Showing 210001 words to 213000 words out of 255051 words
fi a ƙirga. Ƙamshin zo
ɓ
on da ya ji citta da abarba da su flavour, yana kara kwa
ɗ
aitamasa son sha.
"Bismillah."
Ta fadi da wani salon kashe murya kamar ba ita ba. Ya
ɗ
ago kai ya dube ta. Hankalinta na ga zo
ɓ
on da take tsiyayawa a kof
i ammafa kirjinta wani bugu yake don ta san idanunsa a kanta su ke kamar yanda jikinta ya ba ta.
"Na gode."
Ya fadi a ciki-ciki, ta ajiyemishi zo
ɓ
on, ta mike ta bar falon. Koda ta kai ƙofa, ta dan saci kallonsa, har sannan ita ya ke bi da ido
duk kuwa da cewar ya kafa kofin zo
ɓ
on a baka. Mamaki ya sa ta saurin kauda ki ta shige daki.
Wani dadi ranta ya yi tana jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Wato dai haka Hussein ke ji idan ya na mata wannan shan ƙamshin. Ta yi dariy
a ita
ɗ
aya a
ɗ
aki kafin ta kife saman gadon cikin annashuwa. Sai da aka kwashe mintuna talatin sannan Ummi ta shigo kiranta. Ta maida hijabin ta fito, sun kammala har ma Hajiya ta fito, kayan kuwa ta tabbatar Ladidi ce ta kwashe tunda ba ta kai ga tafiya b
a.
Hussein ya miƙe ya fita tare da Ansar, zuwa can sai ga Ansar din ya dawo.
"Mami, ki zo inji Uncle."
Ta dan saci kallon Hajiya da AlHassan, hira suke abinsu kamar uwa da
ɗ
a, ganin ba su damu da kallonta ba yasa ta miƙewa ta shiga daki. S
ai da ta
ɓ
ata mintuna fiye da biyar ba don kuma wani abun ta ke shafawa ko gyarawa ba, can kuma ta fito ta fice.
Yana tsaye a jikin motarsa ya harde kafafu hakanan hannunsa a har
ɗ
e a kirji. Tun tahowarta ya ke kallonta. So da kaunarta na ratsa dukkan
wani
ɓ
angare na zuciy da gangar jikinsa sai dai shafe mintocin da ta yi ba ta fito ba ya yi masifar sosa ransa. Don haka koda ta tsaya sai shima ya ja baki ya yi shiru. Ramlat ta soma gajiya da tsayuwar don haka ta dubeshi babu fara'ar a zo a gani.
"
Shikenan ina iya tafiya?"
Kallon da ya watsamata yasa ta kallon gefe guda.
"Idan har ba ki daukeni a bakin komai ba, kina iya tafiyar."
Shiru ya biyo baya, jin ba ta ce komai ba sai ya sauke ajiyar zuciya.
"Akwai abinda na yi maki? Ko k
uwa duk baƙin cikin na rabaki da masoyinki karo na biyu ne?"
"Komai nufin Allah ne. Haka ya tsaramin a rayuwa. Na kuma kar
ɓ
a da hannu bibbiyu."
"Hakane, sai dai kina nufin ba da son ranki ba?"
Yanda ya yi maganar da wani irin sanyi, yasa ta
yin murmushi kadan.
"Kamar yanda kaima ba da son ranka ba, haka nima yake a wurina. Ina ganin dai mun yi anko."
"Yaushe kika fara duba? Me kike nufi da mun yi anko?"
Daga muryarsa ta gane
ɓ
acin ransa, ta kara gyara tsayuwa gami da
ɗ
an dubans
a.
"Daga ni har kai, mun yarda da kaddara mai kyau da marar kyau saboda mu din musulmai ne. Kamar yanda na ji batun aurenmu da kai daga sama, haka Allah Ya bani ikon kar
ɓ
ar lamarin matsayin kaddarata kuma mai kyau. Ko ba komai na shaida kana da
ɗ
abi
'u masu kyau daidai gwargwado. Hakanan iyayena da suka ha
ɗ
a ni da kai, na tabbatar ba za su cutar da ni ba har abada. Bana so na ƙara yin gangancin sa
ɓ
a umarninsu."
