Showing 24001 words to 27000 words out of 255051 words
ya biyo bayan kallon wulakancin da Aliyu ke mata a lokuta da
dama.
"Sai aka ce miki yunwa nake ji? Ga jaki kin ajiye? Mtsww!"
Ya ja dogon kafin ya mike tsaye ya sa kafa ya ture Centre Table a zuciye har yana kifewa,
ɗ
an flower vase din dake kanta na ado shine ya fashe. Bai ko waiwaya ba ya sa kai ya fice d
aga gidan. Ta zubawa
ɓ
arnar da ya yi mata ido, ko ba komai kudi aka sa aka siyamata. Ba abinda ta nema ta rasa na ƙawata gida wanda iyayenta basu yi mata ba, yayyunta maza kuwa ba wanda bai ba ta gudummuwarsa ba duk kuwa da irin tsanar da suka yiwa Aliyu.
Kuka sosai ta shiga yi tana tattarawa, Aliyu bai damu da ita ba. Ta hakikance ba ya sonta, ba kuma ya tausayinta. Ita kullum ke kwana da tashi da bakin cikinsa, ga so da tausayinsa wanda ke sanyawa ta
ɓ
oye aibunsa a idon danginsu har a gaban Abulle wacce k
oyaushe cikin sanyamusu albarka take. Burin Abulle ta ga
ɗ
a ko ƴarsu sai dai har a sannan Allah bai ba ta ciki ba. Ba kuma ta zargin Aliyu da komai.
"Allah ga mijina, Allah Kai ke shiryawa, Allah Ka shiryamin shi. Ka karkato da hankalinsa gareni." Ta
furta a fili tana mai daga hannu gami da kuka, sannan ta shafe fuskarta ta ci gaba da tsince
ɓ
arnar da ya yi.
A gefen Ramlat hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, hawaye take tana kara dialing lambarsa sai dai amsa daya ce, a kashe. Wannan
ya tashi hankalin Amrah. Ta dubeta a gigice gami da dafa kafa
ɗ
arta.
"Ke, meyafaru da Hilal din? Me yace maki? Mun shiga uku."
Ambaton Hilal da ta ƙara ya farkar da Ramlat. Ta buge hannunta a saman kafa
ɗ
arta ta hau masifa.
"Hilal Hilal! To he
ll with him! Haba! Sai kiramin Hilal kike, a sanadinsa kin sa Aliyu ya yi fushi da ni! Ya kashe wayarsa bansan kuma me zai aikata ba! Dole ne zuwa walimar?! Ba zan je ba! Nace ba zan je ba ko za ki kaini dole?! Wallahi zuwanki bai min rana ba! Ni ki tafi k
awai ki rabu da ni!"
Yanda take rufe ido tana zuba masifa iyakar gaskiyarta shi ya fi komai ba Amrah mamaki.
"Aliyu kuma? Waye hakan? Yanzu akan wani banza Aliyu kike min masifa?"
Ai kiran Aliyu da banza shi ya kara tunzura Ramlat. Ta nuna
ta da yatsa.
"Kin yi na farko ya zama na karshe Amrah don wallahi ba don ina ganin mutuncinki ba sai na gasamaki abinda zai miki zafi a rai! Aliyu ya fi karfin ki kiramin shi da banza! Kika kara kuma Allah Ya isa! Ba zan je walimar ba ki tafi ki kyale
ni! Aliyu shi nake so kuma da iznin Allah shi kadai ne mijina anan duniya!"
Daga nan ta juya a fusace ta soma cire kayanta tana tsaki. Amrah ranta ya dinga suya har bata san sadda ta shiga hawaye ba.
"Akan wani Aliyu kikemin Allah Ya isa? Idan ki
n kara ganina a gidanku kimin abinda ya fi haka."
Daga haka ta juya ta fice. Allah Ya taimaka Hajiya na wurin Abba, A'isha kuwa kallon cartoon da take a tashar Spacetoon ya dauke hankalinta.
Ita kuwa Ramlat ko a kanta, tashin hankalinta fushin
Aliyu. Ta kwanta lamo tana fitar da hawaye, text ta shiga aikamasa kashi kashi.
