Showing 165001 words to 168000 words out of 255051 words
Falo ne mai girma ya sha ado. Ta zauna a saman
ɗ
aya daga cikin hadaddun kujerun da aka zuba. Rasheeda ta gaidata ta amsa fuska a sake sannan ta je ta kawomata ruwa da lemun zo
ɓ
o.
"Na gode." Cewar Ramlat sadda ta dauki ledar ruwan ta sha ka
ɗ
an ta ajiye ragowa. Amarya ta shigo ta zauna. A ladabce Ramlat ta gaidata ta amsa fuska a sake.
"Sai dai kamar ban shaida fuskar ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Eh gaskiya ba ki san ni ba Anti. Sunana Ramlat Khalid Mu'azzam. Kusan sanadin AlHa
ssan Aminu Mamman dake Adamawa na san gidannan. Kwanakin baya ma sun zo biki nan suka biya ta gidanmu."
Kawai sai ta ga Rasheeda ta sa dariya haka Amarya.
"Ke ce Mamin Fatima ko? Mai za
ɓ
amata takalmi? Ya bamu labari."
Da wani irin salama na
jin dadin kalaman Rasheeda itama ta yi dariyar kadan.
"Ni ce, ai kema ina ganinki na shaidaki don ina yawan ganin hotonki a status din Hafsat."
Jin haka Amarya sai ta samu nutsuwa sosai da Ramlat, dama tun farko ba ta yi mata kalar mace marar ka
mun kai ba. Nan aka kara gaisawa da tambayar su Hajiya wanda ba karamin mamaki ya ba Ramlat ba. A karshe Ramlat ta gangaro kan abinda ya kawo ta.
"Ina neman izni ne, ina son ganin Kawu Modibbo."
Jin haka Anti Amarya ta amsa cikin kwarin gwuiwa.
"Wannan ba matsala ba ce Ramlat. Bari na yi miki iso, ina zuwa."
Hakan ya faranta ran Ramlat, ta dauka ganinnasa zai mata wuya ko kuma wani ko wata zai nemi sanin dalilinta na son ganinsa, sai dai akasin hakan ce ta faru. Ko ba komai ta gaskata k
irki na Amarya, wanda ya sha bamban da na Hajja Fatuma kamar yanda ta
ɗ
an ji ka
ɗ
an cikin labarin matannasa a bakin Hafsat. Yarinyar akwai hira idan ta so.
Jim ka
ɗ
an sai ga Amarya ta dawo, yanayin sanyin jikinta sai ya sa Ramlat shan jinin jikinta ita
ma. Amarya ta daure tana murmushi mai kama da yaƙe.
"Za ki iya jira har bayan Magriba kuwa? Ina gudun kar ki dare."
Nan ta gano matsalar, don haka ta saki fuska.
"Lah ba komai Anti, Allah Ya kaimu."
Amarya ta yi murna da hakan, ta kunna
mata kallo ta ba ta remote koda za ta sauya tasha daga nan ita kuma ta koma bakin aiki kasancewar girkinta ne. Ba jimawa da kunna kallon aka dauke wuta, nan take jin Amarya na ba Rasheeda labarin wai Hajja Fatuma ce ta ce tunda ba lokacinta ba ne sai ta yi
hakuri da duk wani baƙonta da ke son ganin Modibbo, idan na ta lokacin ya shigo ta yi duk irin damun da ta so yiwa furarta.
Murmushi Ramlat ta yi na yaƙe, ta dai lura akwai takun saƙa tsakanin matan gida. Waya ta fiddo ta kira Hajiya ta fadamata.
"Anya kya zaunar musu har Magriba? Ba kya dawo ba ki hakura zuwa gobe?"
Girgiza kai Ramlat ta yi.
"Hajiya lokaci zai ƙuremin idan ya kai gobe, mu dai yi hakuri tunda kinga biyar da rabi ma ta wuce, kamar yanzu ne za'a kira sallar in sha Allah."
"Ai shikenan, Allah Ya kaimu anjima. Sai kin dawo."
Ta amsa da amin suka yi sallama. Ba ta kai ga ajiye wayar ba, kiran AlHassan ya shigo. Suka gaisa.
