Showing 6001 words to 9000 words out of 255051 words

Chapter 3 - KARFEN KAFA complete

dariya.

"Haba tawan, ai kema kinsan ya wuce ace sai ta yi wari kya ji. Ba fa wani

abu bane."

Nan ta bata labarin Hilal, suka dinga dariya ta

ɗ

ora da fadin.

"Amma wallahi ya kwantamin, ko ba komai yana da kyau kuma da alama dangin Amarya yake. Nidai ina sonsa."

"Saboda shi son ba shi da wuya ko Ramsy?"

Ta kirata da su

nan da suke fadamata a makaranta. Ta zubamata dara-daran idanunta, kafin ta kara satar kallon Hilal wanda ga mamakinta wajen da take ya ke kallo. Murmushi ya sakarmata ta yi saurin juyar da kai numfashinta na harbawa da sauri. Amrah na lura da su, banda mu

rmushin itama ba abinda take zabgawa.

"Na yarda Ramsy kin harbu. Allah Yasa ya zamemaki alheri. Farin cikinki, shi ne nawa."

Ta

ɗ

ago ta dubeta duba na kaunar ƴan uwantaka da amincin dake tsakaninsu.

"Ameen tawan. Kina son abinda nake so, shiyasa nim

a nake ji da ke."

Suka murmusa sannan suka ci gaba da shagalinsu.

A daren bayan komawarsu gida ta shiga wanka.

"Ramsy! Tun dazu fa wani wai shi Hilal ya kira yana nemanki, yanzun ma ina tunanin shi ne."

Ai da sauri ta watsa ruwa ta ja zani

ta fito gudun kada wani a sashin Hajiyarta ya dauka. Suka dubeta suna dariya ganin kumfa a kafa

ɗ

arta ta dama da kuma ƙeyarta. Ta fisge kan waya a hannun ƴar uwarta da suka zo daga Daura, Naja'atu. Sai dai ganin fisgewar ta janyo kan wayar gaba daya daga s

aman tebur. Ta ja guntun tsaki.

"Ke Ramla, wai hala sabon kamu kika yi?". Fadin Najaatu.

Harara ta bugamata.

"Yo ke Naja sai an hwa

ɗ

i maki? Ai gahi kina gani."

Cewar Sa'adah. Itama dai daga Daura ta zo.

Ita dai Ramla gaba ta yi zuwa

ban

ɗ

aki ta bar su suna mata shaƙiyanci, ba ta kai ga abinda ta yi niyya ba, wayar ta ƙara ringing, da sauri ta fito suna mata dariya ta

ɗ

aga.

"Assalamu alaikum." Ta furta har muryar na

ɗ

an rawa. Ya amsa mata sannan ya ce.

"Haba don Allah, wallahi

ba ki ji yanda gabana ya shiga fa

ɗ

uwa ba duk a zatona halinku na mata ki ka yimin. Wato dai na dauka wrong number kika ban."

Ta dan lumshe idanu sannan ta bude tana murmushi, su Najaatu sun tsuramata ido kuwa, ganin haka ta juyamusu baya.

"Kiyi

magana ko hankalina zai kwanta don Allah."

"Ka yi hakuri, bana kusa ne."

Ta ji ya sauke numfashi.

"Alhamdulillah. Na kasa samun nutsuwa Ramlat, yanda nake jinki a raina tun daga ha

ɗ

uwarmu zuwa yanzu, jikina yana bani kece maha

ɗ

in rayuwata.

Don Allah a amshi Hilal da hannu bibbiyu. Kinji?"

Ba karamin dadi kalamansa suka yi mata ba. Tana murmushi ta amsa.

"In Sha Allah."

"Hakan na nufin?"

Ya nemi sani. Ta gyada kai kamar yana kallonta.

"Na kar

ɓ

a."

Hamdala ta ji ya

yi yana zuba godiya har ya bata dariya.

Sai kuma hira ta

ɓ

arke. Nan yake fadamata shi din cousin din Bilkisu ne. Mahaifinsa Alhaji Aminu, yaya ne ga Alhaji Tijjani mahaifin Bilkisu. Su mazaunan unguwar Goron Dutse ne. Ya hada Degree dinsa a fannin A

ccounting, yanzu haka kuma yana shirin zuwa Malaysia ha

ɗ

o Masters. Ta nutsu tana jin jawabinsa, a karshe ya dora da fadin.

