Showing 111001 words to 114000 words out of 255051 words

Chapter 38 - KARFEN KAFA complete

Ya bar zumunci."

A'isha ta mike tana ƙara yin godiya. Ya yi waje. Hisham ya dubi Ramlat.

"Antinmu don Allah ki yi hakuri ki taso

ku tafi."

"Wai shi ya ce maka zai kai ni? Ni da ka bar ni na hau adaidaita."

"A'a. Wallahi na san Hussein daidai gwargwado, yana da kirki. Ina tabbatarmaki har ƙofar gida zai kaiki."

Ta sauke ajiyar zuciya, dolenta ta taso suka fito, Hisham

da kansa ya budemata mazaunin kusa da direba ta shiga. A'isha na gefe tsaye tana kallonsu. Wanna dacewar da ta ke kira ba zasu yi ba, sai ta ga sun yi fiye da dukkanin zatonta. Murmushi take, wani irin murmushi mai ha

ɗ

e da zumu

ɗ

i da kuma fatan alheri.

Har Hisham ya zagaya suka yi sallama da Hussein da ke tsaye jikin motar ya riƙe murfin motar, ba ta daina kallonsu ba. Suka yi sallama ya kara yi mishi godiya sannan ya shiga motar.

A nutse ya soma tafiya har ya bar layin, wani shiru ne kawai ke gu

dana tsakaninsu. Kowanne da abinda yake saƙawa a ransa. A

ɓ

angaren Hussein murmushi ya yi, tunaninsa kawai Hajiyartasa, da za ta ga yarinyar a gaban motarsa yau kam hauka ne kawai ba za ta yi ba.

"Kin hau motata ba ki sanar da ni inda zan kaiki ba."

Wani kululun baƙin ciki ya tokaremata ƙahon zuci. Yana magana kamar ma ita ce ta ce za ta hau ya manta cewa bisa tilas take zaune a ciki.

"Wace unguwa?"

Ya tambaya kai tsaye ba tare da ya dubeta ba, kuma bai tsaida motar ba.

"Shara

ɗ

a.

" Ta furta a ciki-ciki, sai a sannan ya juya ya kalleta, fuskarta na kallon waje. Ya maida kai ga tuƙinsa, gudu kawai yake ita kam ko a jikinta.

"Alaƙarku fa?"

Ta ji muryarsa cikin kunnuwanta, sai a lokacin ta dubeshi. Cikin rashin fahimta ta

ce.

"Me ka ce?"

Fuskarsa a sake ya dubeta ka

ɗ

an, ta kauda kai shima ya kawar.

"Alaƙarki da Hisham."

Kamar ta ce ba matsalarta ba ce, sai ta ji ta kasa. Ta

ɗ

an ja sakanni ka

ɗ

an kafin ta amsa.

"Mijin ƙanwata ne."

Ya gyada kai da

idai sadda ya sha kwanar da za ta sadashi da titin shara

ɗ

a.

"Sai ina?"

Ta dubeshi, ita wannan magana guntu-guntun takaici yake ba ta, ganin ba ta gane ba ya ce.

"Ina zamu yi?"

Ta yi mishi kwatance har lokacin muryarta ba daidai ba,

ta rasa dalili.

Gyada kai kawai yake yana sauraronta da dukkan hankalinsa, har ta gama ya rasa dalilin da yasa bai so ta tsaya din ba. Ya numfasa ya shiga bin kwatancen har suka iso layin da take fadi.

"Ya isa, zan sauka a nan."

Ya dubi

wurin, akwai jama'a ba laifi, gidajen unguwar ya kalla, ba laifi suna da kyan gani.

"Kofar gidanku fa?"

Girgiza kai ta yi.

"A'a ba sai mun ƙarasa ba. Nagode."

Gyada kai ya yi. Ta mur

ɗ

a kofar ta ji ta gam!

"Kiyi hakuri. Ina ma

i ba ki hakuri on behalf of my wife na abinda ta yi maki kwanaki."

Ta

ɗ

an tsuke fuska.

"Wa kenan? Ai ban sanka ba balle har wani abu ya ha

ɗ

ani da matarka. Ni dai Ramlat kake nufi?"

