Showing 219001 words to 222000 words out of 255051 words
/>
"Aa."
"Kin ma iya ki ci abinci, ni da ban ji ki ba kasa daurewa nayi da komai har sai yanzu da na zo na ganki. Idan na tsaya wassafa kalar farin cikin da nake ciki, zamu kwana mu wuni a nan."
A hankali ya jawo hann
unta mafi kusa da shi ya damƙe cikinnasa. Wani yarr ta ji kamar yanda shi kansa sai da ya ji wani shock. Ya ƙurawa lallen idanu.
"Allah Ya bani ikon riƙe ki amana Ramlat. Ya ba ni ikon yi maki adalci a zamantakewarmu. Na san na
ɓ
atamaki rai da yawa, a
mma ki yi hakuri. Haka nake, ban yarda da soyayya kafin aure ba, bayan aure ke kanki yanzu son zai fi maki armashi a kowace tafiya. Abubuwa da yawa ba ma sai na fada ba tunda ke ba yarinya ba ce ko?"
Ta saci kallonsa don gaba daya sautinsa ya sauya, g
ira ya
ɗ
aga mata yana jifanta da tattausan murmushi. Ta kauda kai ta shiga kokarin zame hannunta.
"Na dauka zaman hakuri da biyayya kawai zamu yi ai tunda cikinmu ba wani mai kaunar
ɗ
an uwansa."
Ba zato ya fisgota kafadarsu na gogar juna kamar ya
nda fuskokinsu tuni ya hadu wuri guda sai hucin numfashinsu da ke gaurayewa.
"Kina da tabbacin bana sonki? If yes, prove it."
Ta lumshe idanu tana shaƙar kamshin lemon mint da bakinsa ke yi. A hankali kuma ta yi nufin yin baya ya rike kanta kafi
n ba zato ta ji bakinsa a nata. Shirun kusan mintuna biyu kafin ta tureshi ya yi baya, babu kwari a jikinsa, don haka ya jinginar da kai yana kallonta da soyayyun idanunsa. Ita kuwa sai afkin goge baki da ta ke yi bayan ta zari tissue dake saman gaban mot
ar. Ya kauda kai kadan yana dariyarnan irin na wanda aka rainawa wayau.
"Kai, ni kike gogewa baki don na ta
ɓ
ashi?"
Ta daure fuska ta harareshi.
"Saboda ban shiryawa hakan ba. Ai ba haka tsarin zamantakewar tamu ya ke ba."
Daga nan ta wu
rga tissue din a jikin motar duk dacewar hatta da kujerun baa ciremusu ledojinsu ba. Tana kokarin bude kofar ta fita ya kara yi mata wata wawuyar fisga, duk kokarinta ta kwace abin ya gagara. Haka ya taramata miyansa a baki kamar yanda bai kauda bakin ba s
ai da ya ji ƙarar tafiyarsa, loko da saƙo sai da ya tabbatar ya gauraye a bakin kafin ya saketa. Iyakar shaƙa ta shaƙa, ta bankamasa wata hararar. Ya
ɗ
aga mata yatsu.
"Good night Love."
Ta bude kofar kawai ta fice, ya bita da kallo yana jin kamar
kar ta tafi saboda wani tsananin kewa da ya kamashi nan take, har sai da ta shige gidan kafin ya lumshe ido da murmushi can kuma ya buga sitayari.
"Ya Rabb!" Ya fadi cike da nishadi, soyayyar Ramlat na kara ƙaimi a ransa. Dakyar ya samu kuzarin jan m
otarsa, kafin ya fice daga gidan ma sai da ya kira wayar Hafsat ya jaddada mata akan ta shaidawa Ramlat ta kunna wayarta.
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://www.wattpad.com/story/229538078?utm_s
ource=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=3RG5g2a5w6izCuKU8HhNqobuQjDF3XsdSGdqdVtdShDrSoD84AKgTAv38ifr8A0P6JNqIoYXqVCm072j3Kj010bX%2FXCFmaovF0BtpPRfTxUwRF7KoTA35HGU0Qpfh9Zn
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
59)
Kusan gaba daya mutan dakin bacci suke yi idan ka cire Amrah da ke zaune tare da amniyarta tana tayata wajen shirya kaya a
ƙatuwar akwati. Wasu kayayyakin kuwa su na fitarwa domin bayarwa. Amrah na lura da yanda gaba daya ba ta da sukuni, jefi-jefi takan sa hannu ta share bakinta.
