Showing 141001 words to 144000 words out of 255051 words
kowa idanunsa a kanta, an takura akan sai ta yi aure. Dama tun da Hajiyar ta soma batun kai yara dangin Babansu don su ci hutunsu a can, ta soma jin ba dadi. Babban takaicinta yanda tun rasuwar Abulle babu
wanda ya kara nemansu banda Malam da ke kira lokaci zuwa lokaci su gaisa ko kuma ita ta kira. Hakanan Justice duk sadda zai yiwa yaran ƴan uwansa kayan sallah toh zai ha
ɗ
a da su. Kannen Aliyu ta yi musu uzurin aure, amma a ganinta hakan bai kai dalilin da
zasu dauke ƙafa da hankalinsu daga kan yaransa ba. Ko ƙafarsu ba ta tako ba ai akwai waya.
"Kin yimin shiru kina wani ƙunƙuni, idan ba za ki je ba sai ki kira ki fa
ɗ
amasa."
Hajiya na kaiwa nan ta mike a fusace ta yi
ɗ
akinta. Sauke ajiyar zuciya
Ramlat ta yi, ranta har sannan babu dadi haka ta gyara zaman mayafin abayarta maroon ta fita rike da kwandon abinci. Idan ka ganta ba za ka ce ta haifi yara har uku ba, Allah Ya yi mata baiwar jiki mai kyau kuma wanda ya samu kulawar da ta dace.
H
ar ta iso asibitin da Amrah suke ba ta cikin walwalarta. Ɗahiru ta soma kici
ɓ
us da shi a barandar emergency, suka gaisa ya fadamata lambar dakin sannan ya fita. Ta karasa, Amrah na kwance tana bacci sai Umma a gefe. Ta karasa suka gaisa da Umma.
"Wai,
gaskiya kin yi kokari, ana wannan ruwan kika fito?"
Murmushi ta yi.
"Umma ai dole ne, ƴar uwata guda ba lafiya fa."
Ƴ
ar dariya Umma ta yi.
"Kinga da sauki ma, likitan ya ce wai Malaria ce kuma kinsan ba'a son Mai ciki da ita, amma yanz
u Alhamdulillah. Ba ta jima da samun baccin ba ma."
Jinjina kai Ramlat ta yi tana maida dubanta saman fuskar Amrah, duk ta ajiye wani kumatu.
"Allah Ya bata lafiya."
Daga nan ta ajiyewa Umma kwandon suka shiga hira kadan-kadan. Sun kai kusan
mintuna sha biyar kafin Amrah ta farka.
"Ya jikin?"
Umma ta furta tana dubanta. Gyada kai ta yi tana kokarin miƙewa zaune.
"Alhamdulillah, kan ya sauka ma."
Yanda ta furta ma ka san ba lafiyar. Suka yi mata sannu. Da taimakon Ramlat,
ta shiga ban
ɗ
aki ta yi alwala ta wanko baki. Suka dawo ta zauna, Ramlat da kanta ta zubamata farfesun naman ragon da ta kawo wanda ya ji karas da
ɗ
ankali. Ta ha
ɗ
amata shayi sannan ta ha
ɗ
a na Umma, itama ta zubamata farfesun.
Suna ci su na ta
ɓ
a hira.
Ruwa na tsagaitawa Umma ta wuce gida da zummar za ta turo kanwarta (ita Ummar), Magajiya ta zo ta zauna da ita.
"Ya na ganki wani iri?"
Amrah ta watsowa Ramlat tambaya tana dubanta. Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba komai."
Girgiza kai Amrah
ta yi.
"Karya ne wallahi. Dama shiru nayi don Umma na wurin amma tun da na dora idanu a kanki na gane akwai matsala."
Shiru Ramlat ta yi kafin kuma ta soma fitar hawaye, a yau dai zuciyarta ta motsa da kewa mai yawa na Aliyunta. Da ace za ta ras
a duk abinda ta mallaka don kawai Allah Ya ba ta damar ganinsa su yi magana ko sau daya ne, da tuni ta aikata hakan. Sai dai kuma ita mutuwar gaskiya ce, barin duniya ce ta har abada da babu dawowa sai dai ka je ka tarar.
