Showing 249001 words to 252000 words out of 255051 words
tana kallon kowa na shiryawa, maganar duniya su Zulaihat da su Kausar sun m
ata akan ta tashi ta shirya amma ta ce sam ta fasa.
"Adda Amal kina cewa ba za ki je ba, ga Hamma Hussein can ya ci uban kwalliya ya fita, kuma wallahi idanun ƴanmatan nan kamar su tsiyaye tsabar kallonsa."
Jin abinda Falmata yar uwar su Hussein
ta Maiduguri ta fadi, ai sai Ramlat ta mike tsaye ranta na susa. Nan aka kwashe da dariya, har itama ta murmusa.
"Kishi kumullon mata, ki zauna dai kar ki je. Wallahi sai dai ki ji ana wani labarin."
Ita dai Ramlat ba ta biyewa zancen Rafee'ah b
a ta shiga bandaki bayan ta rage kayan jikinta, tana ji su na mata dariya. Wanka ta ƙara yi duka rabin hankalin na ga tunanin Hussein, abinka da zuciya, sai nan da nan ta ji itama ai ya mata laifi, ta ji ya bata haushi sosai. Kwafa ta yi tana ƙara cu
ɗ
a sab
ulu a jikinta, aikuwa ta ci alwashin itama ko kallo bai isheta ba a wurin taron. Ta fito ta shirya, da yawansu sun fice har su Rafee'ah da maman Twins. Aisha da Falmata da kuma Asma'u diyar Hajja Fatuma uwargidan Modibbo sai wata Hannatu itama daga Maidug
uri, su ne kadai suka yi zaman jiran Ramlatun don su wuce a motarta.
Leshinta da suka yi anko kalar milk kai adon golden brown ya yi masifar sama a jikinta, ya sha aikin stones shi ta fiddo ta zura. Falmata ta yi mata make-up na fitar hayyaci, kasance
war kwalliyar zamani mai kama da na aljanu bai damu Ramlat ba don ba irinsa ta fi yi ba, sai ta fito ta yi wani azababben kyau. Daman su Rafee'ah yanda suka ga ta sauya fatarta ta kara kyau da sul
ɓ
i yasa suka dinga yi mata zargin mai ciki, ita kanta sau
yawar na ba ta mamaki.
"Wallahi na fadamaki wani abu? Nidai ba ki ta
ɓ
a kyau irin na yau ba, ko bikinki albarka."
Aisha ce ke maganar tana dariya, harararta Ramlat ta yi ta ja guntun tsaki ba ta ce komai ba, wannan duk abinda ta yi
ɗ
anawa Hussei
n tarko ta ke son yi yanda zai yi dana sanin wannan fushin da ya
ɗ
auka da ita. Har tunani take ko wa ya sanya a gaban mota suka tafi? Nan fa ranta ya ƙara sosuwa. Ta mike ta yafa mayafinta golden ta dauki purse dinta mai kyalli shima golden, turare mai san
yin ƙamshi ta fesa kafin ta zura takalminta da ya kasance maha
ɗ
in purse din, ta dauki mukullin motarta. Ku
ɗ
in liki kam dama tuni sun tsufa a cikin ƴar jakar don tun safe suka bada aka yi masu chanji kowacce ta adana abinta.
"Muje." Ta basu umarni, du
k suka fito ta rufe ko'ina na gidan. Su Ummi na sashen Dada da yara ana ta wasa don yanzu ba su fiye wani kewar uwartasu sosai ba balle su liƙe mata.
Tana tuƙin amma fuskar ba wawalar a zo a gani musamman da ta ga dagasken dai babu motar Hussein a far
fajiyar gidan. Aisha ta karanceta tsaf, ta san kishi kawai ke cin ƴar uwarta don haka ta bar janta da hira ta maida akalar hiran ga su Falmata dake zaune a baya haka har suka isa ƙayataccen
ɗ
akin taron na FARHAS Event Centre (Dan Adam).