"Tsakani da Allah nake sonki, kuma da aure. Ba don karatun ya zama dole ba, da sai ince a dauran auren kawai na wuce da ke Malay

sia. Toh na tabbatar kema

ɗ

alibar ce kamar ni, ko kuwa?"

Suka dan dara, har cikin ranta take jin ya kwanta mata dari bisa dari.

"Toh yanzu dai nima sai ki biyani bashin labari. Fadamin tarihinki."

Ya buƙata. Ta fayyace mishi asalinsu da kum

a matakin karatunta a yanzu.

"Nayi murna da samunki My Future, kuma ina ji a jikina kece matata da yardar Allah. Muyi fatan Allah Ya cikamana burinmu. Kafin na tafi zan iya kawomaki ziyara?"

Ta kasa cewa komai din farin ciki, sai dai kuma tana s

hakkar Yaya Munir ya ji labarin ta soma tsayawa hira da wani namiji yanzun. Don haka ta girgiza kai.

"Ka bari da kaina zan gayyaceka gidanmu. Ka ji?"

Yanda ta ƙarashe zancen a shagwa

ɓ

e ya haddasar mishi da wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ya yi

gyaran murya kafin ya samu kwarin gwuiwar amsawa.

"Shikenan My Future, ni naki ne. A koyaushe kuma a kowane mataki na rayuwa da yardar Allah. Zan jiraki, ba kuma zan gaji da nayi ta jira har sadda Allah Ya so ba."

Murmushi take dagaske. Son Hila

l na kara kewaya dukkan ilahirin jikinta. Sun shafe awanni suna hira sannan suka yi sallama. Ta kai duba ga masu yi mata

ɗ

an baki, wasu sun yi bacci yayinda wasu ke waya. Miƙewa ta yi ta maida kan wayar ta ajiye sannan ta fa

ɗ

a ban

ɗ

aki don ci gaba da uzurin

ta.

***

Kamar da wasa, sabo mai tsanani ya shiga tsakaninta da Hilal, tun tana takatsantsan kada Hajiyarsu ta gane har dai wataran ta kama ta tana waya, Hilal ya kira lokacin Hajiya na kusa da wayar ta

ɗ

aga. Kafin ta kai ga magana ta ji muryarta, ta

yi mamakin jin kalaman soyayyar da

ɗ

iyarta ke zabgawa. Karshe ta ajiye kan wayar ta leƙa

ɗ

akin, tana tabbatar da ita ce din, kawai ta ja mata kofar. Idanun Ramla ya raina fata. Washegari da safe ta shiga kicin ta iske Rafee'ah na aiki. Tana ganinta ta yi

kwafa gami da dariya.

"Kin

ɓ

allowa kanki ruwa yarinya, Hajiya ta ji ki kina waya da Hilal. Za ki yi bayani dallah-dallah."

Ta ƙaraso gami da daga kafa

ɗ

arta idanu a waje. Rafee'ah ta ture hannun tana dariya.

"Wallahi kar ki cinyeni kina kallona d

a wannan manyan idanunnaki kamar mujiya."

Tsukke fuska Ramla ta yi, ba fada take nema ba, so take ta ji abinda Hajiya ta ce.

"Don Allah Sister ki bari, me Hajiya ta ce? Za ta fadawa Abba?"

Ta

ɓ

e baki Rafee'ah ta yi tana tsamo dankali a cikin

mai da cokalin girki.

"Oho, kya dai yi bayani, dama na lura ko karatun da kika saba duk karshen sati kin wani rage saboda soyayya, ke ga Laila ko? Toh ai idan ta fadawa Yaya Muniru ya laka

ɗ

amaki duka kin huta."

Haushin Rafee'ah ne ya soma kamata

, kawai ta juya bayan ta harareta ta fice daga kicin din. A falo suka yi kici

ɓ

us da Hajiya tana taimakawa A'isha da tsifar kai tana mitar dama ita ba ta son kitso ya cika ƙanƙanta. Ganin Ramla sai ta daure fuska. Tun daga nan ta sha jinin jikinta. Ta karas

a a sanyaye ta gaidata, maimakon ta amsa ta jefamata tambaya.

"Da wa kike waya haka karfe taran dare?"