Tana kaiwa nan ta sunkuyar da kai don ba ta kaunar kallon da yake jifanta da shi da ta
kasa ganewa.
"Ba wannan na tambayeki ba. Tambayar da na maki, kenan ba...Shikenan dai. Hakan ma is good."
Ya fasa nanata tambayar, sai ya share. Can kuma ya kara magana.
"Ku mata kun fi kaunar wadanda za su tsaya su na furtamaku kalaman s
o a baki alhalin idan aka yi auren ba lallai su iya tafiyar da lamuranku yanda ake so ba. Ina da tabbacin har da wannan a bahagon tunaninki."
"Me ya kawo batun so? Ai bana jin akwai shi a tsakaninmu. Ba ka san cewa ko ba aure ana yin so ba?"
Ya j
i zafin kalamanta don haka shima ya shirya ramuwa.
"Shiyasa ki ka kasa hakuri da auren da babu so?"
Ta dubeshi, wani murmushi ya ke ganin ya ci galaba ta fusata. Ta kasa ha
ɗ
iye maganar da ke cinta, ta maida mishi martani nan take.
"Yanzu ai
gashinan zan yi. Ko ba komai a rayuwa ana koyon darasi, da auren so da wanda ma babu soyayyar, duk darasi ne a gareni. Na kuma gani. Idan a baya na yi na soyayyar, yanzu na hakura zan jarraba wanda babu soyayyar na ji yanda ake ji. Ko itama tana dauwama ko
aa."
Tana kaiwa nan ta soma tafiya da zummar barin wurin, ya riƙo hannunta ta dawo baya. Ta juya da sauri gami da kokarin janyewa amma ina karfin ba
ɗ
aya ba.
"Ka cikani tunda dai ka riga ka san cewa haramun ne."
Idanunsa tuni sun ka
ɗ
a. Shi
Ramlat ke nufi da ba ta so ko me?
"Idan wasa ki ke yi, bai miki kyau ba. Ina miki rantsuwa da Allah, ko yankar naman jikin Hussein za ki dinga yi kullum kina gasawa tsabar ƙiyayya, sai kin zauna da ni muddin aka
ɗ
aura aurenmu. Idan kika ga kin fita d
aga gidana, to ki sa a ranki, ƙasa ce za ta zama makwancinki a ranar. Babu fitar yaji ko kuma saki. Kar ki shigo gidana da makami, zan miki tanadin kala-kala sai wanda kika za
ɓ
a. Zan iya mutuwa, amma har abada kar ki ji a ranki za ki shigo gidana kuma na r
abu da ke. Har abada Ramlat."
Ta dubeshi da idanunta da suka cicciko, ba karamin fusata ya yi da zantukanta ba. Jikinta ya yi sanyi, ya saki hannunta ya fa
ɗ
a motar gami da rufewa da karfi. Ta ci gaba da tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta bar
harabar wurin zuwa ciki.
I just published "BABI NA HAMSIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1018053716?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=R
ufaida-Umar&wp_originator=H1vXb7%2FW6A2U5P8fFwbtuiA8loSGt%2B%2BNft8tDKy3EJM810crtMGUnxqUIIutxZI04rTU84moV3sLlZ4ErYDW%2BHsUJ6yuYaxKr9kgvrgaa2%2BsQQrAwLvUCmdmO42m8ACV
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rah
maanir Raheem.
57)
Kici
ɓ
us ta yi da Alhassan dake fitowa, ta yi saurin sunne kai kamar mai jin kunya. Shi kuwa a fisge da suka hada ido ya gane kamar ranta a
ɓ
ace yake.
"Har ka fito?"
Ta furta cikin dakiya, ya dan yi dariya.
"Na fito Amarsu, zan wuce. Gobe dai zan koma Adamawa sai ranar daurin aure in sha Allah."
"Allah Ya tsare hanya. A gaidamin su Aunty Kausar da Fatima."