"Lafiya kuwa?"
Cewar A
mrah kusan hankali a tashe, ganin tana neman jefa mai juna biyu cikin matsala ta yi saurin dauke hawayenta ta hau murmushin yaƙe.
"Ke ba fa wani abun tada hankali bane."
Nan ta kromata dukkan abinda ke faruwa, murmushi Amrah ta yi. Ta lura ba ma
ganar kai yaran gidan kakanninsu ne tashin hankalin ƙawarta ba sai maganar auren da ake budemata wuta a kai.
"Yanzu don Allah Ramlat kin fi kaunar ki yi ta zama haka ba aure? Kina zaton hatta Abba idan ace yau yana doron ƙasa zai yi murna da zamanki
haka? Ko a tunaninki Aliyu zai yi farin ciki da zamanki haka babu aure? Wallahi kin ji na rantsemaki cikinsu babu wanda zai so ki ƙare rayuwarki a haka. Kema fa mace ce, a karon kanki sai dai ki
ɓ
oye, kinsan cewa kina bukatar auren. Kina son wanda zai kula
da ke da rayuwarki."
Amrah ta ci gaba da kwantarwa Ramlat hankali ta hanyar nasiha da rarrashi. Tun Ramlat na jin haushin maganganun har ta soma gane dagaske duk abinda ta fadi babu ƙarya ko sharri a ciki.
"Batun yara kuwa kema kinsan ba ki isa
hanasu zumunci da dangin mahaifinsu ba koda su din ba sa ta su."
Murmushi kawai Ramlat ta yi a nan.
"Ke ni ina Muhibbat ne? Kwana biyu na ji ta shiru a WhatsApp."
"Tana nan, ko juma'ar da ta wuce mun gaisa. Ta yi rashin lafiya kwana biyunnan
wai."
"Allah Ya bata lafiya." Cewar Amrah.
Zuwan Baba Magajiya kanwar Umma ne ya ba Ramlat damar yi musu sallama ta tafi. Yayyafi-yayyafi ake yi garin ya yi luf-luf da sanyi mai sanya nutsuwar zuci.
Tana tafe tana tauna zantukan Amrah har
ta isa ga motarta.
***
YAKASAI..
Kanta kamar ya tsage biyu, bakinta ya yi mata nauyi yayinda ta ƙurawa Kawu Bello idanu don ji take kamar babu sauran laka a jikinta. Ta rasa ma me za ta ce, ta kasa fahimtar idan bayanan suka dosa. Batun
dai zai bayar da ita ga CHAIRMAN ALIYU DIKKO ya fi komai ba ta mamaki da kuma dariya.
"Kin yi shiru kin tsuramin idanu kamar wani sa'anki?! Sarai kin ji ai abinda na ce! Mun gaji da zubamaki idanu, ke ba ki kawo wani kin ce kina sonsa ba, kuma ke ba
ki ba masu sonki dama ba! Toh na bayar da ke ga Chairman, zai soma zuwa hira wurinki ku fahimci juna. Nan da sati uku ma zan dauramaku aure."
Ya ƙarashe yana fitar da wani huci har da muzurai, bakin ciki ya sa hawayen ma kasa zubowa. Wato Chairman shi
go-shigo ba zurfi ya yi mata kenan? Ta ya akai ma ya san gidan kakanninta?
"Ki je ki saurari zuwansa cikin satinnan, saura kuma wannan karon kamar yanda kika nunamana a baya, yanzun ma ki nuna ba mu isa da ke ba. Dama ai mai hali ba ya fasa halinsa.
To mu zuba da ke."
Wasu zafafan hawaye suka zubomata, ta kasa duban Kawun har ya mike ya bar mata dakin. Jiki a sanyaye ta share hawayenta, ta mike ta koma sashen Dada. Nan ne ta samu Dada ta shiga kwantar da hankalinta da hanyar nasiha da nunamata mu
himmancin auren a gareta. Ita dai ji ta yi gidan duk ya isheta, sallar la'asar kawai ta gabatar kafin ta yiwa Dada sallama ta yi ficewarta.
