Showing 126001 words to 129000 words out of 255051 words

Chapter 43 - KARFEN KAFA complete

bata labarin kaf ha

ɗ

uwarta da Mutumin Mall (AlHassan) da kuma Hussein da ma yanda aka yi ta ga hotonnan.

"Tun ganin bayanin da ya rubuta kasan hoton na kara tabbatar da zargina. A farko da na ganshi a shago na gane ƴan biyu ne, tunan

ina sai ya ba ni ko su na tare ne da ya zo Kanon jin daga baya ya ce shi Adamawa su ke. Wannan ne ya kara sanyawa na dasa alamar tambaya ga lamarinnan. Mai yiwuwa su na nemansa ne basu san ma inda ya ke ba, mai yiwuwa kuwa mallakeshi Hajiyarnan ta yi su

n san inda ya ke amma ya ƙi sauraronsu."

.

"A'a haba dai, me kika ce ya rubuta? Allah Ya bayyanamusu shi, kinga kuwa basu da masaniyar a inda yake rayuwa ma kenan. Gaskiya Ramlat babban jihadi za ki yi idan har kika zama silar saduwarsa da ƴan uwansa

."

Jinjina kai Ramlat ta yi zuciyarta cike da tsantsar tausayin Hussein da AlHassan.

"Ina fatan na yi hakan Amrah, sai dai abu

ɗ

aya, ina tsoron na

ɗ

auki matakin da zai sa ya bar gari a rasa inda ya shiga. Ma'ana, idan kai tsaye na cewa shi Abban

Fatima cewa nasan inda

ɗ

an uwansa ya ke, idan ya zo ya ganshi shi kuma ya ƙara sauya garin da za'a rasa ina ya ke, kinga anan an yi ba'a yi ba, wannan ne dalilin da yasa zan fi kaunar na soma sanin meke faruwa ko ya ya ne daga shi na Kanon kafin a san abi

n yi. Wallahi tun sadda na ga wannan hoton, Hussein ya shiga cikin jerin mutanen da nake tayawa da addu'a. Tausayi ya ke ban, na kuma rasa dalilin da yasa nake yawan tunanin lamarinsa."

Wani murmushi Amrah ta yi gami da dafa hannunta.

"Tunda kika

ga haka, babban alheri ne ha

ɗ

uwarki da wadannan bayin Allahn. Ɗari bisa

ɗ

ari na goyi bayanki, ko yaya ki samu ki soma tunkarar Hussein, sai dai ki sani, idan har bai saba da ke ba, ba lallai ne ya ba ki damar da za ki san wani abu dangane da shi ba. Ki ne

mi yardarsa kafin ki nemi ko menene. Abu na biyu ki yi takatsantsan da duk abinda zai sa matarsa ta ƙara ganinki tare da mijinta. Na uku kuma wanda shi ne ma ya kasance na farkon fari, ki ha

ɗ

a da addu'a sosai, nima zan tayaki. Allah Yasa ta dalilinki wanna

n bawa ya sadu da

ɗ

an uwansa."

Murmushi sosai Ramlat ke yi har dimple dinta na fitowa ra

ɗ

au.

"Amin amin."

Ta amsa cike da jin dadi da kuma farin cikin samun Aminiya kuma ƴar uwa ta gari.

Washegari aka kai Hunainah

ɗ

akinta, Ramlat ba

ta je ba don ta san za ta hadu da dangin Hilal sosai a bangaren Bilkisu. Ta dai ji irin salon Bilkisu wacce ba ta nuna komai ba asalima nunawa ta yi ta kar

ɓ

i Hunainah da hannu bibbiyu za kuma su zauna da juna bisa amana. Da wannan dangin Hunainah suka miƙa

ta

ɗ

akinta wasu na yabon hakurin da Bilkisu ta yi yayinda wasu ke fadin ai ta ciki na ciki.

***

Ranar Litinin ta soma aiki a matsayin sakatariyar Chairman. Tana zaune a inda aka tanadar mata ya shigo bayansa daya daga cikin ma'aikatansa ne rike da

jakarsa. Kallonta ya yi sannan ya shige ciki bayan a ladabce ta mishi barka da zuwa.