Wani murmushi ya yi da har haƙoransa suka bayyana, irin m

urmushin da Hajiya Zeenatu kadai ke da ikon gani. Ta

ɗ

an kauda kai daga kallon da ya ke jifanta da shi, murmushin ya kara kashemata gangar jiki da ruhi.

"Ramuwar gayya kenan fa?"

Ta yi shiru ba ta amsa ba amma ta

ɗ

an murmusa itama ganin ya

ɗ

ag

ota.

"Shikenan. A gaida su Mama."

Daga haka ta ji ƙarar cire lock. Ta dubeshi kafin ta fita ta leƙo ta window.

"Nagode, zasu ji. Nima a gaidamin Hajiya."



Kusan ta fa

ɗ

a da biyu hakan yasa shi dubanta, lokaci guda suka yiwa juna mur

mushi, daga nan ta soma tafiya babu ko waige. Har ta isa ƙofar gidansu ta bude murfin kyaure, sai a sannan ta waiga, yana tsaye ga mamakinta bai tafi ba, cikin sauri ta shige gidan tana mai dafe kirji da wurgawa kanta tambayar abinda ta aikata.

Shi

kuwa ji ya yi kamar ana jan sa, kwakkwaran motsi kasawa ya yi sai aikin kallon tafiyar nutsuwarta har ta shige gidan. Wayarsa ce ta katsemishi tunanin da ya dulmiya wanda ko za'a kasheshi ba zai ce ga dalili ba, sai sannan ya tuna da cewar murmushi yake,

murmushin da ya ƙi

ɗ

aukewa daga saman fuskarsa.

Hajiya Zeenatu ke kiransa, ji ya yi gabansa ya fa

ɗ

i. Ya kasa daukar wayar, haka ta yi ta ƙara har ta katse. Gumi ya shiga tsastsafowa daga goshinsa, ya yi ribas ya bar layin. Gani yake kamar ya aikata

wani ƙaton zunubi ga Hajiya Zeenatu. Ji ya yi ya tsani kansa, har lokacin gabansa faduwa yake don tsoro da fargabar inda zai ce mata ya ke. Bai samu nutsuwar kiranta ba sai da ya ganshi a ƙofar gidansa.

"Ina ka shiga wai? Me kake yi? Wannan wane iri

n ziyara ce da bai isa a kammala a awa uku a koma gida ba?"

Ya kasa tsawatarwa, ya ji ba shi da wannan kuzarin. Ƙarshe ma ya

ɓ

ige da bata hakuri da rarrashi.

"Allah Ya huci zuciyarki, yanzu ganinan a gida. Wanka ma zan yi na kwanta na ci abinci

a gidan Hisham."

"Wanka? Wane irin wanka?"

Ya

ɗ

an yi shiru yana jin zuciyarsa na tuƙuƙi, tuhumar ta yi mishi kama da na zargi.

"Me kike son ki ce?"

Daga can Hajiya Zeenatu ta yi saurin gyara zancenta.

"A'a ba komai, gani nayi

garin da

ɗ

an sanyi."

Ya yi murmushi mai sauti.

"Eh haka fa. Amma kin manta mijinnaki ba ƙazami bane ba ko?"

Ta yi dariya, daga bisani suka yi sallama.

***

HAJIYA ZEENATU...







I just published "BABI NA TALATIN DA

ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/hTaZiBjDOab

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯





*_Rufaida Umar_*



Bismillahir Rahmaanir Raheem.

31)

HAJIYA ZEENATU..

Niamey, Nijar.

Tun ajiye wayartasu zuciya

rta ta kasa sukuni, ta yi shiru kawai ta zubawa talabijin idanu ba don yana fahimtar yaren ba.

"Ba za ki daina shirmen tunanin ba ko? Na fadamaki ba sau

ɗ

aya ba kuma ba sau biyu ba, mun zo inda za'a share kukanmu."

Hajiya Batool Aminiyar Hajiya

Zeenatu ke wannan zantukan. Ajiyar zuciya ta yi ta ci gaba da kallonta, dama tun soma maganar hankalin ya koma kanta.

"Nasan da haka, amma ina jin tsoron tabbatuwar wancan lamarin Batool, kema kin sani kamar yanda na sani, kwa

ɓ

ewarsa ba za ta yi kyau

ba."

