Showing 243001 words to 246000 words out of 255051 words
waya sai
dai hakkinta ne ta sani. Kusan ma akwai wadanda sai da suka sume, wasu kuwa banda kuka ba abinda suke yi kama su yi hauka.
Asibiti kai tsaye Emma ya wuce da Hajiya Zeenatu cike da tashin hankali, Likitan dai da ya zo mata dazun, Dakta Salisu, wurinsa
suka je. Ya yi matukar mamakin ganinta a cikin wannan yanayin, anan Emma ya labartamasa komai. Nan da nan likitoci suka rufu a kanta sai dai kuma sun makaro, Hajiya Zeenatu an samu ta
ɗ
an dawo daidai amma fa ta hadu da shanyewar
ɓ
arin jiki hakanan tana m
agana a jagwalgwale miyau na kwaranya ta gefen bakin. Banda hawaye ba abinda ta ke yi, ba abinda ke yawo a ranta sai kudirinta na zuwa Adamawa. A yanda ta ke jinta, ko a wane hali ta ke sai ta je. Sai ta samu Hussein ko ta halin ƙaƙa.
Nan kuma Dakta
Salisu ya ba Emma umarnin sanarwa mijinta da yan uwanta, Emma nan take ya sanarmasa cewa Ogansu ya rabu da ita. Dama kaf dinsu sai da ya bisu da alheri kuma ya yi musu sallama da zummar ya tafi kenan. Ba su ji dadin hakan ba amma sun mishi murnar rabuwa da
muguwar mata irin Hajiya Zeenatu, ko ba komai sun jima da sanin munanan
ɗ
abi'unta da yanda Ogansu ke shakkarta.
Ba wacce ta fado a ran Emma sai Hajiya Batool, ya san matar aminiyar Madam ce, don haka ya fice daga asibitin ya nufi gidanta.
Ha
jiya Batool na zaune tana jin wani mugun farin ciki yanda
ɗ
anta ya kira waya yana sanarmata da cewa a gobe-gobennan zai taso saboda kewarta da ta cikashi, kuma a shirye yake da bin umarninta, dama ita kiranye aka bata, kuma har gshinan kwalliya ta biya kud
in sabulu, ta kuma ci burin dole ta sanya ya saki Fa'iza ya auri wacce take so. Ta kira wayar Hajiya Zeenatu ya fi a ƙirga don ta ba ta labari amma ba ta samunta, karshe ma ta ji wayara kashe.
Tana shirin sake gwada kiran, sai ga Mai aikinta ta shigo
tana sanarmata da batun zuwan Emma daga gidan Hajiya Zeenatu. Nan ta bada umarnin ya karaso, Emma bayan sun gaisa ya fadamata halin da Hajiya Zeenatu ke ciki. Hankalinta ya tashi ba kadan ba, ta ka
ɗ
u sosai. Ba shiri ta ce ya je za ta leka asibitin. A yamm
acin ta je, ta yi mamakin yanayin da ta riski aminiyarta a ciki.
"Zeenatu! Ke ce haka?"
Hajiya Zeenatu sai ido da kuma hawaye. Da harshenta wanda maganar ba ta fita sosai ta ce.
"Ni..ce. Batool ki kai ni wurin Hussein."
Hajiya Batool ta
girgiza kai ta riko hannunta.
"Ki bari ki warke, ki nutsu kiyi zamanki a asibiti a dinga yi maki magani tukunna. Zan turo Dije ta dinga tayaki zama, za ki warke. Da kafarki za ki je wurin Hussein."
Hajiya Zeenatu dai sai hawaye, a ranta kawai ba
kin cikin abinda ya faru ta ke ji, da ace ta san hakan za ta faru da tun farko ba ta amsa wayar Manaja ba balle ta je kasuwar. Ji take inama ta kama hanyar Adamawa. Ta kara kallon Hajiya Batool dake ba ta labarin dawowar da
ɗ
anta zai yi, haka kawai maimak
on ta tayata farin ciki sai ta ji hassada da kishi sun kama ta, wato aikin Hajiya Batool har ya yiwu ita kuwa babu
ɗ
aya da ta aikata, don aikin tulun ba zai yi tasiri ba sai ta je ta barba
ɗ
awa Hussein hodar da Buzu ya ba ta. Haka tana ji tana gani Hajiya B
atool ta fice daga asibitin gami da jadddamata za ta turomata Dije. Ita dai Hajiya Zeenatu gyada kai kawai ta yi, a yau ta ji takaicin rashin ajiye ƴar aiki mace da ta yi.