Jimawa ka

ɗ

an ya kira wayar dake saman teburinta, ta mike ta shiga ciki tana kara gyara zaman ƙaton hijabinta don ta yiwa kanta alkawarin ba za ta ƙara sanya mayafi t

a zo aiki ba ko don tseratar da kanta daga sharrin Chairman. Idan ma wancan karon wani abin ya hango, wannan karon sai dai ya gama baza idanun ya haƙure. Abinda ba ta sani ba shi ne, tafiyarta ka

ɗ

ai ma abin

ɗ

aukar hankali ne.

Yana zaune ya na waya,

ta shiga da sallama bayan ta kwankwasa ya mata iznin shigowa. Tana tsaye har ya kammala wayar wannan mayun idanunnasa yana kan fuskarta kamar ya cinyeta. Ta yi tsaki ya fi a ƙirga a ƙasan ranta.

"Malama Ramlatu, have a seat."

Abin ya mata banbar

akwai namiji da suna Hajara, ta zauna a

ɗ

arare. Bayani ya shiga koromata akan abinda ya shafi aikinta, ita dai kai take gya

ɗ

awa a ladabce tana amsa da kuma fadin za ta kiyaye. Abu ne da Staff Officer ya gama shaidamata, ba ta ga dalilin da a karo na biyu z

ai maimaita ba, a ganinta don hira ne kawai.

Bayan ya kammala ya ce.

"Ba ki yi mamakin dalilin da yasa kika dawo ƙarƙashina ba?"

Sai lokacin ta dubeshi, ta yi saurin kauda kanta don ba ta kaunar wannan shegen kallon ƙurillar da yake jifanta

da shi. Kallo na ƴan duniya.

"Aiki ba inda ba ya kai mutum."

Abinda ta ce kenan kawai. Ya yi baya ya kwantar da kai jikin kujera yana ƴar dariya.

"Hakane kuma. Har kin kara burgeni, da alama kina da kyautata zato. Nayi tsammanin za ki firgit

a ganin kusancina da Hajiya Zeenatu."

Fadin hakan yasa gabanta ya fadi, ta dubeshi cikin dakiya.

"Ko kusa, ai mutum bai isa yi maka abinda Allah bai yi ba."

Maimakon ta ba shi haushi matsayinsa na shugabanta, sai ta burgeshi ainun, ya kara j

in kamar wani magnet na fisgarsa zuwa gareta. Ba ya so ya ya

ɗ

a manufarsa da wuri, don haka cikin dakiya ya sallameta bayan ya ba ta umarnin duk wanda ya zo idan har staff ne ba ya buƙatar ganinsa. Da wannan ta amsa sannan ta fice daga ofis din don dama abi

nda ta ke jira kenan.

Bayan fitarta Chairman Aliyu Dikko ya runtse idanu ya

ɗ

an bugi tebur yana murmushi.

"Wannan ita ce daidai da ni, ita ce kalata."

Ya fadi a fili cike da jin wani nishadi. Abu na farko da zai soma siye zuciyarta da shi,

shi ne kyauta. Zai yi komai da zai sa ta saki jikinta da shi ta kuma daina yi mishi kallon banza. Idan har hakan ta faru shi zai san yanda zai yi ya shawo kanta.

Da wannan ƙudurin ya ji wani sauki daga abinda ke cinsa duk akan Ramlat.

***

Ruw

a ake tamkar da bakin ƙwarya, tana tsaye gefen titin da babu yawaitar ababen hawa sai tsilli-tsilli, kamar ta yi kuka haka take ji don tsabar baƙin ciki. Ace motarka ba ta tashi

ɓ

aci ba sai a wannan lokacin? Ta dauki duk abinda yake da muhimmanci ta fito b

ayan tsagaitawar ruwan hannunta rike da lema. Sai da ta bu

ɗ

eshi kafin ta rufa jikinta. Ta dauki jakarta ta rufe dukkan gilasai da kuma motar. Nan kuma

ɗ

an sahu ya yi mata wuyar samu. Tsaki ta ja ya fi a ƙirga, ranar Asabar din ƙarshe wata ne, daga gidan Ra

fee'ah ta ke nan kan titin Rijiyar Zaki. Ba don ta riga ta yi mata sallama ba ta fito, kuma daga titi zuwa lungun gida Rafee'ah akwai tazara sosai, da babu abinda zai hanata juyawa ta koma.