Farfajiyar wur
in sai
ɗ
ai
ɗ
aikun jama'a, sai da duk suka fita, sannan ta bi bayansu. Aisha ko jiranta bata tsaya yi ba don ba ta son a huce a kanta. Ta na takunnan mai girgiza zuciyar masoyinta kuma mijinta, wanda ya zama normal tafiyarta. Haka ta ƙarasa har ta shiga ciki
. Wuri fa ya cika, gaba
ɗ
aya kowa na zaune ana kallon MC wanda ya fiddo Amare da Angwayensu tsakiya yana basu umarnin zama saman wasu kujeru a tsakiyar wurin, wannan yasa hankalin da dama suna kansu ana dariya a nisha
ɗ
ance. Sun ha
ɗ
a ido, sai ta dauke kai k
amar ba ta ganshi ba, wani irin tururi kanta ke yi ganin wata kyakkyawar budurwa a gefensa zaune, shi kuwa AlHassan Madam dinsa ce a gefensa sun ba MC hankulansu. Takaici ya sanya kawai ta ja kujera ta zauna ba tare da ta ƙarasa wurin su Rafee'ah ba, sai m
a bayan ta zauna ta
ɗ
ago kai ta ga ashe ƴanmatan gidan kakannin su Hussein
ɗ
in ne.
"Kai Adda Amal you look beautiful wallahi."
Ta dubi mai maganar Teema ta yi murmushin da bai kai zuci ba.
"Thank you. Kuma kun yi kyau."
Daga haka ta maida h
ankali da fiddo wayarta dake faman vibrating, ganin lambar Hussein kawai sai ta maida wayar jaka. Tana
ɗ
aga kai kuwa ta hango su Kausar na
ɗ
aga mata hannu alamar ta ƙaraso. Hannu kawai ta
ɗ
agamata shaidar inda take ya ishe ta. Sai da aka kira dangin Ango
Tahir don su yi liƙi sannan ta mike suka
ɗ
unguma har su Teema, a hanya suka ha
ɗ
e da su Rafee'ah aka shige fili, Maman twins na rantsuwar a farko ba ta ganeta ba. Sai dai su na liƙin tuni mazan suma suka taso don zazzage nasu aljihun, ta
ɗ
aga hannu da nuf
in somawa ya kai hannunsa saman nata. Juyowa ta yi har fuskarsu na ha
ɗ
uwa numfashinsu na gauraya wuri
ɗ
aya. A hankali ya zare kudin a hannunta ya shiga liƙawa kaf a kan Amarya da Angon, ta juya za ta wuce ya riƙe hannun gam suka fita tare. Maimakon su kom
a mazauni sai kawa ya yi waje da ita har wurin motarsa. Ta fincike hannunta, tuni idanunnata sun cicciko da kwalla.
"Ka kyale ni."
Hussein ya tsaya kawai hannunsa a kirji yana karemata kallo, ta yi mishi irn kyan da baki ba zai iya fa
ɗ
i ba. Tsana
nin kewarta da son kasancewa da ita ne ke cin zuciyarsa.
"Da iznin wa ki ka zo nan?"
Ta tsuke baki, ya kuwa bishi da kallo yana cije lebba.
"Ka riga ka san da fitar ai."
Ta fadi cike da dakiya. Bai ce uffan ba ya juya ya yi amfani da m
ukullin motarsa ya bude, hannunta ya kama ya zagaya da ita ya bude gaban motar da nufin sanyata ciki. Ta dubeshi da zummar magana, sai dai yanayin
ɗ
aurewarsa ya ka
ɗ
a hanjinta ba shiri ta hadiye abinda take shirin fadi ta shiga a fusace tana huci. Sai da ya
zagaya ya zauna sannan ta dubeshi.
"Motata fa?"
Bai ce mata uffan ba ya yi ribas suka fice. Ranta ya ƙara zafi gashinan ko hoto ba su yi ba da Amaren balle kuma ƴan ankon.
"Amma kasan ba kai ka kawoni ba ko?"
Idan motar ta bata amsa,
toh Hussein ya bata. Wayarta ce ta shiga ringing, ta ciro, kafin ta duba ko ta
ɗ
aga ya kar
ɓ
e. Ba ta san me aka ce ba kamsr yanda ba ta san wace ce ba.