"Dole ta tsayar da ni a Gombe sakamakon lalacewar abin hawa. Na so kwarai na shigo yau, a
mma gobe da sassafe in sha Allahu zan taso."
Hakan ya dan yiwa Ramlat dadi, ko ba komai lamuran zasu tafi yanda ta so.
"Ayya ba komai, Allah Yasa hakan ya zama alheri."
"Amin, sai dai kin ƙi sanar da ni komai game da abinda na nema."
S
auke ajiyar zuciya ta yi.
"Ka yi hakuri, idan ka shigo har wanda zai ba ka mamaki duk zan fa
ɗ
amaka kuma zan kaika ka ganewa idonka in sha Allahu."
Ya dan yi shiru, shirun da yasa Hussein fa
ɗ
omata a rai, shi ya saba yi mata hakan. Kewar Hussein so
sai ta ke ji ta kuma kudurce ko bai mata magana ba ita kam yau za ta ta
ɓ
oshi ta whatsapp.
"Shikenan. Allah Ya jisshemu alheri."
Ta amsa da amin cike da tausayinsa. Dan uwan da Allah kadai yasan tun sadda ya ke bulayin neman
ɗ
an uwansa. Ta ji ida
nunta sun cika da kwalla daidai sadda suka yi sallama. Ta shiga whatsapp ta aikawa Hussein saƙo, ta jima tana kallon profile dinsa wanda bai dora komai ba a idanunta tana wassafo hotonsa, karshe ta sauka.
Ba jimawa aka shiga kiraye-kirayen sallah, Rashe
edat ta jagorance ta zuwa
ɗ
akinta. Alwala ta
ɗ
aura ta tayar da sallah saman dardumar da ta iske an shimfidamata.
Ta jima tana addu'ar nasara akan lamarin Hussein, shi kansa ta yi mishi addu'a kwarai kafin ta shafa ta miƙe.
Abinci aka zubomata, dole
nta ta ci tana kallon tsarin yaran Amarya gwanin sha'awa. An idar da sallah ana kuma neman haddar karatun da aka biya na Islamiyya. Can kuma sai ga Amaryar ta fito sharr kamar sabuwa, ta shirya cikin riga da siket na leshi ta cakare abinta tsaf. Da fara'ar
ta ta dubi Ramlat.
"Yi hakuri fa Ramlatu, bari idan na shiga zan miki magana sai ki zo."
"Toh Anti. Kin yi kyau tubarakAllah."
Hakan da ta fada ya ba su dariya har yaran. Amarya ta yi godiya ta wuce
ɓ
angaren Mijinta. Sosai abin ya ƙayatar da
Ramlat.
***
Taimakon gaggawa likitocin suka shiga ba Hussein har Allah Yasa ya dawo hayyacinsa. Hajiya Zeenatu ta rasa sukuni, banda safa da marwa babu abinda ta ke yi a harabar bakin kofar dakin da Hussein ke kwance. Can
ɗ
aya daga cikin likitoci
n ya fito, da hanzari har mayafin na sulalewa ta ƙarasa.
"Dakta ya farfado?"
Daktan ya yi murmushi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Alhamdulillah Hajiya,
ɗ
anki ya farfa
ɗ
o, ki kwantar da hankalinki."
Ta tamke fuska.
"Mijina ne."
Mamaki karara a fuskar likitan kafin kuma ya ha
ɗ
iye don ba abinda ya shafeshi ba ne.
"Ok, idan ba damuwa ki biyo ni zuwa ofis."
Daga haka ya yi gaba.
"Matsalar Hussein damuwa ce da ta haddasa masa ciwon kai mai tsanani. Sai jininsa da y
a hau, sai kin kula sosai da cimarsa har ma da walwalarsa domin irin ciwonsa na bukatar kulawa kuma ba ya son yawan tunani."
Hajiya Zeenat ta yi shiru a ranta tana jin takaicin Hussein da zai sa damuwar wani abu bayan ita ce duniyarsa.
"Kin ji
abinda na ce?"
Tambayar ta katse tunaninta. Ajiyar zuciya ta saki.
"Naji kuma zan kiyaye. Yanzu ina iya ganinsa?"
Likita na ƙaremata kallo ya gyada kai.
"Eh Hajjaju."