Daidai sadda wata baƙar Ford ta wuce ta a guje, a hankali

kuma mai motar ya yo baya har zuwa gabanta. Ta kalli motar ta kauda kai, za ta yi gaba ne ya sauke gilas.

"Assalamu alaiki."

Juyowa ta yi ta dubeshi, sanye cikin baƙar rigar sanyi marar nauyi, hular rigar mai igiya biyu kwance a baya wuyansa, du

ka duka tsawon hannun rigar iyakar damtsensa ne wannan ne ya bada damar bayyanar mur

ɗ

a

ɗɗ

un hannuwansa masu zubin ƙarfin, tsintsiyar hannunsa daure da agogon fata baƙi sai zobunan azurfarsa da ba ya rabo da su.

Ta tsinci kanta da maida mishi martanin

murmushin tana mai amsa sallamar. Ba ta ta

ɓ

a tsammanin ganinsa a wannan lokacin ba.

"Motar ce ta samu matsala?"

Maimakon ta yi magana sai ta ji kamar an

ɗ

aure bakinta, hakan ya sa ta gya

ɗ

a kai. Ya

ɗ

an dubi sararin samaniya har ruwa na

ɗ

igarmasa

a saman karan hanci.

"Gashinan kuma ina tsoron ruwa balle na fara gwada aikin kanikanci a kan motarki. Shigo na kai ki."

Turus ta yi, kamar ta ce a'a, maganganun da suka yi da Amrah ya fa

ɗ

omata a rai, ta zagaya ta shiga sannan ta zuge lemarta, za

ta ajiye a ƙasa wurin kafarta ya kar

ɓ

a ya cilla baya. Ta rufe ƙofar ta dubeshi.

"Nagode."

Ya ja motar yana murmushi.

"Rike godiyarki ki fatan Allah Ya kaimu lafiya tukunna."

Murmushin itama ta yi.

'Matsoraci mijin hajiya.'

D

uk a zatonta a zuciya ta fadi, sai ji ta yi ya yi wata dariya kafin ya ce.

"Hajiyar da na yi wuff da ita ko?"

Da sauri ta dubeshi duk sai ta ji kunya ya kamata ta hau kame-kame.

"Lah ni wallahi ban ce ba. Me ma nace? Me wai ka ji na fada? D

on Allah I'm sorry."

Ya kannemata ido

ɗ

aya yana murmushi kafin ya maida idanunsa saman titi.

"Alright, naji ba ki ce komai ba. Ni dama ban ce kin fadi ba duk kika wani tsargu kanki. Kin dai kirani da Your Heart ko?"

Wannan karon ji ta yi ina

ma yana da halin bu

ɗ

e motar ta yi ficewarta.

I just published "BABI NA TALATIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ULR1OMRi4ab

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rah

maanir Raheem.

35)

"Shiru?"

Ta maida kai ga kallon gilas duk ta rude.

"Ramlat."

Ya Rabb, tamkar wani balarabe haka ta ji sunan ya fito ra

ɗ

au a bakinsa. Ba ta san sadda ta juyo ta kalleshi ba. Hankalinsa na kan tuƙi, hanyar da ya

ɗ

auka bai mata kama da inda ta nufa ba, asalima miƙa wa cikin rijiyar zaki kawai ya ke.

"Ina zamu je?"

Ta fadi murya na rawa. Murmushi ya

ɗ

an yi.

"Siyar da ke zan yi, ko ba komai hankalin Madam zai kwanta."

Abin sai ya bata dariya, ta

yi murmushi mai sauti gami da lumshe ido ta budesu.

"Nikam ba zan siyu ba."

"Really?" Ya furta gami da

ɗ

an

ɗ

aga gira yana jifanta da wani irin kallo. Cikin dakiya ta amsa.

"Kwarai ma kuwa, idan ka siyar da ni ba wanda zai kyaleka."

Ya

yi ƴar dariya.

"Kuma sai ya kasance ba wanda ya ga shigowarki motata."

