Showing 12001 words to 15000 words out of 255051 words
da mata suka yi ga Hal
ima ba wacce ranta ke susa da maganganun Ramla. Ta kuma ci alwashin sai ta rama ko ba jima ko ba da
ɗ
e.
***
Suka yi parking
ɓ
angaren da aka ware don ajiye ababen hawa. Kusan a tare suka fito. Kai tsaye Hajiya Zeenatu ta fiddo waya ta dannawa Chai
rman kira. Suka
ɗ
an yi magana sannan suka kashe. Da kwatancensa suka nufi ofishin, ba tare da wani jinkiri ba aka yi musu iso zuwa ciki.
Aliyu Dikko matashin da zai shekara arba'in da
ɗ
oriya ya dubeta fuska a washe.
"Manya gatan wasa, ganinki
sai da dalili."
Ta yi dariya tana mai zama sa'ilin da suka zauna.
"Ai ku ne gwamnati, shiyasa dole ku za'a bi ko an ƙi. Ba don wankin hula na neman kai ni dare ba ai ba ka ganni ba."
Ya ƙyaƙyace da dariya gami da maida hankali da matashin d
a tun gaisuwar da suka yi bai
ɗ
ago ba balle ya shiga maganarsu, asalima waya yake sarrafawa.
"Ah lallai kam. Wannan ƙaninmu ne?"
Tambayar ta sa ya
ɗ
ago kai ya watsamasa wani irin kallo kafin ya dubeta fuska a murtuƙe.
"Please mu yi abinda
ya kawomu."
Ganin haka ta shiga nutsuwarta ba shiri.
"Chairman jama'arka sun min laifi duk da dai da nawa laifin. An ƙullemin shago saboda ku
ɗ
in haraji. Wannan abu ba ƙaramin tozarci ne a gareni ba don haka na zo nayi clearing komai."
Ya j
injina kai, zai so ya san wane saurayin da har ya iya jan Hajiya Zeenatu kamar raƙumi da akala sai dai kuma ba fuska. Waya ya
ɗ
auka ya danna kira kai tsaye ga department
ɗ
in da ke kula da wannan
ɓ
angare. Mintuna ka
ɗ
an shugaban department din ya hallara. Ci
ke da girmamawa ya gaida Chairman. Ya saurari dukkan jawabinsu kafin su mike su bi bayansa don aiwatar da abinda ya dace.
"Bismillah ku zauna."
Oga Ɗalhatu ya umarcesu bayan sun isa ofishinsa. Ya kira abokiyar aikinsa da ya ke da tabbacin takar
dun Hajiya Zeenatu a hannunta suke.
Ramla na zaune ta dukufa shigar da wasu bayanai kwamfuta, tana yi tana hamma da duban lokaci. Sa'arta
ɗ
aya ba ita ke da alhakin
ɗ
auko yara ba a'a ranakun Litinin zuwa Alhamis bisa yanayin aikinta wanda sau da dam
a sai hu
ɗ
u suke tashi. Sai dai a yau
ɗ
in gani take ta gaji ba ka
ɗ
an ba, kamar ba za ta iya kai wannan lokacin ba, haka kawai ba ta jin dadin jikinta. Kiran da Oga Ɗalhatu ya yi mata ne ya katse komai da take yunƙurin yi, ta miƙe
ɗ
auke da file din Hajiya Ze
enatu har wani abokin aikinta Salihu na fa
ɗ
in Hajiya ta ji wuta ta kawo kanta suna dariya.
Da sallama ta shiga ciki bayan an amsa mata. Gaba
ɗ
aya sun bata baya, sai Oga Ɗalhatu dake fuskantar ta.
"Yauwa ƙaraso Ramlatu."
Ta shigo sosai, ido
hudu ta yi da Hajiya Zeenatu, hakan yasa ta gaisheta da
ɗ
an murmushi. Ita kuwa ta amsa ciki-ciki tana kauda kai. Ba ta ga dalilin da za ta sakarwa kowace
ɗ
iya mace fuska ba muddin tana tare da Mijinnata. Tana kishinsa, kishi mai tsanani. Ramla ta kauda ka
i da mamakin hali irin nata, sam ba ta ko kalli mutumin da suke tare ba balle ta maida hankali gurin gaidashi.