"Zasu ji in sha Allahu."
Daga nan suka yi sallama ta shige ciki shi kuma ya nufi wurin mo
tar yana ta tunani. Koda ya shiga, ya dubi Hussein da ya
ɗ
ago kai daga saman sitiyari.
"Lafiya? Na ganka wani iri kamar yanda itama Ramlatun na lura da damuwa a fuskarta. Meyafaru?"
"Nothing."
Ya amsa a gajarce sadda ya tayar da motar suka
bar harabar gidan. AlHassan bai kara magana ba banda baki da ya ta
ɓ
e. Sai da suka yi nisa ne kafin ya ji ya kamata ya ce wani abu ko da shawara ce sanin halin mutumin.
"Idan mutum yana son mace, kwantar da kai ya ke yi ya nemi soyayyarta. Mace ba ta
son gadara ko taƙama, mace kulawa ta ke so da kuma a nunamata soyayya a fili kuma a gaban kowa. Ban san me ya ha
ɗ
aku da Ramlatu ba, amma na kalli abin a mahangar ba ka ta
ɓ
a soyayya ba, asalima matan ke binka a baya kana yanƙwana su. Idan har ka ce ta wanna
n hanyar za ka siye zuciyar Ramlatu, abun zai ba ka wuya daga kai har ita. Kar ka yi wasa da damarka."
Hussein tun soma maganar
ɗ
an uwansa, bai katse shi ba, kamar yanda kunnuwansa ba su bar sauraronsa ba. Sai da ya kai karshe ne ya
ɗ
an yamutse fuska.
"Su matan ba za su iya hakuri da kowace kulawa ta biyo bayan aure ba? Dole burinsu tun su na waje a nunamusu?"
Abin ya ba AlHassan dariya.
"Ka ta
ɓ
a ganin inda aka yi cinikin biri a sama? Ko kuwa su matan kana tunanin sun san gaibu da nan ta
ke za su karanci halayyar mutane irinku? Su ba wannan a gabansu, su dai su gani a ƙas. Kuma dama ai amfanin ta
ɗ
in kenan, a fahimci juna a kuma ga ko za'a iya zama a jure halayyar juna. Na tabbatarmaka idan ka ci gaba da tafiya a wannan shan ƙamshin naka da
rashin maida hankali, za ka sha wuya a hannun Ramlatu bayan aurenku."
Murmushi Hussein ya yi don shi mamaki ma maganar ya ba shi.
"Wai zan sha wuya hannun Ramlat? Anya? Don Allah na yi kama da mazan da za su sha wuya hannun mace?"
Murmushin
shima AlHassan ya yi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Da sauranka
ɗ
an uwa. Bari na kyaleka, gani ya kori ji. Nidai idan ta fara gasa maka aya a hannu, kar na ganka a ƙofar gidana."
Suka yi yar dariya a tare. Shi Hussein dariya yake don ganin hak
an yake kamar wani almara ko tatsuniya. Bai ce Ramlatun ba ta da kyau ko tsarin da namiji zai rikito a kanta ba, tunda shi shaida ne, ganinsa da ita tun farko ya ji kawai ta burgeshi kafin ya tantance abinda ya ke ji taƙamaiman a kanta, sai dai ya na da ja
akan cewa akwai macen da za ta iya juyashi ba tare da asiri ba kamar dai Hajiya Zeenatu a baya. Amma zai jira ya ga irin juyawar ta Ramlatu. Kulawar ba zai nuna ba kamar yanda dan uwansa ya buƙata har sai bayan aurensu.
***
Tana tuƙi a hanyarta n
a zuwa Ofis bayan ta sauke yara a makaranta, tana tunanin zantukan Hajiyarta.