Ta mike tana watsa masa kallo mai kama da harara, ba shiri ya ja
nye idanunsa tunda ya san shi ya jaza wa kansa da ya bita da kallon kurilla. Ba kuma don sha'awa ba, sai don ya ga abinda ya kwa
ɗ
aitar da mara lafiyarsu da ta kira da Hussein har ya ji ita ya ke da muradin zama abokiyar rayuwarsa.
"Su ta shafa." Ya
ƙ
arƙare tunanin ta hanyar furta hakan a fili.
Hajiya Zeenatu ta shiga
ɗ
akin da Hussein yake, wannan karon babu kowa sai shi
ɗ
aya. Idanunsa a lumshe, a farko ta yi zaton bacci ya ke, sai dai rufe ƙofar da ta yi yasa shi kallonta. Ta sakarmasa murmus
hi tana mai ƙarasowa ta zauna gefen gadon ta kama hannunsa.
"Sannu Hussein, ya jikin?"
Gyadamata kai kawai ya yi ya kara kauda kansa.
"Ba zan kwana a nan ba, su sallame mu."
Yanda ya yi zancen ka san iyakar gaskiyar kenan ba wasa.
Cikin rarrashi ta shigo kokarin fahimtar da shi kuskuren hakan, sai dai yanda ta kafe haka ya kafe har abin ya tsorata ta. Aikuwa dai karshe sai sallamar aka ba su da lodin mgunguna bayan an ƙara jaddada masa akan ya kula sosai da jikinsa.
Su na ko
mawa gida ma'aikatan suka tarbeshi tare da yi mishi sannu.
"Dalla Malamai ku matsa! Ba kwa ganin yanayin jikinsa ne?"
Hussein ya dubi Hajiya Zeenat, a fuskarsa ta gane bai ji dadin abinda ta yi ba. Ya tsaya ya amsa gaisuwarsu ita kuwa ta yi ga
ba tana tsaki. Godiya ya yi musu san nan ya shige ya bar su da gulmarta.
Sallar Magriba ya soma yi san nan ya shiga wanka. Yana fitowa ya kimtsa, Hajiya Zeenatu kuwa tana ƙasa ta na bada umarnin abinda za'a girkawa mijinnata.
Ya dauki wayarsa,
ya ga missedcalls din Hisham sai kuma na wani abokin aikinsa. Data ya kunna ya leƙa whatsapp. Shiru ya yi ya ƙurawa sunanta idanu yana kallon saƙon da ta aiko ba tare da ya bu
ɗ
e ba, ya hangi dai sallama da gaisuwa, sauran ne bai da masaniya. A hankali aka
zare wayar daga hannunsa. Hajiya Zeenatu ce, gabansa ya fa
ɗ
i.
"Haba Yalla
ɓ
ai, yaushe ma ka farfa
ɗ
o da za ka
ɗ
auki waya? Ba dai ka manta sharu
ɗɗ
an Dakta ba?"
Ta ƙarashe tana duban wayar, tuni ta shiga key, shima yanda ta ke kallo haka ya ke kall
a, ganin ta rufe ya sanya shi sauke ajiyar zuciya. Gaba daya ta kashe wayar tana mai duban soyayy duk a kokarinta na gudun kar ya sauya shawarar da ta kawomasa a
ɗ
azun.
"Wayar a hakura a bar ta zuwa gobe. Yanzu mu je ƙasa ka jira abinci sai ka sha m
agani."
Ta fa
ɗ
i gami da riƙe hannunsa. Ya ciji le
ɓɓ
ansa, haka nan ya ji bai kyauta ba bisa rashin ba da amsa ga Ramlat sai dai maganganun Hisham na fa
ɗ
omasa a rai sai ya yi gaggawar fidda tunanin.
***
Mintuna kusan goma sha biyar sai ga kiran
Amarya a wayar Rasheedat.
"Muje na yi miki rakiya."
Haka kawai Ramlat ta ji fa
ɗ
uwar gaba, ta amsa da toh tana mai ha
ɗ
iyar yawu mai
ɗ
aci.
Da sallamarta ta sa ƙafa a falon. Dattijo cikin shigar kamala, kana ganinsa ka ga cikakken bafulatani.
