Showing 81001 words to 84000 words out of 255051 words
daga kan diyartasu har sai da aka
ɗ
auki lokaci.
"Aliyu kana wahalar da ni, kana cutar da zuciyata. Aliyu don girman Allah ka sassautamin."
Ta fadi a raunane don ba ta ma san wane irin sassauci ba, ai ba s
hi ta sanya sonsa a kirjinta ba. Kuma bai da ikon cirewa, balle ya yaye din.
"Fadamin, me da me kike so na bari, zan daina har abada. A kanki yau Malam har kuka ya yimin ya kuma rantse idan ban je na nemi gafararki da ta iyayenki ba sai ya kwashemin
albarka."
Murmushi mai ciwo ta yi. Tasan a zuciya da zafi irin na Aliyu ba dai ya tako kofar gidansu a karan kansa ba. Dama dai da walakin goro a miya don Malam din shima har rago ya kawo na suna, ya zamana raguna biyu aka yankawa Ummi da na Abban.
Ta kuma fahimci Aliyun da Malam yanzu ba laifi sun sami jituwa.
Ban baki, rarrashi, alƙawari daban-daban, ba irin wanda bai daukarmata ba kafin ya yi mata sallama da zummar zai kira waya.
***
Hajiya ta yi mata ƙuri da idanu yanda take
ta shirin komawarta gidan Aliyu. Magungunan duk da ta kawomata na gyaran jiki ta shanye tas. Ta sallama lamarin Aliyu da Ramlatun, ta san kuma muddin wani ya shiga tsakani shi zai sha kunya. Tana da tabbacin abinda Abba ya hango kenan shi ne dalilin kama
bakinsa da kuma rashin saurin yankewa lamarin nasu hukunci.
"Hajiya na shirya."
Maganar Ramlat din ya katse mata tunani, ta kara dubanta. Ta sha daya daga cikin atamfarta Holland wanda Abba ya siyamata na fitar suna, ta yi kwalliya daidai gwarg
wado abinta. Ummi an mata kwalliya itama sai kamshi take abinta. Ta kauda kai ta share ƴar kwallar da ta cika idanunta.
"Shikenan Ramlatu, Allah Ya kiyaye hanya. A ci gaba da hakuri dai. Kowa da kaddarar rayuwarsa. Tashi ki je Abbanki na falo."
Ta amsa da toh gami da nufar ciki. Hajiya ta bita da ido, duka-duka yarinyar ko shekaru ashirin ba ta kai ba amma jarrabawar rayuwa sun mata dabaibayi.
"Allah Ya kawomaki sauki cikin lamuranki."
Ta furta a fili.
***
A can ma Abba nas
iha ya yi mata sosai kafin ya ba ta kudi sosai ya kuma ce ta yi kokarin bude bank account ko don ma makaranta. Ta yi ta godiya har da hawayenta sannan ta mike ta tafi ya bi bayanta da ido. Ji yake da yana da halin sauyamata wannan kaddarar da tuni ya yi, s
ai dai komai na hannun Madaukakin Sarki wanda za
ɓ
i da kuma ikonSa ya fi na kowa da komai.
***
IDAN KIƊA YA I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/5VwehILsqab
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
*
_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
23)
IDAN KIƊA YA CHANJA...
Watanta biyu da dawowa gidan, komai ya sauya. Shaye-shayen Aliyu ya ta'azzara duk kuwa da yanda yake kara ramar da shi, yake kara motsewa. Akwai sadda ta ba
r Ummi a falo tana kicin, sai fitowa ta yi ta ga hayakin shisha na tashi a falon yarinya na jan numfashi dakyar. Ranar har dukanta ya yi saboda cecekucen da suka yi. Ta gaji iyakar gajiya, wannan ne yasa gaba daya rabin hankalinta kacokan ya koma ga kula d
a Ummi. Idan ka ga dariyar Ramlatu toh tana tare da
ɗ
iyarta ne. Tana yawan shiga wurin Maman Anas duk kuwa da gargadin Aliyu, har ya yi ya bari. Maman Anas itama takan shigo su yi hira ta kara bata shawara da adduo'i. Don halin Aliyu ba
ɓ
oyayye bane.