***
ADAMAWA
Baƙin Kano sun sauka lafiya a family house, suka yada zang
o a
ɓ
angarensu, wannan karon ma an musu tarba sai dai ba kamar yanda aka saba ba. Kawu dai jikinsa duk ya yi sanyi, a ranar da yammaci ya tara manyan dattawan gidan maza da mata yana kuka yana roƙar gafararsu.
"Sharrin shai
ɗ
an ne, ku yafemin domin All
ah. Itama Aminar da yaran yanzu zan je na nemi afuwarsu."
Kowa kam ya yi farin ciki da jin hakan, ko ba komai har da rashin nadamarsa ne ya ba mutane haushi. Nan dai bisa jagorancin wani
ɗ
an uwan Babansu, Surajo, tsoho mai ran ƙarfe, suka
ɗ
unguma har
iyalin Kawun, a yammacin zuwa gidan Dada.
***
Kwance yake saman doguwar kujera, yayinda ta ke kwance saman kirjinsa. Sai cuku-cukun miƙewa ta ke yi sakamakon ra
ɗ
an da ya ke mata a kunne amma hakan ya gagara. Ta ko'ina ya matse ta gam! Ai kuwa bai y
i aune ba, yana kai bakinsa saitin nata, ta yi azamar kama le
ɓ
ensa na ƙasa ta ciza. Bai san sadda ya sake ta ba gami da kama baki.
"Aush!"
Ramlat na dariya ta mike, daga ita sai riga sky-blue marar nauyi, da ka
ɗ
an ta wuce gwuiwarta. Gashinta wand
a tuni ta warware kitson yana tufke a baya.
"Sorry." Ta fadi tana
ɗ
aga yatsunta bayan ta ja baya sosai tana dariyar mugunta. Hussein ya lashi le
ɓ
ensa ya manna mata harara.
"Zan kama ki, yau ba mai kwatar ki."
Ta narkar da fuska.
"Haba
don Allah Haskena, kai
ɗ
in ne ka ƙi hakuri ka bari na kammala girki. Nikam kana sane ka ce sai wani satin za ka fara zuwa aiki. Don.."
Ganin ya yi wani irin miƙewa ya na kokarin cafkota ya sa da wani irin gudu ta shige kicin ta rufe tana dariya. Ya ji
ngina jikin kofar.
"Za ki fito ki same ni, na san maganinki."
Murmushi kawai Ramlat ta yi mai bayyana haƙora ta ƙarasa wurin tukunyar miyarta, ba don na wutar ka
ɗ
an-ka
ɗ
an ta ke ci ba, ta tabbatar sai ya ƙone.
Shi kuwa gogan yana shirin kom
awa ya zauna, aka kwankwasa ƙofar falon da sallama. Ya amsa da ba da umarnin shigowa.
Hafsat ce, gaba daya jikinta a sanyaye. Ya dube ta fuska a tamke don har lokacin bai gama saukowa daga fushinta ba. Ta gaida shi ya amsa ciki-ciki.
"Dada ce ke
kira."
Ya gya
ɗ
a kai kawai ita kuwa ta miƙe ta fice kirjinta na dukan tara-tara. Tana tsoron abinda zai biyo baya idan ya ga wa
ɗ
anda suka zo gidan. Sanin halin zuciya irin nasa ne yasa Dada kiran AlHassan a waya akan ya zo gidan bayan ta mishi bayanin
komai. Wannan yasa ba
ɓ
ata lokaci, AlHassan ya kamo hanya don ba tazara sosai tsakaninsu.
"Heart, bari na je Dada na kirana. Kinji ko?"
"Toh."
