Showing 27001 words to 30000 words out of 255051 words

Chapter 10 - KARFEN KAFA complete

nan Ramlat ta

ɗ

an sauya fuska.

"Ki bar kiran tsiya akan abinda bawa ba shi da iko a kansa, ko daga labarin da na ba ki na ha

ɗ

uwarmu da Aliyu, ke kanki kin san ha

ɗ

in Allah ne ba yin kanmu ba. Wallahi na guji Aliyu kamar

gudun rai da ajali amma kuma ya zan yi tunda Allah Ya ƙaddara akwai

ɓ

oyayyen lamari tsakaninmu?"

Miƙewa Amrah ta yi a fusace.

"Na gaji da jin wannan tatsuniyar! Na gaji da jin wanin Hilal a bakinki Ramsy! Me ya shiga kwakwalwarki wai? Ramsy Hilal

fa? Mutumin da kika so a ganin farko, ban ta

ɓ

a zaton irin wannan son mai shiga a ya

ɗ

uwar farko yana shafewa ba. Shawarar da zan ba ki shi ne ki nemi za

ɓ

in Allah, kar ki biyewa zuciya ki yi saki na dafe, kar kuma ki biyewa sharrinta ki ƙare a za

ɓ

en tumun d

are! Ki sani babu hannun Amrah a cikin shafin Aliyu, har gobe ina sonki da Hilal kuma ina hango maki kyakkyawar rayuwa da mutum kamili irinsa da yardar Allah. Ban san Aliyu ba ban kuma ta

ɓ

a ganinsa ba, sai dai ina miki rantsuwa bai kwantamin ba. Allah Ya g

anar da ke Ramsy. Kin ban mamaki."

Daga haka ta juya tana shirin barin wurin ta ji amon muryar ƙawarta wanda ko cikin bacci ta tashi ba zai

ɓ

acemata ba.

"Hilal dai! Ke ki aureshi mana muga ƙarshen so!"

Ta yi maganar cike da tsawa da nuna jin

zafi ta ƙarara, anan Amrah ta gane irin nisan da Ramsy ta yi a lamarin Aliyu. Ta juyo a sanyaye, kuka ta yi zaman yi mai nuni da ranta na suya, tana tare da damuwa. Tausayi ta ba ta sai dai ba ta jin za ta ta

ɓ

a ba ta goyon baya ta bar nagartaccen mutum ma

i alƙawari irin Hilal akan wani wanda ba su san halayyarsa ba. Ta koma ta zauna gefenta, sai da ta bari ta yi mai isarta sannan ta soma magana a tausashe.

"Kiyi hakuri Ramsy, ki yi hakuri da dukkan kalamaina."

"Me za ki cemin tunda kin kasa fahi

mtana, idan kika kasance ta farkon juyawa lamarina baya, ya kike son na yi?"

Ɗ

an murmushi Amrah ta yi, tausayin Ramlat da kuma Hilal na cin ranta. Shakka babu an mishi kwacenta lamarin zai ba da wuya.

"Kiyi hakuri, na yi kuskure. Shawara kika bu

ƙ

ata ko?"

Ta gya

ɗ

a kai kamar wata ƴar goye.

"Addu'a, ki yi addu'a sosai na neman za

ɓ

in Allah. Ki hakura ki tausasa zuciyarki kar ki biyewa son ranki. Ramlat ga duk namijin da zai kiraki a lokutan da yake tare da matarsa ta sunnah har a ranki ki j

i maƙurar so yake maki ina tabbatar maki kin yi babban kuskure. Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganeta. Wannan cin fuska ne, ina roƙonki ki bar shiga hakkin wata saboda zai iya zuwa kanki ki ji haushi. Ba karfin sonki bane ya sanya, ki lura."

Ta ci gaba da ba ta shawarar mika lamura ga Allah da kuma ci gaba da

ɓ

oye batun Aliyu a gida, Ramlat ta dauki shawararta tunda ko ba komai akwai sauran lokaci na kammala karatun da kuma auren. A ranta ta kudurta ganar da Hilal a sannu-sannu yanda zai

fahimci ta sauya sheƙa ta kuma bar ra'ayin aurensa. Batun rabuwa da Aliyu bai taso ba!

