Showing 84001 words to 87000 words out of 255051 words
dai ta dawo hayyacinta ba tukunna amma muna da ran itama lafiya don ba ta sha abinda yaronku ya sha ba."
Kowannensu kunya ta kamashi, Malam har hawaye ya share cike da bakin cikin kasa
ncewar Aliyu
ɓ
atacce. Addu'a yake mishi ba dare ba rana akan Allah Ya shiryamasa shi.
Gaba daya mazan suka tafi, duk yanda Abulle ta so a kyaleta har ya farfa
ɗ
o suka ƙi, haka suka tasa uwarsu a gaba da zummar da yamma zasu dawo, Amarya da Ramlat kad
ai aka bari.
Kuka take bayan ta kwance goyon Ummi ta mikawa Amarya yanda ta bukata, ta janyo hijabin ta rufe fuskarta, Aliyun ma ba bukatar ganinsa take ba, takaicinta ya tafi ga abin kunyar da ya jazamusu. Idan ta tuna da mace aka ganshi wacce ba
ma muharramarsa ba ya fi komai baƙanta zuciyarta. Ta ƙara gane ba ta yi sa'ar aure ba, miƙewa ta yi ta nufi hanyar fita.
"Ina za ki je?" Fadin Amarya wacce ita kanta zaman ya isheta.
Ta dubeta da jajayen idanunta tana jan majina.
"Waje za
n
ɗ
an fita yanzu zan dawo."
Amarya ta gyada kai, yau kam ta ji tausayin yarinyar a ranta. Ramlat ta fita tana jan ƙafa har waje, tafiya kawai take cikin tafkeken asibitin na Malam tana zagaye, kuka take, kuka kamar wata ta
ɓ
a
ɓɓ
iya tana ambaton Allah.
Ba ta ko damu da idanun jama'a ba, ƙasan wata bishiya da aka saka kujeru ta samu ta zauna, hawaye take fitarwa tana jin wani ka
ɗ
aici a ranta. Kamar ta yi wani babban rashi alhalin ita din tana da gata, tana da iyaye da kuma yan uwa.
"Abinda kuke jiy
emin kenan?" Ta fadi a fili tana sheshsheka. Jikinta har rawa yake, so da kaunar yan uwanta ke ratsa dukkan ga
ɓɓ
anta. Idanunta ya kai ga wasu ma'aurata kuma inyamurai zaune a can gefe guda. Meatpie da lemu suke sha, mijin na rike da yarinyar a cinyarsa, ma
tar kuwa ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe. Har suka kammala suka mike, yana rike da jakarta da kuma hannun
ɗ
iyarsu da bata wuce shekaru biyar ba.
Kallon ƙurillah take musu har sai da suka kalleta ta ankara ta sauke idanunta. Tana ji suna cewa
watakila mutuwa aka yi mata ba ta ko
ɗ
ago ba. Ta jima a wurin kanta na sarawa zuciyarta na tashi, ba ta samu sauƙin kirjinta ba sai da ta matsa can gefe ta yi amai, wata baiwar Allah na mata sannu har da siyo ruwa ta bata ta sha. Godiya ta yi sannan ta kam
a hanya ta koma da tunanin Ummi kada ta farka.
Ai kuwa Amarya ta gani a waje sai jijjiga Ummi take tana kalle-kallen inda za ta hangota. Tana hangota ta hau fadan inda ta tafi ta bar yarinya na kuka. Kar
ɓ
arta kawai ta yi ta bata hakuri, wuri suka sam
u suka zauna ta sanyata a hijabi ta hau bata mama.
"Ai bai farka ba har yanzu, nima gajiya nayi da ganin tashin hankali na fito. Wani aka kawo kamar ma ƙafarsa ta ru
ɓ
e don kamar an daddatsata abin tausayi.
Gyada kai Ramlat ta yi ta kauda kai.
"Sai fa hakuri Ramlatu, zama da irin Aliyu sai hakuri. Kinga da yanzu kina can gidanki hankalinki kwance amma to, tunda mai afkuwa ta riga ta afku ba yanda aka iya sai hakuri."