Bayanin Oganta take sauraro kafin ta karkata ga Hajiya Zeenatu ta fara yi mata bayanin duk abinda ya dace ta yi kuma ta biya cikin kwarew
a da sanin makamar aiki.
Ya
ɗ
ago kadan ya kalleta, aka ci sa'a itama idonta ya sauka a kansa sadda ta
ɗ
an rausaya ido duk cikin bayani. Kirjinta ya harba, ina za ta mance fuskar da tun kallon farko ya kasa
ɓ
acemata? Shi ne, shi dai da ta yiwa
ɓ
arnar
dubunnai ya yi mata afuwa. Ya ha
ɗ
e cikin maroon voyel sai hula da ta hau da kayan. Ɓata lokaci ne ka tsaya siffanta tsatsar kyan da Allah Ya mishi. Gareshi kuwa, kallo
ɗ
aya kwaƙƙwara ya mata sai ya
ɗ
auke kai.
"Aikinki za ki yi ko kuwa kallon mazan w
asu?!"
Ta ji kalaman Hajiya Zeenatu tsakar kanta, sai sannan ta ankara da tafiyar tsutsar da kalamanta suka soma yayin
furtawa sakamakon kallon sanin da ƙurillar da take yiwa abinda bai shafeta ba. Sai dai zafin kalaman Hajiyar ya sa ta
ɗ
aure fuska. H
ar aka kammala komai suka tafi ba ta ko ƙara kallonsa ba, balle shi kuma da ba ta gabansa.
"Kinsan Allah mijinta ne, makwaftan wata ƴar uwata ce. Wallahi a ranar farko da na gansu tare sun fito daga gidansu ban yarda ba don har ina cewa ta samarmin l
ambarsa, ƙarshe na yarda don akan na gaidashi a bakin ƙofa, matarnan har
ɗ
aga hannu ta yi da zummar marina ya riƙe hannun sannan ya ja hannunta suka koma ciki. Tun daga ranar ban ƙara wannan gangancin ba."
Hirar Najaatu da Halima ta tsinkayo daga nasu
mazaunin, tsalam ta ji Salihu ya sa baki.
"Ke Hali dubu! Yanzu wannan mijinta ne?"
Tana ji Halima ta hau rantsuwa da fadin kwarai kuwa.
Nan da nan aka hau yin caftarsu, daga mai cewa ku
ɗ
i ya gani ya yi wuf da ita sai mai fadin bai yarda ba
saboda sam saurayin bai yi kalar babu ba.
Uffan ba ta ce musu ba har lokacin tashi ya yi, ta ha
ɗ
a tarkacenta ta yiwa kowa sallama ta fice.
Tuƙi take sai dai hirar da akai akan matashin da Hajiyar da aka kira da matarsa ya tsayamata a ƙahon zuc
iya.
'Me ya kai shi? Da ƙuruciyarsa da komai? Kyakkyawa kuma
ɗ
an gayu irin wanda babu macen da za ta ganshi ba ta ji sonsa ba? Me ya kai shi auren wacce ko ba ta yi sa'ar mahaifiyarsa ba, za ta zo a babbar yayarsa?'
Nan da nan zuciyar ta warware
mata zaren da ta ƙulla ba tare da shan wahala ba.
'So! So ne! Ba abinda ba ya sa wa, kamar yanda ya sa na aikata abinda bansan zan iya ba.'
Ta ha
ɗ
iyi miyau tunanowa da ranar da ko daga bacci ta farka za ta bada labarinsa.
***
_*SANADI*_
Bini-bini sai ta kalleta ta ci gaba da tafiya tana murmushi. Ƙarshe Ramla ta gaji ta kai mata duka a baya tana dariya.
"Wai ko ke aka sanyawa ranarnan sai haka!"
Dariyar suka yi gaba
ɗ
aya.
"Wallahi ba ki ji yanda nake murna ba. Ba don
na gama tsallena cikin gida ba da yanzun ƙarawa zan yi."
Tsaki da dariya ta yi kawai ba ta ce uffan ba. Sai da suka ƙarasa har titi Ramla ta samu
ɗ
an sahu kafin su yi sallama ta soma ƙoƙarin tsallakawa hannun da zai mayarta gida.