"Muna tare."
Daga haka ya katse kiran ya jefa wayar aljihun gaban riga. Ramlat dai har da hawa
yen takaici, ba ta bar haskoshi da waccan budurwar ba kamar yanda ta ke jin zafin raba ta da wurin bikin da ya yi.
Su na isa gidan ya sa hannu ya zare purse dinta yana kallonta tsakar ido Ta kauda kai tana tura baki. Dariya ma ta ba shi ya murmusa. M
ukullin motarta ya zare ya miƙa mata. Yana unlocking kofofin ta bude ta fice zuwa sashinta ranta a jagule. Shi kuwa sai da ya ba direba mukullin da kudin mota akan ya koma idan an tashi ya taho da wa
ɗ
anda suka je a cikinta.
***
Tana shiga
ɗ
akinta ta
fa
ɗ
a saman gado ta shiga rera kuka kamar wata yarinya ƙarama. Ganinta kwnace saman gado tana kuka ya hau doka murmushi, kawai ji yake ya rama shariyar da ta dinga yi mishi a kwanaki biyunnan. A nutse kuma ya soma takawa har ya karasa gadon. Jin ƙamshin tu
rarensa sai ta
ɗ
ago ta share fuska, kokarin mikewa ta ke yi ya riƙo hannunta gami da jawo ta ta fa
ɗ
a jikinsa. Kanta bisa kirjinsa gaba daya fuskarta ta nutse yayinda hancinta ke shaƙar dadda
ɗ
an ƙamshin turarensa. Lumshe idanu ta yi sadda ya sa hannuwansa
gaba daya ya rungumeta tsam. Sai a sannan ta kara tabbatar da cewar ta yi kewar mijinta. A hankali ya zame
ɗ
ankwalin kanta ya shiga shafa gashinta.
"Duk kawaici da kauda kan da nayi maki don naga gudun ruwanki, ba ki gane ba ko? Kin maida ni kamar wa
ni hoto, kin nunan sabgar gabanki ya fi ni ƙima da muhimmanci. Tun soma bikinnan ba ki da lokacina, ba ki damu da ni ba. Shikenan ni kuma sai na kasa nuna
ɓ
acin raina?"
Yanda ya ke magana a tausashe sai jikinta ya yi sanyi, shakka babu kam, ba ta kyau
ta ba. Ta
ɗ
ago a hankali ta dubeshi tana narkar da fuska.
"Ka yi hakuri. Na sani ban kyauta ba, amma don Allah ka yimin uzuri tunda dai ka sani biki ne ake yi, ga baƙi ina da su."
Ya kama ha
ɓ
anta suka tsurawa juna ido.
"Sai kuma ki ke jin na
uyin kwana da mijinki don kina da baƙi? Ki ka kyalewa wasu ƴan matan shi su samu matsugunni a nan?" Ya nuna kirjinsa yana
ɗ
aga mata gira da murmushi.
Nan da nan kishin ya dawo sabo fil ta tureshi za ta mike, ya kara fisgota ya rike gam yana dariya.
"Na dauka kishiyar kike ra'ayi."
Ba ta san sadda ta harareshi ba, don mamaki sai ya yi dariya.
"Shiyasa na ganka da wata busashshiya kana yawo da ita a cikin bainar jama'a don ka zubarmin da ƙima a gane ni Ramlat ban da wata daraja da.."
Bai bari ta karasa ba ya tallafi ha
ɓ
anta ya ha
ɗ
e bakinsu wuri guda da zafi-zafi.
Tun tana yunkurin ƙwatar kanta har dai ta saddaƙar. Can kuma da kansa ya sake ta, ya mike yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Da wata irin kasala ya miƙa mata hannu, b
a musu ta miƙamasa, suka
ɗ
unguma zuwa nashi
ɓ
angaren. A nan kam alƙalami ba zai iya wassafa yanda masoyan suka kasance ba cike da matsanancin kewar junansu. Ranar dai dinner anan suka ci suka sha abinsu.
Koda jama'a aka dawo, ta sha tsokana sai toshe
kunnuwanta ta yi kawai.
