Showing 183001 words to 186000 words out of 255051 words

Chapter 62 - KARFEN KAFA complete

abinda ke ranka."

Ya dubi Hisham.

"Me kake nufi? Kuma wa kake nufi?"

Hisham ya bude baki zai magana ya

ɗ

aga mishi hannu.

"Malam bana son shirme, yimin shiru. Kai a komai sai ka sanya wasa da zolaya. To ka fita idona."

Dariya sosai ya ba Hisham. Daidai

sadda AlHassan ya dawo ya dubesu yana dariya.

"Lafiya dai? Tom and Jerry?"

Murmushi kawai Hussein ya yi.

"Dada ce?" Ya tambaya. Gyada kai AlHassan ya yi yana murmushin shima.

"Yes, ita ce. Sai dai ban fadamata komai ba, na dai ce ina t

afe da wani babban albishir."

Jinjina kai Hussein ya yi.

"When? Nima na ƙagu na gan ta."

"Very soon in sha Allah."

"Maiduguri fa?"

Cewar Hussein kamar zai yi kuka.

Dariya AlHassan ya yi.

"Duk za mu je da yardar Allah. Saboda

rashinka na

ɗ

auke ƙafa, ganina yana sa Hajjo kukan tunawa da kai. Wannan ta sa tsakaninmu sai waya."

"Ina son hukunta ta." Hussein ya fadi zuciyarsa na zafi, fuskar Hajiya Zeenatu ya ke haskowa da kuma cu

ɗ

anya iri-iri da ya yi tare da ita.

"Muje

daga waje please. Nan ba wurin tattauna wannan zancen ba ne."

Suka dubi Hisham mai magana, su ka maida hankali ga Halima da ta yi musu ƙuri da kumburarrun idanunta. Duk hirar da ake yi tana ji, kalaman Hussein na ƙarshe ya sa tsoro ya ƙara kamata. Ka

da dai ita yake nufin a hukunta? Ita kam ta shiga uku. Ba ta mance shawarar da kaninta ya ba ta ba da ya zo.

"Idan kinsan ba da gaske kike ba Yaya Halima, ki fito ki fadi gaskiya kafin lokaci ya ƙuremaki. Nidai gaskiya ban yarda da abinda kika fa

ɗ

amin

ba."

Ta share hawaye tana ci gaba da kokwanto a ƙasan ranta. Ta fa

ɗ

a ko kuma ta yi shiru? Ita kanta ta rasa wanne za ta za

ɓ

a. Har suka fice tana kallonsu. Ta bi wurin kwananta da kallo, ta ja majina. Anya Hajiya Zeenatu dagaske ta ke za ta cire ta a

wannan taskun? Shiru ta yi, karshe ta yanke shawara ta aika ƙaninta wurin Hajiya Zeenatu ya yi mata bayanin halin da take ciki.

***

Ramlat ta yi shiru, ita kadai a dakin, su Rafee'ah sun wuce, sai Hajiya dake bandaki

ɗ

auro alwalar sallar Azahar.

Nos Khadija ta kwankwasa ta shigo tana jan kayan dressing din ciwo a

ɗ

an keke. Suka yiwa juna murmushi. Ɗan zaman da ta yi a asibitin sun saba, mace ce mai kirki.

"Su kuma wa

ɗ

annan ƴan sandan da aka zubamana a bakin ƙofa fa? Da alama dai Angonnaki

na baki kulawar da ta dace."

Wannan ne karon farko da ta ji haushin Nos Khadija, sam ba ta son abinda za'a ha

ɗ

a ta da Chairman. Tun kafin su Munir su tafi, suka zoda zummar tsareta bisa umarnin ubangidansu. Har ta soma fa

ɗ

a Munir ya ce ta rabu da shi

kawai. Shi ya sani. Ta

ɓ

e baki ta yi ba ta ce komai ba. Daidai sadda Hajiya ta fito, suka gaisa da Nos Khadija gami da yin ƴar raha don mace ce mai tsokana da kuma ja da wasa. Tana cire Bandage din kafadar suna ta hira abinsu, bayan ta goge ta ƙara rufewa

sannan ya dubi Ramlat jin Hajiya na fa

ɗ

an ba ta son cin abinci.