A zauren suka yi kici
ɓ
us da Kamal.
"Ashe Ramlat arzikina kika raina ban sani ba, kin nunamin ba za ki i
ya aurena ba saboda a gidanmu ba'a sonki, yanzu ai gashinan da wannan maigidannaki ya fito kin kawoshi har ya ga Kawu. Ki dai bi a hankali duniya ce, ta fi bagaruwa iya jima!"
Yana kaiwa nan ya gifta ta ya wuce, ta bishi da kallo sannan ta fice, a han
yar tana tafe tana hawaye sosai. Komai ba ya mata dadi, wannan ne yasa ta za
ɓ
i ka
ɗ
aicewa ita
ɗ
aya ba tare da kowa a kusa da ita ba. Wani Rainbow Park ta je, wuri ne mai karancin hayaniya, mutanen da ke a wurin tsilli-tsilli, ba ruwansu da harkar kowa. Wan
nan ne yasa ta za
ɓ
i can wurin da za ta je ta samu nutsuwar zuciya.
Cikin wata rumfar kara ta nufa inda aka jera kujeru, iska mai dadi wurin ke bayarwa. Akwai ƙarancin jama'a a Park din adalilin ruwan da aka yi.
Tunani kawai take tana fitar da
hawaye masu
ɗ
umi. Duniyar da abinda ke cikinta take ji sun ishe ta, an ce bazawara nada ƴancin za
ɓ
in wanda ta ke so, amma tana ji kamar ba ta da wannan damar.
***
Tafe yake a hanyarsa ta zuwa wurin Gym. Tafiyarsa yake cikin nutsuwa yana sauraron y
abon Ya Habibal Qolbi na Sabyan Gambus. Waƙar sosai yake jin dadinta, murmushi yake. Hankalinsa ya kai ga motar da ko a mafarki, lambarta ba za ta
ɓ
acemasa ba. Ɗan tattara gira ya yi don son tabbatar da abinda idanunsa suka gani, ya nemi wuri ya yi parking
.
"Me ta ke yi anan?" Ya samu kansa da furtawa a fili alhalin ya san babu mai amsawar.
Fitowa ya yi ya kara kallon lambar don tabbatarwa. Can kuma ya fito ya shiga Park din don son tabbatarwa kansa.
Sanye yake da wando da riga na kamfan
in Adidas, farare da layi-layin navy blue a gefen hannu da wandon. Ƙafafun cikin farin canvas.
Gashin kansa ya kwanta luf-luf har a ƙeya, baza dara-daran idanunsa ya shiga yi wanda gashin ido ke kokarin rufewa duk sadda ya kyafta.
Har ya juya cik
in fidda ran ganinta a wurin, idanunsa ya kai gareta cikin rumfa. Tana zaune ta
ɗ
ora gwuiwar hannunta saman kujera ta kama dage kanta da tafin hannu.
Kamar tunani take yi mai zurfi, kamar kuma hawaye ne saman fuskarta. Don so ya tantance, sai ya ƙara
sa. Sallama ya yi amma ga mamakinsa ba'a san ya yi ba. Jan kujera ya yi da ke fuskantarta ya zauna. Wannan ƙarar ce ta maidota hayyacinta, ta dubeshi da idanunta da suka ƙanƙance suka yi ja. Shima zubamata nasa kwayar idanun ya yi fuskarsa da wata kwantacc
iyar damuwa.
Ta yi saurin share fuskarta, sosai ta ka
ɗ
u da ganinsa a wurin, ta kuma yi mamaki.
"Assalamu alaikum."
Ya kara maimaitawa, ta amsa a ciki-ciki. Miƙewa ta yi da niyyar barin wajen, ya yi saurin riƙe gefen dankwalin abayarta w
anda ba shiri ta koma ta zauna.
"Lafiya?" Ta fadi murya a ƙasan maƙoshi. Murmushi ya yi.
"Ke zan tambaya, daga ganina sai ki gudu. Zauna ki ci gaba da hawayen ni tayaki kawai na zo yi."