***
Sati biyu da kammala biki, jama'a kowa ya watse, an miƙa Amarya Hafsat zuwa Kano, tafiyar da ba'a yi tare da Ramlat ba don sam Hussein ya ce ita da Kano ba yanzu ba. Haka ta hakura, Rasheeda kuwa Abuja aka miƙa ta wurin
aikin mijinta.
Tun bayan bikin ya kasance Ramlat ba ta da kuzari, koyaushe tana kwance, wani lokacin bacci wani lokacin kuwa yanayin jikin ne kawai ba ya mata dadi. Dada kanta ta soma fahimtar sauye-sauyen Ramlatun, abinka da babba, sai ta ce mata l
allai ta yi zamanta a
ɓ
angarenta ta dinga hutawa tunda a sannan Dada ba ita kadai ba ce, wata dattijuwa kuma yar uwarta dake Mubi, Mariya ta dawo nan domin taya Dada zama. Mace ce da ba ta ta
ɓ
a haihuwa ba ga kuma girma da ya
ɗ
an kama ta babu mijin aure. I
ta kanta tana jin dadin zama da Dada.
Kamar koyaushe, yau dinma tana kwana a falo, daga ita sai vest fara mara hannu da wando pencil da bai karasa ƙaurinta ba. Tun fitar Hussein take jin tashin zuciya, ta rasa meke mata dadi. Kamshin komai a gidan ma
ji ta ke yana hawa kanta, karshe ma miƙewa ta yi kawai ta zura dogon hijabinta ta zagaya
ɗ
an barandarsu da ake hango garden ta shimfida ƙatuwar dardumarta ta zauna. Ba laifi ta
ɗ
an ji sauyi, ahankali kuma bacci ya yi awon gaba da ita.
Sallama ya yi
har sau uku shiru, da mamaki ya karasa shigowa falon a karshe ya shiga leƙa kicin da dakuna. Bandaki ma wayam, yana shirin leƙawa sashinsa ya hango ƙofar fita ta hanyar kicin a bude don haka ya karasa. Sosai abin ya ba shi mamaki, ba ta ta
ɓ
a yin haka ba, g
a dai iskar fanka da komai a falon amma ta dawo nan ta kwanta, yanzu kam ya yarda ba ta da lafiya. Karasawa ya yi ya sa hannu saman goshinta. Zafin da ya
ɗ
an ji ne ya sa shi shafa gefen fuskar.
"Ya Salam."
Jin hannunsa ta yi firgigit ta farka da
salati. Ya kama hannunta.
"Sannu Heart, dama ba ki da lafiya? Tashi muje asibiti."
Ta mike zaune tana shafe fuskarta, sosai kam ta yi bacci don har yamma ta kawo kai, ta tuno ko sallah ba ta yi ba.
"Ban yi sallah ba."
Ya taimaka mata ta
mike, yana rike da ƙugunta suka ƙarasa ciki, sai dai su na sanya kai a falon ƙamshin airfreshner da ta fesa ya hautsina mata ƴan hanji. Tana kokarin zama jikinsa daga natata hanyar amfani da hannun damanta ta dora saman kirjinsa za ta tureshi, shi kuwa ƙa
ra riƙo ta yake a rude yana tambayar lafiya. Sai dai ina! Tuni ta soma sheƙa amai har yana
ɓ
ata jikin Hussein. Nan da nan ta zaro ido a rikice, ba ta mance sadda ta yiwa Aliyu amai a jiki ba ya
ɗ
auketa da lafiyayyan mari yana
ɗ
ura ashariya.
"Ka yi ha
ku.."
"Shii! Muje ki wanke jikinki." Ya ja ta suka nufi bangarenta, sai da ya cire rigarsa da ta
ɓ
aci har da singilet, kafin itama ya ciremata nata dogon hijabin. Bandaki ya shiga ya hada ruwa. Wankan suka yi tare, duk wani abin ƙamshi da ya
ɗ
auko za
ta girgiza kai ta ce ita ba ta so, Hussein dai murmushi ya ke da fatan Allah Yasa abinda yake tunani ya tabbata. Sai da ya daukomata kaya sannan ya wuce sashinsa
ɗ
aure da tawul a ƙugu. Ƙananun kaya ya sa kawai ya fesa turare. Aikuwa tana jin ƙamshin turare
nsa ta fada bandaki a guje ta shiga sheƙa wani aman, koda zai shigo ya dakatar da shi kamar ta yi kuka.
