Showing 162001 words to 165000 words out of 255051 words

Chapter 55 - KARFEN KAFA complete

/>
ɗ

a

n sakin jiki da shi, ya fahimci koda yana da matsalar, a yanzun ta kau.

"Ke kuma zo dama ina nemanki."

Muryar AlHassan ya katse Hafsat daga tafiyar da ta soma. Ta ji kamar ta sa ihu, Tahir kam ransa ya ƙara fari ƙal sadda ya soma kai lomar abinc

in da ta girka da hannunta. Ta dawo ta zauna ta gaidashi kamar ta yi kuka. AlHassan ya murmusa don yasan kanun zancen.

"Jiya ina kika je? Na zo ance kin fita."

Ta

ɗ

an tura baki.

"Gidan su Iklima na je."

Ya

ɗ

an

ɗ

aure fuska.

"Kuma ai

na hanaki zumuncin da yarinyar ko kin manta?"

"Ka yi hakuri."

Ta fa

ɗ

i a ƙagauce don Allah-Allah ta ke yi ta shiga ciki don tserewa kallon da Tahir ke mata.

"Shikenan, je ki."

Ya ba ta umarni lura da ya yi har sannan babu wata shaƙuwa

tsakaninta da yaron. Shima ya fi kaunar hakan ko don gudun abinda zai je ya zo. Wayarsa ta yi ƙara, ya duba, Rasheed ne daga Saudia.

Ya

ɗ

aga suka gaisa a mutunce.

"Ina ta so na kiraka sai dai Allah bai ban iko ba sai yanzu. Ya su Dada?"

Al

hassan ya murmusa.

"Alhamdulillah, gamunan duka lafiya. Nima rashin lambarka ne ya sa na hakura. Fatan ka iske mutan gidan lafiya?"

"Duka kowa lafiya. Akan Hussein ne nayi kiranka. Na tuna wani abu."

Jin haka AlHassan ya miƙe da sauri har Da

da da Tahir na binsa da kallo.

"Lafiya?" Dada ta tambaya. Ya

ɗ

an dubesu.

"Babu komai Dada, bari na amsa waya ina zuwa."

Daga nan ya fita waje da sauri-saurinsa. Hannunsa har rawa ya ke yi.

"Ina jinka Rasheed, me ka tuna?"

Rasheed

ya ba shi labarin kaf abinda ya faru a ranar da suka yi bikin kammala makarantarsu a DUBAI shi da Hussein. Bai

ɓ

oyemishi wani labari da Hussein ya ba shi ba a ranar har suke dariya.

Safa da marwa AlHassan ya fara gami da dafe goshi.

"Innalillahi

wa inna ilaihir raajiun!Meyasa ban tuna da hakan ba? Meyasa muka kasa tunawa da cewar itama za ta aikata?!"

Rasheed ya amsa.

"Nima ban tuna da lamarinta ba sai yanzun da Mamina ta ankarar da ni!"

Cikim gigicewa AlHassan ya ƙara jefamasa tam

baya.

"Maminka? Ta santa?"

"Eh ta san ta, farin sani ma! Zan tambayi dukkan wani bayani game da ita zuwa safiyarku zan kiraka, ina ji a jikina

ɓ

atan Hussein nada alaƙa da ita. Mu binciki inda take don mu tabbatar."

Gumi sosai AlHassan ke yi,

kirjinsa na bugu da ƙarfi. Ya dafe goshi karo na biyu.

"Please kar ka

ɓ

ata lokaci Rasheed."

Ya fadi kamar zai yi kuka.

"Na damu da Hussein, na daukeshi dan uwa ba aboki ba. In sha Allahu komai zai zo karshe. "

Jinjina kai AlHassan ya yi c

ikin son gasƙata hakan. Daga bisani suka yi sallama.

"Meyasa ban tuna da ita ba?!" Ya fadi a fili zuciyarsa na wani zafi. Kamar faifan bidiyo haka komai ya shiga dawomasa filla-filla. Ya runtse idanu yana addu'ar neman dacewa.

***

DAURA..

Idan Ramlat ta ce bikin ya yi mata dadi toh fa ƙarya ce kawai saboda kusan fa

ɗ

a iyayen aka yi game da aurenta da Chairman wanda ba su da labarin zuwansa har Daura gaida tsoffin sai a sannan. Hankalinta da na yayyun ya tashi.