"Ki dinga cin abinci don Allah Ramlat, haba yar uwa, ina yabonki? Ki ci yanda idan na ba ki magani ba zai sanyaki jiri ba. Yanzu zan dawo."

Ta gyada kai ba don ta so ba, ita kawai ko

mai ma ba dadi ya ke mata.

***

Hajiya Zeenatu tunda ta doshi barandar

ɗ

akin da Ramlatu ta ke ta hangi wasu masu kayan ma'aikata tsaye a bakin ƙofar ta yi turus. Wuƙar da ke cikin jakarta yasa ta kasa ƙarasawa, juyawa ta yi tana tunanin ina mafita?

Ta ya za ta cimma burinta? Yanzun ta tabbatar Hussein ba zai kara yi mata kallon mace mai daraja da ƙima ba a idanunsa, amma tabbas idan ta bar Ramlat na yawo a doron ƙasa tofa shakka babu, wataran za ta ji batun aurensu. Abinda ba za ta ta

ɓ

a

ɗ

auka ba har

abada. A kan idanunta, Nos Khadija ta shiga, hakanan a kan idanunta ta fito. Wata dabara ta fa

ɗ

omata don haka koda Nos Khadija ta zo wucewa ta wurinta ta saki fuska sosai suka gaisa.

"Nace don Allah idan babu damuwa, ina son ganinki."

Nos Khadij

a ta bita da kallo, a shekaru ta girme mata sosai hakanan kuma ba ta yi mata kama da wacce ta fito daga ƙaramin gida ba.

"Shikenan, ba ni minti biyu."

Hajiya Zeenatu na murmushi ta gyada kai. Ba jimawa Khadija ta dawo suka

ɗ

an fita waje.

S

hiru Khadija ta yi tana jin bayanan Hajiya Zeenatu. Kirjinta ya shiga dukan uku-uku.

"Ki sani, wallahi-wallahi duk wani jin dadi na rayuwa kin sameshi kin gama matukar kika yimin aikin da na sanyaki. Zan ba ki duniya iyakar ƙarfina. Za ki taka duk ƙ

asar da kike so, za kuma ki shiga duk inda kike so a fa

ɗ

in garinnan ba wanda ya isa ya ce maki don me?"

Jikin Khadija ya

ɗ

auki wani irin rawa. Tunda take a duniya, tunda ta ke, ba ta ta

ɓ

a jin lamari irin haka ba. Wani irin tsoron da ba za ta iya mis

altawa ba ya shige ta. Daga yanayinta Hajiya Zeenatu ta gane babu nasara don haka ta bude jaka ta fiddo bandiran kudi ƴan dari biyar guda biyu ta miƙamata, Allah Ya taimaka babu jama'a a wurin, ta

ɗ

ago mata lafiyayyar wuƙa sabuwa fil ta nunamata.

"Ki

za

ɓ

i

ɗ

aya Hajiya Khadija, idan ba haka ba ni da kike gani don na kasheki ba komai ba ne a wurina. Sai na

ɓ

atar da ke da ma ƴan gidanku. Don haka za

ɓ

i ya rage naki, na baki nan da awanni biyu, duk abinda kika yanke ki kira ki sanarmin. Kar ki manta rayuwar

ki a tafin hannuna yake."

'Ƙarya kike, Allah ne Mai iko da rayuwakanmu.' Nos Khadija ta fadi a fili don ba ta jin tana da kwarin gwuiwar fa

ɗ

a a zahiri. Ta gyada kai kawai a fili, ta kar

ɓ

i kudin ba don ta so ba ta zura a aljihun wandonta.

"Ina ts

umayenki. Ga lambar wayata." Hajiya Zeenatu ta fadi karo na biyu tana miƙamata karamin complimentary card mai dauke da numbobin wayoyinta a jiki. Nan ma Khadija gyada kai ta yi.

"Je ki." Ta ba ta umarni, ta juya da sauri ta shige ciki har tana cin kar

o da wata mai tsohon ciki.

"Yi hakuri don Allah." Matar ta bita da kallo kawai gami da jan tsaki irin na masifaffun masu ciki. Haka ta wuce ta a mita.