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, tasan dama suna da labarin aurenta da
Hilal da kuma abinda ta aikata, sun jima suna yadamata habaicin da ta san iyakar gaskiyarsu ce. Nadama da dana sani suka ƙara tararmata.
"Ramlatu?"
Ta
ɗ
ago kai jin murya kamar ta Dakta. Shi
ɗ
in ne kuwa ga dalibai a bayansa, dama yakan zo asib
itin sai dai ba koyaushe ba.
Ta miƙe da mamakin yanda aka yi ya ganeta, durkusawa ta yi ta gaidashi ya amsa.
"Me kike yi anan?"
Za ta yi magana kuka ya ci ƙarfinta, Amarya ce ta fadamasa Aliyu ne ya yi hatsari yana ciki.
"Ya Salam
, bari na karasa. Ki yi hakuri, ki bar kukan."
Ta gyada kai sannan ya wuce. Tsoron kada ya ji abinda ke damun Aliyu ya fadawa Abbanta mai fama da kansa ya sa ta miƙewa zumbur har Ummi na kokarin su
ɓ
ucewa daga hannunta sakamakon gefen hijabinta da ta take
ba ta ko lura ba.
"Miƙota." Fadin Amarya. Ba musu ta miƙa ta ta bishi ciki, ta iskeshi tsaye wurin likitan da ta gane shi ya kar
ɓ
i Aliyu.
"Baba Dakta." Ta kira sunan, ya dubeta.
"Ina zuwa Ramlatu." Ta gyada kai ta ja baya kadan. Jikinta
rawa yake ga wani dumi da ya dauka. Ta ha
ɗ
iyi miyau har ya kammala ya nufota.
"Na ji duk abinda ke faruwa, Allah Ya ba shi lafiya."
Ta amsa da wani matsanancin kunya, kanta ta sadda kasa hawaye na
ɗ
iga jikin hijabin nata.
"Abba, don All
ah kar ka fadamasa, bai da lafiya. Kar ya ƙara tada hankalinsa, ni ce silar duk abinda ya faru gareni, don Allah a bar ni na yi kukana ni kadai. Baba Dakta ka rufamin asiri kar ka bari su sani. Abinda na shuka nake girba."
A raunane ta ƙarashe, tausay
inta ya kamashi. Ya ja numfashi.
"Ba zan fadamasa ba Ramlatu kinji? Kema muna miki fatan komai ya zo karshe. Kema ba ki da lafiya ko?"
Ya fadi ganin yanda take rawar sanyi, ta dubeshi.
"Bansan me nake ji ba."
Ya kama hannunta suka nufi
wurin likitocin.
"Dr Amina."
Ya kira sunan daya ciki, ta mike cik da girmamawa ta ƙaraso, umarni ya bata akan ta dubamasa jikinta. Ba musu ta kama hannun Ramlatun cike da kulawa suka shiga wani dan daki.
Duk abinda ya kamata a biya na R
amlatu, Baba Dakta da kansa ya biya. Hutu take buƙata sakamakon juna biyun dake jikinta. Baba Dakta ya jinjina lamarin, hatta Amarya ta yi mamaki ta kuma yi addu'ar Allah Ya raba lafiya.
Cikin ikon Allah bacci wahalalle ya yi awon gaba da ita bayan a
n bata lafiyayyan abinci ta ci. Daki ne a wadace, ga Ac a kunne. Amarya itama abincin ta ci ta kwantar da Ummu gefen Ramlatun ganin ta yi bacci. A waya ta sanar da Malam ya kirata idan sun shigo don tana wurin Ramlatu wacce ake yiwa ƙarin ruwa. Tana so ta
ce juna biyu ne da ita amma ta bar wa cikinta sai sun zo din.
***I just published "BABI NA ASHIRIN DA HUDU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/TmTSyIbktab
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir R
aheem.