"Wai ke kam lafiyarki kuwa?"
Ta dawo hayyacinta.
"Me kika gani?"
Harara ta wats
amata.
"Kamar ya me na gani? Alhalin ina lura da yanda tun dazu kike wani shagala da shafa baki, saurin me kike?"
Ranta ya kara baci ta ja tsaki.
"Me kike nufi? Idan ma wani abin kike nufi gwara ki watsar tun a nan don kinsan irin zaman da n
a shirya za yi da Hussein."
Amrah ta jinjina kai.
"Ko wane irin zama ne ba zan hanaki ba tunda ke ba yarinya karama ba ce da zan tsaya
ɓ
ata bakina, abu daya da zan tunasar da ke, yanzu Hussein ya tashi a kowane matsayi ya hau matsayin mijinki. Id
an kin gyara kanki, idan kin
ɓ
ata ma ke za ta shafa."
Shiru kawai Ramlat ta yi ba ta kara tankawa ba. Can kuma aka kwankwasa kofar dakin da sallama aka shigo. Hafsat ce sanye da riga da wando na bacci kasancewar ita ta kafe ta ƙi bin yan uwansu Hotel,
hakan yasa Hajiya ta mata wuri a makeken gadonta. Hamma ta ke zabgawa duk suka dubeta.
"Adda wannan Yayannamu ya hana ni bacci wallahi, don Allah ki tausayamin ki kunna wayarki ku yi magana. Ni ga wayata ma na bar maki a nan don wallahi da zarar na
soma nisa a baccin yake tashi na."
Dariya ta ba su, aikuwa ba wanda ya kai ga cewa komai sai ga wani kiran. Da sauri Hafsat ta miƙamata.
"Yauwa gashinan. Sai da safe."
Ta fice Amrah na addu'ar Allah Ya tashemu lafiya. Ita kuwa Ramlat wayar t
a
ɗ
aga ta
ɗ
ora bisa kunne yayinda Amrah ta juyamata baya ta ci gaba da aikin da tuni ma sun ƙarƙare sai tattarawa. Sallama ta yi, jin muryarta sai ya sauke ajiyar zuciya. Shiru ya dan biyo baya kafin ya tanka.
"Kin hana ni bacci Heart."
Ta
ɗ
an sa
ci kallon Amrah wacce hankalinta na can wurin harha
ɗ
e kaya ba ta ce masa komai ba.
"Meyasa ba ki kunna wayarki ba? Kinsan zan nemeki, zan so na ji muryarki. Bacci ya kauracemin, ba ni da burin da ya wuce na ganki a gidana. Heart, kin yi shiru."
Ta
ɗ
an daure ta yi magana.
"Me zan ce?"
"Ko mene ne ki fada daidai ne. Amma kar ki kara kuskuren da ki ka yi dazu, idan kuwa hakan za ki ci gaba a zamantakewarmu, za ki sha wahala a wurina."
Murmushi ta yi mai sauti.
"Dariya ma na ba ki
?"
"Ko kusa, bacci fa nake ji."
"Ni kuma ban shiryamasa ba, hira na ke son mu yi. Koda dai tambayar da nake son yi maki ba ta waya ba ce, sai mun ha
ɗ
u ga ni ga ki."
Nan ma ba amsa sai shirun daga wajenta, har Amrah ta mike ta fada bandaki ta
dauro alwala, yana ta magana Ramlat sai uhm ko uhm uhm. Tana kallo Amrah ta kashe fitilar dakin ta bi lafiyar gado kusa da Babynta ta kwanta. Cikin takaici Ramlat ta ce.
"Malam kowa fa ya kwanta, nima gyangya
ɗ
i nake, ina son..."
"Be serious Hear
t, ko kadan ba ki tunanina?"
Ta lumshe ido ba tare da ta tanka ba.
"Talk."
Ya fadi a hankali. Ita har mamaki ma ya ke ba ta.