_*"Magidannaki fa ya bukaci ki bar aiki hakanan tunda can Adamawa za ki zauna. Ko ba don haka ba dama na fadamaki duk radda kika tashi aure idan mijin da za ki aura bai ami
nce ba, to za ki bar aiki."*_
Sauke ajiyar zuciya ta yi. Kenan dai rabuwarta da yaranta ya zo, wani kewarsu ta ji ya kamata. Dama tasan aiki ko ba dade ko ba jima za ta bar shi kamar yanda suka yi da Hajiya a farko. Hon da aka cikamata kunne da shi ya
sa ta kara nutsuwa a tuƙinta, ganin ma ba wani tare hanya ta yi ba sai abin ya yi mata zafi, ta cikin gilashi ta ke duban motar, sam ba ta ganeta ba. Don haka ta yi gefe ta ba mai motar hanya. Ido suka hada ya yi mata murmushi ita kuwa dubansa ta shiga yi
baki a sake sai kuma ta dara.
"Hilal?" Ta furta a bayyane, a hankali ta ga ya ja gefe ya yi parking, itama dolenta ta tsaya don su gaisa. Ba ta kai ga fitowa ba ya rigata isa wajenta.
"Ranki ya da
ɗ
e."
"Yaya Hilal? Saukar yaushe a garin?"
Ya yi ƴar dariya.
"Ko kwanaki uku ban yi ba da zuwa, shima daurin auren abokina ne ya kawoni, amma nan da jibi zan koma in sha Allah."
Ta yi murmushi.
"Allah Ya nunamana. Ya Fa'iza da Ɗiyarmu?"
"Suna nan kalau. Ai nake gidan Sis Bi
lki jiya, na ji kuma abin alheri. Allah Ya sanya albarka. Yasa zamu gani."
Ba ta yi mamakin yanda aka yi Bilkisun ta sani ba, tana da tabbacin daga bakin Mijinta ne. Amma fa
ɗ
awa Hilal sai ta gani kamar da biyu ne. Cike da jin nauyinsa ta amsa.
"A
min. Ina godiya. Wato dai da ace ba mu ha
ɗ
u ba anan sai dai mu ji labarin ka tafi ko?"
Dariya ya yi.
"Ni na isa na shigo garin nan ban je na ga Hajiyarmu ba? Aa sam. Wallahi yau nake cewa zan shiga zuwa yamma haka."
Ta jinjina kai.
"All
ah Ya nunamana."
"Amin amin. Bari na bar ki kada na sa ki makara. Sai na shigo din."
Ta amsa da toh gami da yi mishi fatan alheri, ya rufemata murfin motar sannan ya wuce zuwa tashi motar. Ta ja numfashi ta furzar, Hilal kenan, mutumin da ya kaun
aceta don Allah. Gaba daya ya sauya ya ajiye kumatu. Ga duk wanda ya gan shi zai fahimci yana cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Wayarta ce ta yi ringing daidai sadda ta ke kokarin hawa titi. Ba tare da ta duba ba ta daga gami da karawa a kunnen da salla
ma.
"Ke da waye tsaye a titi?"
Tambayar da aka watsomata ba tare da an amsa sallama ba yasa ta gane ko waye. A hankali ta
ɗ
aga kai ta dubi mirror, motarsa na nesa ka
ɗ
an da nata. Ta fi kyautata zaton daga wurin motsa jiki ya ke. Murmushi ta yi da
idai sadda ta hau titi ta harba motarta.
"Ba ka da hurumin sanin da wanda nake magana. Kar ka manta ban kai ga zama matarka ba."
"Hakane, ba ki kai ga zama ba. Amma kin manta cewa haramun ne nema cikin nema? Ke musulma ce."
Dariya ya ba ta j
in yanda ya zaƙalƙale. Yanda ta ke tafiya a sannu, haka yake biye da ita da motarsa a sannun. Ta kauda kai kamar ba ta san da shi din ba.
"Babu wanda ba ya kuskure."
"Haka kika ce? To naga kin ƙara tsayuwa da wani
ɗ
an iskan! Duk abinda na yi mis
hi, ke kika ja. Sannan lokacin da za ki ajiye yawon gantalin aikinnan ya yi! Ba zan lamunta ba."
"Wannan kuma ba ka da hurumi a ciki, ajiye aiki sai lokacin da naga dama. Ka bar tada jijiyoyin wuya tunda har yanzu aure bai tabbata ba tsakaninmu. Akwai
sauran lokaci."