"Amma ba ka daga cikin marasa imani, ba ka yi kama da

ɗ

aya ba. Ina kyautata maka zato."

Bai ce komai ba banda murmushi irin wanda har fararen haƙoransa suka bayyana. Han

nu ya kai ya kunna music, waƙa ce ta yabon Annabi s.a.w da harshen larabci na Maher Zain mai taken Ya Nabi Salam Alayka. Shiru ta yi duk da ba jin larabcin ta ke ba amma yabon yana ratsata sosai, muryar Hussein mai bin waƙar ya fiye mata muryar mawaƙin da

ɗ

i. Ta kara yin laƙwas gami da bada dukkan nutsuwarta. Daidai wurin wani tukuba wacce a gefenta kujeru ne wuri-wuri cikin wata ƴar rumfa, ya nemi wuri ya tsaya.

Ta kalli wajen tana mamakin yanda ruwa bai sa babu cunkoso a wajen ba, kamar ta ce mishi

sai ya bi uban layinnan zasu tafi sai kawai ta fasa ta yi shiru.

"Ban mintuna ka

ɗ

an." Bai jira amsawarta ba ya

ɓ

alle seat belt ya fita. Sai a sannan ne ta lura da cewa three-quarter ce jikinsa, kunya ta sa ta kauda kai daga kallonsa.

Fitarsa b

a jimawa wayarsa ta shiga ringing.

"Zeenat." Sunan da ta gani kenan saman kafcecan screen din da babu tsaga ko

ɗ

is, gabanta ya fa

ɗ

i. Har ta kammala ringing ba ta yi karambanin

ɗ

agawa ba, kafin dai ya dawo ta yi ƙara fiye da sau uku. Anan ta ƙara gane

naci da rashin hakuri irin na Hajiya Zeenat. Ta tsinci zuciyarta da daukar zafi, har hura hanci take don takaicinta, ita kanta ba ta da dalilin jin hakan.

Yana zuwa ya ajiye ledojin a baya hadi da kallonta.

"Sorry, na bar ki kina jira."

Du

k sonta da ta saki fuska ta kasa.

"Bakomai."

Hannu ya kai ya dauki wayar, nan da nan ya

ɗ

an sauya.

"Ɗan yi shiru please." Kallonsa kawai ta yi ganin yanda ya nutsu, waya yake latsawa kafin ya

ɗ

aga. Anan ta ji yana ban hakuri kafin daga bisa

ni ya ce yana hanyar dawowa. Ta

ɓ

e baki ta yi ta kauda kai gefe, tasan da za'a ce tsoro yake zai ce ba haka ba. Can kuma ya ajiye wayar ya tashi motar suka tafi.

Jin wannan karon bakinsa ya mutu ne yasa ta kalleshi. Fuskarsa kamar a sake kamar kuma

ransa a

ɓ

ace, ta kauda kai cike da jin babu dadi don haka ta ja shi da hira.

"Yaranka nawa?"

Murmushi ya yi ya

ɗ

an dubeta.

"Kina son yara ne?"

Ta maida dubanta ga titi tana murmushin itama.

"Yara ai abin so ne. Wa zai ƙi su?"

"Naki ba su isheki ba?"

Ta

ɗ

an yi shiru tana tunanin wa ya fadamasa tana da yara ne? Ko dai Hisham ne? Muryarsa ta katse tunaninta.

"I saw your WhatsApp profile."

Fadin hakan da ya yi shi ya tunasar da ita hoton yaranta ne akan dp dinta s

annan a settings dinta kowa yana iya ganin dp idan har yayi saving lambarta.

"Hakan na nufin.." Ta fadi da sauri tana kallonsa. Wani kallo ya jefamata da ta kauda ƙwayar idanunta.

"Wajen Hisham na kar

ɓ

i lambar, ba don komai ba kuma, kar ki fas

sara please ki yi zaton sabon kamu kika yi."

Ta murmusa.

"Dama kai kam ai sai Hajiya."

Ya yi shiru ka

ɗ

an yana murmushi, har ta fidda rai zai yi magana can ta tsinkayeshi.

"Amma dai kin san ni mijin mace hu

ɗ

u ne ko?"

Ta dara kadan.