Koda ta karasa dakin Nurses, ba ta tarar da kowa ba don haka da sauri ta ciro kudaden hannu na

rawa ta cusa a jaka ta zuge zif. Bandaki ta shige ta soma watsawa fuskarta ruwa tana salati a ƙasan ranta. Yau da wane rashin sa'a ta fito daga gida? Kawai sai ta shiga hawaye, nutsastsiyar fuskar Ramlatu da kuma na Hajiya mai cike da dattako da kamala t

ake tunawa. Ta ya ya? Ta wace hanyar za ta iya kashe wannan baiwar Allahn? Duk da dai idan ta so abu ne mafi sauki a aikinta, za ta iya kasheta irin kisar da zai yi wuya kafin a gane ita ce silarsa. Amma ina! Ba'a ba ta wannan tarbiyyar ba kuma ita ba ha

ɗ

a

mammiya ba ce akan abin duniya. Ka

ɗ

an ma da ta ke samu ya wadatar da ita.

Sai da aka kwankwasa ƙofar sannan ta fito. Karo suka yi da Nos Jamila. Ta bita da kallo.

"Dije, lafiya?"

Murmushin yaƙe ta yi ta hau murza idanu.

"Ba komai, abu

ne ya fa

ɗ

a idanuna."

"Aa Dije, fa

ɗ

amin gaskiya."

Girgiza kai ta yi, ba za ta iya ba, tana tsoron abinda zai sanadin rayuwarta.

"Ko haihuwar ki ka kar

ɓ

a, don nasan halinki na tausayi."

Dariya ta ba ta.

"Oh na tuna, ashe fa ba dut

y naki bane yau." Cewar Nos Jamila karo na biyu.

Ita dai Khadija ta sulale ta fice daga

ɗ

akin. Maganin ma kasa komawa ta ba Ramlat ta yi sai wata ta aika.

***

Hussein da AlHassan zaune a falon gidan Hisham suna cin lafiyayyen girkin Aisha. G

ogan ci yake kamar an mishi dole.

"Wai Hussein lafiya? Ko kaima jinyar kake taya Ramlat?"

AlHassan ya fadi yana murmushi don tuni ya

ɗ

ago shi.

"Mene ha

ɗ

ina da ita? Kawai dai na damu da harbin ne, na kuma rasa waye zai yi ƙarya da ni ya ha

rbe ta. Shiyasa na kasa fahimtar mai laifin, me ya sani tsakanina da ita da ya za

ɓ

i hanyar kasheta ta amfani da ni."

"Da mamaki kam, amma ko ma mene in sha Allah nan ba da jimawa ba zai bayyana. Har wanda ake

ɓ

oyemana."

Hisham ya furta yana kash

e mishi io

ɗ

aya, AlHassan ya yi kamar bai gansu ba ya ci gaba da kai loma yana murmushi. A yau jinsa yake kamar a duniyar gajimare tsabar murnar ganinsa zaune tare da

ɗ

an uwansa.

Hussein din ma banda harara bai cewa Hisham uffan ba, saboda gudun zar

gin sai ya saki jiki ya ci abinci. Bayan sun kammala ya mike.

"Ina zuwa?"

Fadin AlHassan don ba ya son ya ji Hussein din ya matsa daga gareshi. Murmushi Hussein ya yi.

"Gidan Hajiya Zeenatu."

"Aa, bai kamata ka je kai ka

ɗ

ai ba. Muje tar

e."

Jinjina kai Hussein ya yi cikin amincewa da zancen dan uwannasa. Suka

ɗ

unguma suka fita, Hisham ya takamusu har ƙofa kafin ya dawo ciki. Kusan shima yau dai jinsa yake sak. Babu sauran damuwa.

***

RAMIN ƘARYA....

I just p

ublished "BABI NA HAMSIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/S2N0l9OdWcb

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

50)

Tun daga farfajiyar gidan ma'aikata suka dinga al'ajabin gani

n ƴan biyunnan. Har dai Malam Bala mai guga ya ka sa hakuri.

"Yalla

ɓ

ai ashe ku ƴan biyu ne."