24)
"Ka ji tsoron Allah, da ace kai din mai hankali ne da dogon tsinkaye, wannan lamari da ya afku kadai zai sa ka gane son da Allah ke maka da bai
ɗ
auki ranka a hanyar sa
ɓ
onSa ba. Me kake nema a duniya haka Ali? Meyasa ka fita zakkah ciki
n iyalina? Idan wannan bai isheka ishara ba ban ga kuma abinda zai sa ka nutsu ka yi hankali da lamarin rayuwa ba."
Malam na kaiwa nan ya ja jiki ya bar dakin gami da bin bayan ƴan uwansa, Abulle ba ta ce uffan ba don jikinta wannan karon itama ya yi
sanyi, har kuka ta yi tana ƙaƙaba laifin
ɓ
atancin Aliyu a kanta.
Aliyu ya lumshe idanunsa ya bude yana duban mutan
ɗ
akin, Abulle ce sai Atine uwargidan Malam sai kuwa kannensa mata sannan ƙalilan daga samarin gidansu. Kalaman Malam sun ta
ɓ
a zuciy
arsa, jikinsa ya yi sanyi. Bai ta
ɓ
a dauka zai rayu ba, kusan ma duk abinda ya afku ba'a hayyacinsa yake ba. Ya ji dai sadda Zee ta ja hannunsa akan ya zo ya mayar da shi gida tunda ba zai iya jan mashin dinsa ba. Yana gani bibbiyu ya bi bayanta zuwa motart
a.
"Tana ina?"
Ya yi maganar a fili.
"Wa? Ramlatu? Tana can itama ta samu bacci, tana dauke da juna biyu amma abincin kirki ba ta iya maida hankali wurin ci ba?"
Abulle ke wannan dogon jawabin da ba shi ya nema ba. Gabansa ya fadi, yan
zun ne ya tuna da Ramlat. Da wace fuska za ta kalli abinda ya aikata? Me za ta ce? Kuma ciki ne da ita?
A zuciyarsa yake wannan tattaunawar kafin hankalinsa ya
ɗ
auku kan hirar da ta ji Amarya da Abulle nayi bayan ficewar kannensa.
"Ai yarinyar
ƴ
ar mace ce, uban ma ba'a san inda yake ba wai haka naji su Alhaji na fada. Ba kiga uwa ba, an sha kwalliyar gwala-gwalai da alama dai akwai arziki. Maimakon a ga ta yiwa yarinyar fada ko ta nuna jin kunyar abinda
ɗ
iyar ta aikata, sai kawai ta nemi ma yin
fa
ɗ
a akan dalilin ita yarinyar na yin tuƙin dare. Har da cewa meyasa ba ta kira Direba ya tuƙa ta ba. Sai da ta sa aka sallami diyarta ta biya komai da aka bukata ta fice da ita wai sauya asibiti zasu yi."
Salati sosai Abulle ta shiga yi jin wannan ba
yani, Aliyu kam yana daga kwance kansa ke sarawa da wani irin sarawa wanda yasan dalilinsa. Kwanakin da ya yi bai sha sigari bane ke son tambayarsa.
***
"Girma kake ƙarawa Zakina, ga matarka yanzu wani cikin ne gareta, don Allah don sonka da Ann
abi s.a.w ka daina wannan shaye-shayen. Ba amfanin da yake maka. Don Allah Zakina idan ma kana aikata zina itama ka daina kar fushin Allah Ya sa.."
Riko hannun Abulle ya yi dake faman kuka.
"Zan daina, zan daina My granny."
"Yaushe za ka dai
na? Da ace Allah Ya dauki ranka yanzu, me za ka je ka ce? Ta wane hanya ka mutu?"
Gabansa ya fadi, ya ha
ɗ
iyi miyau maƙwat. Jikinsa ya kara yin sanyi kwatankwacin yanda nasihar iyayensa maza ya jefasa. Jinjina kai ya yi.
"Zan daina."
Ya fadi
a can ƙasan maƙoshi karo na biyu.
"Na fi so naji ka ce ka daina akan za ka daina. Za ka daina na nufin ba lallai ba, kuma akwai sauran lokaci, amma ka daina shi ne ka aiwatar kuma ba za ka ƙara ba."