"Amrah Abdullahi! Bala yana magana!'

Suka juya ga mai maganar, Zuhra Ishaq ce ƴar ajinsu wacce suka fi kira da Big Mama saboda ƙibarta, tun tana jin haushi har

ya zamemata jiki. Tsaki Amrah ta ja tana mai miƙewa da daukar jaka lokaci guda tana aikamata daƙuwa jin ta raina

direban gidansu wanda a haife ma zai haife su. Tare suka tako da Ramlat tana ƙara ba ta shawara.

"Nagode, zan yi aiki da shi. Ki tayani

da addu'a dai." Murmushi Amrah ta yi ta bita da toh, sai dai kuma ta san kafiyar Ramlat, fatanta kar ta jawo abinda zai hargitsa lamura.

Tun da yammacin ranar da suka yi waya ya sanarmata zai shigo bayan Isha'i su gaisa take cika take batsewa, duk wa

nda ya kalleta ya san ba ta cikin walwala.

"Ke kuma meke damunki wai?"

Fadin Zulaihat da ta wuni a gidan.

"Bar ta Uwani, ta yi kuncin ta gama, yanda kika ganta tun sadda ta ji labarin dawowar yaronnan take cika da batsewa. Ban san kuma me

hakan ke nufi ba. Ina fatan kar ta ba ku kunya."

Hajiya ke maganar ranta a

ɓ

ace don dama tun

ɗ

azun ƙuncin da Ramlat ke yi da tsakin da take bugawa akai-akai ke cin ranta, magana ce kawai ba ta yi ba. Maganar Hajiyar yasa Zulaihat kallonta dakyau, ga m

amaki ma hawaye ta shiga sharewa.

"Meke faruwa ne Ramlat? Kun yi fa

ɗ

a ne?"

Ta girgiza kai, takaicinta yasa Hajiya sungumar Khalifa yaron Zulaihat na farko suka bar falon. Zulaihat ta dawo gefenta ta zauna.

"Fadamin damuwarki. Ko Hilal din n

e ba ki yi murna da zuwansa ba?"

Duk kwarin gwuiwar da take tunanin tana da shi sai ta ji ta kasa kata

ɓ

us, ta kasa fadawa Zulaihat abinda ke ranta game da Hilal.

"Ko kin daina sonsa?"

Ta dubeta da sauri ganin ta harbo jirginta. Girgiza kai

Zulaihat ta soma tana murmushi gami da yi mata kallon yarinya karama don duka a sannan ba ta fi sha biyar ba.

"Kar ki soma don Allah Ramlat, ina mai tabbatar maki ba wanda zai goyamaki baya. Kar ki sake ki

ɓ

ullowa da wanin Hilal matsayin saurayinki.

Take-takenki kenan wanda ba zan so ya janyomaki wani tambari kuma abin yayatawa ba a dangi. Ture ma batun dangin da kuma mu, ba ki kyauta ba, za kuma ki amsa sunan mayaudariya. Ina so ki binne kuma ki ci gaba da ha

ɗ

iye abinda ke ranki, ki tattara wajen miƙ

a wa Ubangijinki. Shi zai za

ɓ

amaki abinda ya fi alheri. Kar ki yarda kuma kar ki yi gangancin bada kofar da za'a ƙara fahimtar inda kika dosa. Allah Ya kyauta don kuwa akwai matsala."

Daga haka ta mike ta bi bayan Hajiyar zuwa

ɗ

aki, itama ganin ba amf

anin zamanta sai ta koma

ɗ

akinta, kuka ta yi son ranta sannan ta fito. Ta ga alamar babu wanda zai fahimceta, zuwa yanzu za ta kwantar da hankalinta har ta kammala Sakandire, a wannan lokacin ne za ta san abin yi.

Da wannan shawarar ta

ɗ

an saki ranta

ta sauya, koda Hilal ya zo hakanan ta danne komai ta hau gyara jikinta babu ko kwalliya. Tana jin muryarsa yana gaisawa da su Hajiya, can kuma ta ji an murda kofar

ɗ

akin an shigo. A'isha ta gani.