***
Wataranar Talata ta dawo daga makaranta a gigice, Ummi ke kuka ta rasa meke damunta. Ta yi rarrashin ta shayar da ita amma shiru, kuka ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa. Waya ta dauka ta kira Aliyu bayan ta yiwa yarinyar wanka ta sauyamata sutura.
"Ki ka
i ta asibiti mana."
"Da ace da kudi a hannuna kaima kasan daga makarantar zan kiraka na wuce. Wallahi kudin mota kadai..."
"Naji kar ki isheni. Nima dai kinsan ba wani kudin a jikina. Kuma dama sai yau kika san amfanina har kika kirani, kwanakinn
an ai na dauka kin koma ƴar kanki mai cikakken iko. Tunda ko ba komai na bar ki kin koma jami.."
Ta katse kiran, ba ta son hayaniya, kukan Ummi kadai ma ya isheta. Ta dauketa bayan ta zura hijabi ta fice gidan Maman Anas.
"Kukan me take haka?" F
adin Maman Anas sadda ta sa hannu tana kar
ɓ
arta.
Itama Ramlat kamar ta yi kukan ta ce.
"Wallahi ban sani ba, tun a makaranta take kukannan kinga ba mu tashi ba ma na taho kawai."
Nan Maman Anas ta ta
ɓ
a cikin ta bubbuga.
"Ga abinda ke d
amun yarinya, cikinta ne a kumbure."
Daga haka ta yi mata dabarar su ta manya, gishiri ka
ɗ
an ta sa a ruwan
ɗ
umi ta ba ta, aka samu cikin ya lafa ta yi shiru. Ganin haka ta miƙamata ita.
"Sa mata nono a baki."
Ba musu Ramlat ta kar
ɓ
e ta, sai
lokacin hankalinta ya
ɗ
an kwanta. Ta shiga ba yarinya, karshe ma yarinyar ta daina kar
ɓ
a ta yi shiru, can ta soma nishin kashi. Ganin haka Ramlat ta yi dariya. Harara Maman Anas ta watsamata cike da wasa.
"Kinji ki, sai yanzu kika samu nutsuwa kenan?
Ramlatu kenan."
Dariya ta kara yi. Nan kuma ta mike hadi da yi mata godiya ta bar gidan.
A bakin kofa ta tarar da mashin din Aliyun, wannan ya bata tabbacin ya dawo gidan.
Babu fargaba ko shakkar komai ta shiga ciki, a falon ta tarar da shi ya
na safa da marwa, tana shigowa ya yi kanta kamar zai kai mata duka, ba ta ko kalleshi ba ta gifta ta wuce. Ya bi bayanta zuwa dakin.
"Don tsabar iskanci ina magana kin katse waya kuma kika fita ba da iznina ba? Ita Maman Anas dinnan ko uwarki ba kya
jin maganarta yanda kike jin nata a yanzu! Toh wallahi Ramlat kika kara shiga gidan matarnan ban yafemaki ba!"
Kamar da dutse ya ke magana, haka ta yi shiru ta cirewa Ummi wando ta dauketa zuwa ban
ɗ
aki don yi mata tsarki.
"Kee! Ni kika maida
ɗ
an
iska ina magana kin kyaleni?"
Tana jinsa ta yi banza har sai da ta gama uzurinta ta fito ta sakawa yarinyar wando ta shimfi
ɗ
e. Tana jinsa ya yi ƙwafa ya fice daga dakin a fusace. Sai a sannan ta bi hanyar da ya bi da kallo, kwanakinnan iskancin ƙaruw
a yake. Tunda ya soma wani sabon chatting a waya wai shi Whatsapp shikenan ya zama shagalalle. Sai ya kai biyun dare yana hira a waya, abin yana mata ciwo matuƙa. A gefe daya kuma babban tashin hankalinta na ganin tun dawowarta gidan ba ta ga al'adarta ba,
ga yanayin sauyi da ta ke ji na tashin zuwa da yawan ciwon kai da kuma baya.