_*Sweet na tuba don Allah Ka yafemin. Sweet fushinka barazana ne ga lafiyata. Wallahi sweet kai kadai nake so, Kar ka manta na san da zaman Hilal din amma nake sonka."
_*Wallahi Sweet Aliy zuciyata za ta buga. Wallahi har fada muka yi da Amrah a kanka. Ka yafemin. Wallahi don ba ka yanda na ci mutuncinta ba.*_
_*Sweet Aliy har walimar ban je ba saboda kai. Na kasa samun nutsuwa. Sweet Aliy ka yafemin ka bude wayat
a. Na maka alkawarin fadawa kowa kai nake so. Ka ji? Kuka fa nake. Kaina ma ciwo yake*_
Haka ta yi ta rubuta malamai kashi-kashi tana aikawa sai dai duk ba ya tafiya adalilin wayarsa a kashe. Ta kuwa ci gaba da rusa kuka, dakyar ta samu ta mike ta yi
alwalar la'asar ta shiga sallah. Tun tana cikin sallar ta ji wayarta na kara, sallamewa kawai ta yi ba ta ko ida ba ta nufi wayar a guje. Ganin mai kiran ya sa ta
ɗ
agawa da sauri ba tare da ta jira ya ce ba, ta ce.
"Sweet Aliy ka yafemin don Allah, na
tuba wallahi ba zan ƙara ba."
"Zan yafemaki Baby amma sai kin fito na ganki. Ina nan bayan layinku. Ba zan iya bacci ba idan ban sanyaki a ido ba."
Wani dadi ta ji a ranta,
"Yanzu zan zo Sweet, ban minti biyar."
Sallar da ba ta yi ba k
enan ta bar shi a sai ta dawo, nan da nan ta shafa hoda ta sanya lip gloss, kayan zuwa walimar da ta cire su ta mayar. Ta ja mayafinta, sai da ta kama kofa za ta fice daga dakin ta ji faduwar gaba, me Amrah ta ce ga su Hajiya kafin ta fita?
'Ko me ta
fa
ɗ
a ita ta sani, ke dai kar ki ƙara laifi wurin Aliyu.'
Wani bangare na zuciyarta ya ba ta shawarar da nan take ta dauka. A hankali ta fito tana
ɗ
aga labulen da ya raba dakunansu da falon, babu kowa sai A'isha da ta gaji da kallonta tana bacci. Ham
dala ta yi ta fice da sauri.
Tun kafin ta karasa a hangoshi tsaye gaban mashin
ɗ
insa. Ya ha
ɗ
e cikin shadda kalar sararin samaniya, babu hula a kansa sai dai ya yi kyau kwarai a idanunta. Kirjinta har wani bugu yake tsabar so da kaunarsa. Shima ya zubamat
a ido yana ji kamar ya saceta su gudu.
"Ba ki kyautamin ba."
Ya furta yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Ta yi narai-narai da idanunta.
"Ka yi hakuri don Allah."
"Banda wannan, na hakura ai tun kallon farko da na miki na mance dukkan dam
uwata. Sai dai ba ki kyautamin da kika yiwa Aminiyarmu wulakancin da kika fa
ɗ
a ba."
Sai a sannan ta tuna da ta yi laifi, ta jinjina kai.
"Haushi ta bani, banza fa ta kiraka." Ta fadi cike da wauta.
Ya ji ciwon kalmar sai dai ya yi murmushi.
Har a ransa ya ji haushin Amrah na kiransa da banza.
"Kiyi hakuri, a kanki komai zan dauka zan kuma shanye muddin za ki zama rabona. Idan dai kina don farin cikina ku shirya a yau ba gobe ba."
Ta shiga gyada kai.
"Zamu shirya, zan je har gi
dansu na ba ta hakuri amma yau ba ta nan ta tafi walimar da na fadamaka zamu je dazun. Idan muka hadu a makaranta gobe zan bata hakuri ka ji? Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy."
Ya dan lumshe idanunsa yana murmushi, murmushin da ke ƙara tafiya da iman
inta.