Ta amsa ba tare da ta bu
ɗ
e ƙofar ba. Ya gyara zaman brown tshirt dinsa ya zura silifas dinsa baƙ
aƙe na maza na yawo a gida ya fice. Tun a farfajiyar gidan ya ci karo da motoci, wannan ya ba shi mamaki ya tabbatarwa kansa baƙi suka yi, amma daga ina? Shi ne tambayar da babu amsarta a yanzun. A ƙofar falon ya ci karo da takalman maza da mata. Haka kawa
i ya ji gabansa ya fadi da sauri kuwa ya karasa ciki da sallama. Idanunsa bai sauka kan kowa ba sai a kan mutumin da ya fi tsana nan duniya zaune kusa da Dadarsa su na kuka. Ya fahimci komai, ya gane kuma Dada ta sauko ta yarda da dukkan ƙarairayin da ya s
hiryamata don haka shi ba shi da bukata. Tsigar jikinsa gaba daya ta tashi tsabar
ɓ
acin rai, yayinda idanunsa suka ka
ɗ
a, ya ƙaraso ciki da zummar ƙarasawa kai tsaye ga Kawun ya shaƙe wuyansa babu ko tunanin yaransa da ke zaune a falon. Da sauri Baffa Suraj
o ya mike ya shiga tsakani. Ganin girma da cikar haibar dattijon mai tsananin kwarjini ya sa shi kasa ƙarasawa sai hawaye da suka shiga zubowa kawai daga kwarmin idanunsa.
"Me ya kawo shi nan?"
Baffa Surajo ya dafa kafa
ɗ
ar Hussein kafin ya ja han
nunsa ya bishi suka zauna saman kujera dakyar. Hussein banda girgiza ƙafa ba abinda ya ke yi yana hararar inda Kawun ya ke, ganin haka Baffa ya riƙe ƙafar.
"Ya isa
ɗ
ana. Ya isa."
Kawu ya taso zai ƙaraso inda Hussein ya ke, da wata irin tsawa ya
dakatar da shi.
"Kar ka sake ka ƙaraso nan! Kar ka yi wannan gangancin!"
Daidai da shigowar AlHassan da sallama, ya kalli mutanen falon ya kuma dubi Hussein mai magana ya sauke ajiyar zuciya. Ya san dama hakan za ta iya faruwa, bai ma yi tsamman
in zuwan wannan ranar nan kusa ba, sai dai Allah ne Mai shiryarwa.
Ya karasa ya gaisa da Baffa Surajo da matan Kawu har ma Kawun. Ya koma gefe ya zauna gefen Hussein.
"Ka yi hakuri mu ji ta bakinsa, ya riga ya zo kuma da iyalinsa baki daya, ka t
una, idan shi ne ya yi mana laifi, iyalinsa ba su da laifi tunda shi ne shugabansu."
Da kalamai irin haka Baffa da AlHassan suka taushi zuciyar Hussein. Ya yi shiru bai kara magana ba, wannan ya ba Kawu damar soma magana cike da jin wani tsananin kuny
a, wato wannan a duniya kenan ma, ina ga na lahira? Allah Ya tsaremu.
"Ku yi hakuri, ku yafemin. A ƙiyayyar da na nunamaku har da sharrin zuciya da shaidan. Na sani, Innarmu a baya ita ce kan gaba wurin ƙara rura wutar ƙiyayyarku a zuƙatanmu, sai ya
kasance ni abin ya zame min ciwo domin kuwa ya juye zuwa hassada da tsana. Ban ƙara jin tsanar Amina da Aminu ba, sai bayan auren Amina da mutumin da nake ganin ban kama ƙafar arzikinsa ba. Wato dai Marigayi Naziru, ban kuma gama farfadowa daga wannan baki
n cikin na ci gaban da Amina ta samu ba a rayuwa, sai ga Aminun da muke tunanin ma ya mutu, ya dawo. Tun kan ya zo Kano wurina, labari ya riskeni, na yi bakin ciki sosai, Karime kanwarmu ta fadamin da murnarta ni kuwa ban ga abin murna ba a dawowarsa musam
man da naji labarin ai rayuwa ta mishi kyau ya dawo har da matarsa da kuma yaransa ƴan biyu. A wannan halin sai ya kawomin ziyara duk kuwa da tarin kiyayyar da nake mishi, sai dai na gasamishi baƙaƙen maganganu wanda har ya mutu a lokacin ban yi dana sanin
su ba sai ma dadi da naji a lokacin ganin ya bar min filin duniyar na ci karena babu babbaka."