Wani dan bazawarin murmushi Hajiya Batool ta saki. Ga ta dai siririya da ita amma naira sun zauna. Yatsunta ta jera zobunan gwal har ya yi yawan da bai yi kyan gani ba.

"Ai sai ki yi, gobe da safe wanda zai mana rakiya zai zo mu tafi. Idan

ba ganin wannan saurayin mijinnaki a kwalba kika yi kina juyashi ba, ba za ki kwantar da hankalinki yanda ya kamata."

Sai a sannan ta yi dariya sosai, ranta kuma ya koma ƙal kamar takarda.

"Na ci wuya kafin na cimma dukkan buri a kan Hussein, k

ema kin san da haka ai. Huum, sai yanzu rana tsaka bayan na gama sanin wa nake tare da shi, wata banza ta zo ta tadamin hankali. Anya kuwa ma dagaske Gora yake? Ni dama tun sadda naga ya hau canki-canka da matsalar da ta kawo wata budurwa, na shiga shakku

a kansa."

"Toh ba na fadamaki ba, yanzu haka kawai kudinmu ya ci. Akwai irinsa da yawa ai, ba tsoron Allah su zalunci mutane su damfaresu." Fadin Hajiya Batool har da yamutse fuskarta mai kama da kashi. Ta mance su kansu ba tsoron Allahn suka sa gaba

ba.

***

Washegari kuwa da sassafe sai ga wani tsamurmurin buzu mai jin Hausa ra

ɗ

au ya zo Hotel din da suka sauka. Shi ya yi musu jagora har wurin Isuhu Bakka Tsoron Allah. Layi sosai suka tarar amma kasancewar

ɗ

an rakiyar ba baƙonsa ne mutumin ba, y

asa ya basu umarnin su jira sannan ya shiga ciki. Can ya fito ya musu umarnin su taso.

A bakin kofa suka tsaya suna ji mazauna wurin wadanda mafi yawansu mata me, su na zaginsu da yaren kala-kala, Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool suka kalli juna don a

bin ma dariya ya basu.

"Wai fa harara a duhu." Fadin Hajiya Batool.

Wacce ke ciki na fitowa suka fa

ɗ

a

ɗ

akin bisa jagorancin

ɗ

an rakiyarsu.

Wani ƙaton mutum ne fatarsa har wani ja ta ke yi, yana zaune saman wata ƙaton carpet gefensa kayan

tsubbu ne kala-kala, ya na

ɗ

e fuskarsa da farin na

ɗ

i sai kayan jikinsa baƙaƙe. Kallo

ɗ

aya za ka yi mishi ka san buzun ne na gasken gaske.

Suka gaidashi sai dai yarensu ma ba ji yake ba,

ɗ

an rakiyar ya juya harshe ya shiga nanata abinda suke fa

ɗ

a. Tun

da ya soma bai katseshi ba kansa kawai yake gya

ɗ

awa gami da yi musu kallon ƙurillah. Can ya watsa tambayar wacece a cikinsu. Saurayin ya nuna Hajiya Zeenatu ganin ita ke koro jawabin. Ya yi mata kallon tsaf sannan ya maida kai ga ƙasar dake shimfi

ɗ

e gabans

a. Tambayar sunan mijinnata ya yi da kuma ita kanta.

Bayan an fa

ɗ

amasa ya ci gaba da zanensa a kan ƙasa can ya

ɗ

ago ya dubi saurayin yana murmushi yana jawabi, sai da ya gama tsaf sannan saurayin ya dubesu, dama duk sun matsu su ji abinda ke faruwa.

"Cewa ya yi, ya ga ma mijinnaki saurayi ne, kuma ƴan biyu ne. Shi kansa ƴan uwansa basu zauna ba, suna ci gaba da nemansa sannan sun tashi tsaye da addu'a irin wanda sai an yi dagaske. Ya kuma ce akwai mace

ɗ

aya da babu makawa sai ya aureta koda za'

a shekara goma ne, rubutacce ne. Ita ce za ta rushe dukkan wani gini da kika yi. Ai ya ce ya gani, ba wurinsa kika soma zuwa ba, kafin zuwanki nan, akwai wanda ya yi maki aiki."