Ta kauda kai daga barin kallonsa, ba ta ce uffan ba, z
uciyarta ba ta cikin nutsuwar da za ta yi wani murmushi har ta kai ga darawa. Yau an motsa mata dukkan damuwarta. Yau ta tuna da mutane biyu masu ƙima da daraja a wurinta kuma mafi soyuwa a zuciyarta da ta rasa.
"Kiyi hakuri, komai na duniya mai ƙar
ewa ne. Wannan hawayen fa
ɗ
uwa ce a wurinki ba nasara ba. Babu abinda zai yayemaki. Kema fa kin sani. Wani abin muna ji muna gani amma yake gagararmu tankwarawa saboda ba mu isa ba, sai yanda aka ce da mu, sai yanda akai da mu."
Ya fadi hankalinsa na k
anta. Ta dubeshi, lokacin da ta ji saukar wasu sabbin hawayen, ba kanta kawai ta tausayawa ba, kalamansa na karshe kamar dan tsakure ne daga tasa matsalar a iyakar fahintarta domin kuwa ba shi da masaniya akan nata.
"Ka san damuwata ne? Ya akai ka sa
n ina nan?" Ta furta kanta tsaye a sadda ta ke kokarin share hawayenta. Ya yi murmushi.
"Gashinan rubuce saman fuskarki."
Ta kara tsuke fuska ganin ya share tambayarta ta biyu.
"Kinsan me?"
Ta dubeshi gami da girgiza kai. Ya maida hank
ali kan wayarsa dake ringing, ganin sunan Hisham na yawo saman screen ya
ɗ
aga.
"Ba zan samu shigowa ba." Abinda ya ce kenan bayan sun gaisa. Ramlat ta saci kallonsa, ba shiri ta kauda nata idanun ganin irin duban da yakemata.
Tana jin muryar Hisham
na tambayar dalili.
Murmushi ya yi mai sauti.
"Ina tare da Heart."
Daga nan ya katse kiran. Kalmar Heart da ya furta ta sanya gabanta fa
ɗ
uwa, ta dubeshi, ganin ya
ɗ
agamata kira ta kauda kai. Ya ajiye wayar saman teburin.
"Tambaya
rki ta biyu ce ni kaina amsarta nake nema. Nasan dai a wautana motarki na gani, na haddace lambarta fiye da zatonki. Sai dai na rasa ya akai jikina ya bani ke
ɗ
in ce ke jan ta, kuma har na za
ɓ
i shigowa nan na ga wanda kika zo gani. Sai kuma na ganki ke
ɗ
ay
a kina hawaye. Nan take tunanina ya bani cewar watakila fa
ɗ
a ku ka yi ya tashi ya bar ki ko kuma bai zo ba. Ma'ana, ya yi disappointing dinki."
Murmushin takaici ta yi.
"Babu ko daya cikin hasashenka, asalima a karon kaina na za
ɓ
i nan matsayin
wajen da zan samarwa zuciya da kwakwalwata nutsuwa."
"Kina zuwa kenan?"
Ta
ɗ
an ta
ɓ
e ƙaramin bakinta gami da girgiza kai. Ya bi bakin da kallo ya kauda fuska yana murmushi.
"Heart." Ya furta a hankali, sai dai ta ji shi sarai. Miƙewa ta
ƙara niyyar yi ya hanata ta hanyar rike mayafin karo na biyu. Dole ta zauna.
"Tafiya zan yi."
Yanda ta furta kusan a fusace sai ta ba shi dariya.
"Ba ki isa ba ai, uzuri ne fa da ni kika dakatar da ni."
Ta saki baki da mamaki.
"Yaushe?"
"Yanzu mana."
"Ni na fa
ɗ
a?"
Ya girgiza kai.
"Abar maganar, kawai dai shawara zan ba ki. No matter what, ko meke damunki kar ki bari hakan ya sa ki zo irin wuraren nan. Ki yi hakuri, babu matsalar da wani ko wata zai magan
cemaki. Ki miƙa wa Allah lamuranki. Ki dage da kai kukanki gareShi. Wannan shi ne babban kuskurena a baya wanda a yanzun ya ke farautana."
Ya ƙarashe cike da tsantsar damuwa, ta dubeshi da kulawa.