"Ƴan mata ba
mu chanji mana."
Ta juya inda maganar ke fitowa, adaidaita ce ta yi parking a gabanta, sai da ta ji ba za ta iya yafewa kanta ba sa'ilin da idanunsu suka ha
ɗ
u, da ba ta kalleshi ba, abubuwa da dama ba zasu chanja daga zuciya zuwa gangar jikinta ba. Sai da
i kuma nan take ta ƙaryata. Shima da yake daga cikin
ɗ
an sahun watsi ya yi da nashi a kwandon shara ya maida kai zuwa cikin abin hawar.
"Babu kenan." Ta ji muryar
ɗ
an sahun sa'ilin da yake sauka yana nufar abokin aikinsa da zummar kar
ɓ
ar chanji. Bisa
kuskure idanunsu ya ƙara sarƙewa, ta yi saurin janye kwayar idanunta shi kuwa an zo ga
ɓ
ar da ya yi amannar hakurinsa ya ƙare.
Ta gifta napep din har ta samu nasarar tsallakawa. Haka kawai take zuba sauri don ta isa gida, ba ta yi aune ba ta ji mury
ar mutum a bayanta.
"To ni kuma da ba
ɗ
an unguwa ba kina wannan saurin idan na
ɓ
ata fa? Kar ki kaini gidan ƴan yankan kai."
Cak ta tsaya gami da juyowa, bata san sadda ta yi su
ɓ
utar baki ba.
"Biyoni ka yi?"
Duk yanda ta so kar ta ƙarasa
fa
ɗ
i bayan ta ankara da su
ɓ
utarsa hakan ya faskara. Murmushi ya yi ya
ɗ
an tako ka
ɗ
an. Kusan a gigice take duban layin, fatanta kada koda wasa Yaya Munir ya ganta tsaye anan. Wannan yasa ta juyawa da zummar soma tafiya.
"Don Annabin Rahma ki tsaya."
"Sallallahu alaihi Wa sallam." Ta furta a hankali sannan ta dubeshi.
"Malam wallahi an sakamin rana yau
ɗ
in nan ma, don Allah ka yi hakuri ka daina bina. Matsala za ka jawomin a gida."
Ta furta rai a ha
ɗ
e sannan ta soma tafiya kirjinta na h
arbawa. Fatanta Allah Yasa ya dakata.
"Ni duk ba wannan ba, nima inada matar aure. Kwatance za ki min."
Ba ta fasa tafiyar ba, bai fasa bibiyarta yana magana ba. Dole ta tsaya ganin an kusa shan kwanar layinsu. Ta dubeshi da idanunta masu firgi
ta maza. Ya kuwa lumshe nashi ƙananan idanun masu kama da na mai jin bacci ya bude, shirunta na nufin tana jinsa kenan
"Wani gida nake nema, bansan kalarsa ba. Ba zan ce ga girmansa ba, kuma da ace ma da hali naga gidan ban ƙi ya zama mallakina ba na
har abada. Amma kinsan me? Matar gidan ta nunan ba ni da wurin zama cikin gidanta. Ni ne da nacin tsiya na kasa haƙura. Idan na kasa mallakar gidannan, bana jin akwai gidan da zai ƙara burgeni koda kuwa ace wanda nake da shi yanzu ne! Ki tausayamin don All
ah."
Ya ƙasashe cikin karaya, rabin hankalinta na ga kallon hanya rabin wajensa, ko kusa ba ta gane wannan tatsuniyar ba don haka kai tsaye ta ce.
"Wallahi ban gane komai ba Malam, ka rufamin asiri ka tambayi wani ko wata sai anjima."
"Saƙo
na ƙarshe don Allah, nima daga nan zan juya na tafi kar na sha wahala."
Dole ta ja tunga ta juyo tana dubansa, shima ƙara narkar da idanunsa ya yi cikin nata gami da jingina kansa jikin bishiyar darbejiyar dake bayansa. Ta kauda kai tana ƙara yiwa kan
ta tunin wannan ba HILAL bane tsaye.