Kawu ya numfasa saboda kukan da ya shaƙe shi, iyalinsa da su Dada kuka suke yi cike da mamakin irin wannan salon ƙiyayyar da bawan Allahn ke yiwa
ɗ
an uwansa
na jini. Shi kuwa Hussein ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba, sai dai ko kallon Kawun ba ya son yi.
Kawu ya ci gaba da magana bayan ya sharce majina.
"Bayan shekaru da dama, a wani ziyara da Amina kika sa Husseini ya kawomin, lokacin ya samu
hutun karatun da yake yi a Dubai. A wannan zuwan ne yaron ya ban tsoro har nake ganin nan gaba zai iya cin mutuncina a gaban ko su waye. Saboda tunda nake da ke da Aminu, babu wanda wuyansa ya ta
ɓ
a yin tsaikon da zan fa
ɗ
a ya fa
ɗ
a, sai Husseini, ko Hassan b
ai ta
ɓ
a yimin cin fuskar da nake ganin Husseini ya yimin a lokacin ba. Wannan ne dalilina na farko da na ci alwashin sai na tarwatsa rayuwar Husseini. Sai ya rasa dukkan farin cikinsa. Sai dai me? Kafin na kai ga aikata duk wani abu da na yi niyya, na sam
u labarin
ɓ
acewar Husseini, ya gudu ya bar gida ba'a san inda ya shiga ba. A lokacin idan ka tona zuciyata banda tsananin farin ciki babu abinda na ke ji, har addu'a nayi Allah Ya dauki ransa ma. Bayan watanni uku da
ɓ
acewar Husseini, wataranar lahadi ba n
i mancewa, ni da kaina ke tuƙi a mota daga kasuwa zan koma gida, a hanya na hangi wata tsohuwar kwastama
ɗ
ita, a baya takan zo ta sararwa Hajiyarta atamfofi a shagona ko kuma yadika na maza ta tafi, a sannan tana budurwa ko kuma nace mace mai zaman kanta a
mma a karkashin ikon wata Hajiya mai safarar yara zuwa Makkah da sauran ƙasashen waje don aikatau ko akasin haka. Zeenatu kenan, tun a baya Hajiyar ta sha aiko ta shagona tun ban kai ma ga auren ita Maimuna ba, (Anti Amarya), tun a wancan lokacin muka sab
a, nakan ba ta shawara akan ta yi aure gudun kar ta
ɓ
ata rayuwarta don ni nasan wace ce Hajiya Balki uwar
ɗ
akinta, saboda na sha zuwa gidan muyi cinikin kaya ta siyawa ƴan matan yaran da ke gabanta ko kuma ta siyar, na kuma san irin kalar sana'arta. Daga b
aya kuma sai na bar ganin Zeenatu, sai wata Raliya ake turowa. Koda na tambayi Raliya, ta bani tabbacin ai Zeenatu ta tafi Makkah, a sannan na ji ba dadi kwarai don ban so ta cuci kanta ba sai dai dama daga yanayin Zeenatu na fahimci maganata ba wani shiga
rta ya ke ba."
Kawu ya numfasa, nan kuma dai dakin tsit ya yi babu mai kuka sai jin wannan labarin mai ban mamaki daga bakin Kawu. Ya
ɗ
ora zancensa.