Tundata shigo yake yiwa fuskarta kallon tsanaki don son tantance ko akwai inda ya santa ko kuwa yau ne farkon ganinsa da ita. Ta karasa ta gaishe shi, Amarya tuni ta mike zuwa
ɗ
aki. Hakan kan faru, idan har Modibbo nada baƙo, sukan ba shi wuri ya gana da
ita.
"Baiwar Allah daga ina?"
Ya tambaya cikin hausarsa da har sannan ba ta ginu kamar ta Bahaushe ba.
Ta hadiyi miyau gami da ambaton Allah. Ta gabatar da kanta sannan ta
ɗ
ora bayan ya shaidamata eh ya san Malam Abdullahi kakanta kuma
ɗ
an unguwar da yake, Yakasai.
"Kawu dama magana ce da ta danganci Hussein, dan uwan AlHassan da ake nema."
Shiru-shiru, ba ta ji ya ce uffan ba don haka ta
ɗ
ago kai. Yanayin dake shimfi
ɗ
e a fuskarsa ya tsorata ta, ya kuma ka
ɗ
a hanjin cikinta.
"Kina da labarinsa? Ke wace ce?"
Wannan ne tambayoyin da ta samu da suka ƙara cilla ta a kogin tunani da mamaki.
I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/gqyFr6qwCcb
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
45)
ALLURA TA TONO GARMA...
"Kurma ki ka koma?"
Ta dawo hayyacinta ta kalle shi gami da girgiza kai. To me za ta ce bayan ta gabatarm
asa da kanta?
"Ina garga
ɗ
inki da ki cire kanki a abinda bai shafeki ba. Idan kina son tsira da lafiyar kwakwalwa da na gangar jikinki ki fita hanyar Hussein da Zeenatu."
Da wani irin razana ta dubeshi, wannan ƴar fara'ar dama tun soma labarin ya
kauda ita a saman fuskarsa sai ya zama kamar wani Mugyambo a idanunta. Kwallar da ta cika kurmin idanun suka soma sharara.
"Ka...ka..san Hussein yana nan? Ban ambaci Zeenatu ba, ka san..."
"Ke Bingel! (Yarinya). Ke wacece da za ki tuhume ni? In
a gargadinki karo na biyu kuma na ƙarshe ki tashi ki binne maganarnan a nan wurin da kike zaune. Idan ba ki ƙi ji ba, ba kya ƙi gani ba. Duk abinda ya faru gareki sanadin fasa wannan zancen, ki yi kuka da kanki!"
Ramlat kirjinta na bugu, hawayenta na
kwaranya, kwakwalwar ta tsaya cak ta bar aiki. Ta kasa ha
ɗ
a kowane lissafi, jin ta take yi kamar ba'a duniyar mutane ba. Kamar wata duniyar ta daban ta ke ciki mai tsananin ru
ɗ
ani da azaba. Kallonsa ta ƙara yi, girman tuni ya zube ƙasa warwas! Kallo ne kam
ar wacce ke zaune gaban sa'anta.
"Ka na da hannu a komai? Ka na a
ɓ
atar da Hussein daga zuri'arku? Me ya yi maka haka da zafi?"
"Kina ƙara dulmiyar da kanki cikin tafkin nadama da da na sani, kalaman da kike yi za su rushe duk wani farin ciki na
rayuwarki. Ki kama kanki! Ki tashi ki bar min gida tun kina da sauran lafiyar aikata hakan!"
Miƙewa ta yi a sanyaye, har za ta fice ta juyo ta dubeshi yana faman muzurai. Dattijon da bai kama daraja da girmansa ba, babu amfanin ganin ƙimarsa.
"
Kawu ka sani, Allah na bayan masu gaskiya. Ƙarya fure ta ke ba ta ƴaƴa."
Daga nan ta banka
ɗ
a labule ta fice, ba ta jin za ta iya jiran yin sallama da Amarya. Babu inda ta ƙara shiga a gidan haka ta fice tana hawaye.