"Ya isa, shikenan ya wuce. Allah Ya kaimu goben. Da ban ganki ba, ba zan iya bacci ba."
Wani sanyi da dadi suka lullu
ɓ
e zuciyarta. Nan da nan kuma suka shantake da hirar soyayya kamar kar su rabu. Sai dab da karfe shida suka rabu, ba ta iya
tafiya ba sai da ta ga tafiyarsa sannan ta juya cike da annashuwa ta koma gida.
"Sai yanzu ku ka dawo? Kun so ku yi dare." Abinda Hajiya ta fadi kenan, sai ta ji kaunar Amrah a ranta, wato dai ba ta sanarmata rigimarsu ba.
"Eh Hajiya, ki yi hak
uri."
Hajiyar ta gyada kai tana kallon yanda ƴar ke zuba uban fara'a kamar wacce aka yiwa albishir da aljannah. Gudun kada Hajiyar ta watsamata tambayar da za ta kasa amsawa game da walimar, ya sanya ta saurin shigewa daki gami da fa
ɗ
awa kam gado tan
a murmushi, Aliyu shi ne komai nata a yanzu, ba kuma ta jin har abada za ta bar shi ko me za'a yi, kuma ko me zai faru. Tunawa ta yi da sallar la'asar, da sauri ta mike ta fa
ɗ
a ban
ɗ
aki ta kara dauro alwala sannan ta tayar da sallar kusan ma a sallar banda
murmushi da addu'ar Allah Ya sa ta zama matar Aliyu ba abinda take.
***
Muhibbat tun tana zuba idon ganinsa ya dawo gidan har ta gaji, ragowar abinci ranar ta juye ta miƙawa wasu makwaftansu marayu suka yi ta godiya. Tasan ko ta bar shi Aliy
u ba zai ta
ɓ
a ci ba don a cewarsa ba ya son kwantai. Ba ta gaji ba ta
ɗ
ora sanwar dare, tuwon semo ta yi da miyar danyen ku
ɓ
ewa, a gefe kuma ta yi farfesun kifi sai kunun aya. Komai ta jera inda ya kamata ta fa
ɗ
a wanka, tana fitowa ta ha
ɗ
e cikin doguwar ri
ga ƴar kanti mai
ɗ
ankwali. Ko ba ado ita din kyakkyawa ce, hakan dai bai hanata daukar kwalliyar ba. Ta fesa turare ta fito falon tana addu'a cike da tsoron yanda zai shigo gidan. Fatanta kar ya shigo a maake kamar yanda ya saba. Jin karar mashin dinsa ya
kara ka
ɗ
a hanjin cikinta. Ta miƙe da sauri ta bude kofa, a kan idonta ya yi parking ya shigo. Ta yi mamakin ganinsa cike da walwala. Itama sai ta saki fuska.
"Sannu da zuwa." Ya riko ƙugunta yana murmushi kafin ya kai mata sumba a kumatu.
"Yauwa
Matar."
Ta rufe kofar suka karasa falon zuciyarta kamar ta fito ta taka rawa tsabar farin ciki duk kuwa da tasan silar farin ciki nasa. Ramlat ce! Ganinta ya je ya yi hakan yasa shi sakarmata fuska sai dai hakan bai dakusar da nata jin dadin ba. Murmu
shin Aliyu da dariyarsa ma kadai abin so ne a wurinta.
Ta taimaka ya yi wanka, ga mamakinta sosai ya ci abinci har suna hirar abinda ya shafi danginsu. Ga duk wanda ya ga Muhibbat ya san tana cike da farin ciki. A karshe ma ya ja hannunta suka shige
ɗ
aka.