"Um um, ban ga alamun hakan ba. Kai da aka kafamaka ƙahon zuƙa ana bi duk inda ka yi?"

Ya shiga jinjina kai gami da ka

ɗ

an yatsa jikin sitiyari.

"Ke ba'a kada ki a magana ko?"

Ya ba ta dariya.

"I'm sorry."

Ta furta kanta tsay

e. Ya kai hannu ya dauki gilashinsa baƙi ya manna a idon, ta saci kallonsa, murmushi kawai ya ke dokawa da ya ƙara masa kyau. Wani ajiyar zuciya ta sauke. Ba ta ga baƙin Hajiya na kishin wannan ha

ɗ

a

ɗɗ

en ba.

Har suka isa bai ƙara magana ba banda murya

r Maher Zain da ya ƙaro a waƙarsa ta Thank You Allah. Nutsuwa sosai ta yi har da kwantar da kai jikin kujera tana sauraron waƙar. Koda suka iso Sharada, shiru ta yi ta zuba ido tana so ta gani ko zai gane gidansu. Ta sha mamaki ganin ya shiga kan layin. K

amar wancan karon ta juyo ta dubeshi.

"Zan sauka anan."

"Don me? Kar saurayinki ya ganni?"

Ya furta yana tafiya a hankali a dalilin ruwan da ya cika wurin. A raunane ta ce.

"Ni wallahi ba wani saurayi, kawai dai.."

"Kar ace ni saur

ayinki ne?"

Ya fadi wannan karon idonsa a kanta, daga cikin gilashin yake ƙare mata kallo. Ganin kamar kallon na ƙurillah ne ya sanya shi kauda kai ya maida bisa hanya. Ita ta ma rasa ta cewa. Ganin ya tsaya daidai ƙofar gidansu ne ta fahimci rannan d

ai ya gane gidan da ta shiga. Dubansa ta yi, ya fidda gilashin ya dubeta.

"Shikenan?"

Tsuke baki ta yi kafin ta bude motar za ta fita ta ce.

"Nagode Allah Ya saka da alheri."

Murmushi ya yi ganin tana shirin rufo ƙofar.

"Ji mana."

Dakatawa ta yi gami da duban ƙyauren gidan a tsorace sannan ta sunkuyo kanta ta dubeshi kamar ta yi kuka.

"Mene ne?"

"Ban mukullin motarki. Zan sa a kawomaki."

Ta ciro ba musu ta miƙa masa har da godiya. Dama burinta su saba yanda za t

a tunkareshi da batun ƴan uwansa. Tasan kuma tana bukatar jin ta bakin Hisham ko akwai abinda ya sani shima.

Hannu ya kai ya

ɗ

auko lemarta da ƙullin leda

ɗ

aya na nama ya miƙamata yana fa

ɗ

in.

"Idan ba so kike mu dawo gidannan da Madam ba, riƙe ki

tafi da su."

A tare suka yiwa juna dariya, ta kar

ɓ

a ta mishi wani irin kallo kwatankwacin wanda ta yi don baƙanta ran Hajiya.

"Itama ta san ni din ba kanwar lasa ba ce yanzu."

Ya

ɗ

aga gira.

"Really? Idan kin yarda za ki maimaitan kallo

nnan a gabanta, shigo mu tafi."

Wani irin kunya ya mamayeta, ta yi saurin ficewa ta rufemishi ƙofar, ya lumshe idanu ya bude yana kallonta, dab da za ta shige gidan ta juyo ta

ɗ

aya mishi hannu tana murmushi, ga mamakinsa shima

ɗ

agamata ya yi, ta juya

ta shige ciki shi kuma ya ja ya tafi duk jikinsa a sanyaye.

Kamar yanda mamaki bai bar shi ba hakanan itama ta ke ta mamakin kanta. Abin mamaki har ta shiga falon Hajiya murmushin ta ke yi.

Ta tarbi yaranta har da

ɗ

aga Affan ta juya da fadin

"Oyoyo Babyn Mami."

Suna ta dariya ta karasa ta zauna gami da fadin wash.

"Sannu, amma kin jima. Mun yi waya da Rafee'ah ta cemin kin bar gidanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login