Showing 129001 words to 132000 words out of 255051 words
da wuri. Ina kika tsaya?"
Ta ajiye mayafinta a gefe bayan ta ajiye ledar a saman tebur, lema
kuwa Ummi ce ta kar
ɓ
e ta nufi
ɗ
aki da shi.
"Mota ce ta macemin a hanya wallahi."
"Ya Salam, to yanzu ya kika yi?"
Murmushi Ramlat ta yi, fuskar Hussein ke yawo a kwayar idanunta.
"Abokin Hisham ne ya ganni, shi ya kawoni har ƙofar gid
annan."
"Mijin Hajiyarnan?" Yanda Hajiya ta fadi ido waje sai ya ba ta dariya.
"Shi."
"Ai shikenan ke kika sani, ki yi ta jaji
ɓ
o yaronnan idan ta zo har gidannan ta jibgeki ba abinda zan ce."
Dariya ta yi.
"Ta jibgeni fa Hajiya? A
gabanku?"
"Atoh, ai naga alamar kamar alaƙar taku ƙara yin gaba ta ke."
Jiki a sanyaye ta girgiza kai.
"A'a fa Hajiya, ba komai tsakaninmu wallahi banda mutunci."
Hajiya ta murmusa.
"Allah Yasa toh."
Ramlat ta basar da zancen
.
"Ga nama nan ma ya siyamin."
Daga nan ta mike ta nufi ciki don sauya kaya sai dai maganar Hajiya ta
ɗ
an shigeta. Dagaske sabo ke neman shiga tsakaninta da Hussein. Kamar kuma irin sabonnan da ba shi ta nema ba, irin wanda ba shi suka shirya da
Amrah ba.
Ta kai hannu ta fiddo wayarta daga jaka, kai tsaye ta shiga whatsapp kan dp dinta. Hoton yaranta ne, Affan da Ansar sanye da shadda iri daya, hular Affan har goshi, Ansar kuwa ta zauna
ɗ
as a kansa. Ummi daga bayansu ta dafa kafadunsu suna
dariya kamar yanda mai hoton ya basu umarni. Murmushi ta yi ta shafi hoton tana tuna kalaman Hussein. Wato dai ya san tana da yara kuma ba ta da aure? Da alama a wurin Hisham ya nemi ƙarin bayani.
'Har zuciyarki ta soma saƙa wani abu akan wani
ɗ
a n
amijin?'
Wani bangare na zuciyarta ya ankarar da ita, ta yi saurin kashe wayar ta ajiye gefe, rage kayan jikinta ta yi ta fa
ɗ
a wanka. A ganinta wannan kuskure ne babba. Don haka dole ta yi takatsatsan, kyakkyawan jihadin da ta yi niyya kawai za ta ai
watar akan wadannan ƴan biyun. Daga nan babu komai!
***
Washegari safiyar Lahadi da misalin ƙarfe takwas na yamma, Malam Bala ya yi sallama a kofar falon. Ita kadai ce a falon tana taimakawa Ladidi da tsintar shinkafa, yara na
ɗ
aki wurin Hajiya,ta
amsa ta leka suka gaisa. Muƙulli ya miƙomata.
"Gashinan wani ne ya kawo ya ce a ba ki inji Yalla
ɓ
ai, ga motarnan an shigo da ita ma."
Ta karbi mukullin.
"Ya tafi?"
Malam Bala ya amsa da eh. Ta mishi godiya sannan ta dawo ciki ta ajiye
mukullin. Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta dauka ta duba.
"Mota duk ta yi datti ba wanki, gashinan, za ki biya kudin wankinta."
Abinda aka rubuta kenan, wannan ya ba ta tabbacin har wankemata ya sa aka yi. Dariya ta yi kafin ta maida mishi
martani bayan ta ƙare wa lambar kallo.
"Nagode Yalla
ɓ
ai, Allah Ya bar zumunci."
Ta aikamasa kenan ta ga akwai saƙon da ya shigo ba ta ko lura ba. Hilal ne. Kirjinta ya fadi, idan ba ta mance ba yau an zarta sati da maganarsu, damuwa ta sauka sa
man fuskarta a yayinda ta karanta saƙonsa.