Fa
ɗ
an da ta yiwa kanta, shi ne
ɗ
aure
ɗ
amarar zama da Aliyu a kowane hali na rayuwa. Barin sirrin zamanta da shi a cikinta, ta gaji da yin abin kunyar daka yaji kuma ta dawo.
Ga Abba da kwana biyunnan bai jin dadin jikinsa. Wannan ma babban tashin hankalinta ne.
Ta sauke ajiyar zuciya sadda ta ga dagasken dai Ummi ta yi nisa a bacci sannan ta mike ta kimtsa jikinta da neman abinda za ta sawa bakinta na salati.
**
*
Maimakon karfe sha biyun da ya saba shigowa a ƴan kwanakinnan, karfe takwas da mintuna ne daren ba zato sai gashinan ya fa
ɗ
o gidan. Tana falon tana duba takardun makaranta, Ummi na gefenta kwance idanunta biyu ta ƙura idanunta ga takardun da fitila ta h
askesu. Jefi-jefi takan kalli yarinyar ta yi murmushi ko kuma ta yi mata wasa.
Ko kallonta bai yi ba kamar yanda itama ba ta kalleshi ba har ya shiga
ɗ
akinsa ya fito. Ƙamshin turaren da ta ji ya sanya ta kallonsa, ya sauya ƙananun kayan dake jikinsa zu
wa shadda ruwan madara har da hula abinsa. Sai ya koma mata Aliyunsa sak wanda ta sani tun farkon haduwarsu, bambancin, wannan Aliyun a rame yake ga le
ɓɓ
ansa da suka ciza suka ƙara yin duhu fiye da baya. Ance ko yaya mijinka ya kai ga lalacewa, kana kishi
n abinka musamman ma auren da aka yi akan tafarkin so da kauna. Hakan ce ta faru ga Ramlat, ji ta yi gaba daya ta rasa nutsuwarta, shi kuwa yana tsaye da taimakon fitilar karamar wayarsa da ya sanya a baki yake haska hannunsa yana gyara zaman links. Miƙewa
ta yi ta je har gabansa ta tsaya. Ya dubeta gami da haske fuskar da fitilar bayan ya riƙe a hannu.
"Lafiya?"
Ta matsa kadan.
"Kalau, ina kake nufin zuwa?"
Wani murmushi ya yi.
"Au fita ma a bokon naku akwai ƙa'idarta ko? Toh
zance zan je. Akwai magana?"
Ta daure fuska.
"Babu, amma ka sani duk abinda kake yimin a gidannan, Allah Zai min sakayya. Ka auro dubu ma Aliyu, sai dai ka sani, duk radda ka yi aure toh babu Ramlat a gidannan."
Ya yi dariya sai kuma ya ja
tsaki.
"Ke kika san wannan. Idan kuma sakin a hannunki yake sai mu gani. Kin dai zabi boko yanzu akan kowane hidima na gidanki ko? Sai ki ci gaba."
Daga haka ya gifta ya wuceta yana mai
ɗ
aga wayarsa da ta addabeshi da ƙara.
"Hey Zee, ga
ninan tafe yi hakuri."
Zee din da ya ambata sai da ta ji kirjinta ya buga, wani zafi zuciyarta ke mata. Zee dai shai
ɗ
aniyar da ta ta
ɓ
a kwana da mijinta?
Ramlat ta kasa nutsuwa, sai kuma ta ga da gaskiyar Aliyun, ita ce ta sauya a tafiyar zaman
su, wato dai sauyin maimakon ya jawomata martaba da kyautatawa daga Aliyun, sai abinda yake mata ya ƙaru.
'Yanzu ke Aliyu ma ya yi aure wannan ba abin kunya ne gareki ba? Abin a yi maki dariya?'
Wani
ɓ
angare na zuciyarta ta ankarar da ita.