"Wato dai Chairman mak

ircinnasa ya kai inda ya kai!" Cewar Sauda bayan sun gama sauraron labarin Chairman daga bakin Ramlat.

"Mtsw, iyayenmu ne abin duniya yanzu sai ya rufemusu ido wallahi, daga ƙin gaskiya sai

ɓ

ata fa. Yanzu idan aka bari kika aureshi mene makomarki? N

ikam gaskiya ke na fi jin haushi ma wallahi Ramlat, kiyi hakuri kinsan ban iya

ɓ

oye abinda ke raina ba. Amma kefa bazawara ce, ta ya ya kuma ta ina za ki zauna a tauye hakkinki? Kamar ba ke ce kika jajirce a baya har kika auri wanda ranki ke so ba?"

N

aja ta fadi ranta na ƙuna, Ramlat dai dubansu take kowa da irin kalar ƙorafinsa. Zagi kam Chairman ya sha. Tsam! Ta miƙe ta fita dama hijab ne a jikinta, tana ji suna kiranta da tambayar ko haushinsu ta ji amma ba ta ko iya waigowa ba. Kai tsaye

ɗ

akin Mala

m Yahaya tsoho mai ran ƙarfe, cikin maza shi

ɗ

aya tilo ya yi saura a

ɓ

angare iyayen su Abba, wato Malam Abdullahi, Mu'azzam da ma sauransu. da suka rasu.

Yana zaune yana shan fura ga rediyonsa a kusa, sallamarta ya dauki hankalinsa, ya amsa ta karasa

ta zauna.

"Wace ce ne? Ko Uwani ce?"

Ya tambaya yana kakkanne idanu don ba kasafai ya ke gane mutane ba. Bakin har rawa yake ta amsa

"Malam ni ce, Ramlatu."

Ya yi ƴar dariya.

"Ki ce Amaryar Dikko ce. Ince dai lafiya?"

Kiran

ta Amaryar Dikko ya

ɓ

ata ranta ainun, ta ha

ɗ

iyi miyau mai

ɗ

aci. Idanunta sula cicciko da kwalla.

"Malam don Allah ka taimakamin, kai kadai za ka yiwa su Kawu Bello magana su ji. Wallahi bana son Dikko, don Allah ku ban lokaci na muku alƙawarin kawomak

u wanda zan aura nan kusa da yardar Allah."

"Wane magana kike yi haka Ramlatu? Abinda ki ka aikata a baya ne kike kokarin maimaita shi a yanzun? Ki fita idona wallahi! Ni ba ubanki ba ne da kika raina."

Zuciyarta ta yi wani irin nauyi, ta kasa da

urewa sai da hawayen suka zubo. Wannan baƙin fentin da ta gogawa kanta ba ta san sadda zai gogu har yan uwa su yi mata kallon mutum mai ƙima ba. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta zayyanemishi duk wasu munanan

ɗ

abi'un Chairman da ta sani. Ya yi shiru yana saurar

e har ta kai aya. Shiru ya biyo baya kafin ya jinjina kai.

"Shikenan, zan wakilta Iro (babban

ɗ

ansa) ya bincikamin a can Kanon. Idan har babu

ɓ

ur

ɓ

ushin gaskiya game da abinda kika fa

ɗ

a lallai ki sani, ni da kaina zan

ɗ

aura aurenki da mutuminnan."

Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin dama-dama. Kusan tun zuwanta banda Gwaggo Hansai da ta fahimceta da

ɗ

ai

ɗ

aiku cikin gwaggonnin nata, sai yanzu ta samu nutsuwar da ba ta ji ba. Ga zafin Hussein ba ta ƙara magana da Hussein ba yau kwana hu

ɗ

u kenan da z

uwanta garin.

A sanyaye ta mike ta fita, kici

ɓ

us suka yi da Harira

ɗ

iyar Amaryar Kawu Bello ta biyu, dagaske la

ɓ

e ta yi a zauren. Sai dai ta wayance.

"Af, ke ce a ciki? Dama abincin Malam ne Gwaggo ta ce na miƙa."