"Yaya, Hajiyata ta ce ki je waje ga Yaya Hilal."

Ta gyada kai tana hararar A'ishar cike da bakin ciki. Mayafin abayar da ta sanya kawai ta ja ta rufe kanta, a falon ta tarar da Hajiya don tuni Zulaihat ta tafi.

"Hajiya zan je."

Ga mamakinta fuskarta a sake ta amsa.

"Toh wuce mana. Kar ki

kai dare dai."

Ta amsa da toh tana satar kallon ledojin da ke kusa da kafar Hajiyar wanda ba tantama shi ya kawo.

Yana tsaye jikin motar ƙirar Honda wacce ta yi daidai da zamanin. Bayansa take hangowa, cikar kamala da ingarman jiki irin na maza

ƴ

an kwalisa kuma abin muradin kowace mace, Hilal

ya kai. Tana tafe kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tana karantarsa, zuwa lokacin ya juyo shima ya zubamata idanunsa. Kallon da take mishi da ace a sannan akwai sauran cikakken nutsuwa tattare da shi, zai f

ahimci ba kallo ne mai nuni da kewa ba, kallo ne na ƙurillah, na ƙeƙe da ƙeƙe. Kallo ne na son gano abinda ya fi Aliyunta da shi wanda har ake zubamata gargadin

ɓ

oye sittin zuciyarta. Shakka babu ya sauya, fatarsa ta kara murjewa, farinsa kuma ya kara fito

wa. A gefe guda ya kara kyan da zai burge ƴanmata banda ita.

"Assalamu Alaikum." Ta furamta muryarta can ƙasan maƙoshi. Ya amsa yana mai jin kamar ya sanyata a aljihu su tafi tare.

"Ina wuni. An dawo lafiya?"

Nan ma bai ƙasa a gwuiwa ba ya

amsa kafin ya bata umarnin su koma wurin kujeru zai fi. Suna tafe yana kallonta yana murmushi, ita kuwa banda guntun tsakin da take a ƙasa ranta ba komai. Hankalinta ma kacokan ya koma ga wayar da ta baro jone tana chaji, tsoronta kada Aliyu ya kira ba ta

kusa ya yi fushi.

"Fa

ɗ

in yanda nayi kewarki ma

ɓ

ata baki ne. Ban ma san da kalmar da zan yi amfani wurin nunamaki kewarki da nayi ba. Ina sonki My Future, ba don akwai sauran rina a kaba ba, ai da aurenmu ko wata ba zai kai ba."

Ya ƙarashe za

ncen a marairaice, ba ta san sadda ta watsamishi wani kallo ba wanda ya ba shi dariya don a zatonsa na wasa ne.

"Ok I'm Sorry, I don't meant it. Sai dai har ga Allah ina jinki sosai a raina. Kamar fa karamaki kyau ake."

Duk wasu kalamai da yake

fadi ba burgeta yake ba, murmushin yaƙe kawai take a wasu lokutan don ba yanzu take son fito da abinda ta binne ba. Duk kokarinta sai da Hilal ya gane kamar da matsala. Ganin haka ya nunamata zai wuce sai an kwana biyu tunda ya dawo kenan.

"Kamar ba k

i yi murna da ganina ba. Haka kawai jikina ke ba ni kamar akwai matsala. Please ki fadamin kuskurena ni kuma na miki alƙawarin gyarawa."

Tsaki ta ja a kasan ranta, a fili kuwa ta yi murmushi.

"Na yi murna sosai fa, kawai dai yau na wuni da ciwon

kai. Kuma hakanan nake jin jikina ba dadi. Kar ka damu."

Ta shiga istigfari a ƙasan ranta, shi kuwa tuni ya rude don dagaske ya yarda.

"Shi ne ba ki fadamin ba, ban ji dadi ba. Please yi hanzari ki je ki sha magani ki kwanta kinji? Zan kiraki an

jima."

Ta gyada kai.

"Nagode. A gaida su Umma." Ta juya da sauri don dama jinta take kamar a kan ƙaya.

"Hey!" Dole ta dakata gami da juyowa. Yana rike da murfin mota yana bin ta da kallo kamar ya ha

ɗ

iyeta.