"Ban sani ba ko hidima ce ta miki yawa kamar yanda ta sha kaina har ban samu zuwa akan lokacin da muka tsayar ba. Ina fatan komai lafiya? A sanyamin ranar da zan zo idan ba damuwa."
Sauke ajiyar zuciya
ta yi, ta rasa ma amsar da za ta ba shi. Ita ta sani, babu soyayyar bawan Allahn nan (Hilal) a ranta face tausayi da kuma ganin daraja da ƙimarsa. Ta yi addu'ar istihara sosai amma ba ta jinsa ko ka
ɗ
an. Ta rasa amsar bayarwa don haka ta ajiye wayar kawai
ta ci gaba da aikinta.
Ita da kanta ta yi musu girki, shinkafa da miya. Tana kammalawa ta fito falon inda suke zaune ya yi daidai da shigowar Munir gidan dauke da yaransa. Daga ganin yanayin fuskarsa da irin daurewar da ya yi ka san cewa akwai mat
sala. Ya zauna yana gaida Hajiya a daure, ta amsa gami da jefamasa tambayar dake zuciyar Ramlat.
"Lafiya kuwa? Meyafaru na ganka da su Yasmeen?"
Ya shafi kai yana amsa gaisuwar Ramlat kamar ba ya so. Ya ba Yasmeen umarnin su shige ciki da su Umm
i. Yasmeen ta ja ƙannenta uku suka
ɗ
unguma gaba daya zuwa ciki. Da yake yarinya ce mai wayo, gaba daya itama fuskarta ta koma kalar tausayi.
"Wata ƴar hatsaniya aka yi da Bilkisu da Hunainah akan kawai yarannan su na shiga bangaren Hunainah. Ita yar
inyar tana sonsu tana kuma jansu a jiki, toh ashe ita Bilkisu ranta na baci. Dama ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba ta ke nuna ba ta kaunar zuwan yaranta wurin Hunainah. Yau da na gaji don Yasmeen ta kwana sashin Hunainah shi ne ta kama yarinyar ta buga,
ni kuma na yanke hukuncin zamansu a wurin Hunainah tunda abin haka ne, toh wai shi ne Bilkisu ta dauko wuka har da kai wa Hunainah yanka a kafa
ɗ
a ta yankamata hannun riga, wai ita ta rantse idan har na rabata da su za ta kashe Hunainah. Wannan ne dalilin
da yasa ni kuma na korata gidansu na kwashi yaran na ce bari na kawosu nan idan ya so zuwa anjima sai na tafi da su. Haba! Wannan masifar ta ishe ni, Hajiya kusan kullum sai Bilkisu ta
ɓ
ullo da sabon rikici. Daga wancan sai wannan! Nikam gaskiya ta soma is
ata don zan iya sauwaƙe..."
"Kar ka fara! Nace kar ka fara! Idan ka yi ba da yawuna ba wallahi. Wane shashashan namiji ne zai saki matarsa ta farko kuma Uwar ƴaƴa? A'a kar na kara jin batun rabuwarnan a bakinka. Yanzu kai dama anan ba sai da na gujema
ka irin hakan ba? Ban maka magana game da ha
ɗ
a matannan gida
ɗ
aya ba? Ka nunamin kai namiji ne da mace ba ta isa tankwarawa ba. Ai zaman lafiyar ake nemamaka. Toh ga irinta nan, tun ba'a je ko'ina ba ta soma yunkurin kashe baiwar Allah."
"Hajiya
ɗ
an r
igima fa
ɗ
an rigima ne, koda ba gida
ɗ
aya suke ba, sanin da na yiwa Bilkisu za ta iya takawa har gidanta. Toh Hajiya a hakan ma fa zargina take da rashin adalci ina kuma ace gidansu ba daya ba?"
Ramlat dai ta yi shiru tana kallonsa yanda duk ya fice
a hayyacinsa.
Yanda aka banko labulen falon aka shigo yasa duk suka kalli kofar. Bilkisu ce buguzuzum da ita. Kalar mayafin daban da atamfar da ke jikinta. Da ganinta ka san ba'a nutse ta ke ba.