"Shiru ma fa magana ce ko? Inji Hausawa."
Ya kara fadi yana yar dariya, ta cije lebba don takaici, wato m
a ya riga da ya fassarata.
"Kai ka san wannan, ni abinda ya tsayar da ni daban ne. Sai da safe bacci nake ji."
Ba ta jira komai ba ta kashe wayar gaba daya. Mikewa ta yi tana murmushi har ta na tuntube da ƙafar Dijen Daura da ke bacci a saman kat
ifa. Hakuri ta ba ta sannan ta fada toilet. Alwalar itama ta yi ta nemi wurin kwanciya.
***
Tun da Asuba masu tafiya Adamawa suka tashi ba'a koma ba. Daga mai wanka sai mai sanya kaya, wasu kuwa da ba za su sami zuwan ba, sai suka fada kicin don yin
abin kari. Ramlat dake bacci sakamkon tana fashin sallah, dolenta ta wartsake don ba karamin takuramata su Rafee'ah suka yi ba akan ta mike ta yi wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin atamfar Holland kalar light blue da fari, ta yafa farin mayafi sannan ta
fita wurin yaranta. Ta dauka za ta gansu cikin damuwar tafiyarta sai dai da sauki musamman ga Ummi da Ansar wadanda suka shaku sosai da Hajiya. Affan ne ma ya dan yi wuri-wuri da idanu da ya tabbatar dagasken tafiyar Maminsa za ta yi. Itama dannewa kawai
ta ke amma tsananin kewarsu ta ke ji tun kan a je ko'ina. Kiran da Hajiya ta mata ne yasa ta lalla
ɓ
a Affan da ya kanainaye a jikinta ta fita. Can ƙuryar daki ta isketa. Ba ita kadai ba ce har da Umman Amrah da ta shigo tun sassafe da kuma su Baba Hajara da
sauransu. Nasiha sosai suka yi mata, Hajiya a karshe ta tofa da cewar sun gama magana. Ta yiwa Ramlat addu'a kawai. Ita kuwa banda afkin kuka ba abinda ta ke fitarwa. Iyayenta masu sonta da komai, a baya ta bijirewa saboda son zuciyarta. Nan ta bude baki
ta na mai kara neman gafararsu akan abinda ta aikata a baya. Murmushi suka yi.
"Banda abin Ramlatu, ai kowa ya fahimci kaddara. Ba komai kedai komai ya wuce sai da kawai yanzu ki maida hankali wurin biyayya ga mijinki."
Wata Gwaggonta daga Daura
ta fadi.
***
ADAMAWA...
Hajiya Zeenatu hakanan ta ji faduwar gaba, shigar da Hussein ya yi da irin fara'arsa sai ta soma wani tunani daban. Ganinsa ta ke yi kamar wani Ango. Ya kammala
ɗ
ora agogon hannunsa bayan ya idar da sallah, murmushi ya k
e tun sadda suka yi magana da Hafsat ta tabbatarmasa da isowarsu garin su ma. Dama habyar da ya biyo daban da tasu.
"Hussein."
Jin ta kira sunansa kai tsaye yasa shi dubanta.
"Duk wannan fara'ar ta mecece? Wani kyau ka yi kamar wani Ango.
Gabana faduwa ya ke yi. Yaushe za mu je ka kaini mu gaisa da danginka?"
Ya yi wani banzan murmushi ya rike kafadunta.
"Kar ki damu, kin ga yau daurin auren yar uwata ake yi, ke kuma na sanki ba kya son cunkuso da wani hayaniya, ki yi hakuri gobe
zamu shiga ku gaisa da kowa. Kallon banza aka yi maki Hussein ba zai rabu da mai shi ba. Sannan kina batun wai Ango, na dauka kodayaushe ni Ango nake a wurinki? Toh ki kwantar da hankalinki, babu macen da ta ishe ni kallo har naji ina sonta. Ke kinsan yan
da nake."