"I so much love you!"

Ma

imakon ta amsa, sai ta bishi da murmushi da azama ta juya ta ci gaba da tafiya, a bangarensa ya fassara hakan da kunya. Wanda shi ke karamasa ƙaimi wurin sonta, duk kuwa da wani sashi na zuciyarsa bai gamsu da tarbar da ya samu ba.

'Na yi tunanin fiy

e da haka, zumu

ɗ

i, walwala,

ɗ

oki.'

'Ka manta ba ta da lafiya? Ka yi mata uzuri. Ba ta da abin so idan ba kai ba.'

Da wannan tunanin ya ji karfin gwuiwa, hakan ya dawo da walwalarsa, burinsa yanzu ya ha

ɗ

a dukkan takardun karatunsa ya bautawa ƙasar

sa sannan ya kama aiki. Hankali da nutsuwarsa kacokan su dawo kan abar sonsa.

***

Tafiya na ta tafiya, rayuwa na zuwa na sauyi masu tarin yawa. Kama daga siffofin halittu har ya zuwa zuciyoyi da kuma nasarori ko akasinsa.

Hakan ce ta faru da Ram

lat sadda take cuku-cukun zana jarrabawar WAEC/NECO don hada kwalin Sakandire. Dukkan wata cika ta ƴa mace ta sameshi idan ka cire rama da ƙashin wuyar

da ta yi sakamakon zullumin da ta jefa kanta ciki ganin na taso da shiri gadan-gadan na aurenta da Hila

l da zai biyo baya nan da watanni hudu.

"Ke za ki soma shiga gidan aure a class din mu. Ina ji daga ke sai G smally."

Fa

ɗ

in Amrah sadda take kokarin gutsirar eggroll da ta ke korawa da lemun Pepsi. Da gayya ta ƙi duban fuskar ƙawarta don tasan c

ikin dayan biyu ne, ko ta samu harara ko kuma..

"Mtsw, aikin banza!"

Murmushi Amrah ta yi ganin ta ƙarasamata tunanin da ba ta san tana yi ba.

"Mene abin tsaki? Ai gwara ki yi wani sabon abin, ba abinda zan fahimta. Tunda ke ba kya jin shaw

ara har ta kai matakin da za ki karyar zuwa gidanmu don kawai Aliyu ya zo ku gaisa."

Kwarewa Ramlat ta kusan yi da lemun Mirinda da ta ke sha. Murmushi Amrah ta yi ta ci gaba da cin Eggroll dinta hankali kwance.

"Allah Ya isa, kina neman kashe

ni da rai. Toh wa kike fa

ɗ

awa? Ke bari na fadamaki, yanzu ko kofar gidanmu Aliyu zai taka ba na fargaban komai. Ke dai ban sanki da tone-tone ba. Gwara ki ci gaba da

ɓ

oyen wannan sirrin. Ni wannan yanzu bai fiye damuna ba. Damuwata wai Muhibbat tana da cik

i. Kuma cikin Aliyu."

Ta ƙarashe tana mai jin kwalla na cika idanunta, baki sake Amrah ke dubanta. Karshe sai ta sanya salati kafin ta

ɗ

ora.

"Kin hadu da aiki, kin kuma hadu da wahala wallahi Ramlat. Shiga hurumin kuma da ba naki ba za ki fara?

Amma dai ina fatan ba ki nuna bakin cikinki a gabansa ba? Tunda ke ba kya aiki da hankalinki yanzu."

Guntun tsaki ta ja gami da harararta wanda ya yi daidai da zubowar hawayen.

"Mene naki a ciki idan na nuna toh? Waye ba ya kishin abinda ba y

a so? Ban gama sanin mene aure ba, amma naji a wurin wadanda suka yi cewar idan mace tana da ciki tana samun kulawa sosai a wurin miji, yana kuma son abinda ke cikinta. Hakanan kuma soyayyar zai koma kan abinda ta haifa, duk kuwa da 100% nasan Aliyuna ba y

a son Muhibbat amma kishi halal ne."