Kirjinta na dukan tara-tara dakyar ta samu abin fada.

"Wani ne."

"Shi wanin bai da suna?"

Ta girgiza kai, kafin ta amsa mata, Abba

ya yi sallama ya shigo, cikin Ramla ya bada wani sauti ƙululu. Ta san Hajiya ta fi Abba rashin fahimta sosai sai dai tana da saukin kai lokuta da dama, shi kuwa Abba akwai tsauri akan hukunci wasu lokutan. Idan ya ce a'a, zai yi wuya ya dawo ya ce eh. Wann

an tasa ta tsoraci ya kwace wayarta ya kuma rabata da Hilal har abada.

Bayan an gaidashi, ya shiga yiwa Hajiya fa

ɗ

an tsifa da safiyar Allah ko karyawa ba'ayi ba. Ta ba da hakuri sannan A'isha ta mike ta rufe kan ita kuwa ta fice wanko hannu.

"Zo na

n Ramla, meke faruwa ne ke da Uwartaki?"

Ta mike ta ƙaraso ta zaune gefe sai dai ta kasa magana.

"Jiya ta sanarmin ta kama ki kina waya wuraren tara na dare. Fadamin, wanene shi? Kuma a ina yake?"

Da mamakin sauƙin kan da Abba ya nunamata ta

sunkuyar da kai. Tiryan-tiryan ta shiga labartawa Abba wanene Hilal da kuma da niyyar da yake sonta.

Ɗ

an hade gira Abba ya yi.

"To shi haka ake neman aure? Meyasa ba zai soma yimin zancen ba? Sannan duka-duka a Ss1 kike yanzu Ramla. Kina zaton zan iya a

urar dake yanzu? Ko kuwa kina ganin ya dace a cireki a makaranta ki yi aure yanzu ba tare da kin kammala ba? Inada burin naga kun yi karatu koda a gidajen mazajenku ne. Amma ban ce lallai ba, kuma a sanin da nayi maki kema kina da wannan ra'ayin. Me zai sa

ki sauya?"

Ta

ɗ

ago kai sai a sannan ta kalli Abba idanunta rau rau kamar wacce aka ce kar ta ƙara shiga harkar Hilal.

"Abba dama ya ce yana son zuwa wajenka, ni ce ke tsoro. Kuma na fadamasa ni ba yanzu zan yi aure ba sai na kammala Sakandire."

Murmushin manya Abban ya yi, ya lura dai diyartasa da alama soyayya ta sauyata.

"Kin tabbata kina sonsa Ramlatu?"

Daga yanda ya kira sunan ta tabbatar ba wasa. Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya kara maimaita wa, ta gyada kai. Ya kara maimai

tawa a karo na uku, sai kuma ta tsinci kirjinta da bugu da sauri-sauri. Ta ji wani gumi da ba ta san dalilinsa ba ya ketomata a goshi. Wani yanayi na sanyin jiki ya mamayeta. Ta daure ta yakice nauyin da bakinta ya yi a lokacin ta amsa da "Eh Abba." Sai ta

ga ya yi murmushi har haƙoransa suka bayyana.

"Shikenan, ki ce ina son ganinsa gobe."

Da toh ta amsa sannan ta mike ta yi daki tana jin muryar Rafee'ah dake jera kwanuka saman ledar cin abinci na mata dariya. Jikin kofar dakinnasu ta jingina, wa

su hawaye ta shiga fitarwa da ba ta san asalinsu ba. Damuwa ce ko akasinsa? Murna ce ko bakin ciki? Babu daya da kwakwalwarta ta bu

ɗ

amata. Wayar ta nufa ta kirashi, ya kuwa dauka ta sanar mishi abinda Abba ya ce sannan ta ajiye wayar ta koma falon. Ana cin

abincin amma jikinta a sanyaye yake, abin mamaki sai sannan ta ga sakin fuskar Hajiyar, ba ta san dalilin fushinta a farko ba. Amma ta san dalilin sakin fuskar yanzu na murnar

hukuncin Abban ne don har Rafee'ah na tsokanarta bayan fitar Abba akan za ta yi

kewarmu. Tana fadin Autarhttps://my.w.tt/ub8deMQ0g9



🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

03)

"A farko nayi tsammanin irin samarin zamanin nan ne masu hurewa ƴanmata kunne da zantukan

banza da dare. Sai kuma da naji ko waye, naga ashe na gida ne. Toh Allah Ya tabbatarmana da alheri."