Hanjin cikin Hajiya Zeenatu suka ƙulle, iskar fankar dake ka

ɗ

awa bai han

a gumi ya tsastsafomata daga goshinta ba. Ta ha

ɗ

iyi miyau, ta dubi Isuhu don bilhakki fargaba da tsananin kishi ya mantar da ita ba ya jin yarensu.

"Ya kammanin yarinyar yake?"

Saurayin ya fa

ɗ

amasa. Girgiza kai ya yi gami da yin yare. Duk suka zu

bawa saurayin idanu suna jiran jawabi.

"Ya ce ba zai ce ga kamannin ba, amma yanzun haka sun ha

ɗ

u da juna."

Ta ha

ɗ

iyi miyau hankalinta a matukar tashe, idanunta har hangomata Yarinyar kwance jikin Hussein yake. Dagaske dai Gora ba ƙarya ya fa

ɗ

amu

su ba. Nan da nan idanunta suka ka

ɗ

a har da ƴar kwallarta.

"Don Allah Malam ka taimakamin, wallahi ba zan iya ha

ɗ

a Hussein da kowace

ɗ

iya ba. Idan har Hussein ya rayu da wata mace koda ta hanyar fasiƙanci ne zan iya mutuwa wallahi. Nidai ko kasheta n

e a yi kawai na huta. Idan har mutuwarta zai sauyamin kaddarata shikenan. Ko nawa ne zan biyaka wallahi."

Tana kaiwa nan, saurayin ya fa

ɗ

amishi. Ya yi shiru yana ci gaba da bugun ƙasarsa kafin ya

ɗ

ago ya yi jawabi.

"Abu

ɗ

aya ya ce za'a iya, shim

a yana da matuƙar wahala, bai kuma yi miki alƙawarin lallai ne ya yiwu ba. Idan har za ki iya ku bar garin da ku ke yanzu zuwa wani. Ya kasance komai naku ya sauya daga wannan garin don yana da tabbacin koma wace ce a garin ta ke. Amma kuma ya ce zai waha

la shi mijinnaki ya amince da hakan. Sannan yana mai ba ki shawara da kar ki yi wasa da abinda zai ba ki na mallaka, muddin kika yi sake ƴan uwansa na dab da sanin inda yake. Bayyanuwarsa garesu kuwa daidai yake da rushewar duk wani tubalin da ki ka gina."

Hajiya Zeenatu ba baka sai kunni, gyada kai kawai ta ke. Ai ko bangon duniya ne za ta iya zuwa muddin mijinnata ba zai su

ɓ

ucemata ba. Sai dai dagasken itama ta sani, abu mawuyaci ne ya amince da barin garin Kano.

"Naji, zan kiyaye ko menene. Zan

bi dukkan tsarinsa."

Isuhu ya gyada kai cike da gamsuwa bayan ya ji bayanin daga bakin saurayin. Miƙewa ya yi ya shige ƙuryar

ɗ

aki.

"Hajiya Zeenatu, ki ce gwara da muka zo?"

"Uhum, bari Hajiya Batool, gaba daya cikina ma ya ka

ɗ

a wallahi kam

ar na saki a wando. Jikina yana bani cewa wannan tsinanniyar yarinyar ce da ke bibiyarmu kamar mayya. Ai ko birnin Sin ya ce na koma zan koma balle kuma na bar garin. Naji na yarda zan damƙa amanar dukiyata ga Manaja, idan ya so ko mene ni din sai na dinga

zuwa Kanon. Ba zan zauna a yimin sakiyar da ba ruwa ba. Shekara nawa ina yawon kashe ku

ɗ

i da fashi a maƙabartu akan Hussein? Ko wacece ta yi ka

ɗ

an."

Ta ƙarashe a kausashe. Hajiya Batool ta shiga jinjina kai.

"Nima ban yarda da ki zauna ki zuba i

do komai ya lalace ba. Bari ya fito na shigar da nawa ƙoƙon barar akan wannan shegiyar surukartawa da ke neman mallakemin

ɗ

a. Haba, komai yanzu nashi ƙarewa yake yi a wajenta?"