Yanayin da ya furta kalmar karshen kawai sai ta kara shan jinin jikinta, ga wayarta ta rasa ya aka yi ta fada ruwa balle ta tambayi Kawu Modibbo ko akwai wani labari, yanzun dai ta ƙi tashi Hussein kuma ya kar
ɓ
e ya ce zai siyomata wata da ka
nsa. Abinda ba ta sani ba, da gayya ya tankwa
ɓ
ar da ƙaton jug na ruwan dake saman centre table, burinsa dama ta rasa hanyar jin kowane labari.
Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ya kwantar mata da hankali, har cewa ya yi ta dauko mayafi su fita tund
a hankalinta bai kwanta ba, soyayyar Hussein da ganin tsantsar gaskiyarsa a yanzu ta rufemata ido ta yanda ba ta tuna komai da kowa, hakan yasa ta kasa hasaso wani abin musamman ma da ta ga ta fito falon Kausar na mishi batun bikin da ake yi. Hankalinta ya
kara kwanciya bayan fitar Hussein din da Kausar ta shiga budomata hotunan auren da ake yi tana kallo tana ƙara jin sanyi a ranta. Ta na kuma kara tabbatarwa zuri'arsu Hussein kyawawa ne tsantsa.
***
Bangaren Marigayi Baba Naziru wanda ya sha gyara d
a fenti daga AlHassan, nan aka kai Ramlat kafin lokacin da Hussein zai yi gininsa. A sannan yan uwanta suka hau aikin jere da ma sauran abinda duk ya kamata. A ranar daga su sai su, an kawomusu abinci da abubuwan sha.
Da daddare suna zaune ana hira,
wayarta ta yi kara, Mr.Wuff. Murmushi ta yi ta dan mike ta bar wurin zuwa can wani dakin da ta tabbatar babu kowa ciki.
"Assalamu alaikum." Ta furta a hankali.
"Waalaikumussalam. Fatan an iso lafiya?"
Ta dan lumshe ido kafin ta bude tana bi
n dakin da kallo, shima gado ne aka shimfida a dakin, don wannan karon gatan da ta samu har gado biyu aka yi mata.
"Alhamdulillah."
Shiru kamar ba wanda zai tanka can kuma ya ce.
"Kin shiryawa abinda zai biyo bayan aurenmu?"
Ta ji maga
nar banbarakwai.
"Kamar ya?"
Murmushi ya yi mai sauti.
"Za ki ha
ɗ
u da Uwargidana mana."
Ranta ya sosu matuka, kishi mai zafi na Zeenatu ya mamaye koina na zuciyarta.
"Ina ruwana da ita? Zamana da nata ba iri guda ba ne. Ko ba komai
ita ai auren soyayya aka yi kamar a cinye juna."
"Sai aka fadamaki kema ba zan iya cinyekin ba? Wai meyasa kike son koyaushe ki nunan babu soyayya tsakaninmu? Dama akwai soyayyar da ta girmi aure?"
Ta kasa ba shi amsa don har lokacin kiran Zeena
tu da uwargidansa da ya yi yana mata zafi, ta rasa rashin zuciya irinta Hussein da ya iya rayuwa da matar da ta rushe dukkan wani tubalin ginin rayuwarsa saboda son zuciyarta.
"Shiru ki ka yi?" Ya tambaya.
Ta dan turo baki kamar yana ganinta.
"Bani da abin cewa."
"Saboda kin san ba ki da gaskiya ne kawai. Na dai fadamaki, ki shiryawa hakan. Tsoro ba naki ba ne, dama na riga da nasan ke jaruma ce. Amma ban sani ba ko har a fannin kishiya."
"Wanda aka damu da shi ne ake kishinsa, tun
da ba na kishinka me zai dameni da matarka? Don haka kar ka samu damuwa, ita dai za ka yiwa wannan kashedin. Zan kwanta sai da safe."
Ta katse kiran ranta a tsananin
ɓ
ace. Me Hussein ya gani a tattare da Zeenatu har yake mata son da ba zai iya rabuwa
da ita ba wai? Ita ta rasa dalilin da yasa duk laifin da ta yi masa ba ya ganin ko
ɗ
aya. Wato har shaidamata yake ta shiryawa ha
ɗ
uwarta da ita saboda ya san ba zai yi kyau ba.
Ramlat ta yi kwafa, ta mike da zummar barin dakin sai ga saƙonsa ya shigo.