Ta gyadamata kai kawai ta

yi gaba. Ta rantse dai ba ta auren Chairman. Don haka za ta bi ta salama ta san yanda akai ta rabu da shi. A baya ta yi tunanin za ta iya hakurin zama da shi ko ba so, sai dai yanzun da so da kaunar Hussein ke ƙara ruruwa a zuciyarta, ba ta jin ko kusa za

ta iya. Allah-Allah ta ke yi su koma Kano don tuni ta samu cikakken sunan Kawun su Hussein dake Kano a wurin Hafsat. Dabara ta yi mata da cewar ta shiga Yakasan ta ga wata mai kama da ita. A haka har ta gangaro inda Hafsat ta yi mata bayanin cikakken sunan

Kawunnasu. Babban burinta ta koma Kano ta je ta sameshi. Ta fi kaunar bin komai daki-daki.

Maimakon ta koma

ɗ

akin, sai ta wuce sashin surukar Malam, matar Iro, Hajara, anan ta yi zamanta tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa sannan ta ha

ɗ

ata

da su Ansar da Ummi aka gaisa. Ba karamin kewar yarannata ta yi ba, ta yi musu albishir na dawowarsu a gobe.

Saƙo ta ga ya shigo, saƙon daga AlHassan, ta mike zaune da azama ta shiga whatsapp.

*"Ƙanwata, kinsan wata Hajiya Zeenatu Bashir a Kan

o? Ta ta

ɓ

a zaman Saudiyya, kuma tana ta

ɓ

a siyasa a baya. Yanzu dai ban da masaniyar komai a kanta."*

Dafe kirji ta yi. Shikenan duk yanda aka yi NESA CE TA MATSO KUSA!





I just published "BABI NA ARBA'IN DA

HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/LUjPZHlQycb

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

44)

_*"Eh na san ta."*_

Har ta rubuta hakan, sai ta goge da sauri. Toh idan

ta ce ta san ta kai tsaye me ta yi kenan? Girgiza kai ta yi.

Shiru ta yi na ƴan sakanni ba zato wayarta ta shiga ringing. Ta duba, AlHassan ne. Ta danna gami da karawa a kunne. Dakyar ya samu nutsuwar amsa sallamarta.

"Kin bu

ɗ

e saƙona ba ki ce

komai ba. Kin san ta?"

Ramlat ta sauke numfashi.

"Ka yu hakuri sai dai magana ce mai tsawo da ba za ta yiwu ta waya ba, yaushe za ka samu shigowa Kano?"

"Ko gobe ne zan iya tahowa Ramlat. Ki amsamin da kin san ta ko aa."

Ganin irin ru

ɗ

anin da muryarsa ta nuna, yasa ta saurin amsa mishi.

"Na san ta. Har abinda ba ka zato duk na sani, idan da dama gobe.."

"Kar ki damu, gobe in sha Allah zan zo Kano."

Ya katse hanzarinta da gaggawa. Ta amsa da toh, godiya ya yi mata ya katse

kiran.

Abu na farko da ya daurewa Ramlat kai, ta yaya Hussein ya gane zai iya samun wani bayani ta hanyarta? Sannan a ina ya san sunan Hajiya Zeenatu? Wannan tambayar babu mai amsamata sai shi da kansa don haka ya ha

ɗ

iye abinta. Ta shiga zullumi ba

ka

ɗ

an ba, ganin ta kasa danne abin, kawai sai ta kira Hisham.

"Ran Amarya ya da

ɗ

e."

Ta ja guntun tsaki, Hisham tun sadda ya ji labarin Chairman ya ke zolayarta.

"Ba wannan ba please, magana ce da ta shafi Hussein."

Jin haka sai ya mai

da hankali. Ta ba shi labarin yanda suka yi da AlHassan har da ƙudurinta na zuwa ganin Kawun Hussein dake zaune a Kano

"Da mamaki ace mutumin dake zaune cikin ƙwaryar Kano ya kasa sanin akwai wani jininsa a Kanon. Sai dai ban san irin raunin alaƙar da

ke tsakaninsu ba. Ina goyon bayan ki gwada zuwa ki sameshi. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ta ya ya Hussein zai soma fuskantar lamarin? Anya ba kuskure ba ne kai tsaye AlHassan ya tunkareshi ba?"