Hajiya Zeenatu dai ba amsa, kowa ya ji da nashi matsalar.

Ba jimawa

ya dawo dauke da wasu jarkoki biyu na ruwan magani sai wata leda. Tiryan-tiryan ya yi bayani. Ɗan rakiyarsu ya kallesu.

"Wannan jarkar ya ce tsakar dare za ki tashi daidai sadda hasken farin wata ya fito, za ki fita tsakar gida tsirara ki yi wanka da

shi har na kwana uku. Shi kuwa wannan

ɗ

ayan, tsarki za ki yi da shi ki yiwa Mijinki girki da shi har na tsawon sati daya ya ci. Sai wannan ƙullin maganin, ki tabbata kin sanya cikin turare irin mai maiƙonnan, ki dinga shafawa duk sadda mu'amala da ta ha

ɗ

ak

i da shi. Shi kuwa wannan layar, a tsakiyar bola za ki binneta ba tare da kowa ya ganki ba, wannan layar shi zai sa ki mallaki mijinki yanda ko uwarsa ba ta isa ta ganshi ta ce ya biyota ya je ba. Shi kuwa abincin da za ki girka masa, shi zai mantar da shi

yarinyar muddin ku ka bar garin, ba kuma zai ƙara tunawa da ita ba balle har ya ji yana son zuwa ya ganta. Kinga kenan babu damar da zai ƙara sanyata a ido, idan ya sanyata a ido toh komai zai rushe."

Tunda Hajiya Zeenatu ta ke, ba'a ta

ɓ

a yi mata bay

ani kan aikinta ba ta ji

ɗ

igon farin ciki ba sai a wannan karon. Gaba daya jinta take kamar wacce aka

ɗ

aure da jijiyoyin jikinta, ta kasa kwakkwaran motsi banda kai da ta gya

ɗ

a, shima sai da Hajiya Batool ta ta

ɓ

ota. Hawa saman bola ta binne ba matsalarta b

a ce, ta shiga makabarta ma ta kwaƙule ido akan abin duniya wannan ba ta

ɗ

aukeshi wani abu mai wuya ba. Tsakar dare ne ta tabbatar ba wanda zai iya ganinta kan bola, za ta iya wannan. Abu mafi ciwo mai sanyamata ta ji ta tsani kowace

ɗ

iya mace, bai wuce na

zuciyar Hussein da wata za ta mallaka ba. Wannan ya fi komai yi mata zafi. Gani take kamar ta hakura da sauya garin ta zauna ta bibiyeshi har ta yi tozali da yarinyar ta cakamata wuƙa a maƙoshi.

Murmushi ta yi, sai lokacin ta samu sukuni, sai a sannan ta

samu mafitar da a ganinta ya fi na wannan Malamin. Koda ba ita ba, za ta sanya a kashemata ita yanda wata ma ba za ta ƙara sha'awar shiga rayuwar Hussein ba.

Har Hajiya Batool ta gama shigar da nata koken aka ba ta magunguna, Hajiya Zeenatu ba ta san

anyi ba don ta tafi tunanin yanda za ta kashe baƙar dagar da ke shirin ruguza gininta.

Isuhu kallon Hajiya Zeenatu kawai yake yana nazari, a ido ma karantar mutum yake balle kuma ga ya buga ƙasa. A jikinsa yake jin ba za ta aikata yanda ya ce ba sai

abinda zuciyarta ta saƙa mata. Murmushi kawai ya yi don ya ga irinsu da yawa. Ya kuma tabbatar za ta yi kukan nadama, da ƙafarta za ta dawo wajensa ta nemi wani taimakon, a lokacin ne zai nunamata iyakarta.

Suka kammala suka biya maƙudan ku

ɗ

i kafin

su mike su fito, saurayin shi ya kai musu har mota sannan ya wuce da su gidan ƙawar Hajiya Batool, Hajja Mari (Maryam). Kasuwanci ne ya soma ƙulla ƙawancensu, saurayin yaronta ne yardajje mai mata ire-iren aikinnan. Ita ta ha

ɗ

asu da shi don su je ayi musu

komai.

Hajja Mari ta shiryamusu lafiyayyen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login