Hussein suka dubi juna da AlHassan, kauna ta jini na ƴan uwantaka na ƙara ratsa zuƙatansu, banda kaddara me zai raba su? Su da suka rayu tare a mahaifa

guda.

"Eh Malam Bala, we are twins."

Fadin Hussein wanda ya ƙarashe da kallon su John. Nan suka shiga washe hakora suna gaida AlHassan da fadin abinda ya bambantasu, hakan ya ba ƴan biyun matasan dariya. Hussein ya yi ciki yana murmushi, ya bar

su da AlHassan. Yasan matar gidan ba ta nan kamar yanda ya ji daga masu gadin, don haka ya shiga bin ko'ina na falon da kallo. Tafkeken hotonsu shi da ita ya ƙurawa idanu kamar wani fulanin daji da bai san hoto ba.

"Ita ce. Makira."

AlHassan ya

fadi a hankali, sai sannan Hussein ya juyo da rinannun idanunsa ya dubeshi.

"Idan na ce maka ban san ta ya ya na aureta na za ka yarda? Idan na ce maka ba da son raina..."

"Ba fa sai ka fa

ɗ

i komai ba

ɗ

an uwa, na maka farin sani na kuma san kala

r macen da ka ke so. Ko ka mance cewa ka ban labarin ha

ɗ

uwarku da tayin kaunar da ta yi maka? Ban san dalilin da yasa na kasa tunawa da hakan ba, ban kuma san dalilin da yasa na amince ka bar mu ne saboda ka auri wacce ka ke so. Amma ban ta

ɓ

a kawo wa ita c

e ba nasan dai babbar mace ce kamar yanda ka fa

ɗ

i."

Sauke ajiyar zuciya Hussein ya yi gami da jinjina kai. Falon suka koma suka zauna. Nan kuma AlHassan ya shiga ba shi labarin abubuwan da suka faru a bayansa. Rasuwar Baba Naziru mijin Dada da kuma ra

suwar ƴar uwar kakarsu da ta riƙe su kamar jikokinta da yaran cikinta suka haifamata ba su Dada ba.

"Allah Yay musu rahma. Yasa aljanna makoma. Baba Naziru ya rasu da bakin cikina."

Girgiza kai AlHassan ya yi.

"Kar ka ce haka. Wallahi har y

a rasu kewar ka ya ke, ya kuma fa

ɗ

a ya ƙara, ba halinka ba ne."

Hussein ya jinjina kai.

"Yaushe za ku tafi?"

AlHassan ya tambaya.

"A satinnan. Ina neman alfarma a wurinka, koda kun ha

ɗ

u da ita kar ka nuna mata komai kamar yanda nima ba

zan nuna ba."

Hussein ya fa

ɗ

i idanunsa cikin na

ɗ

an uwan. Da mamaki AlHassannya tambaya.

"Dalili?"

Hussein ya yi mishi bayanin duk abinda ya ke buƙatar yi, a farko AlHassan ya ji abin kamar babu amfani, a karshe kuma sai ya hau murmushi sos

ai.

"Good, hakan shi ne daidai."

Abinda ya ce kenan bayan gama sauraro. Hussein ya

ɗ

an ciji le

ɓɓ

ansa gami da shafa sumar kai.

Daga farfajiyar gidan kuwa, Hajiya Zeenatu ce ta shigo ta yi parking ta fito. Ta sauke ajiyar zuciya ganin motar

Hussein. Ta shirya tunkurarsa, ta shirya fuskantar kowane irin ƙalubale. Ita din mace ce, kissa ba komai bane. Murmushi ta dan yi tana mai jin ƙwarin gwuiwa da haka ta shiga gidan.

***

Yusufa ya zaro ido yana duban Halima da ke faman zuba zance.

"Yaya Halima anya kina da imani? Yanzu saboda kudi ki ka yarda ki aikata duka wannan? Yaya Halima ba ki yi tunanin rana irin wannan za ta zo ba? Ke fa talaka ce, ba ki da makaman yaƙi, su kuwa masu ku

ɗ

i ne, kinsan ba za su kamu ba. Meyasa kullum shi tal

aka kwadayi ke kai shi ya baro? Anya kuwa kin yiwa kanki adalci? Kin mana adalci? Ɗan abinda kike samu na albashi bai wadace ki ba?"