Ramlat ta jinjina kai.

"Shiyasa nake son zuwa na

fa

ɗ

awa Kawunnasu. Idan ma ya sani ka ga za mu sani, amma ba na jin zai sani. Haba,

ɗ

an uwansu fa."

"Hum, shikenan Ramlat. Allah Ya maidoku lafiya. Ya

ɗ

ora mu a kansu."

Ta amsa da amin kafin ya ba Aisha wayar suka gaisa da ta

ɓ

a hirar Daura daga b

isani suka yi sallama.

***

WASHEGARI...

*LAMIƊO CRESCENT*

"Na yarda, wace ƙasar ki ka za

ɓ

a mana?"

Mamakin amsar Hussein ya daskarar da Hajiya Zeenatu lokaci guda, ta ƙara matse layar hannunta domin ta yi imanin shi ne dalilin da yasa

ya yi amanna da zancenta.

'Allah Ya yi maki albarka Hajiya Batool aminiyar kwarai.'

Ta fadi a ƙasan ranta bayan ta tuno shawararta ta bi ta je wurin Bokansu ta kar

ɓ

o layar.

Farr ta yi da ido baki yaƙi rufuwa tana duban Hussein da rabin hankal

insa ke kan Laptop

ɗ

insa yana shigar da wasu takardu don son kauda damuwar da ke sukarsa a ƙirji.

"London nake son mu je, ka ga daga nan sai a binciki lafiyata sosai akan matsalar haihuwa. Kana iya

ɗ

aukar annual leave."

Ta fadi cikin dabara tana

mai kissimawa a ranta shikenan Hussein ya yi bankwana da Nijeriya har abada.

Ba tare da ya kalleta ba ya amsa a gaggauce.

"Ki yi duk yanda ki ka so."

Yana kaiwa nan ya miƙe ya nufi sama. Ba ta dakatar da shi ba don ita fa ya gama biyanta. D

a wani irin farin ciki ta kira Hajiya Batool ta fesamata. Dariya suka yi lokaci guda.

"Habawa! Wa ya fa

ɗ

amasa Borno gabas ta ke? Ai wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa."

Cikin nisha

ɗ

i Hajiya Zeenatu ta gyara zama.

"Allah Ya barmin aminiyar k

warai. Yanzu ki yiwa

ɗ

anmu magana ina so ya yimin duk wani shiri na tafiya."

Suka yi dariya sannan suka ci gaba da ƙulla-ƙullarsu.

***

Kasa zama ya yi sai kwanciya, kwanciyar ma bai fi minti uku ba ya miƙe zaune gami da dafe kai. A hayyacinsa y

a amincewa Hajiya Zeenatu, gani yake nisan da zai yi daga gareta shi zai sa ya mance da dukkan lamuranta. Hisham ba zai yi ƙarya ba don ya baƙanta ransa hakanan kawai, a farko yana mata kallon wata halitta

ɗ

aya tallin tal da ta dakatar da shi daga biyewa H

ajiya Zeenatu tun farko akan su bar garin, yau kam har Ƙasar ya amince su bari idan hakan zai ba shi farin ciki. Zai nisantashi da ita kuma ya yaye damuwarsa. To wa ya ke da shi da zai damu? Ba shi da uwa bare uba, ba danginsa babu na Hajiya Zeenatu. Wanna

n abu sau da dama kan

ɗ

auremasa kai matuƙa kuma ya jefashi cikin tafkin tunani iri-iri. Nan da nan farar fuskarsa ta yi ja kamar yanda idanun suka ka

ɗ

a. Ya riƙe kansa da ke sarawa da ƙarfi yana salati. Tun yana gani daidai har ya dawo gani dishi-dishi. Ya

yi kokarin mikewa tsaye sai ji kake tim! Ya fadi.

Ta turo ƙofar ta shigo ranta fari sol bayan kammala wayarta da Hajiya Batool. Turus ta yi ganin Hussein a ƙasa. Wani ƙara ta saki kafin da sauri ta nufeshi.

"Hussein! Hussein?!"

Babu alamar

zai motsa, don haka ta dauko ruwa ta yayyafa, nan ma shiru. Ganin haka ta yi wurgi da robar ruwan ya malale a kafet ta fita daga dakin.