Tafiya ta ke ƙafafun na ha
rhar
ɗ
ewa, kalaman Kawu daki-daki ta ke tunawa tana ƙarin fahimtar dagaske dai akwai hannunsa a cikin
ɓ
atan Hussein.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ta ambata a fili, tausayi sosai da wata irin ƙauna ta Hussein ya ƙara mamaye zuciyarta. J
i ta ke komai za ta iya aikatawa muddin hakan zai dawo da Hussein cikin ƴan uwansa. Wayarta ta yi ƙara, Hajiya ce. Yanda ta ke kuka ba ta jin za ta iya amsawa, don haka ta mayar da wayar jaka. Kafin ta bar lungun sai da ta tsaya ta saita kanta ta share fus
ka. Abin hawa ta tsayar ta fa
ɗ
a.
"Malama ba ki fa
ɗ
i inda zan kai ki ba."
Ta ha
ɗ
iyi miyau. Dakyar ta fa
ɗ
i sunan unguwar ta yi shiru, kanta ke sarawa ga wani zazza
ɓ
i-zazza
ɓ
i.
***
Tsam! Modibbo ya miƙe ya shiga
ɗ
aki, Amarya na zaune na kallon
wani ƙaramin bidiyo na Ibro tana dariya, ganin mutum ya fa
ɗ
o ba sallama ya sa ta
ɗ
an razana kafin ta sauke ajiyar zuciya. Tun kafin ta nemi ba'asi ya katsemata hanzari.
"Fita zan yi, ki je kawai idan na dawo zan kiraki. Akwai uzurin da zan gabatar.
"
Ya fa
ɗ
i a kausashe, ta miƙe jikinta a sanyaye ta fita fuskar cike taf da tarin tambayoyin da babu mai amsa mata sai Ramlatu. Sai dai sama ko ƙasa babu ita, hatta su Rasheeda sun yi mamakin da ba ta biyo ta musu sallama ba.
Fitar Amarya ya ba K
awu Modibbo damar bu
ɗ
e sif
ɗ
insa ta kaya, can ƙasan ya zura hannu ya
ɗ
auko wani
ɗ
an akwati mai girma da duk fa
ɗ
in gidan babu wanda ya isa ya ta
ɓ
a. Hankalin ma bai kai gareshi ba. Cikin rigarsa ya zaro mukullin da ba ya rabo da shi a jikinsa, ya bu
ɗ
e, kwakw
alwa ce! Kwakwalwa ta ƊAN ADAM! Ta yi baƙiƙirin a madadin jan da ta ke da shi har da jini-jini a shekaru masu yawa. Idanun Kawu Modibbo suka ka
ɗ
a.
"Ita ce! Ita ce yarinyar!"
Abinda ya fa
ɗ
i kenan a fili kafin hannu na rawa ya maida ya rufe. Gumi
ya shiga tsastsafowa daga fatar jikinsa. Ya sa hannu ya share. Tun komai bai ƙarasa lalacewa ba zai yiwa abin tufka. Ya ayyana hakan a ransa yana jin tsanar Hussein tsagwaronsa a fili da
ɓ
oye. Miƙewa ya yi ya dauki waya ya danna kira direbansa.
"Kana
ina?"
Daga can aka ba shi amsa kafin ya dora.
"Ka fiddo mota, fita zamu yi."
Daga nan a gaggauce ya dauki hula ya rufe kansa ya fita yana zuba sauri.
***
Ramlat bakinta ya yi mata nauyi, ta kasa ba Hajiya labarin abinda ya f
aru. Damuwar da ke kwance samam fuskarta yasa Hajiya ta fahimci ba lafiya. Ganin ta shige daki sai ta mara mata baya.
"Ke mene ne wai? Shi Kawun ne ba ki samu gani ba ko wani abin ne ya faru da Husseinin?"
Girgiza kai ta yi. Tunanin ta fa
ɗ
a
ɗ
in
ya rinjayi komai, ko ba komai Hussein na bukatar addu'a, don haka ta karya bille ta labartamata duk yanda suka yi da Kawun. Hajiya ta saki salati.
"Ni Rabi wannan rayuwa da ban mamaki. Ban ta
ɓ
a jin labari makamancin haka ba tunda uwata ta haifeni. Kai
.."
Hajiya sai ta soma hawaye, ita kanta tausayin Hussein ke
ɗ
awainiya da ita. Hatta da abokin haihuwartasa ma tausayinsa take ji. Miƙewa ta yi tana jan hanci.
"Addu'a zamu dage da yi, ke kanki yanzu ki dage da addu'a