Yanda Yusufa ke hawaye haka itama ta ke sheshshekar kuka.

"Na cuci kaina, ban san cewa ni din mahaukaciya ce ba

dai yanzu Yusuf. Nidai don Allah ka taimaka ka je ka sami Hajiya ka yi mata bayanin komai, nasan ba za ta rasa hanyar da za ta fitar da ni ba musamman idan ta ji ina barazanar tonamusu asiri."

Ya share fuskarsa, shiru ya yi don babu alamar zai je din

. Halima ta dinga yi mishi magiya da roƙo har tana durƙusawa. Ɗan uwa daban ya ke, nan da nan ya ji zuciyarsa ta karye, ya daukar mata alƙawarin a yau zai je ya sami Hajiya Zeenatu tunda washegari ne shiga kotu. Ta ba shi kwatancen gidanta har ma da na A&Z

, daga bisani suka rabu akan duk yanda ake ciki zai dawo ya sanarmata.

***

Ramlat ta yi shiru tana tunani bayan tafiyar abokan aikinta wadanda takanas suka zo dubiya. Can dai ta kasa hakuri ya dubu Hajiya dake zaune saman darduma tana shan kankana.

"Nikam Hajiya ya ake ciki batun mayar da kudi? Su Kawu sun ƙara magana?"

Hajiya ta yi murmushi.

"Ina fa Ramlatu, Hajja ta ce na bar komai a hannunta. Yanzu dama abinda ake ciki, ina so ke ki bada katin ATM dinki na damƙawa Yayanki ya je ya ci

ro ya kawomin. Da kaina zan je na same su na damƙamusu ku

ɗ

a

ɗ

en idan ya so ko a yaransu ne su nemi

ɗ

aya su aurawa Dikkon. Ke dai ki kwantar da hankalinki kawai. Kuma kada jin hakan yasa ki dauka na goyi bayan ki yi ta zama a gabana ne babu aure, sam, ba zai

yiwu ba. Shima wannan din halayyarsa ce ba ta yimin ba kema kin sani. Don haka ki yi kokarin fitar da mijin aure. Ko Baba Dakta ai kin ji me ya ce."

Murmushi ta yi mai kama da yaƙe gami da gya

ɗ

a kai. Hajiya ba ta san me ke damunta ba, ba kuma auren n

e ba ta so ba. Kawai dai ba wanda ta ke jin kaunarsa a ranta irin Hussein. Bayan Aliyunta, shi ne namijin da ta yi amannar za ta iya rayuwa da shi a kowane yanayi. Sosai yanzun tana jin saukin hannun don ita kam da ace za'a ba ta sallama a ranar za ta so h

akan. Sallamar da aka yi yasa duk suka dubi ƙofar gami da amsawa. Nos Khadija ce, ta ƙaraso ciki.

"Ke kuwa

ɗ

iyata daga cewa bari ki ke ki dawo na ji shiru sai wata na gani a madadinki."

Murmushin yaƙe Khadija ta yi. Ta rasa ma me za ta ce, tuno z

antukan Hajiya Zeenatu ka

ɗ

ai yakan ka

ɗ

a hanjin cikinta balle idan ta ci karo da salihan bayin Allahn nan da ba su yi kama da mugaye ba. Ita kuwa in za ta iya aikata wannan

ɗ

anyen aikin? Ai koda babu ƴan sanda tsaye a bakin ƙofar ba za ta iya ba.

"Ayi

hakuri Hajiyarmu,

ɗ

azun sallah na tsaya yi bayan na idar kuma wani aikin ya

ɗ

aukemin hankali. Sannu Ramlat, ya jikin?"

Da murmushi itama Ramlat ta amsa.

"Alhamdulillah. Jiki ya yi sauki."

Ta jinjina kai.

"Dama zuwa na yi na muku sallama

sai kuma Allah Ya kaimu. Zan wuce gida."

Suka yi mata godiya sosai sannan ta juya ta fice idanunta cike taf da kwalla. Ba ta tunanin har a ba su sallama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login