Kai tsaye wurin Munir ta tunkaro hannunta a ƙu
gu.
"Ka bani yarana tunda ba kai ka haifamin ba!"
Idanunta jage-jage da ruwan hawaye. A fusace ya mike Hajiya ta yi saurin riƙe hannunsa.
"Kai bana son hauka. Yi shiru abinki Bilki, zauna don Allah ki nutsu. Yaranki suna nan, kuma zan ba
ki kayanki ki tafi da su."
Wani kwafa ta yi ta zauna tana kuka har da share majina. Ramlat ta mike ta yi
ɗ
aki don ita takaicinsu ma ta ke ji. Mace ta riga da ta raina mijinta ko kadan ma ba ta ganin girmansa.
"Allah Ya kyauta." Ta fa
ɗ
i a fili.
Kayan islamiyya ta fiddowa yaranta ta ba kowanne nashi kafin ta shiga shirya Affan. Har ta kammala ta fito ta zubamusu ruwa a robobi ta basu Hajiya na ta shari'a tsakanin miji da matar. Idanunta ya kai ga Bilkisu, wata uwar harara ta watsamata, ita a
bin ma sai ya ba ta dariya ganin ai ba ita ta kai zoman ba, ratayar ma ba'a ba ta ba. Hijab ta sanya don ta fi kaunar ta bar musu gidan wannan yasa ta dauki wayarta ta yiwa Hajiya sallama da zummar za ta kai su Ummi makaranta daga haka ta fice don hankalin
Hajiyar ma ba ya gareta kawai ta amsa da jeki.
***
Koda ta miƙa yaran ta wuce gidan Umman Amrah. Ta saki baki ganin Zaituna.
"Wai Umma har yanzu ba su
ɗ
auketa ba?"
Umma ta dara.
"Sun dauka mana, maidomin abata suka yi. Kusan tu
n bikin Muniru."
Ramlat ta murmusa.
"A'a wannan dai ta zama kishiyar ta gaske. A bar maki ita kawai."
Kama baki Umma ta yi.
"Wannan Babannata ne zai bar ta?Bari kiga nan kusa za ki ganshi ya zo daukarta. Yaran yanzu da shegen son ƴaƴa,
wa ya sani ma ko ita ke turoshi."
Dariya sosai abin ya ba Ramlat.
"Kema dai
ɗ
iyata ina nan ina addu'a Allah Ya za
ɓ
amaki miji nagari mu sha biki. Ba na jin dadin ganinki a gida da kuruciyarki. Ai ina jin ba ki yi talatin ba ko?"
Da murmushi
ta girgiza kai.
"Ban kai ba Umma. Kin manta watanni kawai na ba Amrah."
Umma ta yi dariya.
"Ke da Amrah ai rigimarku sai ku, ki ce kin girmeta itama ta ce ta girmeki."
"Allah na girmi Amrah."
Ita dai Umma ta amsa da toh sannan ta
mike zuwa daki tana dariya, can ta fito rike da wani littafin adduo'i ta mikawa Ramlat.
"Ki dinga karantawa, akwai adduo'i sahihai da kuma nafiloli. Kar ki yi wasa don Allah."
Ta amsa da toh, mutanennan suna da burin ta yi aure, ba za ta ce ba ta
so ba. Sai dai tana duba yaranta, ba ta kaunar yin nisa da su. Aure kuma ance ba inda ba ya kai mutum.
Kwanciya sosai ta yi saman kujera sadda Umma ta mike ta wuce bangaren mijinta da ta ji tsayuwar motarsa. Wannan ya ba Ramlat damar danna waya, lam
bar Hussein ta bude ta ga dacewar ta yi saving. Cak ta tsaya tana tunanin sunan da za ta
ɗ
ora akan lambar, can kuma ta yi murmushi ta rubuta Mr Wuf. Ita kanta abin dariya ya bata.
Daga haka ta fa
ɗ
a whatsapp ta shiga duba contact har ta fa
ɗ
a saman lamba
rsa. Dp dinsa na wani ƙaton ocean ne sai rana da ta
ɗ
auko fa
ɗ
uwa daga sama. Murmushi ta yi ta je kan Status na profile. Busy kawai aka rubuta da alama kuma ya jima sosai a hakan.