Ya lumshe idanu ya bude. Abulle na kara kallon
sa hawayenta na zuba. Kyakkyawan yaro ne a baya, fari ƙal wanda a yanzu ya yi duhu kamar ba shi ba. Aliyu mai fararen haƙora kamar tangaran lokacin da ya fara zama saurayi, yanzun ya rine ya koma kalar ruwan goro.
Hura mata iskar bakinsa ya yi, duk d
a cewa ya yi brush hakan bai sa iskar wari ba, kadan kenan daga illar shan sigari. Abulle ta kauda kai ta share hawayen.
"Ina Babyna? Naji kun ce ciki gareta, Granny Banda jari yanzu, bana so kuma na kara baƙanta ran Baby irin wanda na mata a farko."
Harararsa ta yi.
"Me kake son cewa?"
Murmushi ya yi, yasan ta dauka jari zai nema amma madadin hakan ce ta faru.
"Bashin banki zan ci, ko kuma na siyar da gidannan na siya wanda bai kai shi girma ba, sauran kudin na ƙara a kasuwa muga
abinda Allah zai yi."
Ta yi shiru.
"Ma dai yi maganar idan ka fito kawai."
Bai ja ba shima ya bar zancen kafin ya mike da zummar zuwa wurin matarsa.
***
Bisa jagorancin Abulle suka karasa dakin Ramlat, tana zaune saman darduma ta idar
da sallar Magriba yayinda Amarya ke gefe tana yiwa Ummi wasa. Ya sa hannu ya karbi Ummi ya rungume.
Kallo
ɗ
aya ta yiwa Aliyu ta sunkuyar da kai, kallon ba ta son yi balle ta tuna silar komai. A yau ta gane amsar tambayarta ta baya. A lokacin da aka
daura aurenta da Aliyu ita ke kuka iyaye da ƴan uwanta na dariya. Ashe kukan ma a sannan ta soma, shi ne farko kuma ba shi ne karshe ba. Ba ta san hawaye take ba sai da ta ji tafin hannunsa saman fuskarta ta yi saurin rikewa gami da
ɗ
ago kai. Sai lokacin t
a kula su biyu ne a dakin. Kallon na tsaneka ta ke jefamishi. Shi kuwa kallonta yake idanunsa cike da nadama da dana sani.
"Kar ka kara gigin ta
ɓ
ani, Ramlat b mazinaciya bace wallahi. Ka je can ka.."
Ya yi saurin toshe bakinta da hannu, duk koka
rinta na ganin ta cire hannunsa ta kasa, kawai sai ta fashe da kuka ranta na zafi.
"Baby kiyi hakuri. Baby wallahi wallahi ban ta
ɓ
a kusantar kowace mace idan ba matar aurena ba. Baby yaudarata suka yi, kwaya mai ƙarfi irin wanda ban ta
ɓ
a sha ba suka
ba ni na sha. Ban kuma san inda kaina yake ba har muka shiga mota mai afkuwa ta afku."
A sannan ne ta fincike hannunsa ta watsa mishi banzan kallo, gaba daya ya ji wani nadama ta mamayeshi. Idan ance akwai ranar da zai ji kunyar mace zai rantse ƙarya
ne.
"Wannan ba damuwata ba ce. Damuwata haihuwar da nake yi da kai. Aliyu ba don ina tsoron halakar da zan fa
ɗ
a ba wallahi ina maka rantsuwa da Allah sai na zubda abinda ke cikina. Sai dai na sani laifi ne zan kara akan kuskuren da nayi tun farko na
auren mutum irinka wanda bai san darajar kowa ba sai kansa! Kai har kaima ba ka san darajarka ba! Ba ka san darajar da Allah Ya yi maka ba. Ba ka ta
ɓ
a godemaSa ba ta hanyar aikata nagari wanda kowa zai gani ya sakamaka albarka. Mun haihu da kai kuma ga wa
ni rabon Aliyu, idan a baya ba ka da wani da ka ke jin kunyarsa ai a yanzu ko don darajar yaranka wani abin za ka kiyaye. Wane
ɗ
a ne zai farin cikin kasancewarsa
ɗ
anka? Ummi idan ta isa aure kana tunanin manemanta ba zasu gano tarihin ubanta ba su fasa? Sh
ikenan kai babu wani abu naka nagari, shikenan duk inda za'a je a tambayi tarihinka kai mutumin banza ne? Aliyu meyasa ka rufemin kai waye, meyasa ka
ɓ
oyemin munanan halinka ka nunan kai nagari ne? Kaicon abinda ka sani na aikata, kaicona da na za
ɓ
i na sa
ɓ
awa iyayena akan mutum irinka. Ba duniya ba, daidai da ni kaina tsanar kaina nake idan na tuna irin tijara da fito na fiton da nayi da ƴan uwana akanka. Yanzu gashinan ina girbar abinda na shuka. Wallahi ban kyautawa kaina ba."