Hajiya ke koro wannan bayanin sa'ilin da Ramla ke gyaramata gado ita kuwa tana gaban madubi tana goge jiki ta fito daga wanka. Murmushi Ramla ta yi t

a kara maida kai ga aikinta.

"Allah kuwa Hajiya ba ruwansa. Kuma fa yace zan karasa karatuna."

Abin ya sanya Hajiya dariya.

"Ai shikenan ƴar nema, Allah Ya sanya alheri."

Ta amsa a zuci tana dariyar itama.

Hilal ya zo suka yi mag

ana da Abba, sosai yaron ya shiga ransa. Karshe ya ba shi iznin zuwa hira sai dai ya ce ya kasance jifa-jifa saboda

ɗ

aliba ce. Ya kara da mishi iznin turo magabata a tsaida ranar biki. Wannan magana ta fi kowacce yiwa Hilal dadi. Ya dinga godiya. Karshe su

ka dan ta

ɓ

a hira da Abba cikin barkwanci, koda zai wuce Abba ya hanashi akan lallai ya tsaya ya ci abinci. A kunyace ya ƙaraso cikin falon.

Tana zaune tare da Rafee'ah a falo, sai ganinsa suka yi. A guje ta mike ta nufi daki don sanya hijabi, ita kuwa Ra

fee'ah me za ta yi banda dariya.

Ya zauna suka gaisa tana fadin.

"Masha Allah Angon ƙanwata. Allah Ya sanya alheri."

Cike da jin dadin wannan maganar ta Rafee'ah ya amsa yana shafa keyarsa. Abba ya shigo tare da Hajiya sanye da mayafi. Cikin gi

rmamawa Hilal ya kwashi gaisuwa sannan suka dunguma saman ledar da tuni Rafee'ah ta ha

ɗ

a komai na abincin dare. Abba ya shiga wulga idanu.

"Ina ita Ramlar? Auta kiramin ita maza."

A'isha ta mike da sauri ta nufi hanyar dakinsu. Daidai nan Yaya Munir

ya yi sallama, a bayansa Amaryarsa Bilkisu. Hangame baki Yaya Munir ya yi ganin Hilal, shi kuwa sunkuyar da kai ya kara yana dariya ƙasa-ƙasa. Bai mancewa gidansa ya soma zuwa suna ƙusƙus da yar uwarsa Bilkisu game da zuwa ganin Abba. Koda ya tambayi wane

Abban, sai ya bagarar yana fadin idan ta yi wari zai sanarmishi. Wannan ta sanya Munir kallon Bilkisu, ta yi mishi dariya cike da kunya ganin idon surukan a kansu. Ya dauke kai bai ce komai ba suka ƙarasa. A wurin cin abincin yake jin abinda ke wakana tsa

kanin kannennasa. Murmushi kawai ya yi gami da fatan alheri. Ajiyar zuciya Ramlat ta yi don ba haka ta zata ba.

"Kin ci sa'ar Yaya Munir, da alama dai giyar soyayya ke kwasarsa. Ba ki ga yanda yake nan nan da Anti Bilkin ba. Amarya ba ta laifi."

Zantukan

Rafee'ah ya sanyata dariya. Hararar da Yaya Munir ya watsomusu tamkar ya ji abinda suke tattaunawa shi ya sanyasu nutsuwar dole. Bayan tashin iyayen, Yaya Munir ya dubi Hilal.

"Kai wato abin ƴar rufa-rufa ce ko? To gashinan ai ya fito fili. Allah Ya

sanya alkhairi." Hilal ya murmusa yana satar kallon masoyiyartasa.

"Ameen Yayanmu."

Dariya Anti Bilkisu ta yi gami da riƙe ha

ɓ

a.

"Oh ni, yau Mami ta zo ta ga autanta a gidan surukai."

Ya

ɗ

an harareta don koda ta girmeshi da ka

ɗ

an, shi har

yau bai ma yarda ta girmeshi din ba.

"Toh ke wa ya sanyamaki ido wai? Kuma ai ta san da zancen. Ni yanzu dai gaskiya a bani aron my wife to-be mu

ɗ

an yi hira."