"Kishi da matar aure? Matarsa ta sunnah? Ramlat kina tsoron Allah kuwa? Kar ki yarda ki zama mai irin wannan kishin na hauka, kar ki yarda ki haramta abinda Allah Ya halarta. Cin amanar Muhibbat da ku ke yi kuna w

aya har tsakar dare bai isheki ba sai abinda ke cikinta ya tsonemaki idanu? A'a Ramlat, kar ki kusa kuma kar ki yarda ki dora kanki a wannan turbar. Wallahi da ace akwai halin da za'a iya ciro zuciyar mutum a cire son wani a ransa, da tuni na ciro taki na

wanketa tas na cire sunan Aliyu na maida gurbinsa da na Hilal. Ke da kanki kin fada da bakinki Hilal yana sonki, ya kuma gane cewar yanzun ba kya sonsa, kin ce ya sha kiranki ya ji call waiting, hakanan bai karaya ba kuma bai fasa batun aurenki ba. Wane so

ne zai biyo bayan wannan? Yan uwansa da Mahaifiyarsa suna sonki, suna ganin girmanki, ji yanda Anti Bilki ke miki kamar kanwarta da ku ke ciki

ɗ

aya. Akan wani can da ba ki da tabbacin aurensa kin sanya ƙafa kin ture duka wannan karramawar da Ubangiji Ya y

i miki, kina kara cusa kai inda ba lallai ki yi kwarjini ba a idanun ƴan uwa da iyayensa. Kar ki manta, Muhibbat cousin sister

ɗ

insa Kuma matarsa ce, ina rabaki! Ina rabaki!"

Ko ba'a fa

ɗ

a ba jikinta ya yi sanyi, sanyin da ya zama na fargaba. Ko ba ko

mai kalaman Amrah sun dan ta

ɓ

a zuciyarta amma hakan bai sa ta ji za ta iya hakura da muradinta ba. Don haka ta dubeta kurr.

"Kamar yanda ki ka ce Allah Ya karramani, kar ki manta Shi ke iko da zuciyata. Ba ni na sanya son wannan Bawan a raina ba, hak

a kawai na wayi gari da so da kaunarsa. Ba kuma zan iya hana kaina ba, batun shiga hakkin Muhibbat naji zan karbi hakan, zan daina. Amma ki sani, ba zan taba ganin kiran Aliyu na ƙi

ɗ

agawa ba koda ace ina tsakiyar Teku ne ina kokarin nitsewa ba. Ba zan yi

ba kuma ba zan fara ba. Zan kuma yi kokarin

ɓ

oye kishina a kanta, saboda abu ne da idan aka yimin ba zan ji dadi ba, sai dai so hana ganin laifi. Ki bar sanya auren Hilal cikin ƙaddarata, babu shi, babu shi kwata-kwata a littafin rayuwata, kedai Allah Yasa

mu kammala karatu lafiya. Duk wannan shirin da su Abba da Hajiya ke yi kallonsu nake, don zai tafi ne a gidana da Aliyu in Sha Allah."

Murmushin da take bugawa ya sa Amrah ƙara gasƙata zurfin soyayyarta ga wannan mutumin.

"Allah Ya kyauta, Ya

hanemu mugun ji da gani." Abinda ta iya furtawa kenan kuma magana ta karshe tsakaninsu kafin su mike su shiga aji karfe uku don gabatar da lesson duk a cikin shirin zaman jarrabawa.

***

Juyi yake yana kara tunanin zantukan da ya yi da Ramlat game

da shirin aurenta da aka fara, gaba daya kansa ya kulle don ji yake muddin ya rasata ba shi da sauran nutsuwa balle kwanciyar hankali, ya kai duba ga inda Muhibbat ke kwance tana bacci sannan ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. https://my.w.tt/At9

9ZcOeF9



🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯





_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

10)

Tarr ta bude idanunta jin motsin bude kofar. A hankali ta kai hannu saman dirowa ta dauko wayarta gami da duba lokaci, karfe uku saura

mintuna, mayarwa ta yi ta ajiye kirjinta na wani irin zugi tana cin

ɗ

aci a maƙogwaro. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar falon, kunnuwanta ba zasu iya juriyar sauraron

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login