"Ni bana son kamshin turarenka."
"Toh fa." Ya tsinci kanshi da fa
ɗ
i, turaren da a baya take masifar so kenan, Sorry kawai ya furta sannan ya f
ita daga dakin. Kaya ya je ya sauya sai dai wannan karon bai yi gangancin fesa turaren ba. Suka
ɗ
unguma suka wuce asibiti, ta waya ya shaidawa Dada ya kai Ramlat asbiti. Dada murmushi kawai ta yi da addu'ar Allah Ya bata lafiya.
Kyakkyawan albishir di
n da ya yi fata kuwa shi ya samu, wato dai ciki ne da ita. Yanda ya dinga tarairayarta tun daga asibitin har gida, ita abin ma kunya ya dinga ba ta.
Tun daga ranar kuwa kulawar da Hussein ke ba ta na musamman ne, tausayi sosai ta ke ba shi ganin yand
a ta ke laulayi mai wahalarwa. Ita kanta abin tsoro ya dinga ba ta, gani take kamar wannan haihuwar farko ne za ta yi don komai sabo ta ke ganinsa.
Kafin watannin haihuwar su cika gaba daya ta sauya, ta rame, sai ƙaton ciki wanda scanning ya nuna
ɗ
a
ɗ
aya ne kawai. Kowa kallon mai haihuwar biyu yake mata, duk yanda ta so ya bari ta je Kano ta haihu ya ƙi, itama don kanta ta hakura da batun zuwa don ko nawa za'a ba ta a yanda take ji, ba za ta iya bin hanyar Kano ba.
***
Bacci ya ke sosai, yayin
da ita kuwa baiwar Allah ta zubawa silin din
ɗ
akin idanu wanda hasken farin wata ya haska, mararta da bayanta babu inda ba ya ciwo, a hankali ta miƙe zaune tana cije baki, ta rasa ma ina za ta sa ranta, wani irin mur
ɗ
awa da ya yi ba ta san sadda ta
ɗ
akawa
Hussein duka ba. Ya mike kuwa firgigit don a farko bai dauka mutum ne ya dakeshi ba, hannu yasa ya kunna fitilsr bedside yana kallonta gami da ruƙo ta.
Ta matse hannunsa ƙam!
"Mutuwa zan yi wallahi!"
"No! Naƙudar ce? Bari muje asibiti."
Haka ya mike tsaye yana gyara zaman pyjamas dinsa. Dakyar ya samu nutsuwar ganin mukullin motar, ficewa ya soma yi da ita, Buzu Maigadi da fitowarsa daga bandaki kenan, ya ajiye butar ya karaso da sauri ya taimaka ya karbi mukullin motar ya budemishi ya
na kwaranyo addu'ar Allah Ya bata lafiya. Lokacin wuraren ukun dare ne. Sai da Hussein ya zaunar da ita kafin ya koma a guje ya dauko akwatin da tun shigar cikin wata tara ta ha
ɗ
a abinta.
Su Dada basu sani ba sai ƙarar bu
ɗ
e kyaure da rufewa suka ji.
Ba shiri ta fito ita da Baba Mariya a ru
ɗ
e, nan Buzu ke fadamusu Madam ce ba lafiya. Nan da nan a rude suka kira wayar Hussein, amma ina tana ta ringing bai
ɗ
aga. A dole suka koma ciki don ba direban da zai kai su. Nafiloli suka shiga yi da addu'ar Allah Y
a sauketa lafiya don sun sani loda sun je, ba abinda za su iya yi mata sai addu'ar.
***
Ramlat suna zuwa ko awa
ɗ
aya cikakka ba ta yi ba ta haifo
ɗ
anta namiji, sai