Ai Ramla ji ta yi kamar ta nutse. Ta kasa cewa komai, bayan sun ke

ɓ

e da Hilal ya zuba

mata idanu kamar ya hadiyeta. Kunya ta kamata ta sanya tafukan hannunta ta rufe fuskar.

"Wai me? Kunya ko? Na ci alwashin kawar da shi wataran. Ko ince nan ba da jimawa ba da yardar Allah. Yau fa ina cikin farin ciki."

Ta sauke hannun tana murmushi.

Ya nuna ta da yatsa.

"Ko ba ki fa

ɗ

a ba nasan kema hakan ne."

"Yaushe ne tafiyarka?"

Ta sauya akalar zancen.

"Nan da sati biyu in Sha Allah. Zan fa yi kewa. Kinga da kin kammala zan iya tafiya da ke kawai."

"Gwara da ban kammala b

a kenan."

Ya

ɗ

an fiddo ido.

"Au bakya kaunar ki bi ni? Kin fi so muyi nesa da juna kenan."

Girgiza kai ta yi.

Sun

ɗ

an jima suna hira sannan suka yi sallama ya wuce don dama ya yi sallama da mutan gidan.

***

"Kin tsaida Hilal mat

sayin mijin aurenki. Kar na ji ko kuma na ga kin tsaya da wani saurayin koda wasa. Duk wanda ya nuna yana sonki, ki ce an miki miji. Sannan banda yawan waya, muddin naga kin rage maida hankali a karatu da kaina ba saƙo ba zan amshe wayar har sai kin zana S

SCE. Kin ji ko?"

Kirjinta ke wani irin bugu, ta

ɗ

ago ta dubi Yaya Munir, fuskarnan tamkar bai ta

ɓ

a dariya ba. Daga ita sai shi a hanyar barandar fita daga cikin gidan, kici

ɓ

us suka yi yayinda yake shirin fita. Ta gya

ɗ

a kai.

"Magana za ki yi da b

akinki."

"Naji Yaya, zan kiyaye in Sha Allah."

Sai sannan ta ga murmushinsa har abin ya bata mamaki.

"Shikenan." Abinda ya furta kenan ya yi gaba, ta bi bayansa da kallo kafin ta soma tafiya zuwa falon jikinta a sanyaye. Tana shiga nan ma B

ilkisu da Rafee'ah suka yi mata ca da tsokana, nan take Rafee'ah ta kira Zulaihat ta fesa mata. Abin ya mata dadi itama sosai ta kuma yi musu fatan alheri.

***

Sati daya da wannan zancen, aka kawo kudin sa rana da karamin akwati daga gidan su Hilal.

An sanya shekaru biyu da wata uku wanda ya yi daidai da sadda za ta kammala sakandire. Amrah a gidansu ta wuni ranar suna murna. Sai dai jikin wacce ake tayawar a sanyaye.

"Wai ke mene duk kin yi wani sanyi kamar ba ke ba?"

Fadin Amrah. Ta yi saurin

riƙo hannun Amrah din ta

ɗ

ora saman kirjinta.

"Kin ji yanda yake bugu, bansan dalili ba. Tun soma maganar aurena da Hilal gabana ke fa

ɗ

uwa, ki tayani addu'a Amrah."

Murmushi Amrah ta yi.

"Kar ki wani damu wallahi, kawai dai baƙon al'amari n

e kike ji saboda zancen auren. Kinsan kowace mace dole ta ji sauyi idan aurenta ya taho, ko kin manta Anti Zulaihat da kika ce ita har kuka tayi ranar sanya ranarta?"

Ta gya

ɗ

a kai tana jin wani sanyin dadi, hakane fa. Ta yi murmushin samun nutsuwa ka

ɗ

an.

Misalin hudu da mintuna na yamma ta sanya mayafin abayarta, fitowa ta yi da zummar takawa Amrah ta hau tasi. Ba tare da sanin kaddarar da ke bibiye da fitowar ta a daidai wannan lokacin ba.

Suka miƙa suka fito daga lungun gidan zuwa babban titi

, hirarsu suke sha har da dariya.

Wannan fitar ita ce Mafarin komai. Ita ce silar soma shigarta cikin dukkan matsalolin da take fuskanta a yanzu.

***

Buga ƙofar

ɗ

akin da ake yi ba kakkautawa ya katse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login