Tana komawa kan whatsapp ta ci karo da sallamar Alhassan. Ganin yana onli
ne ta amsa da sauri. Suka gaisa ta tambayi Dada da iyalinsa. Ya amsa har da turo emoji na nuna jin dadinsa da hakan. Ya tambayi mutan gidansu shima.
_*"Ina nan shigowa Kano karshen satin da zamu shiga in sha Allah. Zan kawomaki Fatina ku gaisa idan
ba damuwa. Address?"*_
Ganin abinda ya rubuta ne yasa ta saurin miƙewa zaune. Alhassan zai shiga Kano? Kodai yana da ƴan uwa a Kano?
Wannan tambaya ce da ba ta da amsarta. Ga ha
ɗ
iyi wani yawu kafin ta amsa mishi.
_*"Kano na marhabin da k
u, Allah Ya kawoku lafiya. Ashe muna da ƴan uwa a Kano kenan._*
Ta tambaya cike da ƙaguwa . Dariya ya aikomata kafin ta ga yana recording. Ta bude ta saurara.
"Eh toh, muna da yan uwa. Akwai yayan Babanmu a Kano. Yanzun ma biki za'a yi na samarin
yaransa har biyu, shi ne zan kawo su Dada da Maman Fatima. Ina fatan za ku hadu ku gaisa?"
Abinda ya ce kenan, ta yi shiru, gaba daya ya dulmiyar da ita cikin tunani. Kenan Alhassan suna da dangi a Kano? Toh ta yaya zai yiwu ace ba su ta
ɓ
a cin karo
da Hussein ba? Anya zai yiwu? Ace kuna gari daya ba ku ta
ɓ
a sanin juna ba. Kodai Hussein din ne bai da zumunci?
Abinda ta yi ta rayawa kenan,can ta tuno ba ta ba shi amsa ba, gudun kar ya yi tunanin wani abin ne yasa ta ba da amsa.
_*Wow, Allah
Ya kaimu toh. Zan so na ga Fatima.*_
Suka
ɗ
an ta
ɓ
a hira kafin su yiwa juna sallama. Ita dai ta ajiye wayar kawai amma hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin wannan lamarin mai ban mamaki da
ɗ
aure kai.
Ba ita ta bar gidan ba sai da lokacin tash
in yaranta ya yi, ta so ta ƙi shiga wurin Baba Dakta saboda kar ya yi mata batun aure, a karshe dai ta daure ta shiga kuma har suka gaisa ta fito suka ta
ɓ
a barkwanci, bai mata zancen ba.
Tana shiga da yaran falon Hajiya, ta ga babu su Munir balle yar
ansu sai Hajiya da Ladidi da ke tattaunawa. Hajiya na ganinta ta yi dariya.
"Ja'ira, wata kika gudu kika bar ni da su ko?"
Tana dariya ta zauna.
"Me zan ce? Na saka baki Yaya Munir ya ce na mishi rashin kunya? Ya suka ƙare?"
Ta
ɓ
e baki
Hajiya ta yi.
"Na yi musu dai nasiha daidai gwargwadona. A karshe sun ba juna hakuri suka kwashi yaransu suka yi gaba."
"Allah Ya daidaita lamarin."
Suka amsa addu'ar Ramlat da Amin.
***
LAMIƊO CRESCENT.
Kallon abincin ta ke k
amar ta fasa ihun kuka tsabar takaici da bakin ciki. Ta dage ta yi girki da ruwan maganin tarkinta amma Hussein ya tahomusu da wasu manyan kifaye har uku gasassu da aka sanya chips a gefe da kayan tumatir albasa sai
ɗ
an yaji a wata ƙaramar roba. Ci ya ke y
ana jin dadinsa ya dubeta.
"Madam tunanin me kike ne? Wannan fa don ke na siyo. Please come and join me."
Ita a dole shagwa
ɓ
a irin ta masoya, ta yamutse fuska.
"Ni a'a gaskiya, na dage na maka girki da kaina da hannuna yanzun kuma ka cemin
ka ƙoshi?"