"Bana yiwa mace kallon da ya wuce biyu, amma kin janyomin sauka a unguwar da kusan bani da kowa, ban ta
ɓ
a bin mace a baya ba, don wannan ba ya cikin sabgar ALIYU, kin sanya na biyoki. Bansan gaskiyar sanyamaki rana
ba duk da cewa fuskarki ba ta maƙaryata bace, sai dai ki taya kaina da kuma ke addu'ar kada mu kasa cika alƙawarin wa
ɗ
anda muka
ɗ
auka matsayin abokan rayuwarmu. Fatan alheri MATAR GIDA."
Daga nan ya juya bai ƙara waiwaye ba, duk da dukan da kalaman s
uka yiwa zuciyarta, bai sa ta fasa ci gaba da tafiyar ba. Sai dai fa tana tafe tana yiwa kalaman filla-filla, sannu-sannu kuma take haddarsu. Ta kasa fahimtar manufar, ba kuma ta marmarin ta fahimta
ɗ
in don a ganinta bai da amfanin komai, wannan ta sa ta y
in watsi da shi. Sai dai daga lokacin Aliyu ya yiwa mafarkanta illar da har ta soma tunanin ba mutum bane!
Hilal ya zo suka yi sallama sadda zai wuce Malaysia, kowannensu wata irin kewa yake ji, Ramla kuwa kasa jurewa tayi ta shiga hawaye.
"
Aa please, za ki yimin illa babba fa. So kike ina tafe ina tuna kuka maimakon murmushinki? Kar muyi haka da ke. Kinji? Idan kin yi kuka ni kuma na yi me?"
Ganin duk yana neman hargitsewa sai ya ba ta tausayi. Ya shiga rarrashi.
"Ki kwantar da han
kalinki kinji? Da kaina zan siyamaki waya na aikomaki don ba zan jure rashin jinki ba. Ramla ba don karatu dole ne ba kuma ina sonmu da shi wallahi Hilal zai iya ajiye karatun ya aureki daga baya ki ƙarasa naki a gidana. To ba zai yiwu ba, komai bisa tsari
ya fi. Ki yi hakuri kin ji?"
Ta share fuskar tana murmushi. Kukanta biyu ya ha
ɗ
armata, kirjinta bugu yake bana wasa ba, tana ganin kamar akwai wani
ɓ
oyayyen lamari da zai fi ƙarfinta, jikinta na bata akwai babbar matsala sai dai wani
ɓ
angare na zuciy
arta na
ƙ
arfafarta akan kar ta ba shai
ɗ
an damar wasa da hankalinta. Yanda Hilal ya dage rarrashi ma duk sai ya bata tausayi dole ta nuna mishi ta sauko, suka rabu kamar kar su rabun. Tuni ya yi sallama da su Hajiya da Abba, wannan tasa kawai wucewa ya yi.
Hotunanta kala-kala na takarda ta ba shi har yana fadin zai sa a mishi enlargement dinsu ya kafa a
ɗ
akin kwanansa na makaranta. Dariya kawai ta yi. Daf da zai bar gidan ya dakata gami da fiddo wani
ɗ
an akwatin ƙarami na zobe, kai tsaye ya miƙamata yana mur
mushi.
"Kar
ɓ
i mana."
Ta sa hannu ta kar
ɓ
a tana kallo.
"Duk da ba zancen alƙawari yanzu, saboda inada yaƙinin irin kaunar da muke yiwa juna, ina da tabbas a kanki Ramlata. Ki sanya a hannunki, ya kasance har bayan dawowata shi zan tarar a ha
nnunki. Wannan ka
ɗ
ai zai sa ni farin ciki. Ina miki fatan alheri."
Daga nan ya fice a gaggauce don da alama ya soma karyamata zuciya.
"Azurfa mai kyau." Shi ne abinda Rafee'ah ke kira yayinda ita kuwa ta mike ta bar falon zuwa
ɗ
aki. Kuka ta ci s
osai na abu biyu da ta rasa da wanda za ta ji. Sai da ta yi mai isarta ta share fuska, ta
ɗ
au alwashin rabuwa da tunaninsa balle ya kai ta da mafarki. Ta ƙara gaskata mafarkan Aliyu duk kissimawar shaidan ce, shi ke mata yawo da hankali a mafarkanta.