Karatun da ba ta iya ƙarasawa ba kenan, tattare takardun ta shiga yi ta maida jaka, ta dauki Ummi suka nufi daki. Bacci ya gagareta kamar yanda nutsuwa ta kauracemata. Ta rasa ina za ta sa ranta ta ji dadi, waya ta ciro ta shiga kokarin kiran Aliyun, ya yi
ringing har ya katse bai
ɗ
aga ba.
***
A lokacin shi kuwa yana tare da su G Baba da su Zee ana banke-banken hayaƙi da shafa jikin ƴan mata. Zee na kusa da shi kamar ta koma jikinsa. A duniya tana son Aliyu, ta kuma lura ba ta samun damarsa sai idan
yana cikin
ɓ
acin rai da ta gida, abinda ta karanta kenan. Don haka yanda ya dinga biyemata suna faranta ran juna da soyayya irin ta shan minti abin ba karamin dadi ya yi mata ba.
_*"Duk sadda kika samu dama, ki yi yanda ki ka yi ya kusanceki. Koda
ciki bai shiga ba, ki mishi karyar kina dauke da cikinsa, duk yanda zai yi akan ki zubar, ki nuna ba ki shirya hakan ba sai dai ya aureki"*_
Kalaman ƙawarta Nancy suka fa
ɗ
omata a rai. Ta tabbatar yau din ce damarta. Tana kallon sadda wayarsa ke fama
n hasken kira, da kanta ta dinga katse kiran. A karshe ma ta kashe wayar gaba daya.
'Sorry Babyn Aliy, yau ma nawa ne. Wancan karon koda ban yi nasara ba, wannan karon zan yi.'
Fadin Zee wacce take faman
ɗ
urawa Aliyu lemu wanda ta sanya kwayoy
in da shi kansa sun fi karfinsa.
G Baba ya kalleta suka kashewa juna ido gami da ƴar dariya. Wannan shi ne burinsa, zai fi so ma Aliyun ya kusanceta, ko ba komai yana tare da bakin cikin Aliyun yanda bai ta
ɓ
a kwanciya da wata mace ba a harkar Bariki
. Kusan ma ba wannan a gabansa, bar shi da abinda ba za'a rasa ba. So yake ya kashe bakin fariya da jin kai a wannan fagen irin na Aliyu.
***
Sanyin Asuba da na gari ne ya farkar da Ramlat, ta bude idanunta ganin hasken fitila tar a kansu shaidar an k
awo wuta ma cikin daren amma bacci
ɓ
arawo bai sa ta ankara ba. Fanka kam tun shigowar sanyi ta daina kunnawa. Ta miƙe ta sauko bayan ta gyarawa Ummi lullu
ɓ
in da ta yi mata da bargo. Alwala ta soma t gabatar da sallar Asuba.
Cike da fatan ya kasance Aliy
u ya dawo gidan ta fita zuwa dakinsa, gwuiwa a sake ta ja ƙofar ganin bai dawo gidan ba. Kasa komawa dakin ta yi ta zauna a falon. Wuraren bakwai kukan Ummi ya fargar da ita daga tunanin da ta afka, ta mike ta daukota.
Abin mamaki da tashin hankali
n, har sha biyu na rana babu Aliyu ba labarinsa. Ta kasa nutsuwa, ta kira wayar kuma ya fi sau talatin ba ta shiga. Jikinta kuma sai ya yi bala'in sanyi. Tsoro da fargaba suka shige ta. Ta goye Ummi tana jijjigata ba don ta yi bacci ba.
Bugun da ta j
i a bakin ƙaton kyaurensu shi ya maidota hayyacinta. Da sauri ta shige daki ta fiddo muƙulli ta yafa gyale ta nufi kofar.
"Waye?" Ta tambaya da tsoron amsar da za'a bata.
"Ni ne Idi direban Alƙali."
Ta san waye Idi don sadda ta je yawon
arba'in na Ummi, Justice da kansa ya sanya Idin ya maidota gida. Kamar yanda ta san Alƙalin mahaifin Muhibbat, amma tsabar rudewa ma ta manta ko waye.