"Ganin da na yiwa Zeenatu a ha
ɗ
a
ɗɗ
iyar mota, bai sa na kasa ganeta ba, asalima fuskarta ko ka
ɗ
an
ba ta sauya ba duk kuwa da
ɗ
umbin shekarun da aka
ɗ
iba. Parking ta yi a gaban wani katafaren shagon siye da siyarwa na maƙulashe, na juya kan mota da sauri na faka a gefenta. Sai dai ban kai ga fitowa ba, idanuna su ka sauka akan Husseini, ba karamin razan
a nayi ba, sai nake ganin abin kamar a mafarki, fuskokinsu kadai ya nuna suna cikin tsantsar farin ciki. Ban karasa ba, har suka shiga suka fito, mantuwa suka yi ko mene? Ban sani ba, na ga Husseini ya fita ya koma ciki, har zan je wurinta sai naji tsoron
kada ya fito ya gan ni, sai kawai na koma cikin mota na jira har ta tashi motarta ta kama hanya ta bar wurin, na bi su a baya har suka isa gidansu. Koda na ga gidan kawai sai na juya da zummar zan dawo na same ta don ba na kaunar Husseini ya gan ni. Bayan
kwanaki biyu, a wani yammaci na isa kofar gidan, cikin saa na isketa tana kokarin shiga cikin kyauren, ganin ita kadai ce na yi hon ta juyo, ni kuwa na ja na tsaya na fito. Ta shiga bi na da kallo kamar na neman ƙarin bayani da kuma son tuna inda ta san fu
skar, nan take ta tambaye ni. "Kamar na sanka." Na ba ta amsa da eh, kafin na ce kin manta Modibbo na Kwari? Nan da nan ta saki fuska muka kara gaisawa. Na ce "Yaushe kika dawo?" Nan ta ke sanarmin ai ta kai shekara guda da dawowa, daga nan kuma na nemi mu
ke
ɓ
e don mu tattauna wata muhimmiyar magana. Sai dai na tambayeta ko akwai wani saurayinta a ciki? Idan akwai na juya. Ni kuma na dadi haka don na gane irin zaman da suke yi da Husseini, burina ta cemin ba zaman aure ba ne.
Abin ya ba ta dariya. "Aa ai
kuma yanzu an girma da wannan kalar rayuwar, aure nayi." Na jinjina kai ina murmushin da bai kai zuci ba don ba haka na so ba. Sai dai ina bukatar mu zauna na ji bayani sosai. Koda muma shiga ciki, ta sanya aka kawomin lemo da ruwa, abinci kuma na ce aa.
Bayan mun nutsu na kara kai duba ga hoton Husseini da ita wanda tun shigowata ya dauken hankali, shakka babu aure ne suka yi. Anan na sanar da ita gaskiyar alaƙarmu da Husseini, a farko ta razana sosai har ma ya
ɗ
aure fuska tamau. Nayi dariya sosai na ce
ta kwantar da hankalinta ina bayanta domin ba na shiri da iyayensa, don haka ni ko nan da bangon duniya ma tana iya kai Husseini muddin ba za'a gan shi ba. Fa
ɗ
in hakan keda wuya ta kwantar da hankalinta saboda na biyomata ta sigar da dole ta samu nutsuwa.
A karshe ta ban labarin duk yanda aka yi na dinga dariyar mugunta. Ni kuma na yi mata alƙawarin ko na ji ana ra
ɗ
e-ra
ɗ
in an gan shi zan sanarmata, zan kuma yi asirin da zan rufe bakin duk wanda naji yana ra
ɗ
e-ra
ɗ
in ya ga ko mai kamarsa ne a kwaryar Kano. Na
kuma kara mata da cewa dole tana bukatar asirin da zai kara jin nan duniya ya tsani a tayar da zancen danginsa ko a tambayeshi, amma ta bar komai a hannuna. Wannan ne abinda na san na aikata, ya kasance ana neman Husseini, ni kuma nasan inda ya ke, amma n
a yi gum. Shiyasa koda Ramlatu ta zo da zancen Husseini, na kore ta na ce ba ruwana. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na sanar da Zeenatu, nan muka ce kawai a kashe ta yanda babu wata hanya da za'a san labarin komai. Sai dai kuma abinda Allah Ya riga ya tsara, ba w
anda ya isa dakatar da shi."
Kawu Modibbo na kaiwa nan ya dakata ya ci gaba