Tun da ya soma sarrafata yake kiranta da suna Baby, wani sa'in ya ce Ramlat sai kuma ya ce oh i an sorry na manta. Har ya yi ya gama ba ta fasa fitar da hawaye na baƙin ciki, ta waiga ta dubeshi yana baccinsa hankali kwance, miƙewa ta yi ta tsa
rkake jikinta ta fito zuwa
ɗ
akinta. Nafila ta yi ta zauna tana addu'a tana kuka. Sau da dama takan ji kishin Ramlat, sau da dama kuma takan ji ko ma mene Aliyu ne ya ba da fuskar da komai ke faruwa. Sai ta dinga kallon wasu abubuwan ba laifin ita Ramlat di
n bace. Ta gaji da kukan ta dau Kur'ani ta karanta sannan ta haye gadon
ɗ
akinta sai bacci.
Da asuba koda ta mike ta yi alwala ta shiga tashinsa. Wayar da yake ta tsaida ta.
"Baby ki tashi mana ki sallah, ban san wannan baccin fa. Uhum? Ina magan
a kina min magagin bacci ko?"
Kasa ƙarasawa ciki ta yi da sauri ta maida kofar ta rufe ta koma
ɗ
akinta cikin hawaye. Mutumin da sai ya ga dama yake tashi salla idan ta tashe shi, shi ne har ya iya tayar da wata yin ibadar. Abinda bai ta
ɓ
a yi gareta ba
kenan, koda dai lokuta da dama ita keda kokarin tashi salla ta tayar da shi.
Wannan karon kasa zubda hawayen ma ta yi ta ha
ɗ
iye abinta.
***
_*Alhamdulillah, your future husband is back. I can't wait to see you. Love you.*_
Saƙon da y
a shigo wayarta misalin bakwai na safe kenan, sa'ilin da take shirin fita makaranta, saƙon da ta tabbatar na Hilal ne. Wani makokon bakin ciki ya turnuƙe zuciyarta har ba ta san sadda ta ja tsaki ba. Sai me idan ya dawo? Ba dai za'a yi mata dole a auren wa
nda yanzun ta tsana ba. Haka ta kammala saka uniform ranta na suya, ba don Sweet Aliyunta zai kira ba da ta kashe wayar gaba daya ta bar ta a gida. Sai dai duk sadda ta samu dama takan
ɓ
oye a ban
ɗ
akin makaranta ko cikin aji idan ba malami ta kirashi su gai
sa.
"Ke kuma lafiya kike cin magani? Hala ba ki da labarin dawowar mutuminki?"
Hajiya ke zancen cikin murmushi don tun jiya Munir ke fadamata Hilal ya dawo. A dole Ramlat ta ƙaƙalo murmushi bayan ta ha
ɗ
iye dankali da kwai da ta sanya a bakinta.
"Yanzu da safe yake fadamin."
Ta kai duba ga agogon fatar dake daure a hannunta tana mai miƙewa.
"Hajiya zan yi latti muna da test. Sai na dawo.". Daga haka a gurguje ta fice Hajiyar na mata addu'a sai dai tana dan nazarin yarinyar da yanda ta
ga kamar ba a walwala da zuwan Hilal din. Fatanta kar abinda take tsoro ya tabbata.https://my.w.tt/ub8deMQ0g9
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
09)
Tun shigarta ajin ta hango Amrah ta
sauya wurin zama daga kujera mafi kusa da ita zuwa can
ɓ
arin hagunta, ba ta yi mamaki ba don dama duk sadda sa
ɓ
ani ya ha
ɗ
asu sai an gane a ajin ko don sauya wurin zama. Ba ta yi gigin zuwa inda take ba ganin malaminsu ya taho. Sai dai kusan rabin hankalin
ta yana gareta, a yanzun ta gane kurenta sosai, Amrah yar uwa kuma Aminiya tun suna yara bai kamata ace ta yi mata hakan ba. Yanzun ta fi koyaushe bukarta kasancewarta abokiyar shawarar da suke haƙowa su binne ba tare da kowa ya ji ba. Sai dai a ranta tana
da yaƙinin muddin ba za ta bata goyon baya game da sheƙar da ta sauya ba, komai ma ya biyo baya ba matsalarata bace. At her age, Babu wani ko wata da za ta bari ya tauyemata ƴancinta.
Test har biyu suka yi, da na Economics da Commerce, bai bata wuya sos
ai ba, ko ba komai tana da basira daidai gwargwado sannan ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin karatu bisa shawara sanyin idaniyarta.