"John! John! Ola!"

Kusan lokaci guda ma'aikatan dake kicin har wajen su uku suka fito.

"Yes Ma!"

Uma

rni ta ba su akan su hayo su taimakamata. Da gudu suka nufi saman, suka cicci

ɓ

i Hussein. Mayafi kawai ta dauka sai mukullin mota da ta damkawa John ta bi bayansu tana kuka. Kai tsaye suka wuce asibiti.

***

Sun sauka lafiya a Kano. Bayan kimtsawa suka

hadu suka ci abincin rana. Fuskar Ramlat cike da fara'a don tun safe bayan dawowarsu Muhibbat ta kawo su Ummi. Affan ya maƙale mata duk inda ta sa ƙafa yana biye. Labarin gidan su Aliyu da na Muhibbat kuwa ta sha har ta gode Allah. Ta lura dai ba su fusk

anci kowace matsala daga dangin Aliyu ba don a yanda bakin Ummi ba ya shiru sai ta fesamata.

Da yammacin ranar gidan ya rage daga ita sai Hajiya da su Ansar don tuni masu auren duk sun tafi gidajensu. Ta shirya tsaf da niyyar zuwa ganin Kawu Modibbo

kafin zuwan AlHassan wanda tun safe ya shaidamata cewar yana hanya. Ba ta

ɓ

oyewa Hajiya komai ba na halin da ake ciki. Hajiya ta jinjina lamarin.

"Ramlatu Allah Yasa a dace. Allah Yasa karshen wahalar yaron nan ce ta zo."

Cike da tausayawa Ramlat

ta amsa da amin. Suka yi sallama ta fita, ba ta

ɗ

auki mota ba don haka kawai ta fice. Har za ta wuce ta ga kyautuwar leƙawa gidansu Amrah su gaisa da Baba Dakta. Wannan yasa ta karya kwana ta shiga gidan da sallama.

Umma ta amsa fuska a sake.

"

Mutanen Daura, saukar yaushe?"

Dariya ta yi tana mai kama hannun Zaituna da ta maƙalƙaleta tana oyoyo.

"Tun safe muka iso, Hajiya ma ta kira ba kya kusa."

Umman Amrah ta bude baki.

"Af, an yi haka. Na ga kiranta toh da alama dai wannan



ɗ

iyartaki ce garin son a kunna mata kallo ta kashemin ƙarar."

Murmushi sosai Ramlat ta yi gami da shafa kan Zaituna tana mitar yanda amosali ke cinyemata gashin. Can kuma ta

ɗ

ago.

"Baba Dakta ya na nan kuwa?"

"Ba ki taki sa'a ba Ramlatu, y

ana asibiti."

Ta mike tsaye.

"Toh Umma zan dawo anjima in sha Allah. Zan

ɗ

an fita ne."

Umma ta amsa da toh, suka yi sallama ta fice.

***

Gidan ta tsaya tana ƙarewa kallo. Gida ne da ta sha zuwa ta wuceshi, ba ta mancewa akwai sadda

suka ta

ɓ

a shiga tun suna yara ita da su Amrah tsinko mangwaro aka koro su. Murmushi ta

ɗ

an yi tunawa da cewar gidan ƴan uwan mutum mafi soyuwa a zuciyarta ne ashe. Ta ƙarasa ta yi sallama ga mazauna ƙofar gidan sannan ta sa kai ciki. Ɓangare biyu ta gani s

ai kawai ta fa

ɗ

a na biyun. Wata baiwar Allah dattijuwa ta soma cin karo da ita zaune a tsakar gida, a gefenta wata budurwa tana gyaran alayyahu, wanda nan take ta gane fuskarta dalilin hotunanta da ta ke gani a status din Hafsat, sunan ne dai ba ta jin za

ta iya tunawa.

Suka amsa sallamarta suna dubanta, duba na rashin sani.

"Sannu da zuwa, bismillah. Rasheeda kai ta falo ina zuwa. " Fa

ɗ

in Amarya fuska a

ɗ

an sake, sosai Ramlat ta ji dadin tarbar da ta samu. Ta bi bayan budurwar da aka kira Rasheeda

zuwa falo.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login