Ta cure wuri guda gami
da saka kanta cikin cinyoyinta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, idanunsa suka ka
ɗ
a suka yi ja, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi, a gefe guda kalaman Ramlatun suna mishi zagaye cikin ƙwaƙwalwa da zuciyarsa. Ummi kuka take yi ganin yanda uwarta ke ku
ka, Ramlat ta kasa
ɗ
ago kai balle ta kar
ɓ
e ta. Cak ya mike ya fita kafin ya dawo ya yi zaman dirshan a gabanta, har sannan kansa ciwo yake kamar ya kife a wurin.
"Kiyi hakuri Baby, kiyi hakuri."
Ɗ
ago kai ta yi tana kallonsa da
ɗ
an murmushi. Maji
na ta ja.
"Um um Aliyu, ai kamata ya yi muyi yanda muka saba, ka kamani ka jibga, ka kamani ka zagi iyayen da suka kawoni duniya. Iyayen da na bijirewa umarninsu a kanka, na guji za
ɓ
insu duk domin na faranta maka. Idan yau ka zagesu waye ya bada ƙofar
? Gani kake ni na baka ƙofar ka yi musu duk abinda ka so, ka fadi dukkan wasu bakaken kalamai a kansu. Toh Aliyu naji ni ce, amma na dauka idan so da kauna na gaskiya ne, karen gidanmu ma sai ka girmamashi balle kuma wadanda suka yi silar zuwana duniya? Na
gaji, Aliyu na gaji. Aliyu idan kana sona dagaske, kana kaunar Allah da ManzonKa s..a.w, kana kuma kaunar iyayenka ka sauwakemin na je na yiwa iyayena biyayya. Ka sakeni na je nayi auren da martaba da darajata za ta..."
"Ramlatu!" Gaba daya suka kai
duba ga bakin ƙofar, Baba Dakta ne a bayansa Amrah da Umma. Ya ƙaraso ciki da sallama suka amsa. Aliyu ya mike ya gaidashi, Amrah sakin baki ta yi tana duban hawayen da Aliyu ke fitarwa. Baba Dakta ya amsa gami da yi mishi sannu da jiki. Daga nan ya gaida
Umman Amrah cikin girmamawa. Itama ta amsa ta mishi sannu.
Bayan sun zauna ya dubi Ramlat.
"Kina cikin hayyacinki kuwa? Mijinki kike cewa ya sakeki? Kinsan zunubin da kika kwasa sanadin wannan furucin? Kar na ƙara ji, duk tsanani yana tare da sa
uki musamman idan bawa ya miƙa lamarinsa ga Allah. Kar fa ki manta kina dauke da juna biyu, wannan damuwar sai kin daina sakawa ranki. Kinji ko?"
Ta gyada kai tana share hawaye wasu na zubowa. Amrah mai saurin kuka har ta soma tayata. Baba Dakta ya mi
ke suka fita tare da Aliyu. A waje ya yi mishi dukkan nasiha ya kuma kara da cewar ya riƙe amanar ƴarsu da suka damƙamishi. Aliyu ya yi godiya don ko ba komai ya taimaka masa daga daurin dabaibayin da Ramlatu ta yi mishi, yasan ba don shi ba haka zasu yi t
a ja in ja akan ita sai ya saketa.
***
Ranar da aka sallami Aliyu ya dawo gidan,