"Banganeba." Ta fadi kamar ta yi kuka. Ya hau dogon bayani ta bude kofar a karshe.
"Cewa a
ka yi na zo na kaiki asibitin Malam, maigidanki ne suka yi hatsari daren jiya. Amma jikin da sauki."
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Toh, to ganinan."
Ta fadi tana jin kuka na tahomata, ta juya kamar za ta koma gidan sai kuma ta ce.
"Ai zan iya zuwa a haka ko?"
Tsabar rudewa ma ta rasa da wanda ya cancanta ta yi shawara. Idi ya kauda kai cike da tausayawa.
'Allah wadarannaka ya lalace, banda ma aure aure ne, me mace kamila irin wannan za ta yi da yaron da ya kusa mutuwa a
hanyar dawowa daga sa
ɓ
on Allah?' Fadin Idi kenan a ƙasan ransa don ya
ɗ
an tsinkayi fadan da iyayen maza ke yi game da abinda suka tsinta daga bakin yan sandan da suka kawosu asibitin.
"Kiyi hakuri." Shi ne abinda ya iya fada. Ta koma ciki don kanta
ta sanya hijabi ta fito ba ta ko dauki waya ba, silifas din amfaninta na gida ne a kafarta.
***
A Emergency ta iske mutan gidan su Aliyu ciki har da Abulle a gefe tana ta kuka da salati. Ta karasa kawai ta durkusa gaban iyaye mazan wadanda su ne
mafi kusa da inda take.
"Lafiya kalau Ramlatu, sai hakuri kin ji? Kar ki damu jikin ba wani rauni ya samu sosai ba."
Wannan shi ne jawabin Malam gareta. Ta gyada kai tana dauke hawayen fuskarta. Sai da ta je wurin Abulle sannan take jin abinda
ya faru cikin
ɓ
arin zance irin na Abullen.
"Yanzu yaronnan sai da ya jawomin abin kunya abin magana a gidannan? Fisabilillah wannan wane irin bakin ciki ne ace wai a motar mace ka yi hatsari kuma likitoci sun auna sun tabbatar ma ba a hayyacinka ka
ke ba, ka sha kwayoyin da suka fitar da kai hayyaci? Ke yanzu haka kike zaune da shi ba ya kwana a gida shi ne ban isa ki fadamin ba? Yanzu da ko rubutu ne da rokon Allah ba sai na saka a shiga yi mishi ba?
Wani kallo take yiwa Abulle wanda kai tsaye
za ka kirashi da harara, ita kanta ba ta san sadda ta yi din ba, ga mamakin Amaryar Malam dake kallon wannan dirama, Abulle ta kauda kai gami da fadin Allah Ya kyauta ba tare da ta nemi maida baƙa da hayayyakowa Ramlatun ba yanda ta saba yiwa duk wanda ya
yi mata ba daidai ba.
Ramlat ta kauda kai, jikinta har wani tsuma yake, bakin ciki da takaici ne suka tararmata. Da ta san abinda akai kenan da ba ta zo asibitin ba. Likita ya tabbatar za'a iya sallamarsa da dare don ba wata buguwa ya yi ba Banda b
uguwar kai da ya jawomasa nannauyan baccin fita hayyaci. Fatansu kawai ya farfa
ɗ
o cikin hayyacinsa.
"Ita yarinyar fa?" Tambayar da Justice ya yi ya maido Ramlat hayyacinta, kunya ta dabaibaiyeta, hawaye take kanta a ƙasa, jiri take ji tana daga zaun
e wanda ta tabbatar da a tsaye take zubewa itama za ta yi.
"Af, an samu an kira wani nata kuwa?"
Fadin Likitan.
"Tukunna dai, bamu santa ba. Sai dai ko idan ta farfa
ɗ
o a tambayeta."
Likita ya jinjina kai.
"Da sauki jikinta, ka
raya ce kafa da hannu sai rauni a goshi, mun yi mata dressing, ba