Ya yi murmushi.
"Shikenan, ki sanyamin a fridge I promise you, da shi zan yi breakfast. Hankalinki ya kwanta?"
Ta ji sanyi a ranta, murmushi ta kasheshi da shi, ya maida kai ga abinda ya ke ci. John ta kwalawa kira ya shigo sanye
da rigar kuku, umarnin ya juye ya sanya a fridge ta ba shi sannan ta matso ta soma tayashi cin kifin. Sanin da ta yi Hussein ba ya magana biyu, zai wuya ya ƙi yin abinda ya furta yasa hankalinta kwance ba ta ko damu ba.
Sai dai kuma ga mamakinta da
safe tashi ta yi sai filin gado ita kadai babu shi ba dalilinsa. Takardar da ta gani ta dauka ta karanta, sanarmata ya yi ya samu kiran gaggawa zai wuce Abuja meeting, abu ne da suka sanya rai har sun fidda za'a samu sai gashinan ya yiwu, ta yi hakuri idan
ya yi rashin kyautawa. Hawaye ne kawai Hajiya Zeenatu ba ta yi ba. Ta kirashi a waya sai dai a kashe, ta ja tsaki ya fi a ƙirga.
***
Ku
ɗ
in take ƙarewa kallo ba tare da ta iya kata
ɓ
us ba. Ta kasa bin umarnin Chairman
ɗ
in nata ta dauka balle har ya
je jakarta. Ku
ɗ
in da ya ninka albashinta sau biyu. Da mamaki ta dubeshi, kallonta yake ƙasa-ƙasa.
"Me zan yi da su?"
Dariya ya yi, duk a zatonsa ta ru
ɗ
e ne saboda yawan ku
ɗ
in, bandir na dubu har guda uku ai ba wasa ba. Ya kara turo ku
ɗ
in.
"Dauka dai ki riƙe tukunna Madam Ramlat."
Girgiza kai ta yi.
"Ka yi hakuri Yalla
ɓ
ai ka fa
ɗ
amin kudin na menene tukunna."
"Kyauta ce daga gareni, wannan ba komai bane daga irin kyautar da nayi maki tanadinsu. Don Allah kar ki ce ba za ki kar
ɓ
a ba. Ke musulma ce,k kuma kin san ba kyau maida hannun kyauta baya."
Har wani gumi ta ji ya tsastsafo saman goshinta duk da sanyin nu'arar Ac dake ka
ɗ
awa.
"A'a, a'a, ka yi hakuri. Nagode wallahi amma ba zan iya kar
ɓ
a ba."
Daga haka ta kama
hanya har tana tuntu
ɓ
e ta shiga kokarin ficewa daga ofishin, kiranta ya yi ta tsaya cak jin muryarsa ta koma irin ta ubangida da bawansa.
Sai da ta juyo ya
ɗ
an saki fuska ya koma magana a tausashe.
"Ga duk wanda ya sanki a wannan ma'aikatar, y
abon kyawawan dabi'unki ke fitowa daga bakinsa, ban ci karo da wanda har yau ya kusheki ba. Don Allah kar ki sa na ga baƙinki, ki kar
ɓ
i kyautarnan domin girman Allah da Annabi s.a.w"
Kallonsa ta ke kawai, ya koma kamar ba Chairman ba, ya maida kansa m
utum mai rauni. Banda ma rainin wayo, su waye suka santa a wannan ma'aikatar har haka da yake cewa wai an shaideta. Bandir daya kawai ta dauka shima sai da ta ji wani faduwar gaba, ta kudurta a ranta ba za ta kashe ko sisi daga kudin Chairman ba. Za ta ada
na ko don gaba. Zai kara magana ta ce.
"A'a, ka yi hakuri don Allah, wannan ma ya isa. Kar ka yimin dole. Nagode Allah Ya kara girma."
Ya yi murmushi, ko ba komai ya ji dadi. Ta sanya kudin a jaka ta fice ta barshi da shafa sanƙo. Gani yake kamar
yanzun ba son jikinta kadai ya ke yi ba, har da ma halayyarta da
ɗ
abi'unta. A hankali ya shafi sanƙonsa yana jin kamar ya