"Ban yi zaton kana da damuwa ba, Allah Ya maka
dukkan ni'ima. Kuma.."
"Ke Allah bai miki dukkan ni'ima ba?"
Ta kauda fuskarta daga kallonta.
"Ni kuwa Allah Ya yiwa ni'ima. Ya bani lafiya, Ya ban iyaye da ƴan uwa masu sona, Ya ban ƴaƴa. Alhamdulillah."
Tana kaiwa nan ta saci kal
lonsa. Kamar ta so karantar damuwarsa da yanda ya sauya lokaci guda. Can kuma ta ga ya
ɓ
ige da jinjina kai.
"Yes, you are right. Alhamdulillah."
Yanda ya yi maganar a sanyaye sai ya bata tausayi.
"Gwara ki tafi, yamma ta yi."
"
Kana da ƴan uwa a garinnan?"
Abinda ta ce kenan. Wani banzan kallo ya watsamata da ya razanata.
"Ba ki damar shiga rayuwata hakan ba yana nufin har da lasisin da za ki tambayi abinda ya shafi rayuwata bane. Ya kamata ki san wannan."
Yana
kaiwa nan ya mike a fusace ya yi gaba.
Ta bishi da kallo duk sai ta ji hankalinta ya tashi, bata ta
ɓ
a ganinsa a yanayi makamancin wannan ba. Labarin da Hisham ya ba ta sadda magana makamanciyar haka ta ha
ɗ
a su shi ya fado ranta. Da sauri ta mike ta
dauki jakarta da zummar mara mishi baya. Wayarsa ta gani ajiye, ta dauka ta bi bayansa. Sai dai har ya kai ƙarar fita. Kafin ta karasa har ya shige mota ya tayar. Zagayawa ta yi da sauri ta bude mazaunin gefe ta shiga.
Ya buga sitayari murya a kausa
she ya ce
"Fita!"
Girgiza kai ta yi hawaye na zuba.
"Ka yi hakuri don Allah, wal..."
"I said get out!!"
Ya fa
ɗ
i cikin tsawa hadi da buga sitayari iyakar karfinsa har sai da ta razana. Idanunsa kamar an watsa barkono. Yanda ji
kinsa ke rawa itama haka nata jikin ke yi. Ta bude murfin motar ba shiri ta fita. Bai bari ta karasa rufewa ba ya fisgi motar har yana kokarin buge wani mota. Mai motar ya dakata da sauri yana duramasa ashar. Hussein bai ma san yana yi ba. Ita dai Ramlat k
irjinta je dukan tara-tara da irin gudun gangancin da ta hangoshi yana yi, hawaye kamar famfo take fitarwa ba ta ko damu da kallon da jama'ar wurin ke bin ta da shi ba. Ta shiga motarta ta bar wurin cike da jin haushi kanta, me ya kai ta wannan gangancin?
***
MAFARIN KENAN.....
I just published "BABI NA TALATIN DA TARA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/dCw5vESQqbb
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir R
ahmaanir Raheem.
39)
Jikin Hajiya ya yi sanyi bayan gama sauraron Ramlat. Sam ba ta tsammaci hakan ce za ta faru ba. Ta dauka dai fa
ɗ
a akan fiddo mijin kawai za'a yi mata. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yanda Ramlat ke kuka kamar ranta z
ai fita.
"Ke fa na yarinya ba ce, kin kuma sani dama can ba'a yi miki dole ballantana a kwata wannan karon. Da ace wani ne ba shi Maigidannaki ba, toh ba lallai ya dameni ba. Amma sam bana son wannan ha
ɗ
i na Yaya Bello. Duk ke kika jaza wa kanki ai R
amlatu, tun yaushe ake biyamaki karatun fidda miji kin ƙi haddacewa balle ki yi aiki da shi? Yanzu gashinan an miki shigo-shigo ba zurfi."
Ramlat ta dubeta tana sharce hawaye.
"Nima Hajiya ba wai ba zan bi umarninsa ba ne, sai dai nasan waye Cha
irman tunda ni ke aiki karkashinsa. Ya sha