"Daga rana irin ta yau babu ni ba tuna dukkan wani abu da ya shafeka Aliyu, har abada. Allah ina neman tsarinKa daga sharrin shaidan da kuma na zuciya da saƙe-saƙenta."
Sai dai kuma wasu lamuran sun fi gaban yanda dukkan bawa ke
ɗ
aukarsu. Duk a rash
in sanin cewar yanzu aka fara!
***
Ƙarar ababen hawa ya cika kunnuwanta, dole ta saita kanta ga ci gaba da tuƙi cikin nutsuwa da kwarewa, a hankali ta sa bayan hannunta ta share fuska. Daidai wani boutique ta yi parking ta fito. Kai tsaye ta shi
ga, tunda Ummi da Ansar suka ƙwallafa rai akan halartar Children's Day. Ta shiga ciki kai tsaye ta nufi
ɓ
angaren kayan yara. Tun kan ta ƙarasa ta hango bayan mutumin riƙe da waya a hannunsa yana video call
bai ko damu da tsilli-tsillin mutanen dake shagon
ba wadanda wasu ke kallonsu suna dariya wasu kuwa su yi gaba.
"Wannan kina so?"
Ya
ɗ
aga wani takalmin, yarinyar ta turo baki kamar mai shirin kuka ta girgiza kai da mirza idanu. Ya sauke ajiyar zuciya.
"Tee ya zan miki uhm? Duk wanda na
ɗ
a
ga bai miki ba? So kike Mominki ta yi mana dariya ko?"
Matar shagon ta ƙara
ɗ
auko mishi wasu tana dariya ka
ɗ
an-ka
ɗ
an. Ramla kallon yarinyar kawai take tana tasbihi ga Ubangijin da Ya ƙageta.
"Daddy ga wata Mami can a baya, ni ta za
ɓ
amin. Dada ta
cemin ba ka iya za
ɓ
e ba."
Cewar yarinyar har tana riƙe ha
ɓ
a da turo baki, jin abinda yarinyar ta fa
ɗ
i yasa ta saurin juyawa ta
ɗ
ora hannu saman shelf din da ya fi kusa da ita kamar hankalinta bai kansu. Tana jin dariyar yarinyar, shi kuwa uban koda y
a juyo sai ya ji kunya ka
ɗ
an cikin yaren fillanci ya yiwa yarinyar sallama ya katse kiran.
"Ki ji fa, idan matar aure ce kuma fa?"
Ya yi maganar yana duban Matar dake aikin ciro mishi takalma, ta dubi Ramla da ke sauraron su kadan kadan. Ta yi da
riya.
"Wannan Customer
ɗ
inmu ce Oga,na san Madam ba ta da aure."
Ya kara duban Ramla kafin ya mike da nufin aiwatar da abinda
ɗ
iyar ta nema, a sannan ita kuwa Ramla har ta
ɗ
auki wata doguwar riga mai hula wanda ta tabbatar zai yiwa
ɗ
iyarta.
"Assalamu alaikum."
Ta dubeshi, zaro idanu waje ta yi. Ganinsa anan ya yi masifar ba ta mamaki da kuma tsoro. To ina Hajiyar? Yaushe ya sauya kaya daga voyel maroon zuwa shadda ruwan toka? Ta kasa magana, shi kuwa bai maida hankali wurin kula da hak
an ba ya
shiga neman alfarmar ta za
ɓ
amasa takalmin da zai yiwa
ɗ
iyarsa. Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata.
"Hello."
Ya ƙara fa
ɗ
i gami da
ɗ
an rankwafar da kai. Ta
ɗ
an yi firgigit sai ta basar cike da dakiya.
"Ba damuwa."
Suka ƙar
asa wurin takalmin, ta shiga dubawa bayan ta tambayi size dinta. Jefi-jefi za ta kalleshi da tsantsar mamaki, sai dai duk abinta ba za ta ta
ɓ
a yin shishshigin tambayar ko shi ƴan biyu bane. Wani takalmi ja ta
ɗ
auki mai adon fulawa, tana murmushi ta miƙa ma
sa.