"Kashe waya ba shi zai sauya zancena ba, ba kuma zai hana na fa
ɗ
i ba. Ki shiryawa ha
ɗ
uwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya."
Ta harari wayar tana jin kamar shi din ta harara, sai kuma takaici yasa idanunta cikowa da kwalla ta
yi azamar daukesu ba ta bari sun zuba ba. Daga nan ta ja tsaki ta fice daga
ɗ
akin.
***
Washegari da safe suka gudanar da shagali irin na al'adarsu da suke kira Fansa, inda dangin Ango ke kawo kayan abin ci da sha ga dangin Amarya ba tare da sun ga
Amarya ba.
Da yammaci aka hau shirye-shiryen bu
ɗ
ar kai. Maryam Sambo (Cutie) ta fente fuskar Amarya da kwalliya wanda ya fi na ranar daurin aure. Maganar kyau ma na Ramlat ba sai an tsaya ana
ɓ
ata baki wurin fa
ɗ
a ba. Ta yi kyau iyakar kyau, ga ta na
n dai ba farar mace ba, amma Allah Ya mata baiwarSa a halittarta. Wannan karon ma Leshi ne golden cikin kayan da Hussein ya bata ta sanya an mata dinkin gown. Bilkisu dai gaba daya sai ta kara raina kanta, bakin ciki kuwa kamar ya kasheta. Ba ta taba zaton
family din da Ramlat za ta shiga su na da wannan ku
ɗ
in ba. Hatta da muhallin Ramlatun, ya ci a kalla a ƙara kalla duk kuwa da cewar tsohon gini ne sai dai ya yi tsari sosai.
Gaba daya suka fita katon rumfar da aka tanada a babban filin tsakar gidan
gadon na Marigayi Alhaji Gidado. An lullu
ɓ
e jikinta gaba daya da turmin zanin atamfa yanda ko fuskarta ba'a gani.
Nan kuma dangin su Hussein aka shiga fansar fuskar Amarya, Dada nan take da ba da Dubu
ɗ
ari na fansa, haka nan ma yan uwansu na Mubi da
Maiduguri kowa ya shiga kawo nasa. Amrah ce gwanar fa
ɗ
in nawa Amarya ta samu. Ita dai Ramlat na ƙunshe tana murmushi a ƙasan zanin don al'adar tasu ta burgeta matuka sai dai da zarar ta tuno batun ha
ɗ
uwarta da Hajiya Zeenatu da Hussein ya yi sai jikinta y
a yi sanyi sai dai kuma ta tabbatar addu'a ne maganin komai.
Hafsat a matsayinta na ƙanwar Ango ita ta mike don za
ɓ
awa Amarya suna, a karshe ta radamata suna Amal. Sunan da kafatanin dangin za su dinga kiranta da shi kenan. Bayan an kammala aka kwashesu
zuwa gida.
Da daddare ana zaune gaba daya ana hirar bankwana.
"Amal."
Suka yi dariya gaba daya jin sunan da Amrah ke kiran Ramlatun. Ita kam tasan kafin ta saba da sunan za'a jima.
Anan wata ma ke tambayar Kishiyar Ramlat.
"An c
emin tana nan amma ban ganta ba."
"Anya ta zo Adamawa? Ina ji fa a Kano za ta zauna ita." Cewar Rafee'ah.
"Ta huta. Zama da dangin miji gari daya ai sai tsautsayi."
Babu wanda bai kalli Bilkisu ba, ita kuwa sai karkade kafa ta ke don dama d
a biyu ta yi maganar tana jira a tanka. Umman Amrah ce ta hana kowa magana karshe ma aka maida hankali ga hirar bikin yanda ya yi kyau.
Koda za ta kwanta tana ganin kiran Hussein ta ƙi
ɗ
agawa don ba ƙaramin haushi ya ba ta ba. Karshe ma ta katse waya
r.
***
A bangaren Hussein sam bai samu ya fita ko'ina da Hajiya Zeenatu ba sai a washegarin bikin bayan dangin Ramlatu sun kama hanyar Kano, ya zo tare da su AlHassan, Kausar da
ɗ
iyarsa. Har