin ƴa na haifa? Rabi'atu wace irin ƴa kika haifamin?! Anya ba'a yimin musanye a asibiti ba?! Don ina mamakin kasancewar Ramlatu jinina!"
Ta riga ta gane, ba'a hayyacinsa yake ba, t
a san
ɓ
acin rai ne. Ta ƙaraso sosai gwuiwa a sanyaye ta kai karbi takardar da Hilal ya rubuta sakin.
Na saki Ramlatu saki daya bisa tursasawarta. Allah Ya za
ɓ
amin wacce ta fiyemin ita alheri. Itama Ya bata abinda take so.
Abban ya mike zuwa daki
nsa. Waya ya
ɗ
auka ya kira Yaya Munir ya fadamishi dukkan abinda ya faru. Ya kara da fadin.
"Gobe da safe ka zo muje gidan su yaronnan. Ina rantsuwa da Allah, muddin ina numfashi Ramlatu sai ta auri za
ɓ
inta. Sai ta auri wanda ta ke so."
Daga hak
a ya katse kiran, ya zauna
ɗ
abas gefen gado. Bai san ya akai ya soma gani bibbiyu ba, sai ji ya yi ya kife zuwa ƙasa.
***
Hajiya tana kuka ta ke magana a falon.
"Kaicon mai taurin kai da bau
ɗ
a
ɗɗ
en hali irin naki. Kaicon ƴa da ba za ta yi biyayy
a da