Tana kaiwa nan ta katse wayar ta taka motarta, sai dai ba ta je ko'ina ba ya zo ya gifta ta har yana kokarin buge wani
ɗ
an sahu. Bai ko tsaya ba ya yi gaba. Ta bi shi da kallo tana dariyar farin ciki, ko ba komai ta san ta ba shi aiki
. Wannan nishadin yasa ta ware waƙar Breaker na Jarumar Mata tana saurara har ta karasa wurin aiki.
Hussein bai kara kiranta ba kwata-kwata a wannan ranar.
***
Bisa umarnin Yayanta Munir, ta rubuta takardar barin aiki. A wannan satin Rafee'ah
ke zuwa ta kai ta gidan mai gyaran jiki. Ya kasance Ramlat ba ta da lokacin kanta balle na yara,
ɗ
awainiyarsu ta koma hannun Hajiya da direba mai safa da marwar kai su makaranta da daukowa. Waya ba ta kara shiga tsakaninta da Hussein ba sai dai kokari kawa
i ta ke yi itama don tana kewarsa. Ya aiko da wani leshi mai tsadar gaske da kuma atamfofi har kala uku suma masu tsada sai mayafai da jaka da takalma, sai kuwa tsarka kala biyu da abin hannu duk na fitar biki. Ba
ɓ
ata lokaci aka kai wurin dinki tare da wa
nda Munir ya siyamata.
"Wai ke angonnaki yana zuwa hira kuwa? "
Ta dakatar da shafa man da take yi a jiki ta dubi Amrah wacce ke zaune saman gado tana shayarwa. Ta
ɓ
e baki ta yi.
"Mutumin da ko waya ba ya kirana."
Da mamaki Amrah
ta ce.
"Bana son sharri Ramlat."
Harararta ta yi.
"Kawai sai na zauna na kantara maki karya saboda ina tsoronki ko?"
Murmushi Amrah ta yi. Nan ta kwashe duk yanda ake ciki ta fa
ɗ
amata har maganarsu ta karshe.
"Kai amma kin fadi m
ai zafi da yawa Ramlat, to ko za ki rama ai kya bari ya zo hannu tukunna. Shima dai da alama yana da zafin kishi tunda ya kasa nemanki har yau. Amma kar ki kara tunanin wai ba ya sonki, wallahi Hussein na miki son da ba ki san adadinsa ba. Da kansa fa ya j
e ya fadawa Baba Dakta yana sonki da aure tun ma a lokacin Chairman. Abinda kawai na kula, kamar yanda ya fa
ɗ
amaki, shi mutum ne da bai yarda da wata soyayya kafin aure ba. Ya fi imanin cewa soyayya ta gaske tana zuwa ne bayan an yi aure. Kuma kar ki yi ma
maki, irin su Hussein sun iya tattali da nuna kauna ga mace. Ina goyon bayanki, idan ku ka yi aure ki nunamasa kefa mace ce, amma ba wai ina nufin kar ki masa biyayya ba, aa, ki dai ja ajinki yanda zai gane shayi ruwa ne. Ke ba yarinya ba ce, na tabbatar k
in gane me nake nufi."
Suka yi dariya gami da cafkewa don tuni Ramlat ta taso ta dawo gefenta.
"Ai ko yanzu ya ganki ya san kin sauya. Kin kara kyau gyaran jikin ya kar
ɓ
eki. Duk inda kika gifta kamshi kawai kike kamar mai wanka da turare. Nidai a
kwai tsarabar da zan maki na kananun kaya, saura ki ƙi sanyawa."
Murmushi Ramlat ta yi, sai kuma ta ji zuciyarta na neman karyewa.
"Allah Ya jaddada rahma ga Aliyu."
Ta furta a fili, Amrah ta amsa da amin. Nan kuma suka shiga tuna baya, sai
da Amrah ta ga dagasken Ramlat kukan take son yi don idanun sun cicciko da kwalla, sai ta share gami da sanyo wata hirar.
"Zan