Ana tashi break ajin duk an fita sai ita sai kuma Amrah da ta maida hankali ga kwafar note. Wurinta ta nufa kai tsaye, ko
ba ta
ɗ
ago ba ta san ita ce, takaici ya kamata. Nan da nan kalaman da ta jefata da su suka dawomata, wasu hawaye ta ji sun soma wanke mata fuska.
"Ko ba amintaka tsakaninmu Ramlat, zan ci darajar kaunar da nake miki kamar ƴar uwata ta ciki
ɗ
aya. Akan
namiji kika zageni kika wulakantani tamkar ba ki sanni ba. To ni kuwa me za ki cemin? Tsayuwarki ba ta da amfani don yanzun babu komai tsakanina da ke face gaisuwar musulunci, shima gaisuwar idan naga za ki wulakantani ba lallai ba tilas."
Tana magan
ar tana jijjiga biro tana fidda hawaye, itama kanta uwar gayyar hawayen take. Damuwa biyu suka tarar mata, ga na bakin cikin dawowar Hilal da kuma gaggawar bari a sanyamusu ranar aure da ta yi, ga kuma na zafin abinda ta aikata ga Aminiyarta wanda har sai
da Aliyu ya ankarar da ita
kuskurenta. Hannunta ta kama wanda dole Amrah ta tsayar da rubutun don dama tuni ta daina fahimtar abinda take kwafa sakamakon hawayen da ke maida idanunta gani dusu-dusu. Littafin kuwa duk ya soma jiƙewa.
"Ki yafemin don Al
lah don Manzon Allah s.a.w, nayi kuskure ba zan ƙara ba. Na fahimci laifina. Idan na kara ki dauki dukkan matakan da kika yi niyya."
Jin chanjawar muryarta da kuma kukan ya karya zuciyar Amrah, basu soma ƙawance don wani can ya rabasu ba. Sun saba su
yi fadansu kuma su shirya ba tare da sun bari wani third party ya shigo tsakaninsu ba.
Dakyar ta yarda suka shirya karshe kuma suka hau hira har da dariya tamkar ba su ba.
"Waye Aliyu?"
Tambayar da Amrah ta jefomata kenan. Sai da gabanta ya fa
di tsabar so da kaunar mai sunan. Ta lumshe idanu ta bude tana murmushi gami da duban agogon tsintsiyar hannunta.
"Saura 3mins a dawo class, ki bari idan an tashi i promise to tell you everything about him."
Murmushi ta yi.
"Shikenan."
Ana tashi kuwa suka ci sa'a ba'a zo
ɗ
aukar kowannensu ba, don haka suka samu wuri can ƙasan bishiya saman kujera suka zauna. Babu abinda ta
ɓ
oyemata dangane da Aliyu da karfin dangantakarsu a yanzu. Cikin hawaye ta kara da fadin.
"Wallahi wallahi kin
ji rantsuwa ta ƴar musulmi, ban ta
ɓ
a son wani yanda nake son Aliyu ba, ciki kuwa har Hilal! Ba zan iya auren Hilal ba, ba kuma zan yarda a auramin wanin Aliyu ba ko waye shi."
Baki sake Amrah ke dubanta. Ko a jiyan da suka yi wannan rikicin, ta san ce
wa ko wane Aliyu, Ramlat ta yi nisa a begensa.
'Ko asiri ya mata?'
Girgiza kai Ramlat ta yi gami da dariya mai ciwo.
"Kinsan Allah ba wani asiri, wannan son tsaftatacce ne."
Amsar yasa ta fahimtar zancen zucinta ne ya fito muraran.
"Wallahi gani nake kamar wata Ramlatun ce zaune anan ba Ramsy Ramlat da na sani ba. Kwanakin nan dama na lura da yanda walwalarki ta sauya, na lura sauyi a yawancin abubuwanki ta yanda hatta da wayarki kina kaffa-kaffa kar a ta
ɓ
amaki. Ashe wata tsiyar ki
ke shirin tafkawa!"
Nan da